Join Our WhatsApp Group

SUDA DAN KANE DILLALI Complete Hausa Novel Document by SUDA DAN KANE DILLALI


SUDA DAN KANE DILLALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22079



SUDA DAN KANE DILLALI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Unknown ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 119.4 kb

File Type: txt

Views: 687+

Download: 242+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: SUDA-01

ƊANƘANE DILLALI

Da mutum ya saba wannan alkawarin gara yayi jinyar wata guda domin wannan kaffara ce.

Wanda suka gane Ɗanƙane da sun dau bashinsa daya tura ɗansa sai su baiwa Yaron kyauta kamar sule biyar ko naira daya in Yaron ya dawo da wannan albishiri ko babu kudin Ɗanƙane dillali bazai damu ba don yasan ya karu. In kuma da kansa yaje neman mutum da an fito da abinci musamman ma fura don ita yafi kauna aduniya sai ya manta da zancen bashin ya tsugunna ya sha hawaye na zuba yana santi kamar mahaukaci domin bukatarsa ta biya ya samu bati siddan.

Shi Ɗanƙane dillali bama sai yana bin mutum bashi ba duk inda yasan zaije ya ƙoshi Kokuma ya sami wani abu saiya kashe sana'arsa ta dan wani lokaci har sai ya sadu da biyan bukata.

Wanzami baya san jarfa amma shi in ka je gidan sa ko ruwan sha bazai ma tayi ba in kuma zaka wuni dashi ko gutsuren goro bazai bawa mutum ba in kuma mutum da niyyar kwana yaje gidansa shi
Sai yace lokacin zaiyi tafiya dole mutum ya juya ya kama gaban sa.

Shikuma gogan naka duk inda yasan zashi ya sayi abinci da kudin sa to ranar saiya kwanta da niyyar azumi dashi zai tashi a bakinsa in ya je yaga sabanin abinda yake zato yaga sha shida ta arziki saiya karya azumin.

Saboda fahimtar da mutane sukayiwa Ɗanƙane dillali abokansa da suke wasa da sun ganshi sai su rikayi masa kirari.

KIYASHI JAWO ABUNDA YAFI KARFIN KA

KIFI WA YAGA SAWUN KA

HANKAKA MAI DA ƊAN WANI NAKA

KURUNGU MUGUN KIFI KADA NA GANIN KA YA KWANA DA YUNWA

SAKAINA MAI IYA RUWA

KASKA RAƁI MAI JINI

DILA BAKA SAN TSANANI

CHILAKOWA MAI CINIKIN LALATA

TSUMMA MAƘUNSHIN CUTA

Ku Cigaba Da Kasancewa Da YARIMA GANGARIYASUDA- 02

ƊANƘANE DILALLI

Allah wadaran naka ya lalace al'amarin Ɗanƙane Saidai a nema masa sauki don in mutum zai zargi ubansa yakuma mare shi ya dauki naira daya ya mika masa shikenan zai maida abun wasa koda baisan shi ba. Amma Ɗanƙane sai ya mika hannu ya karba ya wuce abinsa yana muzurai kuma maganar ta wuce har abada albarkacin wannan naira dayan.

Ɗanƙane dillali ba'a birnin Kano yake kwana ba amma yana riga kowa zuwa kasuwa wani lokacin sammakon sa na banza ne domin koda asuba yazo ya shimfida kayansa in ya sami wani wanda zai bashi wani abu sai ya nade ya Rika yawo da kayan sa akai. Tun da Ɗanƙane yake bai taba fashin zuwa kasuwa ba ko bashida lafiya sai yasan yadda yayi ya lallaba ya sami wuri ya kwanta yasan bazai koma gida haka ba.

Sama da shekara hamsin Ɗanƙane yake zuwa kasuwa kullum amma tunda yake bai taba biyan kudin mota daidai ba ko surukinsa ne yaran motar. Kuma tunda Ɗanƙane yake bai taba aikin banza ba a rayuwar sa domin ko kwatance yayiwa mutum yaga bashida niyyar bashi wani abu toh zai tambaye shi gutsiren goro.

Ta kai ta kawo saboda sanin darajar kudi da Ɗanƙane yayi in mutum yaga wando a jikinsa koda tsakiyar kasuwa ne in Ɗanƙane yaga ya sami riba yadda yake so saiya cire ya sayar shi kuma ya rika yawo daga shi sai babbar rigarsa da jamfar ta ko hanya ce ta kawo Ɗanƙane yaga a nata ciniki ya tsaya yaci la'ada amma shi tunda yake ciniki sama da shekara hamsin bai taba bawa wani la'ada ba akan ya bada la'ada Saidai cinikin ya rushe.

Duk wata hanya da Ɗanƙane zai bi ya sami kudi zai bi domin ko rigima ya tarar anayi shi baisan hawa ba baisan sauka ba kuma maganar ace takai ga shari'a in har mutum zai bashi wani abu ko da shine bashida gaskiya zaiyi Uwa yayi makarbiya yaje yayi shaida zurr Albarkacin Awalajar.

Kuda wajen kwadayi akan mutu in Ɗanƙane na tafiya yaga tsakuwa tafiye haske akasa saiya sunkuya ya dauka ya kulle a jakar sa in ya sami Abokan sa saiya tambaye su ta hanyar hikima ko wata abar amfani ce in ma kace bazai yi amfani ba saiya tambayi mutane kamar bakwai sannan zai jefar.

Al'amarin irin na Ɗanƙane sai shi ko hanya ce Ɗanƙane yake bin ta yau da gobe kuma yaga baya tsuntuwa akan hanyar hakika ya daina binta kenan har abada.

KIYASHI JAWO ABINDA YAFI KARFIN KA
Kiyashi mai jaye-jaye kiyashi yajawo abinda yafi karfinsa watarana wani dan fursuna ya gudu daga kurkuku daya taho hanya saiya zubar da kayan firsunan yayi nasa wajen shikuma Ɗanƙane hanya ta biyo dashi ta wurin saiya tsinci kayan saiya yaje gida ya wanke abinsa ran nan zai fita kasuwa saiya saka abinsa ya nufo kasuwar.

Kafin ya karaso kasuwa sama da mutum arba'in sun tare shi ahanya suna tambayar sa lafiya don sun ganshi da wannan kaya tun yana bayani har in ma an tambaye shi sai yayi tsaki ya wuce jama'a nayi masa dariya.

Dama kuma sarki ya baza yan doka da gandirobobi don akama wannan dan fursunan suna shigowa kasuwa babu wata wata sai suka danawa Ɗanƙane ankwa a hannu akai gaba dashi sai gaban alkalin lardin.

Jama'a kuwa da suke bin su Abaya sunfi tarin wata kasuwar

Suna zuwa aka shiga dashi da Gandirobobin da yan doka suka sarawa mai shari'a su ka mai bayanin ga danfursunan daya gudu an kamo shi.
Alkali na daga kansa sai suka yi ido hudu da Ɗanƙane. Alkali yace da yan doka su cire masa ankwa cire masa duk jama'ar sukayi shiru suna sauraren abinda alkali zaice.........

KUMA MASU SAURARO SAI KU JIRA MUJI ABUNDA ALKALIN ZAICE

DON NIMA YARIMA GANGARIYA BANSAN ME ZAI BIYO BAYA BA

ZAN SAMAR DA WATA YAR ƘWARYA KWARYAR GROUP A WHATSAPP KO TELEGRAM DON SAKA WANNAN LABARIN DAMA WASU.

MENENE RA'AYIN KU?SUDA-3

ƊANƘANE DILLALI

Jama'a sukayi shiru suna sauraren abunda alkali zaice.

Ga Ɗanƙane da kutse-kutse duk wani attajiri yasan shi Kokuma mai mulki saboda yanayin cinikinsa shi kuma alkali shekaranjiya suna tare da Ɗanƙane amma kuma ya ganshi da rigar fursina wacce ta nuna mai ita yayi shekara guda saura shekara guda.

Sai yace da yan doka a Ina kuka samo wannan bawan Allah. Sai yan doka suka ce a kasuwa.

Alkali kuma yasake waiwayawa ya kalli Ɗanƙane kamar baisan shi ba yace bawan Allah mecece sana'ar ka? Ɗanƙane yace dillanci alkali yace masa me ya kaika guduwa daga kurkuku bayan kayi hakurin shekara guda?
Ɗanƙane yace yallabai ai ni hanyar kurkuku ma ban taba bi ba don nasan babu wani alheri da zan samu sai tsiya.

Alkali yasan Ɗanƙane kamar yadda yasan yunwar Cikinsa yayi kamar yayi dariya Saidai ya cije yasake tambayar Ɗanƙane mai ya hadaka da kayan kurkuku?

Ɗanƙane yace ni dai sana'ata dillanci kuma ina saye da sayarwa Shine wani yakawo min kayan na saya da alkali yaji saiyace a koma da Ɗanƙane ko zai gane mutumin daya sayar masa Ɗanƙane yaga babu abinda yafi komai tashin hankali agare shi irin a koma dashi kasuwa da jama'a na binsa kamar ɓarawo daga can Ɗanƙane ya nisa yace yallabai kada na wahalar da kai nakuma wahalar da shari'a kayannan tsintar su nayi shekaran jiya ahanyata ta dawowa daga kasuwa.

Duk jama'a da suka ji bayanin Ɗanƙane wanda suka biyo ta hanyar suka shaida sunga kayan bayan wancan dan fursunan ya gudu da alkali yaji yayi ta dariya jama'a sukayi ta dariya aka saki Ɗanƙane aka karbe kayan sarki.
Mai rai baya rasa motsi duk da wannan kayan sun zame masa bala'i da za'a karba saida ransa ya baci daya rasa abunyi sai ya zare lawurjensa da wasu botira na rigar guda uku suma ya tsinke su.

Wani saurayi balarabe da suke tareda baba suda yace shin wannan bawan Allah Ɗanƙane dillali bai taba haduwa da wanda zasu cuce shi ba? Kuma yaya rayuwar sa take yana ganiyar kuruciyarsa koko haka ya taso da wadannan tsatstsauran dabi'ar?

Baba suda da yaji wannan tambayar sai yayi dariya yace da balarabe yaro kayi yanka akan gaba Danni nasan Ɗanƙane ni kuma zan bada labarin sa kuma an dace yau inada sha'awar hira kodayake nagaji tun safe Nake tsaye ban huta ba amma duk da haka bara na amsa maka tambayoyin ka kuma nama yi ma wasu bayanan da baka tambaye ni ba. MALLAM UMARU aboki ne ga baba suda shima suna tare ya kalli baba suda yace SUDA MAI YAWAN LABARI INDAI AN MATSE KA ASHA LABARI. sai baba suda ya yayi dariya ya dauko goro ya gutsura ya jefa a baki ya kalli balarabe yace kaji ko yaro.

YAWON DUNIYA MAKARANTA CE.
Dama tun tuni Ɗanƙane bashida kishin zuci don haka duk wata hanya da zai nemi abinci indai zaisha wahala baya so sai ya kewayeta in ma yafara sai ya watsar domin guminsa zai fita don haka yayi sana'a da dama babu wacce yake ganin ta dace dashi.SUDA-04

ƊAN ƘANI DILLALI

YAWON DUNIYA MAKARANTA CE.
Dama tun tuni Ɗanƙane bashida kishin zuci don haka duk wata hanya da zai nemi abinci indai zaisha wahala baya so sai ya kewayeta in ma yafara sai ya watsar domin guminsa zai fita don haka yayi sana'a da dama babu wacce yake ganin ta dace dashi.
Saboda kowacce sai yaga saiya motsa jikinsa in kuma ya hango mai sauki kamar dinki ko kashe kashen kayayyaki na zaune sai yaga baya iya jure zama kuma ba wata sana'a ce mai kawo kudi da wuri ba. Shikuma burin sa ya sami abin duniya a huce.

Rannan yana cikin wannan hali sai yayi tunanin ya bar garinsu ya kewaya duniya don zama kawai bazai fisshe shi ba yaje yayi sallama da iyalansa ya dauki hanya ya shiga duniya.

Acikin guzurinsa ya sayi babbar riga mai kyau ya tara kasumba yabar gemunsa yayi tsawo ya sami katon kandiri ya rike ga gafaka ya rataya a hannun dama kuma ga katon carbi yana ja yana daga kansa sama kuma yayi kumuryar da goro a baki yana zare idanu wai nan shi ala dole babu wasa fa.

Daya isa gari sai ya wuce gidan sarki ko Hakimi yasa ayi masa sallama da anyi masa iso yayi gaisuwa sai yace shine SARKIN SHARIFAN garin su ya ratso ne su gaisa zai wuce nan sarki da manyan attajirai da malamai zasuyi ta yi masa alheri in ya kwana biyu ya sami abin duniya sai ya wuce haka yake tayi har ya tara abin duniya yakawo gida ya ajiye yayi ta ci a tsanake jama'ar gari na gaishe shi don ganin ya sami sukuni dayaga abunda ya tara sun kare saiya sake shiga duniya acikin irin garuruwan da Ɗanƙane yake kai ziyara akwai wani gari wai shi GANDU Ɗanƙane ya sami karbuwa awannan gari jama'ar garin har sun san lokacin zuwan sa da lokacin zuwan sa yayi sai mutane suyi ta yi masa tanadi na kudi da tufafi da kayan abinci wanda za'a bashi sadaka Albarkacin kakansa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassalam.
Kamar yadda yake musu karya.

Da lokacin zuwan Ɗanƙane yayi sai yayi shiri kamar yadda ya saba ya tafi gandu yana isa mutanen gari sukan yi ta zuwa suna gaishe shi don neman tabararraki mata kuma dayake ba dama su gaisa dashi sai bin sa suke duk inda ya taka sai su maida kafar su a wurin Kokuma su Debi Kasar wajen ana jikawa ana sha har mara lafiya ake baiwa.

Ashe wani zuwan da Ɗanƙane yayi akan idon wani dan garinsu yake zuwa daya ga haka sai yayi ta mamakin mai yasa mutane suke girmama Ɗanƙane har yayi tambaya mutane suka gaya masa ai shine sarkin sharifan garinsu da wannan dan garin su Ɗanƙane yaji haka saiya ce ai nasan shi karya yakeyi magana kamar wasa sai tayi sama wasu daga cikin mutanen gari suka kama wannan mutumin sai gidan sarki don su na ganin kamar ma sabo yake saboda yace Ɗanƙane ba sharifi bane. Da sarki yaji wannan magana sai ya sa aka kai Ɗanƙane masaukin sa kamar yanda aka saba.

RAMIN KARYA KURARRE NE.
Sarki yasa a kaiwa Ɗanƙane sauka ta kasaita kamar da. Bayan duk jama'a sun watse daga fadawa sai sarki yasa aka kira masa nasa sarkin sharifan Kasar sa ya gaya masa cewa ya sami labarin sarkin sharifai Ɗanƙane karya yake amma yana son ya gwada shi don wasu lokutan masu tsaho da suka Shude agarin sharifai kanyi wasa sai a hura wuta gan-ga-ganga suyita shiga babu wani fargaba jariri ma indai sharifin ne sai a jefa shi babu wani abu da zai same shi.... Da sarkin sharifan gandu yaji bukatar sarkin su saiyace wannan ai mai sauki ne bara yanzu in zan koma gida sai in bi ta masaukin bakon namu in shaida masa gobe yafito da shirin sa dan muyi wasa a kofar fada......

GOBE FA AKWAI KALLOSUDA-05

ƊAN ƘANI DILLALI

Bara yanzu in zan koma gida sai in bi ta masaukin bakon namu in shaida masa gobe yafito da shirinsa dan muyi wasan a kofar fada....

Da sarkin sharifan GANDU yayi sallama da sarki saiya biya ta masaukin sarkin sharifai dankane yatarar dashi ya fara gyangyadi saiyayi masa sallama sarkin sharifai dankane ya amsa yatashi suka gaisa da dare yafara sai sarkin sharifan gandu yayi sallama da dankane zaifito don yabar shi ya dan runtsa har zai tafi saiya dawo da baya yace da dankane nayi wata mantuwa dankane da fara'arsa yace wace mantuwa kayi sai sarkin sharifan gandu yadawo suka zauna yacewa dankane dama ba wata mantuwa nayi muhimmiya ba abinda yasa na dawo tuntuni nake so inyi maka magana naga tun lokacin da kake zuwa nan garin baka tarar damu muna dan wasanni ba da nuna baiwar da Allah yayi mana dan haka nake so gobe da safe in Allah ya kaimu zamu karasa kofar fada inda zaka debewa jama'a kewa don yanzu nasa mutane suyita hura wuta har gari ya waye da dankane yaji wannan batu sai hankalinsa ya tashi amma saiya cije ya daure yace ai babu komai Allah ya kaimu wayewar garin.

Sarkin sharifan gandu yayi sallama ya fice
Duk gajiyar da dankane yayi da barcin dayake kansa dayaji wannan batu saiya wartsatstsake ya tashi zaune yanata kulle kullen wacce zata fishshse shi yayi tunanin ya gudu acikin daren yaga yayi abin kunya aduniya don za'a gane inda yake yayi tunanin in gari ya waye bai shirya ba yaga wannan lamari ne da baya bukatar shiri yaga kuma wannan lamari ya wuce ayi shahada dan sai a halaka. Sarkin sharifai dankane yana zaune yana tunani sai yaji zakaru suna cara saiya mike tsaye don zama bai same shi ba sai yayiyo waje da sauri da ya fito kofar gida saiya hanga kofar mai gari yaga wuta nata ci ganga ganga babu kakkautawa ga kuma samari majiya karfi sai kayan itace suke yiwowa ana ta zubawa acikin wutar babu sassautawa kamar wanda suka tasamma kona garin.

Da dankane yaga wannan lamari yaga kuma in gari ya waye nan ne inda zasu shiga suyi wasa yakuma hakikance duk mutumin daya shiga wannan waje saidai buzunsa yaga kuma ga gari yakusan wayesa sai ya yiwo cikin gari da sauri yana tafe yana can carbi kamar da gaske daya dan taba tafiya...


Read / Download SUDA DAN KANE DILLALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album