Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MAJOR SALMAN Complete Hausa Novel Document by MAJOR SALMAN


MAJOR SALMAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15753



MAJOR SALMAN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Maman Hanan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 701 472 7066‬

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 89.8 kb

File Type: txt

Views: 631+

Download: 423+

Last download: 6 hours ago

Description/Story: [1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 1-5

My today's novel is different from the others
Ban taba littafi makamancin wannan ba kuma ban taba littafi me daukeda manyan sakonni kamar wannan littafin nawa ba na *major salman* yana daya daga cikin littafan danafiso a duk cikin littatafai na..dafatan zaku bani goyon baya 100% don littafin yazo da sanje sanje na musamman...

Bismillahir rahmanir rahim...


Yes sir...Ok Sir...i will try to be there soon..Ok sir take care

Waya yakeyi amma idan kaga yanda yake saluting awayar seka zata yana gaban me wayar kenan....be dade a kwanceba ya tashi ya fito palour din gidan nashi cikin sauri ya shiga kitchen ya kunna electric kettle din nashi daya cikashi da ruwan tea sannan ya debo kwai guda 4 ya soya omlet be wani bata lokaciba ya dawo dauke da tray din daya jero abincin nashi a ciki.....
A hankali yake yin breakfast din nashi sannan ya dauko remote ya kamo mbc Bollywood don mostly series movies dinsu baya wucesu yanason kallonsu sosai....

English wears ya sanya grey colour sun karbeshi sosai sannan ya debi wayoyinshi da trolly bag dinsa yayi waje

Manyan maaikatan gidan ne suke faman kwasar gaisuwa A farfajiyar gidan nashi ....yawan jama,ar daya hango suna faman tururuwa a bakin gate din gidan shiya tabbatar masa sa cewa lallai yan jarida ne suke jiran fitowarshi don haka yana shiga mota yayi wajen da gudu babu alamar tsayawa amma da yake mutanen sunada yawa yasashi tsayawa dole don idan be tsayawaba be iya bugesu

Aiko tuni suka fara zuro mick din nasu cikin motan nashi suna cewa major salman..major salman..major salman...

Dakatar dasu yayi yana nuna musu agogonshi alamar ya makara sannan ya bude baki cikin isa yace next time...dukansu suka ja baya ya rufe glass din motan nashi yayi waje...

Tafiyar tashi doguwan tafiyane don tun safe amma har magrib yana hanya be karasa inda zashiba wani gari zashi achan gaba da agadez don daga agadez din kusan tafiyar awa 5 ce babu abinda kakeji a motar se karar kida da kamshi me dadi da yake tashi da haka harya karasa gidan sarkin garin....

Ya samu kulawa da tarba ta musamman da masauki mekyau don seda safiya ne sarkin yake masa bayanin dalilin kiran nashi akwai wasu yan bindiga dadi da suka takurawa mutanen yankin nasu musamman bangaren dajin garin suna tare buzaye da sadakar yalla masu zaune a daji su kwace musu rakumansu da dukiyoyinsu su gudu suna yi musu kisan wulakanci.....bayan duk yaji bayanansa ne yake tabbatar masa zeyi iya bakin kokarinsa don ganin an samu saukin alamarin

Babu damuwa ranka ya dade insha Allah i will try my best.....da hka sukayi sallama ya juya ya dauki hanyar komawa gida..

Gudu takeyi sosai kamar ranta ze fita wasu mutanene suke biye da ita suma suna bin ta da gudu...kamar baze tsaya ba se kuma yaga yarinyar was so young zasu iya cutar da ita don haka yai saurin parking ya fito a guje yasha gabansu...kallo daya yayi musu ya tabbatarda sune criminals din da mai martaba yake zance da sauri ya daga kujeran motanshi ya dauko bindiga ya fara harbinsu tuni suka watse ita kuwa yarinyar da gudu tayi gurinsa ta tsugunna gabanshi da irin muryanta na sadakar yalla ta fara magana....

Ka shemakeni don Allah...zashu kachenine shun kache min ammi na sannan shun harbi abu a hannunsa da yayana sun kwashe mana chaniya da rakuma don Allah ka shemakeni nima karsu kacheni....

Tunda ta fara magana yake kallonta duk da cikin duhune amma ya fuskanci karancin hankali da shekaru a tareda yarinyar

A nutse ya kalleta yace yanzu inane gidan naku

Tace gidanmu yana gabas da wancan tankin sojijin

Ok to shigo motar muje gidan

Gudu sukeyi a motar sannan suka karasa gidan cikin sauri gaba daya jini ne kwance a gidan don duk yankan rago akayi musu banda babanta da aka harbeshi shima numfashi ykeyi sama sama

Da gudu ta karasa tana kuka abu don Allah karka mutu banida kowa sekai abu ka tashi wani ze shemake mu abu da sauri ta kamo hannun salman ta dora akan na mahaifin nata da yake kakarin mutuwa ya rike hannun salman gam sannan ya fara magana

Bawan Allah ka shemakemu ka rufawa yarinyar nan asiri karikeshi amana bashi dakowa se kai se Allah daya halicceshi gatanan sunanshi suhana na daura maka aure da suhana yanzunan Allah ya baku zaman lahiya ka rikeshi da kyau kaje suhana ze gaya maka duk wani tarihin rayuwanshi......
Yana gama fadar haka ya cika ya amsa kiran mahaliccinmu.....

Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 5-10

*Na*
*Maman hanan*

Cikin tashin hankali salman ke jijjiga mahaifin suhana..please ka tashi wannan auren daka daura bame yiwuwa bane don Allah ka tashi..ganin bashida niyar tashi gashi dare yana sakeyi yasashi kallon fuskar suhana da take faman jijjiga mahaifin nata...wani haushi yaji ya kamashi yayi tsaki ya mike tsaye yace impossible i cant make it....ya juya yai ficewarshi amma yana zuwa bakin kofa seyaji ya kasa daga kafafuwanshi dole ya juya ya riko hannun suhana suka shiga mota suka tafi....

Tunda suka shiga mota suhana sam taki magana shima kuma dama ba maganar tata yake bukataba,haka sukaci gaba da tafiya har suka karasa gidan nashi se a lokacin ne ya tuna bashi kadai bane yake tafiya cikin motarba toshi yanzu ina zekai suhana?meze cewa jama a harsu yarda dashi idan suka ganshi tareda suhana a matsayinsa na babban mutu me fada aji a yankin nasu

Shahada yayi ya fito daga motar yana tafe tana binshi duk tsoro takeji a tarihin rayuwarta bata taba ganin gida makamancin gidan major salman ba balle har yakai ga gidan nashi.....Aljannar duniya kenan komai na gidan kalar diamond ne💎💎kuma komai diamond shape akayi a cikin gidan shiyasa gaba daya kalar gidan launinta daban yake se kayi tunanin ba,a duniya kakeba wani irin boom light diamond colour gidan yake bayarwa.....

Ganin zata bata masa lokacine yasashi riketa gam don kana hawa baranda din gidan lifter ne ze sadaka da palour gidan...komai na gidan major akwai security me karfi don se ya danna code a duk wata kofa dayazo shiga sannan take budewa.....a palour yasaki hannunta sannan ya nuna mata kujera yace ta zauna amma seta zauna akasa seda yayi mata wata mummunar tsawa sannan ta hau tazauna

Wanka ya shiga ya fito yana fitowa ya cilla mata towel ya nuna mata toilet yace ta shiga tai wanka kafin ya dawo...
Suhana kam tasha kauyanci data shiga toilet din don kasa yin amfani da shower din tayi seda ruwan sink ta samu tayi dabara tayi wankan wani kamshi taji yana tashi na dadadan sabulun da take wankan dashi ta jima tana wankan sannan ta fito daure da towel din ta maida hijabinta ta saka....

Be dadeba ya dawo hanunsa dauke da manyan ledoji da alama wani mall dinya shiga mafi kusa yayi siyayyar...kayan sawa ne da kayan kwalliya har takalma hatta panties seda salman ya siyowa suhana....ya nuna mata dakin da zata dinga kwana da komai

Da kanshi ya dafa musu abinci ita dai banda mamaki babu abinda takeyi....shi wannan mutumin ina matarshi?inma bashida aure to ina yanuwanshi da iyayensa tambayar da take tayi kenan a zuciyarta amma babu amsa....seda taci abinci sosai sannan ta kwanta shima ya nufi nashi dakin a zuciyanshi yana ta tunaninn samun mafita...

*WAYE MAJOR SALMAN?*

Salman matawalle shine cikakken sunan nashi matashi wanda be haura shekara 30 ba a duniya,,mahaifinsa munir matawalle tsohon ministern kudi ne na nigeria tun salman na karami sam basuda jituwa da mahaifin nashi yaro ne wanda abin duniya be dameshiba sbd karfin addininsa sam be yarda aci haramun ko ayi cuta a gabansaba dalilin hakane mahaifin salman yake cewa yaro beyo halinsaba don mutum ne mara tausayin talakawa burinshi shi dai ya gina duniyarsa da girma lahirarsa ko oho shiko salman tun yana karami yaci alwashin ya zama soldier don ya hukunta duk wasu azzalumai......Matan munir matawalle su 2 ne haj zuwaira mahaifiyar salman da kuma hajiya rakiya da takeda yara shida....haj zuwaira tunda ta haifi salman bata sake haihuwaba babu irin gorin da ba,ayi mata ba dalilin haka yasa munir matawalle kara aure inda ba dadewa haj rakiya tazo ta fara haihuwa
Salman yaga soyayya wajen mahaifin nashi tun yana karami har ya girma mahaifin nashi yana mutukar sonshi tareda kashe masa kudi sedai lokuta dayawa salman na yiwa mahaifin nashi wa azi akan kudinnan bafa nashi bane na jama,ane shiko mahaifin nashi seya hau fada da haka suka taso cikin wannan yanayi.....wanda har salman ya zama major na sojoji kuma ya damka mahaifin nashi da hannunsa gurin hukumar EFCC aka rabashi da kudade masu yawa kuma akayi masa bore aka saukeshi daga ministan kudi na kasa aka bawa wani me adalcin....tun daga wannan lokaci mahaifin salman yayi masa korar kare sannan yaci alwashin se ya zama ajalinsa tunda shiyasa aka saukeshi...


Read / Download MAJOR SALMAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album