Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

(Innocent Girl) ANEESERH Book 1 Complete Hausa Novel Document by (Innocent Girl) ANEESERH Book 1


(Innocent Girl)  ANEESERH Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28983



(Innocent Girl) ANEESERH Book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 23, Jun 2024

Author: Nanameera ,The Nainarh KD ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08081129487, 0908 603 0007

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 157.09 kb

File Type: txt

Views: 980+

Download: 620+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ✨✨```ANEESERH```✨✨







*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*





*بسم الله الرحمن الرحيم*




*Ep. One.*







Shigowa suka yi ganin yadda aka taru yasa ta ce.

"Dan Allah menene yake faruwa ne?."



Kallonta guard ɗin ya yi yayi gaba abin sa, suna shiga compound ɗin gidan ƙara waro idanu tayi ganin jama'ar har sunfi na waje yawa har suka ƙaraso gabansa wani mutumine wanda aƙalla zaikai 65yrs ɗin ta kalleshi bakinta narawa ta ce.

"Your Excellency ko bakai bane ba president of Nijeriya ba."

Kamo hannunta ya yi ya ce, "Ni ne Aneeserh."


Da mamaki ta ce "A'ina kasan sunana please and Menene waɗannan mutanen suke yi a gidan mu?."


Kallon ta ya yi cike da tausayawa ya ce. "Aneeserh kinsan duk abin da ya faru da mutum Allah ya riga da ya rubutashi a cikin littafinsa, kuma ba'a gujewa ƙaddara saboda haka inason kizama mai ɗaukan ƙaddarar data zomiki mai kyau ko akasin haka."



Shiru tayi dan ita batasan ma'anar waɗannan maganganun dayake ba kamar antsikareta ta ce.

"Yawwa bari naje nagasu Abba suncemin yau zasu dawo."

Gaba tayi dan shiga gidan tana zuwa entrance ɗin parlour'n su taga anjere mutane har uku akwance kowanne ansaka masa likkafani anrufe kamar gawa. Jikinta ne yahau rawa saboda Allah ya zuba mata tsoro tayi cikin gidan da gudu tana cewa.

"Abba!! Ummi!! Yaya!!."

Kowa na gidan kuka yake domin duk rashin imaninka sai kaji tausayinta.








Haka ta gama bincike gidan amma bataga familynta ba hakan yasa ta fito lokacin His Excellency yazo ƙofar entrance ɗin tana fitowa ya riƙeta cikin rawar baki ta ce.

"Ka sakeni waje zanje naduba naga su Yaya Farooq basu dawoba kuma sunce idan nadawo daga makaranta zanga sun dawo."

Hawayen fuskarsa ya goge sannan ya ce "Kinga Abbanki da umminki can akwance an rufesu."



Buɗe dara daran idanunta ta yi, sai kuma ta tafi kan gawwakin ta tsuguna a hankali kuma ta buɗe likkafanin ɗaya daga cikin su, wata ƙara ta saki cikin tashin hankali take faɗin.


"Abba! Abba!! ka tashi, menene ya sameka Abba ka daina wannan wasan kaji bana so."





Kowa na wurin kuka yake, ta ƙara buɗe ɗayar gawar inda tayi arba da Umminta sosai jikin ta yayi weak dan ganin abun take kamar mafarki cikin mutuwar zuciya dakuma rauni ta sake buɗe ɗayar, jikinta banda rawa babu abin da yake yi take faɗin.

"Yaya Farooq! Ummi!! Abba ku tashi please ku daina irin wannan wasan please banaso zan mutu, kutashi kunji..."


His Excellency ne ya ƙari so wajen ta, ya ɗago ta yana faɗin.



"Ki nutsu Aneeserh kinji."



Riƙe shi tayi gam bakinta na rawa ta ce.




"Your Excellency please kacewa Abba na ya tashi kaji kacewa Yaya Farooq su daina wannan wasan Ummi ta tashi wayyo Allah."


Ganin yadda ta rikice yasa ya rungumeta jikin sa yana shafa kanta yake faɗin.



"Aneeserh kiyi haƙuri kinji amma Abbanki, Umminki, your brother Farooq sun rigamu gidan gaskiya kiyi haƙuri kiyi musu Addu'a kawai kinji..."





Jin kusan two minutes amma babu respons yasa ya ɗagota kafin yayi magana ya ganta aƙasa jikake timm, cikin tashin hankali ya tsuguna kanta ya ɗa go ta, da aka kira guards dan kaita Asibitin.





****


Har ranar bakwai batasan waye akan taba, suna uku kawai take kira wato "Abbanta, Umminta, sai kuma Yaya Farooq ɗinta."



Yau ma kamar kullum Your Excellency ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya sameta ta rufe idanunta amma ba barci take yi ba, zama ya yi gefenta ya taɓa ta yana kiran Sunan ta.





"Aneeserh!!"


A firgice ta buɗe idanunta ta ce da shi.


"Ummina."



Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ce.


"Ba ita bace."



Shiru tayi masa kusan five minutes sannan ya kuma cewa.



"Ya kamata ki daina wannan tunane tunanen Aneeserh kisani duk wanda ya mutu baya dawowa kiyi haƙuri, ki koma cikin mutane ki dawo rayuwarki kamar da, ki dinga yi musu Addu'a a duk lokacin da kikayi sallah kinji?."





Kallon sa take amma kana ganinta kasan ba fahimtar abin da yake faɗa take yi ba, girgiza kai ya yi yana tuna sanda sukai sallama da iyayenta bayan sun taho ne aka kira aka ce sunyi hatsari kuma babu wanda ya yi rai a cikin su...





*FOUR MONTHS AGO*


Fitowarta kenan daga ɗakinta ya kalleta ya ce.



"Ke Aneeserh kiyi sauri idan ba haka ba wallahi zanyi tafiya ta na barki."



Turo baki tayi tana ƙunƙuni ya kalleta ya ce.




"Kee!! Ni kike yiwa tsaki ?."




Shiru tayi masa ya ƙara cewa, "Ba magana nake miki ba?."




Daidai nan wani Babban mutum ya fito wanda aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan sai kuma wata mata a bayansa wacce kamarsu ɗaya da Aneeserh fara ce tass kana ganinta kaga asalin bafulatana.






Ƙara sawa suka yi, ai kuwa ta fashe da kuka ta tafi wajensa ta ce.



"Abba kaga Yaya Farooq ko?."



Rungume ta ya yi ya ce "Farooq menene kayi ma ta?"



Murmushi Farooq ya yi ya ce, "Ai Abba kasan halinta kawai dan nace tayi sauri taje nayi dropping nata tunda driver'n ta bayanan, shi ne take wannan kukan."



Shafa kanta Abba ya yi ya ce.



"Shikenan ya isa rabu dashi kinji ƴar albarka kiyi tafiyarki school kinji?."


Goge hawayenta ta yi ta ce ''Abba zaka kaini shopping idan na dawo?."


Dariya ya yi ya ce "In sha Allah amma kiyi karatu da kyau."



Murmushi tayi ta ce "In sha Allah, Ummi ina abincina?."



"Yana kitchen.'


Ummin ta bata amsa.

Kitchen ta tafi ta ɗauko sannan ta dawo kallonta Ummi tayi ta ce.


"Aneeserh zo nan."




Zuwan tayi ta ce "gani Ummi."


Hijab ɗin ta ta gyara ma ta sannan ta ce

"Naga randa zakiyi hankali Aneeserh.."



Kwaɓe fuska ta yi Abba ya ce "Maza ki tafi makaranta banda wasa kinji baby na."




Murmushi tayi ya miƙa ma ta tafin hannunsa ita ma ta sanya nata akai ya ce.

''Promise " gyaɗa kai tayi ta ce "sure'' sannan tayi waje da gudu.



Kallon Farooq ya yi ya ce "Please Farooq kayi tuƙi a nutse banda gudu katafi a hankali sannan ka tabbata ta shiga makaranta sannan ka dawo.


Girgiza kai yayi ya ce "In sha Allah Abba zan kula da rigimamiyyarka."



Dariya suka yi duka sannan ya yi waje yana cewa "sai mundawo"


"Allah ya kiyaye." suka amsa masa sannan yayi waje.










Zashiga motar bayan sunbar layinsu ta kalleshi ta ce.



"Yayaaa"
Murmushi ya yi idanunsa akan titi ya ce "Na'am ƙanwaaa"
Kyalkyalewa tayi da dariya shima yana tayata saida suka yi mai isarsu sannan ta ce.


"Daman Yaya ka iya irin abuna?."



Yana shan kwana ya ce " har ma nafiki iyawa, ni lokacin danayi tawa shagwaɓar ai tafi taki " ganin mai yalo ta yi ta taɓoshi ta ce da ƙarfi " yayaaaa " birki ya ja ya tsaya yana kallonta dan ya ɗauka wani abun ne ya sameta ta kalleshi ta ce.


"Yaya kasi yamin yalo please."

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce. "Lallai ma Aneeserh bakida hankali to wallahi duk randa kika sake yimin wannan rashin hankalin saina miki dukan tsiya."

Yana gama faɗin hakan ya ja motar suka cigaba da tafiya, ganin bai siyamata ba yasa ta fashe da kuka yana jinta har suka isa makarantar tasu sannan ya kalleta ya ce.

"Sauka kona mareki."
Goge idanunta ta yi ta ce.
"To kabani kuɗin makaranta mana."
Da mamaki ya ce.
"Dama ni nake baki kuɗin makaranta?."
Turo baki ta yi ta ce. "Ni sai ka ƙaramin."


Girgiza kai ya yi sannan ya ɗauko ɗari biyar ya miƙa mata ya ce. "Ƙarɓi ki sauka malama."
Kallon kuɗin tayi sai kuma ta ɗauke kai ta ce.
"Ni ɗari biyu zaka bani wannan yayi min yawa."
Maidawa ya yi ya ɗakko mata ɗari biyun sannan ta ɗauki jakarta da lunchbox ɗinta ta sauka tashiga makaranta, saida yaga tashiga sannan ya girgiza kai ya ce.
"Aneeserh rigima Allah ya shiryeki."






Tana shiga class ɗin nasu kasancewar private school ce yasa su goma ne ƴan ajin nasu biyar maza biyar mata zama tayi kusada seatmate ɗinta mai suna Asma'u amma suna cemata Ma'u murmushi Ma'u tayi ta ce.

"Yau kuma waya taɓaki naganki rai ahaɗe?" harararta ta yi ta ce "ina ruwanki dani naga yayana nane yaƙi saimin yalo" murmushi Ma'u ta yi ta ce. "Yau shi ne ya kawo ki ke nan?, ina driver'n naki?."


Shiru tayi ma ta ta ɗauko littafinta saboda malami daya shigo musu..






Wajejen ƙarfe biyar da rabi aka tashi daga makarantar kasancewar anan suke islamiyya, kusan mintuna goma da tashi amma ba'azo ɗaukanta ba tayi tagumi tana tunanin abinda ya hana azo a ɗauketa ta ji ya ce " ƙanwata " tajisa sarai amma sai tayi kamar bata jiba tayi shuru ko motsi batayi ba murmushi ya yi dan yasan tanajinsa batayi auneba taji ya ɗauketa gabaɗayanta ai kuwa suka hau kokawa sai ta kwace ƙarfin namiji da mace ba ɗayaba yasa ta haƙura, bayan ya sayanta a motar sun bar harabar makarantar ya kalleta ya ce " Sorry kinji Aneeserh wallahi nayi busy ne shiyasa banzo na ɗaukeki ba amma karki faɗawa Abba kinji " ɗaga kai tayi ta ce " chaɓ
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download (Innocent Girl) ANEESERH Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album