Join Our WhatsApp Group

SANADIN LINK Complete Hausa Novel Document by SANADIN LINK


SANADIN LINK

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8433



SANADIN LINK

Reading Time: 0 Hours

Added On: 11, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 51.06 kb

File Type: txt

Views: 539+

Download: 127+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: 

🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
SANADIN LINK
🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ 🖋

*Short story*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```




Page_1

Kwance take bisa makeken gadonta, tana sanye da ash colour night wear, earpiece ne manne a cikin kunnanta tana jin wakarasu DJ-AB mai taken DA SO SAMU NE, hankalin ta kwance babu abunda yake damunta a rayuwa,chatting take yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da alamu chatting din yayi mata dadi shiyasa hankalinta baki daya ya karkata agun chatting din, Allah sarki Safiya kenan...


"Sofy! Sofy!! Sofy!!!, oho ni Fiddausi wannan wata kalar rayuwace yarinyar nan ta daukarma kanta, ace shi mutun baida aikin da ya wuce jin wakokin sai kuma rige waya aikin kenan ba dare ba rana, ke Sofy wai baki jinane, ta buganmata baya sanna ta juyo cikin firgice da tsoro,"Mami, wallahi Mami kin bani tsoro sosai, bansan kin shigo ba sai kawai naji kin bigeni, "ai dole kice haka Sofy, yanzun sofy abunda kika daukarma kanki kena sabo da Allah, wannan ba hali bane mai kyau,"haba Mami, yanzun ke kullun saboda Allah ni mai laifi ce, baki san ki ganni cikin farin ciki, yanzun Mami maiye aibun chatting? Kuma ni yanzun ba yarinya bace tunda har degree nagama, haba Mami ai ya dace ki duba man mana...


"Sofy, yanzun ni kike gayama haka, to nidai a matsayina na mahaifiyarki ba zan fasa gaya maki gaskiya ba, kuma tun wuri ki dawo cikin haiyacenki wallahi Sofy, haka za'ayi maki auren kina wanann MUMMUNAR DABI'AR, ai in ba shi Aliyun ba, ba wanda zai iya rayuwa da ke, dan haka ki tashi daga wannan dogon baccin naki, ina ma fatan kinyi sallahr isha'i? "Aah daman yanzun nike da niyar tashi nayi sallahr kike shigo, "Innalillahi yau naga ikon Allah ni Fiddausi yar-malan, yanzun Sofy har sai yaushe zaki ringa yin sallah kan lokaci? Ke kullun baki sallah sai nace maki kiyi, kinsan ko karfe nawa yanzun? "Eh duka yanzun karfe 10 fa Mami, kuma ai isha'i har gabannin asuba duk cikin lokacinta ne, "To shikenan tunda haka kika ce, tashi kiyi sallah, salan kuma inkin gama sallahr k ikoma bisa network din...


Allah sarki uwa, Nan fa Sofy ta tashi tana gunguni tashiga toilet tayi alwarla sannan tayi sallah tana gama wa ta tashi, ta cigaba da chatting dinta, kuma bata fasa jin music dinta itace bata sauka online sai 1:00am, sannan ta kwanta, babu adu'ar kwanciya bacci babu komai, itadai kawai tayi kwanciyarta, haka Mami tazo da asuba taita aikin Tara Sofy bacci, Amman taki tashi wai ita abarta ta huta, duka duka yaushe ta kwanta har asuba tayi, Sofy bata tashi tayi sallah ba sai wajen 7:30 sannan ta tashi tayi sallah, tana gama sallah ta tashi ta koma baccin safe, ba ruwanta da aikin gida tunda suna da mai yi masu aiki, ita a cewarta,bata tashi bacci ba har sai 11am sannan Sofy ta samu ta tashi, tayi wanka tasa wasu English wears riga da sicket dinta,sunyi mata kyau sosai, daman Sofy bata harka da manya kaya namu na hausa...


"Mami, ina kwana, "lafiya lau Sofy, an tashi lafiya? "Lafiya lau, Mami mai kukayi mana yau breakfast? "Doya da kwai mana, tashi kije kice ko,"To Mami, yauwa Mami, daman yau Aliyu yace man zai shigo gida ya gaidaki, "To shikenan Allah ya kaimu anjima, ai sai ki shiga kitchen keda Asabe ku samu abunda zaku girka mashi, "haba Mami yanzun harda ni za'ashiga kitchen din? Nidai gaskiya ya kamata Mami ki duba man, "To wallahi Sofy sai kin shiga Kitchen dinna kin ma Aliyu abinci, ba bakon ki bane, ina tunanin saura wata uku a yi bikin ku, in anyi bikini ubawa zai ringa yi maki sauwar? Dole ki shiga kitchen kuwa, "To shikenan Mami, zan shiga yi hakuri..


Bayan Sofy ta gama yin breakfast, ta shirya taje aka yi mata kunshi da kitso, ta biya ta anso dinkinta, sannan ta wuce gida, sallah tayi sannan suka shiga kitchen ita da asabe, suka yi ma Aliyun nata girki mai rai da lafiya, sannan ta shiga wanka tayi kusan 40min tana wanka sannan ta fito, ta fara daukar kwaliya kuma, daya ke Sofy kyawkyawace ta karshe ga fara kuma, ga dara -daren idanu masha Allah, hanci har baka,gashi kuma har gadon baya, kuma Sofy tana son gayu, yar gayuce sosai, bayan ta gama yin make-up, sannan ta dauko atamfarta super hollond mai ratsin ash, dan ta Sofy tana son ash colour sosai, dinki ya hau jikin Sofy Sosai ta kuma murza daurin dan-kwalinta wanda ake yayi yanzun, ta dauko gyalenta pink colour tasa dayake jikin atamfar akwai pink a jiki, sannan ta dauko turare ta fara barinshi a jiki kamar ba gobe, bayan ta gama shirya wa Aliyu yace mata ya iso, nan tasa Idi mai dadi ya kanshi dakin baki, sannan tasa Asabe takaimai kayan matsa baki,sannan Sofy ta wuce gun Mami tace mata ita ta wuce wajen Aliyu..


"Sallama Alaikum, Amincen Allah ya tabbata agareka ya kai ma'abocin murmurshi, wani handsome guy ne naga ya juyo yana yi ma sahibar tashi murmurshi, Aliyu yana da kyau sosai shima fari ne, yana barin suma, sumar ta kwanta tayi lub-lub da ita ga idanu da hanci sai kace shiyayi kanshi tsabar kyau da aji,"Amin wa'alaikum sallama, yake sanadarin rayuwata, bissilmilah mana kizo ki zauna, kinsan dai nayi missing dinki sosai, "To Habibi, nan fa Sofy tazo, ta zauna kujerar dake opposite dinshi tana yi mai murmushinrta Mai tafiya da imani mutum..


"Habity, ki tausayaman, wallahi sonki yana shirin kasheni,baki ji yanda na kosa ba, ji nike kamar na janyo wannan wata ukkun ya dawo kwana 3,habity Allah ya saman sonki, ina yi maki son da koni kaina bansan adadinshi ba, "Habibi kasan nima ina yi maka son da bansan adidinshi ba, sonka yayi man mugun ila, bani fatan abunda zai shiga tsakanin mu, "shsssss, Habity, bani fatan abunda zai shiga tsakanin mu, nidai Habity bani son ina ganin ki always online, wallahi raina na baci kuma ina Kishinki sosai, "Habibi karka sama kanka damuwa, bani chatting da kowa sai kai, nidai kawai kabarni nayi chatting dinna a group, kasan dai inason karanta Novel, shiyasa duk wani group din dai na novel ne nike shigarshi, "To shikenan na yarda Habity, yanzun dai je ki man iso gun Mami naje na gaisheta sai na wuce gida,"haba Habibi tun yanzun? "Sorry Habity wallahi zan biya nayi magana da wani, na taho Abba ya yi man waya karfe shidda naje Company zaniyi magana da wani customer din mu shiyasa, "to Habibi, Allah ya tsareman kai, "Amin Habity, kiyi sauri ina jiranka, "To shikenan...


"Mami kuje ku gaisa to zai wuce, "To gani nan zuwa, bayan Sofy taje tace ma Aliyu ga Mami nan zuwa sun dan Kara fira sannan Mami tazo suka gaisa, sannan Aliyu ya tafi gida...






Jameelah jameey 🖋


Share and comment pls



🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
SANADIN LINK
🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ 🖋

*Short story*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```




Page_2


Wacece Safiya


Safiya Ibirahim Bello, kenan, sunan Mahaifinta Ibirahim, haifenta dan jahar kano ne, a unguwar hotoro, ya taso cikin kulawa ta uwa da uba, mahaifinshi Alhaji Bello baban dan kasuwa ne a cikin kasuwar kwari, yana da babban shigon atamfofi da shadodi su materials duk wasu kayan sawa India dikasu za'ayi to akwaishi a shagon Alhaji Bello, sunan matarshi Safiya itama yar unguwar hotoro ce a garin kano, Ibirahim yayi makaranta ta arabi da boko, yayi degree din shi a bangaren mass communication a nan BUK kano, ya fara aiki a gidan radion FM kano, sanann shima ya shiga kasuwa suna gudanar da business din babanshi a tare, ya hadu da matarshi Fiddausi a nan cikin unguwarsu, sun kulla soyayya cikin aminci da kaunar juna, Fiddausi tana gama makaranta Secondary aka sa bikini su wata hudu, da yake ita mahaifinta baya barin a wuce makarantar gaba da secondary, anyi biki nagani na fada, inda aka kai Fiddausi dakin mijinta...


Bayan anyi walima kowa ya watsa ya kama gabanshi, nan aka bar Fiddausi daga ita sai halinta, tayi kuka kamar ba gobe, bayan kowa ya kama gabanshi nan ango ya shigo shida abokanshi, bayan anyi budar baki, suka yi masu fatan alkhari kowa yasan inda dare yayi mashi..

Bayan Ibirahim ya dawo daga rakiyar abokanshi ya shigo dakin amaryarshi bayan sunyi sallah raka'a biyu, sun gode ma Allah daya nuna masu wanann lokaci main albarka, yayi mata tambayoyi kamar yanda addini ya tsara sannan suka ci kazar amarcin su,bayan sungama cin kaza Fiddausi tafara shiga wanka sanann Ibirahim, kafin ya fito Fiddausi tuni tagana shirin yawa ta kwanta, shima bayan ya gama shirinyawa ya kwanta asuba tagari...


Washer gari Fiddausi ta daure ta kara gasa jikinta sosai, ta shirya ta shiga kitchen ta hada masu abunda zasuyi breakfast dashi, haka dai rayuwa ta kama ta fiya tsakaninmu Fiddausi da mijinta Ibirahim zama suke cikin kalawar juna...


Soyayya suke main karfin gaske, baka jin junansu koda wani abu ya hadasu tsakaninsu suke sasanta kansu basai sunje gida ba, a kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Allah ya azarta su Fiddausi da karuwar ciki, sunyi farin ciki da murna sun reni cikin sosai, dan harta aiki Fiddausi daina yinshi tayi saboda likita yace sai ta rage yin aiki sosai wanann dalilin ne Ibirahim ya hanata yin aiki, inko Fiddausi tayi aiki to Ibirahim ya tafi wajen aiki, sanann take samu tayi aiki kafin yadawo...



Bayan cikin ya cika watan haihuwa Fiddausi ta haifo shentaleliyar yarinyar ta kyakyauwa da ita, ranar suna yarinyar taci suna SAFIYA amman ana kiranta sa SOFY, tunda Sofy ta taso babanta baya barin ayi mata fada, koda kuwa tayi abunda ba dai-dai ba,, sai yace yarinya ce nan gaba bata yi ba...


Wanann dalilin shine yasa Sofy ta taso cikin shagwaba da gata, duk abunda take so shi ake yi mata ba main ye mata fada shidai Maminta, itama da Dadynta yadawo zata gaya mashi Mami tayi mata fada, nan fa ya ringa yin fada kenan, yana cewa abarma shi yarinyarshi tayi abunda take so a gidan ubanta...


Haka dai rayuwa taciga da tafiya, Hajiya Fiddausi tana ji tana gani amman abu yafi garfinta, bata da ikon hana Sofy yin abu, kuma bata da ikon sata yin abun, da Alhaji Ibirahim yaga matarshi ta matsama yarshi sai yaje wani dan kauye ya dauko yar aiki mai suna Asabe, dan shi baya son ana sa diyarshi aiki main yawa...


Sai da Hajiya Fiddausi tayi da gaske, sannan ta samu Alhaji Ibirahim ya yarda a koya ma Sofy sauwa, daga bayan sauwa bai yarda a Kara koya mata wani abuba, haka dai Hajiya Fiddausi tayi kokarinta gani ta gyara ma diyar tata tarbiyarta amman ina ta MAKARO, amman duk da haka ta dan guard wata...



Haka dai Sofy ta cigaba da rayuwa cikin son da kauna, bata aikin komai sai shiga kitchen, shima kitchen din ba ita daya ba, ita da su Mami, ahak dai har Sofy tayi JSCE, ta shiga secondary school, Sofy bata son san manyan kaya ace warta manya kaya sa zafi garesu a jiki, shiyasa duk inda Alhaji Ibirahim yaje yakan dawo ma da Sofy English wears kala kala..

Bayan ta gama Secondary school,tayi jamb kuma taci dan haka tasamu addimission a BUK kano, kana karanta BCH, wato BIOCHEMISTRY, tana level 3 ta hado da Aliyu ya shigo cikin unguwarsu nan fa suka hadu, Aliyu yasha wuya kafin ya shawo kan Sofy ta soshi, shi kuma Aliyu dan GRA ne, da sannu Aliyu ya tusama Sofy Soyayyarshi a zuciyarta, taji baya son kowa sai shi,suna soyayya main kyau da shi'awa, shi kuma Aliyu ya gama MSC din ya karanta COMPUTER SCIENCE, yana aiki a campany Abbanshi...

Sofy tana son chatting sosai, kullun tana online, bata da aiki sai chatting, duk LINK din da ta gani ana talla sai ta shiga, amman bata shiga kowa ne inba group na novel ba, tana karanta novel sosai, saboda yawan karatun novel, Sofy bata sallah kan lokaci, har sai Mami tayi magana sannan take tashi, indan kuma ta gayama Alhaji sai yace ai yarinya ce nan gaba komai zata daina, sai dai Mami tayi shiru, tana yima mijin nata adu'a Allah ya nuna mai gaskiya, sanann wannan duk ba gata bane yake nuna ma Sofy ba, domin yana bata mata rayuwa...



Sofy nagama university a kasa ranar bikinta da Aliyu wata shidda, saboda Alhaji Ibirahim zaiyi wani course na wata biyar, shiyasa aka bikini wata shidda, sai ya dawo daga SUDAN , sannan za'ayi bikin su..





CIGABAN LABARIN




Jameelah jameey 🖋







Share and comment pls


🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
SANADIN LINK
🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_...


Read / Download SANADIN LINK

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album