Join Our WhatsApp Group

BINDIGAR KWALI Complete Hausa Novel Document by BINDIGAR KWALI


BINDIGAR KWALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31805



BINDIGAR KWALI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 168.5 kb

File Type: txt

Views: 853+

Download: 251+

Last download: 1 day ago

Description/Story: BINDIGAR KWALI
(c) Nazir Adam Salih
.
Daga - http://fb.com/hausaebooks
Ga wayanda suke son su samu littafan hausa a cikin ebook sai kui sauri ku ziyarci shafin http://hausaebooks.cf



BINDIGAR KWALI--> 1
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Typing: Yarima Gangariya(Jikan Sidi Mai Jaka)
.
In ban da dai lamari irin na makaranta musamman ma
kuma
lokacin jarrabawa to da babu abin da zai sa ni zuwa
makaranta
yau."
Dan kyakkyawan saurayin ne ke
fadin haka cikin zuciyarsa,
adaidai lokacin da ya kawo bakin titin, bugu da kari kuma
yana ta
faman kokawa da sassanyar
iskar ruwan daminar dake kokarin wafce ledar dake
hannunsa, sau biyu kenan akan
hanyarsa ta zuwa bakin titin iska
tana bankare lemar, shi kuma
yana maida ita yadda take. Haka
nan kuma lema bata hana shi jikewa ba musamman ma
gaban rigar makarantarsa saboda
sassanyar iskar dake kadawa.
Saurayin dogo ne wankan
tarwada kyakkyawa.
Da yawa daga cikin yan matan
zamani sun sha kamuwa da
ciwon son sa kawai daga ganin
hotonsa.****
Shi kansa yakan yi mamakin abin
da yan matan ke gani a jikinsa da
har suke rububinsa haka, tamkar
shi ne halittar karshe ta yan samarin duniya. To amma
duk
sa'ar da ya dubi madubi ya ga
dogon hancinsa, da kyakkyawan
lebban bakinsa, gami da fararen
idanu ma'abota girar baki sidik
gazar-gazar, gagara tunku, to sai
ka ga ya yiwa kansa murmushi
domin tabbas ya san shi kyakkyawa ne to amma kuma
wannan ce kawai take sa yan
mata kaunarsa ?? Abin da bai sani
ba shi ne tattausan murmushinsa
ma kawai narkar da zuciyar su
yake, ballantana dariyarsa.
Tun kusan karfe goma sha biyu
na daren litinin din ake ta tafka
ruwan, shi ne kuma ya kawo har
ya zuwa wannan safiya ta litinin
wacce ke da matukar
muhimmanci ga dan saurayin.****
Yau ita ce ranar da zai fara jarrabawar sa ta karshe a
sakandire, daga nan kuma sai
shirin shiga jami'a. Hakan ita tasa
ruwan saman da kakkarfar iskar
ba su hanashi fitowa ba, domin
ya san ko da ya zauna a gida, to
wasu daliban zasu je su yi, idan
kuwa jarrabawar ta wuce shi, to
ta wuce shi kenan har abada, sai
dai ko ya sake zama shekara mai
zuwa.
Ya share ruwan daya fara shigar
masa idanu, sannan ya dada
kankame lemar da ke hannunsa
don gudun kada iska ta sake
bankareta. Abin da ya fi tayar
masa da hankali shi ne titin babu
motoci kamar an share, kuma
yan tsirarun motocin ma dake ta
murginawa a cikin ruwan saman
da ya cika kan kwaltar, a ciccike
suke zuwa da jama'a, mafi
yawancinsu ma'aikata ne da yan
makaranta sai yan tsirarun yan
kasuwa ma'abota zafin nema.****
Saurayin ya dubi agogonsa sai ya
ga tuni ya kusan makara, domin
karfe tara za a jarrabawar gashi
yanzu tara saura minti ashirin.
Nan da nan sai ya yanke shawara
kawai ya bi turba a kasa ya tafi
makaranta a kalla dai koda zai
makara bai fi ya makara ta minti
biyu ba zuwa uku ba. Ya sunkuya ya
nade kafafun wandonsa, dan
gudun jikewa, domin duk kusan
in da zai bi yan kananan fadamu
ne na ruwan saman. Ya fara
tafiya kenan sai ya hango wata
dankareriyar marsandi daga can
nesa ta nufo inda yake da gudun
gaske. Tayoyin marsandin sai
tsaga ruwan suke yana ta
faffaflatsa gefe guda, hakan ita ta
sa saurayin sauka daga gefen
titin tun kafin ta karaso don
gudun kada ta bata shi da ruwa.
Koda ya koma gefe guda sai ya yi
mamakin ganin motar ta rage
wuta kuma ta fara gangarowa
bangaren daya ke, sannan kuma
sai ya ga tana kokarin tsayawa
daf dashi. Tun kafin motar ta
gama tsayawa ya hangi abin da
ya sa zuciyarsa Das ! Das !! Das !!! Kamar
zata tsaga kirjinsa ta fito waje.
Abin ya dame shi domin tun da
yake bai taba ganin wata
kyakkyawar halitta da tasa
zuciyarsa bugawaba sai a wannan karon. A daidai lokacin
ne to iska ta sami nasarar wafce
lemar dake hannunsa, ta yi jifa da
ita gefe guda kamar fulfulwa.*****
Hajiya Zainab Jumare bata ji dadin irin yanayin da aka
tashi
dashi ba a ranar litinin din
saboda dalilai guda biyu. Na farko
shi ne babu abin da ta tsana a
rayuwarata irin tuki a cikin ruwa
musamman ma idan aka ce
ruwan saman bai tsagaita ba. Na
biyu kuma shi ne hargitsin daya
shiga tsakaninta da masoyinta na
boye, Dakta Sadi. Hakika ba
karamin tashi hankalinta ya yi ba
lokacin da sabanin ya faru. Dakta Sadi likita ne a asibitin
JUMARE MEMORAL HOSPITAL.
.
Ku Biyoni Don Jin Cigaban Labarin Wannan Somin Tabi
Ne
.
Salon Rubutun Yayi Kokuwa Yayi Yawa A rage Yawan
shi ????
BINDIGAR KWALI--> 2
...Dakta Sadi likita ne a asibitin
JUMARE MEMORAL HOSPITAL.
Tun sa'ar da ya gama makaranta ya yi
dace aka daukeshi aiki a
matsayin likita a asibitin. Yau
shekararsa hudu kenan yana aiki
a asibitin. Tun da yake bai taba
ganin mace da kyawun halitta
kamar Zainab ba. Ba kuma
kyawunta ne kawai ya rudeshi
ba, akwai wani abu daban dake
jikinta wanda a kullum yake hana
Sadi barci. Da zarar ya rufe
idanunsa sai ya ga fuskartatana
yi masa murmushi. Dan haka tun
sa'ar da ya kyalla idanu ya dora a
kanta. To amma a lokacin da aka
ce dashi Zainab matar mai
asibitin ce, sai duk maitarsa ta
narke a cikinsa. Ya fitar da rai, sai
dai kuma duk sa'ar da ta kawo
ziyara to shi ke kan gaba yana
nunnuna mata gurare da ci gaban da aka samu a asibitin.
Sannan kuma idanunsa akan ta
kamar maye.*****
Alhaji Hamisu Jumare shi ne mijin
kyakkyawar matar kuma shi ne
mai asibitin na jumare Memorila
Hospital, ko kusa Alhaji Hamisu
bai damu da zama gida Najeriya
ba, manya yawan harkokinsa ya
fi yinsu a kasashen ketare. Sai ya
yi wata shida yana zazzaga
kasashen ketare. Sai ya yi wata
shida yana zazzaga kasashen
duniya kamar wani tauraron dan Adam.
Mutum ne da kullum yake cikin aiki babu hutu kamar
zuciya. Ya fi damuwa da kudi fiye da komai a rayuwarsa,
mutane na kusa dashi kan yi mamakin abin
da ke sashi barin
wannan zukekiyar mata
Zainab ya yi tafiyarsa ba zai
koda waiwayeta ba sai bayan wata shida koma fiye da
haka. Zainab ta dade da
gajiya da
irin wannan halayya ta mijinta.****
"Bai kyautu ba abin da kake yi, ka tafi ka bar ni a
gida ba ka ko tunanin hakkina a
kanka, ka tuna
fa so da kauna ce ta sa ka aure ni, amma dubi shekara
biyu kawai da auren ka yi
fatali da ni kamar ma ni ba
matarka ba ce." Ta ce dashi wata
rana suna zaune.
"kada ki damu zainab, ni
mata basu fiye damu na ba,
kuma in ban da abin ki ma
me ye na damuwa da
rashin zamana ?? Ga kudi nan ki yi
abinda kika ga dama,
ki shakata abin ki, ga kuma asibiti na nan kina kula
dashi." ya dafa kafadarta
ya ce. "Haba Zainab meye na damun
kan ki ma ??"
Tun daga ranar Zainab ta daina yi masa zancen.
To sai dai kuma shedan ya yi halinsa. Ba ta dade da
fara zuwa asibitin ba, sai ta hango Dakta Sadi, nan da
nan sha'awa da kaunarsa ta lillibe zuciyarta ta ga
babu wanda take sha'awa ya zo kusa da ita in ba Sadi
ba. Dan haka sai ta fara gayyatar sa gida ta hanyar
sashi ya kawo mata wasu
bayanan asibitin marasa
dalili zuwa gidanta. Da
farko Sadi bai saki jikinsa
da ita ba, to amma da ya fahimci
abin da take nufi sai
ya ga abin da ya kamata
kawai shi ne shima ya saki
jikinsa ya sha gara.*****
Yau kusan wata uku kenan da kulla huldar masha'a
tsakaninsa da Hajiya Zainab Jumare, sau da yawa ma a
gidan yake kwana yau wata biyar kenan da tafiyar Alhaji
Hamisu Jumare, ba shi kuma da ranar
dawowa.
A daren litinin din ne to suka sami rashin fahimta
tsakanin Dakta Sadi da
Hajiya Zainab Jumare,
saboda wasu kudi da ya nuna
mata yana son ya
handame. Ba zai yiyu ba, Hajiya Zainab ta ce da shi.
Ya ya ma zata yiyu haba
Sadi miliyan uku fa!!
Kai baka gode Allah ne ka tuna fa
duk yan kananan
kudin da kake cinyewa a
asibitin bana cewa da kai komai, amma duk da haka
kuma kake son daukar
miliyan uku, kanka ya tabu ne ?? Ta
tambayeshi.*****
"kaina bai tabu ba, kuma da kike zancen ina cinye
kananan kudin asibitin ai
wannan kamar biyana kike
yi tun da dai ni nake taya ki jin
dadin rayuwa a asirce, ba tare da mijinki uban
gantali ya sani ba".
Hakan shi ya bata mata rai
ta fatattake shi, ta ce kuma
kada ya sake shigo mata gida,
fitarsa ke da wuya sai
ta kifa kai ta fara kuka, domin ita ba zata taba iya
rayuwa ba sai da da namiji, to gashi kuma mijinta bai
damu da ita ba, idan ta nemi ya
saketa kuma ta tonawa
kanta asiri, domin babu
sauran jin dadi in ta rabu
dashi, ba kudin kashewa,
ba kuma za a sake
girmamata ba tun da daman duk
girman da
mutane suke bata na kudin ne. Dole ne na sami wani
sabon masoyin da zai ke biya min bukatuna a asirce ta ce
da kanta.*****
Wannan ita tasa
safiyar
litinin din ta zo mata cikin
mawuyacin halin tunani.
Kamar dai kuma dan
kyakkyawan saurayin,
itama in ba dan tana son kai yar
karamar yarta
Zuhuriyya makaranta ba, to da babu abin da zai sa ta
fito cikin wannan ruwan.
A daidai lokacin da take
tukin motar ne, to tana tunanin
abin da ya faru a
daren jiya tsakaninta da Sadi, ta hango dan
kyakkyawan saurayin a gefen titi yana tafiya cikin
ruwan. Ga dukkan alamu kuma
makaranta zai tafi,
wani abu ya yi yar! Kamar tafiyar kyankyaso a cikin
jijiyoyin jikinta. Kai
wannan yaro da kyau
yake ta ce a zuciyarta. A daidai lokacin ne ta Hango..........
ME HAJIYA ZAINAB TA HANGO KUMA ???
BINDIGAR KWALI--> 3
.
Kai wannan yaro da kyau yake ta
ce a zuciyarta. A daidai
lokacin ne ta ga iska
ta wafce lemar sa ta yi jifa da ita.
Nan da nan ta taka
birki a gabansa ta sauke gilashi
ta ce.
"Makaranta za ka ne ??" Dan
kyakkyawan saurayin ya dubi
kyakkyawar matar kirjinsa na
harbawa
kamar dakikar agogo,
sannan kuma ya dubi yar
karamar yarinya dake bayan
motar bata fi
shekara uku ba, tana wasa da
dan karamin mutum-mutumin
karen roba gashi
kamar na gaske. Sannan
kuma a gefenta bindigar roba ce
akan kujerar
motar.
"Makaranta za ni".
Hajiya Zainab ta yi
murmushi sannan ta kashe
idonta na hagu ta ce. "Wace
makaranta kake
zuwa saurayin ya dubeta cikin
mamaki, sannan ya ce. "JUMARE
PRIVATE SCHOOL"****
Zainab ta dubeshi cikin mamaki
tana murmushi.
"JUMARE ?? Amma kuma ban taba
ganinka ba, ai kusan
kullum sai na kai yarinya ta
makarantar" Ta dubi
zuhuriyya dake zaune a bayan
motar.
"Shigo to mu tafi na rage ma
hanya" Saurayin ya
bude motar ya shiga
sannan ya ce.
"Ai ba dole bane ki ganni, tun da
ke bangaren
(Nursery School) din kike zuwa"
Hajiya zainab ta dubi
saurayin ta kyalkyale da wata irin
daddadar dariya mai
kamar busar sarewa a kunnen
saurayin ta ce. "Ai makarantar
miji na ce,
ni ce Hajiya Zainab Jumare ba ka
taba jin sunana bane ??
Ta sake murmushi. Saurayin ya
dubeta cikin mamaki da kaduwa
ya ce
bakinsa na rawa.
"Daman ke ce ?? Na sha jin sunan
ki amma ban taba
ganinki ido da ido ba, mijinki dai
na taba gani"
Hajiya zainab ta dubeshi
cikin sha'awa. Ba ta taba ganin
kyakkyawa
kamarsa ba, shin ko
wannan yaro zai iya zamowa
canjin SADI ? Ta tambayi
kanta.*****
"Wannan yar ki ce ?" Zainab ta yi
murmushi har
hakoranta suka fito,
sannan ta karawa motar gudu ta
ce.
"Oh! Zuhuriyya, ya ta ce". A daidai
lokacin ne to
Zuhuriyya ta turo mutum-
mutumin karen robar ta
tsakanin kujerar motar ta ce da
saurayin. Kana son wannan?"
saurayin ya yi mata dariya,
sannan kuma ya yi
mamakin irin kamar da suka yi
da mahaifiyarta, kamar an tsaga
kara.
"Ashe tana magana". Ya ce da
Zainab.
"Lah!! Wace, ai surutu ne da ita".
Zainab ta ce tana murmushi.
Zuhuriyya ta zuro bindigar robar
ta zunguri kunnen
saurayin ta ce.
"Wa na kama?" Zainab da
saurayin suka fashe da
dariya gaba daya.
"Na tuba zuhuriyya kada ki
harbeni". Saurayin ya ce yana
satar kallon fuskar
zainab, Zuhuriyya ta fashe da
dariya ta ce.
"Kai ba ta gaske ba ce,
BINDIGAR KWALI ce!" Zainab ta
fashe da dariya kamar zata
saki sitiyarin motar.
"Shashashar banza,
bindigar roba za ki ce ba ta Kwali
ba."****
Dan saurayin ya fito daga cikin
motar ya dubi agogon dake
hannunsa, tara saura
minti goma, tuni har dalibai sun
fara shigewa tangamemen ajin
da aka tanada don zaman
jarrabawar.
Ya dawo da hankalinsa gurin
Hajiya Zainab wacce ke ta faman
kallonsa kamar zata hadiye shi.
"Sha daya da rabi". Ya amsa yana
dubanta.
"Ban san kuma sunanka ba". Ya
dubeta da lallausan
murmushi ya dauke kansa kadan
ya ce.
"Sunana Hilal... Hilal Aliyu". Ta yi
murmushi ta ce.
"Hilal sunan larabawa ne". Suka yi
dariya gaba daya,
sannan sai zainab ta miko masa
Naira ashirin-ashirin
sababbi fil. Hilal ya dubeta cikin
mamaki yace.
"Hajiya wannan na mene ne?"
Ta yi murmushi.
"karbi mana, ai ba ka na yi,
kyauta ce, kada ka maida
hannunta baya." Halil ya
karba. "Na gode. Ni zan tafi na ga
an fara shiga aji".****
Zainab ta dubeshi ido da ido ta
ce. "To Hilal Allah ba da sa'a."
Ta dan yi shiru tana
dubansa, sannan sai ta ce. "In ba
ka damu ba, ina gayyatarka"
Birthday Party" bikin haihuwar
Zuhuriyya
ranar Asabar din
nan mai zuwa." Hilal ya yi
murmushi.
"Ba damuwa Hajiya." ya dubi
zuhuriyya.
"Shekara nawa za ta cika"
"Shekaru Hudu kenan a duniya,
Ina fatan dai zaka
zo bari in baka adireshin gidana......"*****
Ta laluba ta dauko biro daga jakarta ta
dubeshi ta ce. "Ba ni littafin ka daya in
rubuta maka, dan bana jin ina da takarda a motar nan,
wannan rigimammiyar
kuma ba ta barin a yagi littafinta". Ta dubi Zuhuriyya.
Hilal
ya mika mata littafin. Zainab ta saci
kallonsa, ta dan kara
littafin a kirjinta, sannan ta ajiye shi akan cinyarta ta
rubuta masa adireshin. "To Hajiya
ni zan tafi lokaci
ya yi sai na zo din".
"To... Hilal sai na ganka". Mutanen biyu masu kusan
shekaru daya suka dubi juna, idanun kowa ya aika da
sakon dake zuciyar
kowa izuwa gurin kowa sannan sai suka yiwa juna
murmushi. Hajiya Zainab ta ja motar tana daga masa
hannu, ta nufi bangaren da (Nursery) makaranta
kananan yara take. A
fuskarta akwai wani
tattausan murmushi na gamsuwa. Ko shakka ba ta
yi akan lamarin ta san Hilal ya yi
masifar kamuwa
kamar yadda itama ta
kamu Koda ta karawa
motar wuta, sai tunanin mijinta Hamisu Jumare ya
fado mata shin ko yana ina? Ta
tambayi kanta.****
Lokacin da ya zo rubuta sunansa akan littafin amsa
jarabawar sai ya yi
mamakin ganin kalmar farko da
alkalaminsa ya yi
kuskuren rubutawa ita ce (Z)
Hilal ya rikice saboda dalilai da dama. Wasu daga cikin
dalilan rikicewarsa sune abin da
ya gani a idanun
Zainab. Kauna ce a gareshi ba ya ko shakkar hakan.
To yaya za ta yi wannan abu kuwa ya yiwu ai bashi
yiyuwa kwabar kasa da Cokali, yaushe!! Ya ya ma za a yi
ace matar babban
mutum kamar Alhaji
Hamisu Jumare ta kaunace shi, bayan kuma har yanzu
da aure a tsakaninsu. Sai kuma gayyatarsa da ta yi da
sunan wai za a yi (birthday) shima ya jefa shi
cikin tunani, domin ko shakka ba ya yi ya san ba bikin
haihuwar yarinyar ba ce kawai ya sa ta
gayyaceshi ya san akwai wani abu daban, musamman da
ya dubi cikin
kwayar idanunta
murmushinta, dariyarta, kallonta,
kai hatta motsinta
duk suna nuni ne da abu daya wato So, to amma
zuciyarsa ta kasa imani da
hakan. Lokacin da aka tashi daga
makarantar sai ya ji bashi da ra'ayin magana da kowace
budurwa da ke
ajinsu, ballantana ma namiji,
zuciyarsa babu komai a ciki sai fatalwan murmushin
kyakkyawar fuskar Zainab ne ke kai kai kawo cikin
zuciyarsa, wata zuciya ta ce dashi kada ka je (birthday)
din nan. To amma ya san babu abin da zai hana shi sake
ganin kyakkyawar
fuskar shi ya san ba daidai bane hulda da matar wani
musamman ma idan ka ga kamar wani abu na shirin
shiga tsakani*****
To amma duk da
haka zuciyarsa bata iya jurewa sai ya sake ganinta.
A daidai lokacin ne to ya ji an taba kafadarsa.
Hilal ya juya firgigit! A farfajiyar makarantar. "Tunanin
me kake yi ne?"
Rukayya ta ce dashi tana dubansa fuskarta a hade.
Ta dade tana bata lokacinta akan kaunarsa, amma shi
bai ma san tana yi ba. Duk da yake dai da yawa daga
cikin yan matan ajinsu suna
mutuwar sonsa, to amma babu wadda maitarta ta
fito fili kamar ta, Hilal ya dubeta. "Ni ba tunanin da nake"
"Ya ya jarrabawar ta yi sauki?" Rukayya ta tambaya. Hilal
ya yi
dum dashi
yana kallon gabansa bai bata amsa ba.
"Na ce da kai tunani kake ka ce a'a."
Rukayya ta ce tana dubansa.
"Me ya sa ne kika cika damun mutum?"
Rukayya ta dubeshi a yatsine ta ce.
"Wace ce wannan dazu ta kawo
ka a mota?" Hilal ya dubeta a fusace ya ce.
"Kin cika shiga harkar da ba ta ki ba, wata rana za ki yi
dana-sani." ya juya a fusace
ya nufi kofar makarantar. Har ya
kai daf
da rumfar masu gadi bai...


Read / Download BINDIGAR KWALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album