Join Our WhatsApp Group

GIMBIYA HAKIMA Complete Hausa Novel Document by GIMBIYA HAKIMA


GIMBIYA HAKIMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 75000



GIMBIYA HAKIMA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 11, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Manazarta Writers Association

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 443.68 kb

File Type: txt

Views: 560+

Download: 350+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```







01&02







"Ranki ya dade, gimbiya Hakima, Fulani tayi aike, tace tana son magana dake, "Lantana aje ace mata yau bani san yin magana da kowa....




"Maryamu, yau gimbiya Hakima tace bata son yin magana da kowa,"wai Allah kice yau an tabo jaraba a cikin gidan nan? "Aiko dai, "Lantana! Lantana!! Lantana, "na bani Maryamu, gimbiya na kirana, ni yau na shiga ukku, yau buguna ne Kawai baza tayi ba...



"Allah ya kara maki lafiya, rain Gimbiya ya dade, ina neman sausaci rain Gimbiya ya dade, "Lantana, mai kika tsaya yi waje ina ta kiranki kin gyaleni?

"Ina neman afuwarki ya uwargijiyata, "yi man shiru ba wanann na tambaye ki, "nace uban me kika tsaya yi a waje? "Eh naje nakai sakonki ne, "wani sako? "Na baki san yin magana da kowa yau..


"Shine kika yi ma wannan uwar tsayuwar, ke Bilki, "Naam Allah ya da rainki ya dade gambiya,"wuce maza ki kiran man Sarkin bulala, yanzun nan, "to Gimbiya, "dan Allah Gimbiya ki man rai, ki duba tsufa na, kiyi hakuri, kuskurene nayi ina neman afuwa..



Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana cewa, "yi man shiru tsohuwar banza, tsohuwar wofi, ke har wani tsufa ne dake da za'a kalla aji tausayinki, to ni *GIMBIYA HAKIMA,* bani tausan Yaro balle tsoho...



Suna cikin wannan yanayi sai ga Sarkin bulala yazo, "Ran Gimbiya ya dade, gani na ansa kiranki, yake uwar Marayun masarautar kano...



"Sarkin bulala, ina son yanzun kayi ma Lantana bulala hamsin, indan ta sosa ta zube, ko kuma tayi kuka, itama ta zube, bayan ka gama, ka kai ta gida Maza, tayi sati biyu, ana yi mata horo mai tsanani....



"Angama uwargijiyata, Yanzun ko zani zartar da hukuncin da kika bani, nan Sarkin bulala ya fara zane Lantana, ko dogon tausayi babu a idonshi, sai da yayi ma Lantana tsinanan bugu, sannan aka dauke ta zuwa gidan Maza...



"Allah ya taimekike, "Maryamu, lafiya naga kin shigo haka, hankalinki tashe? "Allah ya taimakeki, Allah ya kara maki nisan kwana, da man Gimbiya Hakima ce tasa ake yi ma Lantana hukunci...



"Subuhanalillah, mai tayi mata? "Da man dan ta dade, da ta ce aso ace man nace maki yau bata son yin magana da kowa, shine tace ta dade, ta barta tana ta magana...



"Allah sarki, je ki kira man sarkin gida, "to Ranki ya dade, nan Maryamu ta wuce jiki na rawa ta taho da sarkin gida..



"An gaisheki, Amaryar sarki, daga ke ba kari, " Sarkin gida, kai dai baka rabuwa da zolaya, kaje kace ma Hakima nace ta soke wannan hukuncin da tasa ayi ma Lantana, in ba haka ranta zai mumunan baci, kuma kace tasan tayi maza tazo kiran da nayi mata...



"To Ranki ya dade, nan Sarkin gida ya tafi, yana zullumin yanda zai hadu da Gimbiya Hakima, dan ya san lamarin ta ba mai sauki bane...




Nan Sarkin gida yana zuwa, ya aika ayi mashi neman iso,"Gimbiya Sarkin gida, yana son ganin ki, "Bilki kice mashi na ya san ida dare yayi mashi kafin raina ya baci...



"Allah ya taimaki Sarkin gida, Gimbiya tace yau bata son yin magana da kowa, "kije kice mata Fulani ta aiko ni, "Gimbiya yace sakone daga wajen Fulani, "kije kice ya shigo, ya jira ni gani nan zuwa....



Sai da Sarkin gida yayi awa daya zaune, yana jiran fitowar Gimbiya Hakima, amman shiru kake ji, ba bu alamunta..



"Bilkisu, dan Allah kije kice ma Gimbiya Hakima ina jiranta, "to sarkin gida, "gafara dai ran Gimbiya Hakima ya dade, nan Bilkisu tana shiga ta tadda Gimbiya Hakima tana chatting hankalinta kwace, "Ke lafiya kika yi man tsaya? "Allah ya huce zuciyarki yar sarki jikar sarki, da man sarkin gida yace yana jiranki, "je kice mashi ina zuwa, "to Gimbiya, sarkin gida tace tana zuwa...



Tafiya take cikin takama da jin kaika, tana tafiya tana harbin iska, tana busa hanci, "takawarki lafiya yar'masu gida, "yauwa sannunka Sarkin gida, lafiya kake nema, sai kace biyan bashi?



"Allah ya huci zuciyar Gimbiya da man Fulani ta bani sako, "wani kallar sako ne? Bana ce yau baniyin magana da kowa ba? "Allah ya huci zuciyarki, "naji mai tace maka? ka cika ni da surutun banza marar anfani, "da man tace ki maza ki soke hukuncin da kika yanke ma Lantana, tun ranku keda ita bai baci ba....



"Je kace mata naji, amman sai gobe zani sa a fiddo ta"godiya muke Gimbiya Hakima ikon Allah, nan gani nan bari, kinyi ma makiya nisa, "da kata sarkin gida, kana iya ta fiya dan ka matsa man da shirmainka



Nan sarkin gida ya tashi, jiki duk a sanyaye, yana mamakin yanda Gimbiya take gaya masu magana san yaranta, ko dan ta ganta ita yar sarki ce...



Ai a haife na haifi kamar Hakima sau ukku, amman dan ina karkashinta take zagina, baki daya bata biyo halin iyayenta ba, Allah dai ya shirya...



"Allah ya taimaki Fulani, "sarkin gida, ya kuka yi da ita? "Eh tace zata saketa amman sai gobe, kuma tana kan bakarta na yau bata son yin magana da kowa...



"Hmmm shikenan, sarkin gida, Allah ya shirya mana zuri'a, ka haifi da' baka haifi halinshi ba...



Nan dai Fulani ta kama fada tana mamakin halin diyar tata, ta rasa inda ta gado wannan bakin halin na wulakanta tallaka, tana mamakin yanda Hakima bata son tallakawa ko daya...




A rayuwa kenna, haka dai fulani ta gama sannan ta wuce shashen Yakumbo.....





"Ranki ya dade Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Fulani, tana neman iso, "kuje kuce mata ta shigo,nan Gimbiya Fulani ta shigo ita da kuyunganta suna take mata baya...


"Sannu da hutawa Yaya, "yauwa sannu da zuwa Fulani, naji ance Hakima ta yanke ma baiwarta hukuncin sati biyu a gidan maza, "Hmmm hakane yaya, amman yanzun tace gobe zata sa a fiddo ta..



"Gaskiya Fulani, Hakima tana bukatar gyara, ban san ina ta samu wannan halin ba..


"Hmm wallahi nima Yaya wannan halin na Hakima yana da muna ban san ya zanyi da ita ba, kai haifi d'a baka haifi halinshi ba...



"To kuma naji ance tace yau bata san yin magana da kowa! "Eh hakane ai yanzun shashenta zan wuce dan ya zama dole ta tsaya ta saurare ni, tun kafin maimartaba yaji abunda tayi a yau..



"Gaskiya ya dace ai, "to ni na wuce Yaya...

"Nan Gimbiya Fulani ta tafi sheshen Gimbiya Hakima dan sunyi magana da ita..



"Ran ki ya dade ga mai girma Gimbiya Fulani a hanya, "to naji wace ki ban waje..

"Nan Bilkisu ta fita jiki duk a sanyaye, tana cewa haka dai zasu hakuri da uwargijiyar tasu..


"Fulani sannu da zuwa.

"Yauwa Hakima, ai ke keda sannu tunda kin nuna ban isa da ke ba, to ni gani na taso da kaina..


"Fulani zan fiddo Lantana gobe dan har umarni na bada na fiddo ta a gobe..


"Ni ba wannan ya kawo ni ba, inkin fiddo ta kanki inma baki fiddo ta ba shima kanki, tunda kinfi kowa anfana da Lantana..


"Nazo ne nayi maki bayanin addimission dinku a fito, dan haka Maimartaba yace ki fara shiri ko wani lokaci kina iya ta fiya makaranta..


"Haba Fulani, taya za'ayi Baffah yayi man haka?


"Yanzun kamar ni HAKIMA ace a rasa inda zani university sai a Nigeria, Nigeriar ma wai wata A. B. U. Zaria, salon tallkawa su rai nani su dauka matsayin mu daya dasu Fulani..


"Ke wacece inda mutun ba kamar su? Wai Hakima maiyasa baki san tallakawa? Basan ina kika dauki wannan mugun halin ba, shi tallaka ba mutun bane?


"Ke ba kowa bace face Gimbiya Hakima, daga nan baki wuce komai ba, kuma ya zamai maki dole kije karatu kasar zauzau, ni naji dadi da Maimartaba yace baki fita kasar waje..


"Ya zama dole ki koyi huda da tallakawa , dan baku da banbanci a wajen Allah nidai ina gaya maki gaskiya Hakima..


"Amman gaskiya Fulani ni bani zama hostel, "wanna kuma, ni na wuce, "to a huta lafiya..



Haka Fulani ta baro Gimbiya cikin bakin ciki da bacin rai dan Gimbiya tasa Maimartaba wasa yake da yace bai fidda data kasar waje karatu..


"Kash ni Hakima wai maiyasa Maimartaba yake san yana hadani da tallakawa, bayan ni ya san na tsani tallaka amman yanzun wai a rasa school din da ni *GIMBIYA HAKIMA* zani sai wai *ABU ZARIA* , amman shikenan..


Haka dai Gimbiya Hakima ta kama yan maganganun ta..



"Bilkisu!

"Naam Allah yaja da ran uwargijiyata, gani ina jiran umirninki na aiwatar..


Sai da Bilkisu tayi kusan minti goma tsugune tana jiran umirnin Gimbiya Hakima sannan tace..


"Ni kike jira naje na hada ruwan wankan da kaina kena?


"Tuba nike ranki ya dade..



"Yi man shiru duk baku da wani anfani a wajen, da zaran na hukuntaku ace ban yi maku adalci ba, bayan duk baku san aikin ku ba..



"Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausaci rainki ya dade, anyi man afuwa insha Allah haka ba zai sake faruwa ba..


"Yi man shiru wawiya kawai dake, ku baku kama girmanku kurkure har na nawa kuke yi man cikin gidan nan, dan haka tashi kiyi aikinki kice ma yan uwanki gobe ina san ganinku dan tashi ki bani waje..



Nan Bilkisu ta tashi jikinta na rawa tana godema Allah da hukuncin Gimbiya Hakima ya tsaya iyakar zagi da bata yi mata hukuci irin na Lantana ba..


Haka ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka..


"Ranki ya dade, na gama hada ruwan, haka Bilkisu tayi tsaye tana jiran tashin Gimbiya, tana jin ina ace tana cikin masu yi ma Gimbiya girki ko gyaran gida da yanzun ta can ta na hutawa, amman yanzun su ke hadama Gimbiya ruwan wanka da kuma bata labari har sai tayi bacci ita da Lantana, sai da Gimbiya ta gadama sannan ta tashi ya shiga wanka, kafin ta fito Bilkisu ta gyara gado ya fiddo mata kayan sawa.



"Je ki hado mani tea ki taho man da tufa..


"Angama ranki ya dade, Bilkisu ta tafi jikin na bari ta hado ma Gimbiya Tea mai kyau da dauko mata tufa harda ayaba ta kawo mata, nan ta bare mata ayaba ta miko mata, sannan ta zuba mata Tea din a cup ta mika mata..


Kawai sai Bilkisu taji an watsa mata ruwan zafi a fuska cikin bacin rai Gimbiya ta fara magana..


"Dan mai zaki hado man Tea ki sa man sugar?

"Allah ya huci zuciyarki, naga haka kika ce adinga samaki sugar in za'a hado maki shayi..


Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wankama Bilkisu mari tana wurga nata ayaba a jiki da sauran Tea din da ya rage tana ce mata..


"Dan nace ku ringa sa man sugar sai nace maku kullun ko?


"Aa Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausacin hukunci gurin uwargijiyata uwar Marayun masarautar Kano..


"To ubanwa zai gyara maki wajen? "Ina neman afuwarki yar masu gida, yanzun nike jiran umirnin tashi Gimbiya..


"Tashi maza ki goge wajen ki ban waje ki sheda ma shashasun masu Aiki bangareni irinki gobe karfe shiddan safe ina bukatar ganinku kafin kowace ta fara Aiki..


"To insha Allah, godiya muke Gimbiya uwar-adalci ga tallakawanta, nan ta tashi tayi mopping din wajen sannan ta wuce tana godema Allah da ya kubutar da ita daga mumunan hukunci Gimbiya Hakima..













_By jameelah jameey 🖋__









Share and comment pls

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey 🖋_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





03&04




Tunda Asuba su Bilkisu suke tsaye jiran Gimbiya Hakima, hankalinsu duk a tashe yake baki dayan su suna tsoron hukuncin da zata zartar a kansu..


"Wai Ba'ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya Hakima?


"Wallahi A'bu nima bansan mai mukayi ma Gimbiya Hakima ba, amman karki so kiga yanda jiya ranta ya baci, ko nima nan dakal nasha dan harda mari sai da na sha cikin daren nan..


"Yanzun Ba'ba Bilkisu ke din Gimbiya Hakima ta mara? "Yo sau nawa akayi Murja ai sai dai kar'asake indai marine munsha shi wurin Gimbiya Hakima nida Lantana yunzun kinga Lantana tana gidan hukunci dan ma Allah yaso ta yau za'a fiddo ta, da sati biyu ta yanke mata..



"Wai dan Allah maiyasa Gimbiya Hakima bata biyo halin iyayenta ba, baki daya Gimbiya Hakima bata da tausayi balle imani, da tana da tausayi da bata mari kamar su Ba'ba Bilkisu ba..



"Hakane gaskiya Ladi, shiyasa na godema Allah da nike wajen dahuwa kawai, shiyasa kullun nike kiyaye wulakancin Gimbiya Hakima, domin bata gani girman kowa cikin masarautar nan..


"Aiko Larai, kinga yanzun har karfe goma na safiya yayi amman har yanzun bata yi lokacin mu, itada tace tun shiddan safe take san ganinmu, amman shiru kuke jinta..



"To ya zamuyi Ba'ba Bilkisu, ai hakuri zamuyi tunda haka Allah ya kaddari rayuwarmu, "aiko dai ai hakuri ya zama dole Larai..


Su Ba'ba Bilkisu suna can tsaye tun asuba, amman Gimbiya ta gyalesu kuma sarai ta san da tsayuwarsu a bakin shashenta saboda tun takwas din safe take ido biyu tanata chatting dinta sai da goma tayi sannan ta shiga wanka, bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata purple din doguwar riga sannan ta fito tana tafiya cikin isa da mulki irin na sarauta..


"Sai yanzun kuka gadamar zuwa kenan?

"Muna neman afuwar Gimbiya, uwar Marayu, tun dazun muke nan muna jiran isowarki..


"To maiyasa bakuje kuka yi man magana ba?


"Allah ya huci zuciyarki, ai bamu da ikon zuwa turakarki batare da wani dalili ba, kuma ai kina bacci shiyasa..



"Matsalarku ce wannan, kuna jina?

"Eh muna ji uwargijiyarmu, muna jiran umarni daga gareki..


"Mtssss, wai ku wasu kallar jahilai ne dabobi wanda basu da gwakwalwa basu da lisafi...


Read / Download GIMBIYA HAKIMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album