Join Our WhatsApp Group

DOCTOR SAGEER Complete Hausa Novel Document by DOCTOR SAGEER


DOCTOR SAGEER

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41375DOCTOR SAGEER

Reading Time: 3 Hours

Added On: 27, Dec 2023

Author: Nana Diso ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 703 475 7034

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 252.53 kb

File Type: txt

Views: 831+

Download: 418+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: .[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 1-5

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Fit...fit...Motoci ne suke faman hucewa A bak'in titi sanadiyar ruwa da ak'eyi. Wata budurwar yarinya ce k'e faman zanbada sauri har takai bakin wane gate, Nan ta tura A hankali saka kafarta da zatayi zuwa cikin gidan sai kuwa ji tayi an dak'a mata tsawa wacce sai da littafin hannun ta suka fad'i....

    " Kee yasmin??? Cewar matashin saurayin nan!
   
     " cikin tsoro da kuka tace kayi hakuri yaaa...

      " Idiot kawai kalli ki sai kace almajira uban ina kuma kika tsaya...

   "Cikin hawayen da batasan dashi ba tace kayi hakuri wallahi lesson na tsaya...ta kalli jikinta da gaba daya ruwa ya jik'ata....

    " Wani mugun tsaki yajaaa sannan ya nunata da hannu ..Gashi yanzu na makara sai shigen son makarantar tsiya babu abunda kikasani to bari kiji a sannu sai kin daina makarantar sai dai kidinga wankau...

    " fuskar ta cike da damuwa tana shiga tsakar gidan sai tayi karo da dr cikin hanzari tayi baya tana danAllah kayi Hakuri wallhi bansani ba shiyasa...

    " Murmushi yayi yace yasmin sarkin tsoro,can kuma yace yaya akai ruwa ya zaneki???

    " Shiru tayi hawaye na bin fuskarta babu ta yadda zatace masa su abida ne sukace bazata hau musu mota ba..

    " Ki daina kuka kinji yasmin kinga kinfara zama 'yan mata kada ayimiki dariya kije ki canja kaya kinji idan nadawo zanbiyo dak'in mama kinji?

    " Har cikin ranta tanajin dadin kalaman dr Amma kuma k'annan sa basa sonta kwata kwata...

    " Wayar sa ce ke faman ringing cikin k'idan my love! Cikin nutsuwa ya dauka tare da fad'in Assalamu alaiki!..

    " Cikin wata lausassar muryar ta tace bak'asona dr sageer yau 3days baka kirani ba sai dai kullum na kirawo ka? Ta saka kuka..

   " Haba Ramlat menene abin kuka to bayan kinfi kowa sanin ina mutukar sonki!..

    " Amma kullum kake nunamin aikin ka yafini mahimmanci gaskiya ni gwara ayi auren a huta wannan soyayyar taka kada ta salwanta ni...

    " Dariya yayi yace oyaa to kiyi dariya naji!..

    " Dariya tasaka sannan tace bari naje hajiya na kirana mayi magana anjima..

   " Badamuwa ramlat ki kula da kanki kinji?

   " i love u my doctor!!!

" baby same..cikin fara'a ya katse wayar tare da shiga cikin motarsa yana 'yar dariya..

   
  Juya wa yak'eyi akan laushashiyar kujerar sa cikin sanyin office ya K'alli halifa yace kasan me bro??

   " inajinka?

" yasmin din mama ina bala'in son yarinyar nan naso aci ta isa aure da kawai sai dai nafara neman auren ta....

     " Halifa ne ya ajiye wayar hannun sa yace Doctor sageer kenan ka fiye barkwanci wallahi!!! Hahaha in banda idonka ya rufe ina kai ina yasmin a jss 3 fa take kai kuma kana babban likita mai aji wanda duniya tasan da zaman sa...Kuma yaudarar barister ramlat zakayi ???

   "  Kai Abokina nagartar mace ake dubawa ba kyau ba, addinin yasmin ko mu da muke manya iya abunda mukeyi kenan,ga nutsuwa kalmar hakuri ta aure bak'inta duk gidan nan private school sukeyi amma baffa dan bashida kudi babu wanda yace bari yasaka yasmin a irin makarantar yaransa sai a gawamnati ya sakata kuma bata taba damuwa ba... maganar ramlat kuwa ka ajiyeta gefe!!!

    " Tabbas hakane daman ai ka guji wanda kayiwa alheri...

    " Let talk later ina da cs yanzu...

    " To Dr see u later...

Yasmin yasmin yasmin bakyajina ne??

   " Baffa sallah nakeyi...

" yauwa yarinyar kirki inafatan mahaifiyar ki tagaya miki sak'ona???

     " A'a bata gayamin ba..

  " To yasmin ke yarinya ce mai tarbiya kinga kuma bani da wata d'iya sama dake yar uwarki tayi nisa tana aure a benin kullum tunani na akan naga kinyi karatu ne...

    " Cikin murmushi tace baffa kadaina damuwa dani wallahi banda wata matsala kai dai kacigaba da yimin addua...

    " Yasmin inason zan kaiki boarding nasamu kudi Akallah wanda har kigama zan iya biya zuwa litinin sai ki shirya d'an Alhaji sule da yaranshi zaku tafi...

    " Toh baffa Allah yakara budi nagode zanyi yadda kace...

     " Dak'in mama tashiga ta rungumeta tana kuka dagota tayi tace daina kuka auta babu yadda banyi da mahaifinki ya kyali k'i agida ba,...

    " Mama banason nabarki, ke daya duk gidannan basason mu kar susaka miki damuwa...

    " Dariya tasaka tace haba auta babu mai samin damuwa kikwantar da hankalin ki kinji...

    " Tohm bari naji gurin Anty zulai...

     " Tunda tafito maryam ke faman hararar ta har tazo hucewa ...

     " Sannu da gida maryam ya makaranta...

    " bansaniba 'yar talakawa kudin makaranta ma ubanki yakasa biya miki haka zaku kari ai sai dai talauci ya kashe ku...

    " Adaidai lokacin dr sageer yayi parking motarsa maganar data duk'i kunnan sa shine baban ki ma sai mun sa an koreshi a gadi...

     " Yasmin ce tace Ai shi arzuki bako ne wanda baizo masa ba shine bai san saba wanda kuwa yazo masa to yasan zai kari, kuma duk iskancin ki kada ki kara saka iyayena tunda naga ke islamiyar taki bata amfana miki da komai ba, banza mara hankali kawai...

    " wani dadi yaji ashe yasmin ta iya fada lallai...

    " Maryam ce ta wanka mata mari wanda sai da dr yajiyo...

  " Sai da ya kifa mata mari har guda 3 sannan yace baki da kunya ke?? to nakara ganin kin zagi yasmin Allah sai nayi miki illah shige kibani guri nonsense kawai...

     " Kuka tasaka ta shige tana wallahi sai na gayawa mamee...

     " Hannun yasmin dr ya riko yace yi hakuri 'yar kanwata sannan yasa hannun sa ya goge mata hawayen fuskarta sannan yace muji nasiyo miki laptop saboda naga kina kokari a makaranta...

   " A'a ni kabarshi nagode sannan ta shige gurinsu...

   " yajima yana kallonta sannan ya tafi ....

  
  Kasancewa yau litinin yasmin ta shirya domin tafiya boarding sai kuka takeyi har suka tafi itada baffa mama sai addua takeyi mata...

   " yau da daddare dr sageer yace mama ina auta ne??

   " Auta tayi makaranta kwana ai..

  Boarding??? Why aka kaita haba mama..

    " kayi hankali kada baffa yaji...

   " Fita yayi cike da damuwa zuciyarsa sai zugi takeyi masa gashi ko zai mutu baffa ba zai kaishi makarantar ba...!!!yanzu yaya zanyi da kaunar yasmin???

ASALIN SU...

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 5-10

*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

http://deejarhberver.wordpress.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Alhaji Rabiu ba fulatanin mutum da yazo daga garin bande zuwa garin Adbas ya k'anzo garin domin k'awo dabbobi cikin hukuncin Allah tun yana zuwa sau biyu a wata har kasuwancin sa ya habaka ubangidan sa yace zai dinga yimasa zaman kanti anan ne yabar kiwon da yakeyi..

Cikin shekaru shima Allah ya buda masa sai yasamu daukaka takai baya bada kaya sai dila dila, sanadiyar matansa biyu a lokacin hajjo da asabe kowaccen su tanada yara bibbiyu acikin yaran hajjo akwai kawu maikal da suwaiba, ita kuma asabe tanada haruna da isa kowannen su yafi shekara 20 a lokacin mahaifin su rabiu yana bala'in jidasu har takai mutane suna musu kirari da 'ya'yan gata. sanadiyar garin sakoto dayaje daurin aure sai Allah yasa yaga hajiya sadiya har Allah yasa suka dai daita akayi aure yakawota cikin gidansa, Nan ne fa mata biyu suka addabeta har abun yafara isar ta.

Lokacin da ta samu cikin baffa tundaga lokacin Alhaji rabiu yake mata hidima abun yana bawa maikal da haruna haushi har takai suka bayyana bayan lokuta ta haihu bata kuma dade ba Allah yayimata rasuwa tabar baffa a hannun su asabe babu irin azabar da baisha ba mahaifinsu kuma yana sansu bayan wasu shekaru kowannen su akayi masa aure, bayan shekaru sai aka shirya tafiya zuwa wata kasar inda maikal da iyayen nasu gaba daya suka rasu... tunda lokacin haruna da isa suka kwashe gadon suka barwa baffa dan wani part ita kuma suwaiba suka bata dubu 50...

Hajiya suwaiba itace babbar 'ya agidan tayi auren fari sai Allah yayiwa mijin rasuwa daga nan sai tadawo gidansu tare da d'anta sageer yasha fama kalakala amma haruna ya daukeshi lokacin da tayi aure,ta kan cewa baffa kadaina damuwa da lamarin yan'uwan domin su sunyi asara...

Haruna bayan sageer dayake roko akwai yarsa mace abida da maryam sukenan Allah yabashi amma sai mugunta da zalunci atattare dasu ga kuma borin kudi yadda kasan babansu ke bugawa...

Isa kuma yanada yara 3 akwai bilal akwai jafar sai kuma kubra,duk cikin yaransa yana sangarta bilal shine sanadiyar lallacewar shi baya ganin kowa da mutunci sai bin mata da kashe kudi...

Baffa kuwa yanada yara biyu Aisha itace tafarko tun tana karama hajiya suwaiba ta dauketa ta tafi daita benin acan ma ta aurar da'ita, sai yasmin daga nan matarsa bata kara haihuwa ba...

Baffa yasha wahala kala kala arayuwarsa bama lokacin dayace sai yayi karatu dan kudin da yake samu a makaranta da hidimar iyalai yake tafiya, yan uwansa haruna da isa ko kallon arzuki basa yimasa kuma Allah daya bashi yasmin babu ruwanta ba kamar yaransu ba abun yakan basu haushi wataran ko kudin zuwa wajen gadi bashi dashi, watarana suna zaune da mama yake cewa wai ace ni mai kwalin masters amma gadi nakeyi sai yasa kuka...
Yasmin sau ta kalleshi tace baffa Ai lamarin na Allah ne inshaa Allahu wataran sai kazama wani kamar yadda yan uwanka suka zama wasu...

Yakanyi dariya yace Yarinyar kirki Allah yasa, mama tace ameen...

Yasmin yarinya ce fara amma irin siraran nan, ga kuma hanci kina ganinta kinga jik'ar ba fulatani, Babu ruwanta tun tana karama kawayen ke ce mata 'yar aljanna saboda hakurinta, lokacin da take aji biyu a islamiyya kwata kwata bata gane karatu hakan ya kansata kullun cikin kuka har mama ta gane sai tafara tambayar lafiya?? Ta sanar daita halin da take ciku daga nan tace ba kuka zakiyi ba addua zaki dingayi nima zan tayaki inshaa Allahu zaki fara fahimta, "Allah to yasa kamar wasa tana zuwa makaranta tana addua cikin shekaru 2 sai gashi tafara karbar kyauttuka, su abida maryam kuwa da kubra sai ma tsanarta da suka karayi haka ta dinga rayuwa cikin kuncin rayuwa. A kwai lokacin da bata da ikon zaman gate anayi mata karatu sai kiga bilal yazo ya zaneta ita kuma aduniya ta tsani bilal saboda zaluncin sa,Dr sageer kuwa irin hidimar da yakeyi masu takanyi masa Addua sosai duk da karancin shekarunta amma bata sakewa da kowa, tana kallon yaran gidan za'aja su amota amma ita sai dai akafa,tana makatantar gamnati amma su sunayin ta rabin million kullum burin su su zageta dalilin haka mahaifinta yace zai kaita boarding ko tasamu ta huta, Mahaifiyarta taso ya barta ta cigaba Amma ina yaki hakan nasa zuciyarta k'una...

Cigaban labari...

Dr sageer ke faman juyi akan kujerar sa ta office babu abunda ke damunsa irin tafiyar yasmin kai yanzu ba zanga kyakyawar fuskarta ba kullum ga lafazunta mai sanyaya zuciya, har khalifa ya zauna akusa da mashi amma bai kulaba...

" Haba doctor wannan tunani ince dai lafiya???

" Jiyowa yayi yace ina kuwa lafiya? Baffa ya kai yasmin makaranta...

" To a gaskiya dr zangaya maka gaskiya ka ajiye maganar yasmin a agefe kafara zancen bikin ka...

" Hmmm daman ai na lura kafi son ramlat, to bari ingaya maka yasmin tsoka tace babu ta inda zamu rabu ni inaso ka binciko min boarding din da suka tafi...

" ai nasanta ko yabzu sai na rakaka sai dai nisanta...

" yanzu kayi magana mutumi na ina godiya ran sunday maje...

Yasmin dake aji azaune tana karatu kamar daga sama taji anyi mata sallama tana daga kanta taga wata yarinya ce da bata huce suyi shekaru daya ba cikin murmushu ta amsa mata sallamar...

" sunana yusra nima last week nazo skull dinnan kuma naga babu ruwanki ga son karatu ko zamu zama kawaye?

Murmushi tayi tace ni yasmin sunana, ina kuma fata zamuyi kawanci nagari??

" inshaaAllah daga nan suka kullah kawance...

Mumy ce tafito zata tafi office tace dota?

" Tace yes mum har kinshirya?..

" Eh ramlat idan dr yazo kya gaishe shi..

" ohh mum bakyason dr sageer dina wallahi....

" haba my barister ni kuwa nake son sa...

" rungume mumy tayi tace har naji dadi lurv u momma...

Yau sunday kowa acikin makarantar ana kawo musu visiting kowacce tana shigowa da abubuwa amma yasmin tana gefe bata cewa komai, alokacin dr yazo yana zuwa yace yar aljanna kamar daga sama ta ruga ta rungumesa tace yaya??

" Dr sageer ne yaji dadi yadda tayi murna da zuwansa cikin murna yace yakike kanwata?kina dai karatun ko??

" inayi sosai wallhi ga mama da baffa?

" Suna gaida ke! Yasmin yasmin?

'Naam ?? " kinsan ina sonki ko?

" eh tace.." to kada ki kula kowa kinji da niyar soyayya kinga yanzu karatu kikeyi...

" Tohm bazan kulaba, nagode da zuwanka lokaci yayi..

" sawa yayi aka shigo masa da abubuwa da yakawo masu yawa sannan yace duk nakine..

" Nagode Allah yabiyaka sai anjima..

" har tayi nisa yace yasmin??.

"Naam..

Kikula da kanki kinji?

" Tohm tace sannan aka shigar mata da kayan..

Tundaga nan ya huce gidansu barister ramlat cikin fara'arsa yashiga palour tana zaune tayi bala'in kyau, yanayin saĺlama ta miki...

" to bakin munafuki bakin dan iska yaudarata dakakeyi to Allah ya rufamin asiri murabu tu daga yau...

" haba ramlat me yayi zafi haka??

" dan iska mai bin mata fitar min agida...

" kifa mata mari yayi see this stupid kika kara jifana da zafaffan kalaman ki wallhi sai na hukunta ki, kuma daga yau babu ni abu ke sannan yafita rai abaci......

Cikin kuru ruwan kuka ta nunashi daga nan kuma tafara nashiga uku inason ka sagee....

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_

_Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

*i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 10-15

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Kuk'an da barister ramlat ke famanyi yasa gidan gaba daya ya dauka, adaidai lokacin da momy take kokarin shigowa gidan sautin kukan 'yarta tace yakara firgeta ta cikin sauri da hanzari taisa cikin gidan nan ta tarar da ramlat a shaime tana wasu irin maganganu, dotar??? What wrong with you? Ya'ilahi.....

    " Rungume mumy tayi sannan tace baya sona mumy yace mun rabu wallhi zaki'iya rasani akan dr sageer,mumy please kibashi hakuri kuskure nane...

  " Ya'ilahi me kikayi masa? Always ina...


Read / Download DOCTOR SAGEER

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album