Join Our WhatsApp Group

NANCY YAR KARYA Complete Hausa Novel Document by NANCY YAR KARYA


NANCY YAR KARYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31743



NANCY YAR KARYA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 09, Aug 2023

Author: Zainab Habib Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 188.31 kb

File Type: txt

Views: 565+

Download: 268+

Last download: 1 day ago

Description/Story: .💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa_.

_story and writing_

By


*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MA DAUKAKIN SARKI TSIRADA AMINCIN ALLAH SUKARA TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALLAM*


*ALLAH NAGODE MAKA DA KASAKE BANI IKON RUBUTO WANAN TAKAITACCEN LABARI ALLAH KASA ZAMU AMFANA DA DARUSSAN DA SUKE CIKI AMEEN YA ALLAH*

*WANAN LITTAFI K'RK'IRA NE BANYISHI DAN WANI KO WATA BA INYAZO DAI DAI DA LABARINKI/LABARINKA, TO HASA SHENE KAWAI*👌.


*DUBUN GODIYA GA UWA TAGARI MAGANIN KUKANMU WATO SHUGABA ADILA (ANTY HAUWA MAMAN USAWAN) KEDIN TA DABANCE A CIKIN MUTANE 👌*.


*BAZAN GAJI DA MIK'A GODIYATA GA (DOCTOR MARYAM IBRAHEEM) BA SABODE KECE SILA😭*


*GODIYA A GAREKU WRITERS NA (AREWA WRITERS ASSOCIATION) FATAN ALLAH YAKARA HADE KAWUNANMU BAKI DAYA*


*INA TAYA KUNGIYAR MU ' MURNAR CIKA SHEKARA ALLAH YASA SHEKARA MAI ZUWA IDAN MUNADA RAI DA LAFIYA TAFI HAKA ' AMEN YA ALLAH*.



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


PAGE *ONE AND TWO*


_____Wata kyakyawar budurwa na hango sanye da , riga da zani kod'ad'u , da 'alamu sunji jiki sosai , amma kasancewar wanan budurwa kyakyawa, yasa ko yagaggun kaya tasa baya yimata muni , budurwar zatakai shekara goma sha biyar , tafiya takeyi cikin yanga da iya taku, duk a ganinta kaf cikin k'auyen (ZANKANA) itace wayayya, tunda ta doso gurin wasu samari suna shan rake, naji suna cewa saike Duduwa , 6ata rai tayi kana tace "wallahi duk wanda yakuma fad'amin wanan sunan saiyayi dana sani , cikin tsiwa take maganar, wani matashin saurayi ne ya taso yazo kusada ita yace " saike kyakyawa , washe hak'ora tayi tana dariya tace"yauwa Yasir ai kai kafisu mutunci,


Suna tafiya suna hira, har suka zo daidai k'ofar gidan su Duduwa , gidane mai zagaye da galan galan saboda bazaka kira gidan masu kud'iba saidai ace talakawa , bayan sunyi sallam da Yasir ta shige gida, tasami Umman ta 'tana tuk'a tuwo , yamutsa fuska tayi kana tace" waike Umma bakya gajiya da cin tuwo ? kullum tuwo ,wallahi ni nagaji cikin masifa take maganar , Umman ta da ko kallonta batayi ba tacigaba da tuk'a tuwon ta , Duduwa ce ta wuce d'akinta daya kasance mai katifar yayi ,ta janyo wata leda data mak'ale a mararta ,dan tasan hardai Umma ta ganta da ledar to saitayi mata nasiha , awara ce da yaji cikin farar leda , tanaci tana karkad'a k'afa tana mita, Umma ce ta k'wala mata kira ,seda tad'au lokaci sanan ta 'amsa , bayan ta goge hannunta ta fice zuwa gurin kiran Umman,


Tana zuwa Umma tace" ga tuwonki nan , kamar zata fasa ihu tace " ba yanzu zanciba sai zuwa anjima, tsayawa kallonta Umma tayi , tana tunanin girman kai 'irinna Duduwa, bayan Umma tagama tattare kwanukan abincin data zuba ta koma d'aki, bata ko kalli gurinda Duduwa ta tsaya ba , bayan sallahr isha'i , yaro yazo yana sallama , Umma ce ta amsa sallamar tare da cewa , waye? yaron yana daga k'ofar gida yace" Duduwa ake kira , kafin yaron ya k'arasa fad'ar sunanta ta fito cikin masifa Umma na tsaye tace" dan uwarka wacece Duduwar ? rik'e baki Umma tayi tana kallon ikon Allah tace" inkin gama masifar saiki tambayi waye mai kirannaki, bayan ta gallawa yaron harara tace"wai' injiwa ? yaron da tsoro ya kamashi yace " inji Yasir ne, da fara'a d'auke a fuskarta tace kace ina zuwa,



Bayan yaron ya fice, Umma ta dubi Duduwa tace"nidai nasihata dake shine kirik'e mutuncinki , wlh ke y'a mace ce mai rauni , tunda Umma tafara nasihar Duduwa ta had'e rai tace"Umma kullum kekenan fad'a kuma kinsan ' niba k'aramar yarinya bace, sanin halinta da Umma tayi yasata komawa d'aki , ita kuwa Duduwa kwaskwarima tayi tayi kwaliya tasa kayan sallanta ta fice zuwa gurin Yasir , tunda ta doso yajiyo k'amshin turarenta yafara fad'in, maraba da kyakyawa saike y'ammata murmushi takeyi tana sunkuyar da kai ,ammafa tak'i bud'e baki wai, saboda kar janbakin ya goge , bayan sund'an ta6a hirane yayi mata sallam , ganin bai mik'o mata komai ba yasata 6ata rai , shikuwa saboda tsokana yazagayo yace"kawo hannunki , a hanzarce ta mik'o , ganin wainar k'awai ce a leda tahau dariya , daganan sukayi sallama cikin farinciki,


Washe gari da safe , bayan Duduwa tayi sallah tazo gaida Umma , bayan sun gaisa ne Umma tace" maza tashi ki had'a wanke_wanke kiyi mana saboda yau inason zuwa anguwa ,da har ta6ata rai , amma jin Umma tace zataje anguwa yasata fara'a ta mik'e da sauri dandanan ta gama , lokacin Umma tagama shiri , dari hud'u ta bata kud'in cefanen abincin rana , tace "kafin ta dawo tasamu tagama , aikuwa Duduwa jiki na rawa tace" Umma insha Allah zan kammala kafin kidawo , Umma tayimata sallama ta wuce unguwa,


Duduwa na kwance tun k'arfe tara na safe har shad'aya na rana tana bacci , k'arar dabbobin gidansu ne ya tayar da ita daga baccin, gyalenta ta d'auke da kud'in da Umma ta bata ta nufi shagon mai saida kayan shayi , bredi d'an nera d'ari ta siyo sai madara ta hamsin sai k'wai na d'ari takuma siyo maggi na goma tasiyo indomie ta ragowar canjin , tana tafiya ne sukaci karo da wani saurayin dake kusada gidan su yace"ah kyakyawa ina zuwa ? naga kamar kayan dad'i kika siyo mana , tana dariya tace"Abdul yunwace ta isheni shine nazo siyan kayan shayi , Abdul daketa lek'en ledar yace"to sammin burodin inci ,mak'ale kafad'a tayi tana dariya,

Tunda ta koma gida tafara had'a wuta bayan ta d'ora shayin ta had'a takuma d'ora indomie , bayan ta kammalla girkin ta d'auko plet d'inda tasiyo a kasuwa , a cewarta bazata dinga cin abinci a kwano mai tsatsa ba , bayan ta d'ibarwa Umma tata ta shige d'aki da sauran tanaci hankalinta kwance , bayan tagama ci taji bata k'oshiba , komawa tayi kwanonda
tazubawa, Umma ta d'ebo kad'an tarugo da gudu taje ta wanke kwanukan duka ....✍️✍️✍️


*TABBAS ALK'ALAMI ✍️YAFI TAKOBI🤺*.


_Alk'alamin mom islam✍️._


*Please share 🤝*
*Comments*
*vote*✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 3_4


___Umma na dawo wa tasamu ankai mata abinci a kwano k'ato , ganin haka tafara sawa Duduwa albarka , Duduwa na ganin haka tafara mur mushi, bayan Umma ta bud'e kwanon 'ne taga indomie da k'awai a k'arshen kwano , zaro ido Umma tayi kana ta dubi Duduwa tace" wato fad'an danake yimiki baya shigarki kenan? kina y'ar talaka amma kin d'auki buri kin d'orawa kanki , kuka Duduwa ta k'a k'alo tana bawa Umma hak'uri ,

Suna cikin haka ne sai ga sallamar dillaliya nan , Duduwa najin muryar ta aikuwa ta rugo a guje tana oyoyo hajiyar mu ,
da fara'a dillaliya ta tari Duduwa tana cewa zuwan danayi yau gurinki nazo ,

Washe baki Duduwa tayi tace "wallahi dama ina nemanki 'ido rufe sekuma gaki , dillaliya ce tace" to mu k'arasa ciki , cikin fara'a suka k'arasa d'akin Umma ,

Bayan sun gaisa da Umma ne dillaliya take gayawa Umma maganar zuwan Duduwa birni ya taso , farinciki ne ya lulu6e Umma tace " alhamdulilah haka akeso ,

Dillaliya ce tace" kinga gidan da Duduwa zata sauka sunbada kud'i dubu hamsin , zaro ido Duduwa tayi kana tace " har anfara biyana kud'in ' ne tunkafin infara zuwa?

Dariya dillaliya tayi kana tace " a'a sunce dai za'a siya miki kayan sawa masu kyau , dakuma hijabai da gyalu luka suma masu kyau,

Tsalle Duduwa tayi tana dariya , Umma dake gefe tace"nidai nasihata kullum itace ki kulada mutuncin ki , insha Allah Duduwa ta amsa , bayan dillaliya tabawa Umma kud'in , Umma tak'i amsa tace"Duduwa ta shirya suje kasuwa suyi siyayya , tunda tafiyar gobe ce ,

A yaudai farincikin da Duduwa take ciki baya fad'uwa saboda yau ko rashin kunya bata yiwa Umma ba , nan tafara had'a kayanta tana kyautar wa saboda duk sun kod'e ,

Shirin zuwa kasuwa tayi , bayan sunje ne dillaliya ta za6o mata wasu riga da skirt na kanti masu kyau sunkai kala goma , sai atamfa kala biyar sannan pants da bra sukuma rabin dozin tasiya mata yadin hijab suka tsaya aka d'inka da takalmi masu kyau , tunda suka dawo gida bakin Duduwa yak'i rufuwa saboda ita burinta taganta cikin kayan ba zuwa birni yin aikin ba ,

Umma naganin kayan ta yaba dasu sannan tace" wa Duduwa ta kula sosai kar tabi maya daran samari , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a fuskar Duduwa , Umma na ganin hakan tasan ba k'aramin abu bane yake sata kuka , bayan tagama kukanne ta d'auki buta domin yin alwala ,Umma ma tashi tayi zuwa yin alwala ,

Washe gari misalin k'arfe takwas na safe sukajiyo sallamar dillaliya ,da cikin sanyin jiki Duduwa da Umma suka amsa sallamar ,bayan sungama shirye shiryen da zasuyi , tayi sallama da umman ta suka d'auki hanyar zuwa Abuja ,

Da isar su gidan dillaliya tayi nocking , mai gadi ne yazo ya duba , yana ganin dillaliya ya washe baki yace "barka dazuwa hajiya , goro dillaliya tabashi , yanata yimata godiya , ita dai Duduwa na biye da dillaliya , saboda duk inda tasa k'afa nan Duduwa take sawa,

Da isar su gidan wata kya kya kyawar mata fara sol, da 'a shekaru zatakai shekara hamsin a duniya , amma inkaga yanayin jikinta bazaka gane yawan shekarun ta ba , tunda suka iso cikin parlorn matar take yimusu sannu da zuwa , gaisawa suka farayi Duduwa ma ta gai sheta ,matar tace" what's is your name my daughter , jin wanan bahagon yaren yasa Duduwa mik'ewa tace "Hajiya zanyi kashi ......✍️✍️✍️

_mom Islam ce_✍️.


*Please share*🤝
*Comments*
*Vote*✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 5_6

__Matar ce tace" bari azo a nuna miki bathroom d'in , Duduwa najin ance bedroom tasa ihu , Matar da ake kira da Hajiya tace" lafiya kuwa daughter ? cikin kuka Duduwa tace" Hajiya kiyi hak'uri karki sa 'a maidani garin mu , cikin rashin fahim ta Hajiya tace" ban gane ba , Duduwa ce tak'ara share hawayen ta kana takuma duban Hajiya tace" kalma biyu zunyimin zafi , na farko kince min (bi dreba)🤣 yanzu kuma kince (buta) ni wallahi Hajiya ko wankin duka y'an gidannan ne zanyi akan a maidani garin mu , dariya ce taso ku6u cewa Hajiya , tace" yo daughter banda abinki , daughter yana nufin yarinya kokuma y'a , shikuma bathroom gurin wanka ne , OK Duduwa tace" kana ta waske tace ai nasani Hajiya kawai 'inason jin 'naku yaren 'ne,

Dillaliya ce tayiwa Hajiya sallama tayiwa Duduwa nasiha ,kana ta wuce garinsu ,

Da tafiyar dillaliya Hajiya ta nunawa Duduwa ai yukan dazata dingayi , kamar su gyaran d'aki dakuma gyara d'akunan y'an matan gidan saikuma zuwa super market siyayya,

Hak'ik'a Duduwa tayi murna saboda babu aiki mai wahala , godiya tayiwa Hajiya kana ta nufi kitchen saboda cikin ta yana kukan yunwa,

Tana zuwa ta samu Nanny d'in tana farfesun kaji , lashe baki Duduwa tayi kana tafara magana a cikin ranta tana cewa , inama nice aka bari a d'akin girkin 'nan da wallahi saina ci na k'oshi zankai musu sauran amma yanzuma bata 6aci ba,

Ganin hankalin y'ar aikin yakoma gurin aikin ta yasa Duduwa kwad'a sallama , amsawa tayi ba tare data d'ago kai ba saboda tana san kammala aikin cikin 'nutsuwa,

Duduwa ce ta k'arasa kitchen d'in cikin taku sai k'amshi take zubawa mai aikin da take sanye da rigar aiki tace "sannu Duduwa da zuwa, cikin fushi Duduwa ta galla mata wata uwar harara ...

Kana tace" as from today my name is Nancy..

Wani kallo y'ar aikin tayi mata kana tace to inma zagina kikayi keda Allah🤙,


Haka dai suka k'are kamar zasuyi fad'a haka Duduwa tabar kitchen d'in a zuciye ,


Washe gari bayan tayi sallahr asbah , taje ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya take gaya mata anjima ita da su Humaira wato yaranta zasuje shopping ,wani tsalle ta daka kana tafara jerowa Hajiya godiya,

D'akin ta 'ta nufa ta shiga wanka bayan ta fito daga wankan'ne tazo gaban mirror d'in d'akin da yazama nata tafara tsara kwaliya saboda ko gidan makeup sun shafa mata lafiya,


Wani riga da wando ,da rigar iya guiwa wandon kuma tsukakke , wayo kuzo kuga Nancy ,

Kar ince Duduwa ta fasamin baki🤫,

Kunsan fa ba mu muna bace kuma ko batayi kwaliya ba tanada kyau to inaga tayi kwaliyar ,

Tunda ta fito daga d'akin ta take yanga tana wata kalar tafiya kamar mai tsoron k'asa ,

Ganin y'an matan gidan a parlor suna jiran ta yasata k'ara sowa da sauri tana cewa( ai sorry sit ,wata dariya suka sa , d'ayar mai suna Humaira itace babbar su tace "ba haka zakice ba cewa zakiyi ,am sorry sis ,

Godiya tayiwa anty Humaira kana suka d'auki hanyar parking spice, ganin motar dazasu hau sukayi an wanke ta , Duduwa cikin bahagon turancin ta 'tace....✍️✍️✍️.


_Mom Islam ce_✍️✍️

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 7_8


"Tace very support🤣 anty Humaira da tagaji dayi mata gyara tace" please Nancy kidin ga daurewa kina k'yale turancin nan saboda , a gaban classmate d'inmu zaki bamu kunya , cikin k'awrewa Duduwa tace" au anty Humaira yanzu babu gyaran kenen, cikin takaici anty Humaira tace" cewa zakiyi very surprise , tsalle ta buga kana suka shige mota , da Isar su wani katafaren super market , kayane kala kala babu wanda babu , kuma duka gurin babu kayan talaka , suna shiga Duduwa ta sauya taku su Anty Humaira ko basu lura da ita ba , tana cikin takun 'nata ne taji wani hansom yace hey Lady , cikin firgici ta juyo tana k'aremai kallo , farine sosai kamar balarabe , gashin kanshi kamar na larabawa , idanuwan shi kuwa lumsa sune gasu bak'ak'e ,sai dogon hancin daya k'ara fito da ainihin kyaun shi , ganin ta tsareshi da ido yasa shi cewa are you ok k'ak'alo murmushi tayi ganin turancin ma bai 'iyaba , cikin zuciyar ta tace" mugu wai 'inci wanan uban kwaliyar yacemin LADI , shikuwa wanan saurayi ganin bata kulashi ba yasashi cewa dan Allah kya kyawa kiyi magana , wani...


Read / Download NANCY YAR KARYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album