Join Our WhatsApp Group

BASO BANE CUTA CE Complete Hausa Novel Document by BASO BANE CUTA CE


BASO BANE CUTA CE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 45461BASO BANE CUTA CE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 15, Apr 2024

Author: Usaina B Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : DA BAZAR MU WRITEER AS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 239.67 kb

File Type: txt

Views: 344+

Download: 226+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: [7/28, 10:52 AM] Mrs Abubakar 🌹: 🎊🎊🎊 *BA SO BANE* 🎊🎊 🎊

*_STORY $ WRITTEN_*
*_BY USAINA.B ABUBKAR_*
*_(MRS ABUBAKAR CE)_*💫 *DA BAZAR MU WRITEER ASS* 💫
*We are here to make you happy, smile, educate and to realizd that we are best among all.......DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

1⃣➖5⃣


BISMILLAHIR RRAHMANIR RSHIMKuka take sosai tamkar Ranta zai bar gangar jikin, har tana shid'ewa dan tsananin kuka.

Shiko yana tsaye akan ta sai aikin rarashi yake da ban baki, cikin sanyi halin, irin na shi yace"haba JAWAHIR, me kike so ki zama ne? shin wai baki yarda da kaddara bane?, Allah da ya bamu shi ya fi mu kaunar sa, karki manta duk wani me rai sai ya d'an-d'an na d'acin mutuwa, yanzu da kike wannan kukan kin kyau tawa Baffa kenan? a halin da ake ciki a yanzu babu abin da yake buk'ata a wajen ki sai Addu'a, kuka babu abinda zai kara mki sai ma dai ya ja miki wani ciwon, karki manta ina tare dake, kuma nayi mai al'kawarin baki farin ciki har karshen numfashi na." ya fad'a cikin sigar rarashi.

JAWAHIR ta d'ago tayi mai wani kallo kana ta mayar da kan ta k'asa ta ci gaba da kukan ta, gani bata da niyyar yi mai magana dole tasa ya bar d'akin, zuciyar sa na mai kuna.


yana fita tace"mugu kawai." ta fad'a tana hararar in da ya tsaya tamkar yana wajen.


yana fita yaci karo da matar Baffa, cikin nutsuwar sa yace"sannu Adda ya 'karin hak'urin mu?." ya fad'a yana mata kallon tausayi.

"Umm! hak'uri mun gode Allah, halan wajen JAWAHIR kaje ko?." ta fad'a tana mai wani kallo.

"Eh kin san ita yarinya ce dole sai anayi ana duba ta, musamma yanzu da take cikin halin kad'aci da maraici, na babu uwa babu uba Adda ina masifar tausayin JAWAHIR, dan Allah ki taya ni rok'on amanar nan da aka bani." ya fad'a yana mata kalar tausayi.

ita ma fuskar tausayi tayi mai kana tace"kar ka ji komai in dai ina gidan nan ai JAWAHIR ta ka ce Allah ya taya ka ri'ko." ta fad'a tamkar za tayi kuka.

haka yayi waje yana jin sa gaba d'aya sai a hankali, dan yana tsoron wannan kukan da take.

tana tafe tana tafa hannu wa har ta isa cikin d'akin sai da ta rufe 'kofar, sannan ta isa gare ta, A hankali ta zauna, tana me sauya fuskar ta zuwa damuwa tace"taho nan yarinya ta kinji, bar kukan haka nan, kar kan ki yayi miki ciwo." ta fad'a tana jawo ta jikin.

JAWAHIR tayi tamo a jikin Adda tana share k'walla aka-aka, in dai Adda ta dage sai shafa mata baya take alamar rarashi, sai da taji tayi shiru sannan tace"yarinya ta ya kama ta ki kwantar da hankalin ki haka nan, na gaya miki mudin ina raye bazan bari ki tare a gidan yaron nan ba, ni da kai na zan saka shi ya sake ki, kin ga sai ki aure wanda kike so ko?." ta fad'a tana d'ago fuskar ta dan ganin yanayi da zata shiga.

hannu ta saka tana share k'wallar da ta zub'o mata tace"yauwa Adda ki taimake ni, dan wallahi bana son shi, a yanzu bana ko kaunar gani fuskar sa, ina mutu'kar mamaki dalilin da yasa Baffa ya aura mini shi, ni wannan wasihar tashi ba tayi mini dadi ba wallahi." ta fad'a tana sake rushe wa da kuka.

Adda tayi murmushi irin nasu na manya tace"to ai duk laifin ki ne, ko ni a baya nayi tunanin soyayya kuke, yanda kuka nuna wa junan ku kula wa, ya d'auke ki ya kai ki wajen sha'katawa ku jima a can, ko kun dawo gida babu hutu haka zaku kara dasa sabon zama kuna hira har sai nayi magana sannan ku tashi, mahaifin ki bai da laifi ko kad'ai da ya aura miki shi, da tun farko kin fito kin nuna bakya son shi ai da ba'ayi miki auren zumuci ba." ta fad'a cikin kula wa.

Tamkar dolowa haka ta dawo, ta d'ago da sauri tace"to yanzu ya zanyi Adda?." ta fad'a cike da neman mafita.

Adda tayi murmushi gefen baki tace"hanya me sauki da zaki bi shine ki fito, ki gaya mai gaskiya bakya son shi, ki gaya mai ke a d'an uwa kika d'auke shi uwa d'aya uba d'aya ba wai miji ba, ki ce mai baza ki iya zaman auren dashi ba, in dai kika fad'a mai haka to ba makawa tunda yana son farin cikin ki zai sake ki, nima daga nan kin ga sai na bashi k'anwar ki gudun duniya kar ta zargin wani abu."

tayi shiru tana son tayi tuananin me tsaye amma Adda ta hanna ta, sai zance take d'ako mata, kuma duk gaskiya take fad'a mata aiko tayi na'am da maganar ta.__________
___________

Zaune suke shi da abokin sa, yayi shiru ya tafi duniyar tunanin Abdulrahman, ya tsara mai idanun yana kallon ikon Allah, domin gaba d'aya abokin na sa ya sauya, zuwa can yace"IMARAN wai yanzu me yake damun ka ne?, gaba d'aya ka sauya tun rasuwa Baffa, kar fa ka manta kai ne kake yiwa matane wa'azi akan mutuwa ko in wata kaddara ta fad'o musu, shin yanzu kai baza ka iya hak'uri da ta kai kaddara ba, tabbas na san akwai zafin da ciwon rabuwa da iyaye amma wannan damuwar da kake sawa kan ka, akwai matsala gaskiya yana da kyau ka farga, ka rage ta ko yaya ne, yanzu irin sakkayar da za kayi ma Baffa kenan? mutumin da bai da burin da ya wuce sanya ka farin ciki, yanzu ya bar duniya addu'ar da za kayi mai ta gagare ka sai tunanin da sharar hawaye, anyya kuwa MAN din da na sani ne?." yayi maganar cike da shak'u.


ya sauke wata ajiyar zuciya kana yace"tabbas ba kayi karya ba, rasuwar Baffa na tab'a ni sosai domin yanzu ne nake jin kewar sa, amma abinda yafi damu na a yanzu shi ne JAWAHIR, ban san me yasa Baffa ya aura mini ita ba?, wallahi ban tab'a mata so na aure ba ina mata son ne kawai na 'yan uwan taka, domin kallon 'kanwa nake mata, ga kuma marainci uwa, ban san me yasa yayi wannan tunanin ba na had'ani aure da ita, yanzu fa matsayin da muke da ita tunda Baffa ya rasu yarinyar nan ko kallon mutunci bata mini, kuma kullum cikin kuka nake samun ta, ka dai duba tsayin lokacin da muka d'auka da sani akawai aure, sannan ni yanzu ya zanyi da NABEELA?." yayi magana cike da damuwa.

Abdulrahman, ya sauke ajiyar zuciya yace"kana da gaskiya aboki na, amma abinda nake so ka gane a nan shine, Baffa yayi haka ne domin JAWAHIR ta samu ingantaciyar kulawa tunda ya san duk rutsi bazaka cutar da ita ba, kuma zata samu farin ciki me d'aure wa a tare da kai, MAN ina so kayi biyayya ga wannan bawan Allah da ya riga mu gidan gaskiya tabbas zaka samu alhairi akan abinda yayi, karka manta shine komai na ka, NABEELA kuma wannan ba wata matsala bace, tunda tana da fahimata ko ni nan zan mata bayani, ka shawo akan yarinyar kawai ku zauna lafiya, kai da ka samu aure a sama malamn ai kai d'an gata ne, ni ai mini mana." ya ka karshen maganar da zolaya.

IMRAN ya kai mai duka yana cewa"yanzu fa ka gama maganar kirki amma sai ka had'a sha'kiyanci, insha Allah zanyi abinda kace aboki na zan gwada naga ko zanyi nasara, a wajen ta na kuma cika mai burin sa na saka 'yar sa cikin farin ciki." ya fad'a yana murmushi da d'aukar niyya..

Abdul yayi dariya yace"ko kai fa mutumi na angon shekaru da dama." ya fad'a yana tashi a wajen sa dan ya san duka zai sha.
IMRAN yayi mai wani banzan kallo sannan ya mik'a yana barin wajen.


Su biyu ne a d'aki, sai hawaye take sharewa akai-akai tace"to yanzu ya zanyi, fisabilillahi mutmin nan sabida mugun abu shine ya aure mai 'yar sa, sabida kar na samo abinda nake hari, to wallahi bazan yarda ba ko ya aure ni ko kuma ita ma kan ta yarinyar na raba ta da duniya ko wa ya huta, ni kuma na samu zab'in rai na." ta fad'a cikin kuka.

"Kwantar da hankali ki, matakin da muke akai yanzu ita JAWAHIR din na da muke komai akan ta to, ita ba ma ta shi take ba, dan bata da burin da ya wuce na saka ya sake ta, dan yanzu haka daga wajen ta nake tun safe take kuka ita lallai sai na saka an sake ta, nayi mata dabaru da wayo sosai ta yanda bazata gane ba, kuma Ahmadullahi ta hau kan hanya yanda nake so, dan sai da na tabbatar da tayi barci sannan na fito, shi kuma yaro ai kamar kin mallake shi ne, mu dai bari yazo hannu sai yanda mu kayi dashi." Adda ta fad'a tana dukan cinya.

Jameelat ta tab'e baki tace"ke dai Adda kin cika sauri, ni abinda nake so naji kawai shine ya sallama ta shine kwanciyar hankali na, dan wallahi in ban same shi ba sai na kona gida nan." ta fad'a tana wani ciza baki sabida tsananin masifa da take cin ta.

Adda tayi murmushin gefen baki tace"ai bama za'ayi haka ba mudin kina tare dani, to ko da yaushe kece da nasara, abinda nake so dake shine kawai ki cigaba da boye kiyayyer ki gare ta har mu samu abin muke so bana so ki kuskure ko a face din." ta fad'a tana mata wani kallon.

Jameelat ta wani yamatsa fuska haka ne ya bani damar 'kare mata kallo, farace ita ma kyakykyawa da ita, domin tayo gado a wajen maman ta, tubarkala kawai zamu ce domin ta had'a komai ita ma, matsalar ta d'aya shine muguwar zuciya da son abin duniya...
*ASALIN LABARI.*Alhaji BASHIR d'an asalin garin kargi ne aiki ya kawo shi garin kano, a nan ya had'u da matar sa me sunna ASMAU'l, cikin yarda Allah su dai-dai ta har aure ya shiga tsakanin su, da yake yana da d'an abun hannun sa ba laifi.

a hankali ya ringa d'ako yan uwan sa na can gida suna dawo wa maraya da zama, cikin yarda Allah ya kwashe su kaf manya ne kawai suka ki biyo su,

su hudu ne a cikin gidan su kuma duk a cikin su shine babba, haka kuma shi ya fara aure a cikin su, Alhaji BASHIR, Abdullahi, ADAM, NAFI'U. kan su a had'e yake sam basa nuna wa juna su bam-bamci ko hassda akan abinda wanin su yake dashi, da yake mahaifiyar su taji ma da rasu wa sai mahaifin su kad'ai ya rage musu wanda ya kafe ya'ki biyo su,

zuwan su birnin su ma suka fara aiki cikin yarda Allah komai ya fara zuwa musu cikin sauki da rangwamin, d'aya bayan d'aya suka fara koma wa gida suna aure, a hankali duk su biyun su kayi aure a can gida matan su suke da zama, sai da suzo birnin suyi yan kwana ki bayan kamar sati biyu zuwa uku su koma gida, haka su ke rayuwar su cikin rufin asirin Allah, BASHIR bai rage su da komai ba haka ya kan dauki matar sa suje garin su suyi kwana biyu a can kana su dawo maraya.

Ahmadulillahi ta wani bangare kuma dukiyar sa na kara hab'aka da bun'kasa, domin yana samu sosai lokacin tun duniya na kwance kudi na daraja, sai yayi dabara da zarar ya samu kudi masu dama da nauyi, sai ya siyi kadara ya ajiye a haka, a haka har ya tare filaye da gidaje sosai a garin kano da kauye, a cikin k'anne sa babu wanda ban mallakawa fili ba hata matar sa na ta daban, basu da wata matsala a rayuwar su da ya wuce rashin haihuwar ta, basu d'aura kan su damuwa ba sai suka mi'ka lamarin su ga Allah buwayi gagara musali, su ka dage da Addu'a babu dare babu rana,

NAFI'U ne kawai ya rage acikin su wanda bai yi aure ba shi ma iyayen su ne suka hana shi, domin yayi k'an'kanta a lokacin, RASHIR ya d'auke shi gaba d'aya suka dawo maraya zama tare dan ko ganin gida zaje to ba ya jimawa yake dawo wa, sun shak'uwa tsakanin su sosai wanda duk cikin yan uwan yafi ji dashi amma bai fito ya nuna a fili ba, haka abin yake a wajen NAFI'U,

kwacin tashi babu wuya a wajen Allah su sake shafe shekaru da watani, har Nafi'u ya samu matar aure a nan cikin garin kano BASHIR ya tsaya mai akan komai har akayi aure a nan jikin gidan sa ya bashi waje shi ma ya zauna tare da matar sa ZAINAB, suna cikin haka Allah ya bama su BASHIR karuwa wace tazo ma da ASMAU'L da larura, kullum cikin ciwo da jalen zuwa asibiti, a haka har Allah ya sauke ta lafiya bayan b'akar wuyar da taci, ta samu d'an namiji wanda ya samu gata wajen dangi biyu na mama da baba, yaro d'an gatan NAFI'U ranar sunnan yaro ya ci sunnan IMRAN , fari ne sosai na karshe ga kyau da yayi gado a tsatso biyu, haka aka cigaba da rainon yaro cikin yarda da amincin Allah.

Bayan shekara biyu da haihuwar IMRAN jikin Asma'ul yak'i dadi yau da lafiya gobe ciwo,
batai wani dogon ciwo ba Allah ya amshi abar sa,BASHIR yashi ga tashin hankali da rud'ani, haka yayi hakuri ya ci gaba da rayuwa inda aka mi'ka yaro ga zainab ta ci gaba da kula daIMRAN tamkar...


Read / Download BASO BANE CUTA CE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album