Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

DUNIYA MAKARANTA Book 1 Complete Hausa Novel Document by DUNIYA MAKARANTA Book 1


DUNIYA MAKARANTA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9054



DUNIYA MAKARANTA Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 04, Jul 2024

Author: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08064661666

Book License : Free

Category: Education

File Size: 47.41 kb

File Type: txt

Views: 357+

Download: 111+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: DUNIYA MAKARANTA

1
(Hikimomi 1-250)

Rubutawar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1

Bugawa da Yadawa:
Bugu na biyu 1437H/2016
Haqqin Mallaka @ Mawallafi

mansursokoto@yahoo.co.uk
isbn 9960-49-972-3

2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gabatarwa
Yabo da godiya da’iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama su dawwama ga
fiyayyen halitta, shugaban Annabawa kuma jagoran Manzanni Annabinmu
Muhammadu, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.
Waxannan kalmomi na fito da su ne daga cikin Alqur’ani da Hadisai da
maganganun masu ilimi da basira da fahimtar rayuwa na da, da na yanzu. Na kuma
rubuta su ne musamman don amfanin kaina game da darussan da wannan rayuwa
take xauke da su. Kuma tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv ita ce take da
yaxa su a kullum safiya ta Allah domin amfanin jama’a. Haka kuma ana yaxa
waxannan kalmomi masu amfani a shafinmu na Minbarin Malamai wanda yake
group ne na faxakarwa a Whatsapp wanda ya qunshi darussa da fa’idoji masu
amfani.1
Babu shakka, wannan littafi ya samu karvuwa a fitowar sa ta farko wanda ya sa har
aka yi ta maimaita buga shi sau da dama, wasu kuma suna raba shi a wuraren
tarurruka da bukukuwan aure da makamantansu. Wannan ya daxa ba ni qwarin
guiwa wajen ci gaba da fito da waxannan Hikimomi masu amfani. Ga shi yanzu
wannan bugu na biyu zai fito a tare da littafi na biyu. Bayan haka kuma in sha
Allahu za mu buga littafin “Abokin Fira” wanda yake bayyana darussan “Duniya
Makaranta” a cikin qissoshi na tarihi masu ban sha’awa da sa nashaxi da ban
al’ajabi.
Baban Ramla
A Sakkwato
27 ga Safar 1437H

1

Waxanda suke son shiga wannan zaure za su iya aika lambobinsu ta Whatsapp
zuwa ga 08064661666. Haka kuma masu buqatar wannan littafi suna iya bugawa
ko su aiko saqo zuwa ga wannan lamba: 09030606028
3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

1. Sauqi yana tare da tsanani. Mai haquri yana cim ma daxi. Mai kyauta ba ya
rasawa. Kowa ya ji tsoron Allah, Allah zai yi ma sa mafita. Manta da
damuwa ka fuskanci rayuwa. Kowa ka gani a duniya akwai abin da ya dame
shi.

2. Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori.
Wannan shi ne halin mutanen kirki!.

3. Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka to ka yi sadaka daga cikin
haqoranka. Murmushi ga fuskar xan uwanka shi ma sadaka ne.

4. Ba kowane aiki ne qarfi yake yi ba. Wani aikin haquri ne yake yin sa!

5. Yaro akwai lokaci da qarfi amma babu kuxi. Dattijo akwai kuxi da qarfi
amma babu lokaci. Tsoho akwai kuxi da lokaci amma babu qarfi. A rayuwa
in ka samu wani abu ne za ka rasa wani. Cikakkiyar ni'ima kawai tana
aljanna. Ya Allah ka ba mu aljanna.

6. Maqiyanka mutane uku ne: Mai qin ka, da mai qin masoyinka, da mai son
maqiyinka. Mai son uwa dole ne ya so xanta.

7. Macce ce ta haife ka. Macce ce ta yi rainon ka. Macce ce kuma
uwargidanka. Ta ya ya za ka raina macce?

4

8. Uwa ita kaxai ce take manta kanta a addua, ta shagaltu da yi ma xanta. Mu
so iyayenmu.

9. Abubuwa uku ne su ke kawar da bala'i: Sadaka da Addu'a da Sada Zumunta.

10. Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da Lokaci da Mutunci.

11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar
magani suke, akai akai ake buqatar su. Wasu kuma kamar abinci suke, a
kullum dole ne a neme su. Yi qoqari ka zama wanda a kullum ake neman sa
saboda amfaninsa.

12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne ko
Mala'ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka.

13. Ana yin da-na-sani ne a kan magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba.
Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin magana ba.

14. Kada ka damu da masu qulla ma ka sharri, duk iya qoqarinsu ba su wuce
zartar da qaddarar Allah a kan ka.

15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne:
a. Fadin gaskiya
b. Cika alkawari
c. Riqon amana
d. Jin tausayi da
e. Kyautata ma mutane.

5

16. Rayuwa kamar kasuwa ce. Ka zagaya ka tsinci duk abin da ka ke so. Idan
ka zo fita za ka biya duk abin da ka xauka.

17. Wanda bai iya karatu da rubuta ba jahili ne! Amma wanda ya fi shi jahilci
shi ne wanda ya san gabas amma kuma ba ya salla!!

18. Idan ka mutu an rufe labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a
bayanka:
a. Ilmi da
b. Haifuwa da
c. Aikin alherin da ka shuka
19. Abokai iri uku ne:
- Mai son ka don abinka.
- Da mai sonka don kanka.
- Da mai son ka don kansa. Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu.
Idan ka rasa zai yi ko-sama-ko-qasa.
20. Idan ka yi fushi ka kama bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a
lokacin, Shexan ne!

21. Kada ka bar aikin yau ka ce sai gobe. Gobe ai ta mai rabo ce.

22. Kada ka zolayi masu aikata zunubi. Dukanmu muna cikin suturar Allah ne.
Amma ka yi ma su nasiha da lafazi kyakkyawa. Duk masu laifi ba su kai
Fir'auna ba, kuma duk masu wa'azi ba su kai matsayin Annabi Musa (Alaihis
Salam) ba. Amma Allah ya ce da shi: Ka gaya ma Fir’auna magana mai
laushi, wataqila zai karvi wa'azi ko ya ji tsoron Allah.
6

23. Huda-huda tsuntsu ne da ya kawo rahoto, ya isar da saqo, ya nuna kishin
addininsa. Kada ka bari tsuntsu ya fi ka son Allah da kishin addininsa.

24. Abu Jahali cikakken Balarabe ne, mai kuxi, kuma Baquraishe. Amma yana
wuta. Bilal talaka ne, kuma bawa ne, baqar fata. Amma yana tare da Manzo
a aljanna. Aikin kowa shi yake fisshe shi.
25. Idan namiji bai ji daxin aure ba zai yi tunanin qara mata ne don ya samu jin
daxi. Idan kuma ya ji daxi zai yi tunanin qarawa don ya qara jin daxi. Mata
ku yi haquri. Qarin aure xabi'a ce a cikin mazajenku.

26. Ba zaka iya yin hukunci na gaskiya a kan mutum ba, sai idan ba ka da
buqata zuwa gare shi. Wanda ya miqa hannu bai miqe qafa! Idan baki ya ci
dole ne ido su ji kunya!!.

27. Maganar gaskiya ba lalle ne ta zama mai daxi ba, amma tana da kyau da
amfani.

28. Duk lokacin da zunubinka ya fara damun ka to, ka riga ka kama hanyar
tuba.

29. Zuciyarka ita ce adireshinka. Harshenka shi ne ma'auninka. Gyara zuciyarka
sannan ka kula da harshenka.

30. Haquri iri biyu ne: Haqurin abin da kake so idan ba ka same shi ba, da
haqurin abin da ba ka so idan ya same ka.
7

31. Idan kana tafiya babu takalma watarana za ka gamu da wanda yake tafiya
ba qafafu. Kalli wanda ka fi shi a kullum sai ka gode ma Allah!

32. Rana a cike take da wuta mai zafi a cikin ta, amma haskenta ne take ba mu.
Ba abin da kake da shi ne yake da muhimmanci ba, abin da kake bayarwa.

33. Yana da kyau ka yafe idan aka yi ma laifi. Abin da ya fi haka kyau shi ne ka
manta da laifin da aka yi ma ka.

34. Ba za ka sauka tashar nasara ba sai ka hau motar haquri da qoqari da
sadaukarwa.
35. Wani ya iya karanta komai amma bai iya fayyace abin da ke cikin zuciyarsa
ba. Yana gane aibin kowa amma bai iya ganin nasa. Laifi tudu ne, sai ka
take naka ne kake hango na wani.

36. Wanda duk ya yabe ka da qarya watarana sai ya zage ka.

37. Namiji ba ya raki! Jarumi ba ya ja da baya!! Fara ko ta mutu akwai idanu!!

38. Da yawa na nesa da kai zai amfane ka, na kusa da kai ya cuce ka. Kusancin
zuciya shi ke da amfani ba na gangar jiki ba.
39. Duk qofar da ka gan ta a rufe tana da mabuxi. Kada ka saki baki kana jiran
ta buxe da kanta!

8

40. Komai a duniya yana da mabuxi. Mabuxin ilimi shi ne tambaya. Mabuxin
nasara haquri. Mabuxin arziki tsoron Allah. Mabuxin zaman lafiya adalci da
gaskiya.

41. Hattara da mabuxai guda uku:
- Fushi, mabuxin azaba.
- Tsoro, mabuxin fitina.
- Kwaxayi, mabuxin wahala.

42. Babban mabuxin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi matsalolinka za
su kau, damuwarka za ta gushe, sauqi daga ubangiji zai zo maka.

43. Kafin ka yi tambaya ka yi tunanin amsar da za a ba ka.

44. A cikin mutane akwai wanda ya cancanta ka jira shi komai daxewar sa.
Wani kuma sam bai cancanta ko da ka waiwaye shi ba.

45. Komai ya fi kyau idan yana sabo amma ban da imani. Shi kam ana qara
daxewa yana qara kyau da qwari.
46. Duk yadda ka yi sai wani ya zage ka. Manta da mutane ka yi komai yadda
ya kamata!

47. Mutane da yawa ba su iya bayyana uzurinsu. Rinqa ba su uzuri ba sai sun
faxi ba.

9

48. Duk abin da za ka yi ka yi shi da zuciya xaya.

49. Kowa ya iya haquri ya iya komai.
50. Idan Allah ya ba ka lafiya ya ba ka komai.

51. Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. Kada yau ta sha ma
kai, domin gobe ma rana ce.

52. Yafe ma wanda ya cuce ka ni'ima ce....


Read / Download DUNIYA MAKARANTA Book 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album