Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BINDIGAR KWALI
(c) Nazir Adam Salih
.
Daga - http://fb.com/hausaebooks
Ga wayanda suke son su samu littafan hausa a cikin ebook sai kui sauri ku ziyarci shafin http://hausaebooks.cf



BINDIGAR KWALI--> 1
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Typing: Yarima Gangariya(Jikan Sidi Mai Jaka)
.
In ban da dai lamari irin na makaranta musamman ma
kuma
lokacin jarrabawa to da babu abin da zai sa ni zuwa
makaranta
yau."
Dan kyakkyawan saurayin ne ke
fadin haka cikin zuciyarsa,
adaidai lokacin da ya kawo bakin titin, bugu da kari kuma
yana ta
faman kokawa da sassanyar
iskar ruwan daminar dake kokarin wafce ledar dake
hannunsa, sau biyu kenan akan
hanyarsa ta zuwa bakin titin iska
tana bankare lemar, shi kuma
yana maida ita yadda take. Haka
nan kuma lema bata hana shi jikewa ba musamman ma
gaban rigar makarantarsa saboda
sassanyar iskar dake kadawa.
Saurayin dogo ne wankan
tarwada kyakkyawa.
Da yawa daga cikin yan matan
zamani sun sha kamuwa da
ciwon son sa kawai daga ganin
hotonsa.****
Shi kansa yakan yi mamakin abin
da yan matan ke gani a jikinsa da
har suke rububinsa haka, tamkar
shi ne halittar karshe ta yan samarin duniya. To amma
duk
sa'ar da ya dubi madubi ya ga
dogon hancinsa, da kyakkyawan
lebban bakinsa, gami da fararen
idanu ma'abota girar baki sidik
gazar-gazar, gagara tunku, to sai
ka ga ya yiwa kansa murmushi
domin tabbas ya san shi kyakkyawa ne to amma kuma
wannan ce kawai take sa yan
mata kaunarsa ?? Abin da bai sani
ba shi ne tattausan murmushinsa
ma kawai narkar da zuciyar su
yake, ballantana dariyarsa.
Tun kusan karfe goma sha biyu
na daren litinin din ake ta tafka
ruwan, shi ne kuma ya kawo har
ya zuwa wannan safiya ta litinin
wacce ke da matukar
muhimmanci ga dan saurayin.****
Yau ita ce ranar da zai fara jarrabawar sa ta karshe a
sakandire, daga nan kuma sai
shirin shiga jami'a. Hakan ita tasa
ruwan saman da kakkarfar iskar
ba su hanashi fitowa ba, domin
ya san ko da ya zauna a gida, to
wasu daliban zasu je su yi, idan
kuwa jarrabawar ta wuce shi, to
ta wuce shi kenan har abada, sai
dai ko ya sake zama shekara mai
zuwa.
Ya share ruwan daya fara shigar
masa idanu, sannan ya dada
kankame lemar da ke hannunsa
don gudun kada iska ta sake
bankareta. Abin da ya fi tayar
masa da hankali shi ne titin babu
motoci kamar an share, kuma
yan tsirarun motocin ma dake ta
murginawa a cikin ruwan saman
da ya cika kan kwaltar, a ciccike
suke zuwa da jama'a, mafi
yawancinsu ma'aikata ne da yan
makaranta sai yan tsirarun yan
kasuwa ma'abota zafin nema.****
Saurayin ya dubi agogonsa sai ya
ga tuni ya kusan makara, domin
karfe tara za a jarrabawar gashi
yanzu tara saura minti ashirin.
Nan da nan sai ya yanke shawara
kawai ya bi turba a kasa ya tafi
makaranta a kalla dai koda zai
makara bai fi ya makara ta minti
biyu ba zuwa uku ba. Ya sunkuya ya
nade kafafun wandonsa, dan
gudun jikewa, domin duk kusan
in da zai bi yan kananan fadamu
ne na ruwan saman. Ya fara
tafiya kenan sai ya hango wata
dankareriyar marsandi daga can
nesa ta nufo inda yake da gudun
gaske. Tayoyin marsandin sai
tsaga ruwan suke yana ta
faffaflatsa gefe guda, hakan ita ta
sa saurayin sauka daga gefen
titin tun kafin ta karaso don
gudun kada ta bata shi da ruwa.
Koda ya koma gefe guda sai ya yi
mamakin ganin motar ta rage
wuta kuma ta fara gangarowa
bangaren daya ke, sannan kuma
sai ya ga tana kokarin tsayawa
daf dashi. Tun kafin motar ta
gama tsayawa ya hangi abin da
ya sa zuciyarsa Das ! Das !! Das !!! Kamar
zata tsaga kirjinsa ta fito waje.
Abin ya dame shi domin tun da
yake bai taba ganin wata
kyakkyawar halitta da tasa
zuciyarsa bugawaba sai a wannan karon. A daidai lokacin
ne to iska ta sami nasarar wafce
lemar dake hannunsa, ta yi jifa da
ita gefe guda kamar fulfulwa.*****
Hajiya Zainab Jumare bata ji dadin irin yanayin da aka
tashi
dashi ba a ranar litinin din
saboda dalilai guda biyu. Na farko
shi ne babu abin da ta tsana a
rayuwarata irin tuki a cikin ruwa
musamman ma idan aka ce
ruwan saman bai tsagaita ba. Na
biyu kuma shi ne hargitsin daya
shiga tsakaninta da masoyinta na
boye, Dakta Sadi. Hakika ba
karamin tashi hankalinta ya yi ba
lokacin da sabanin ya faru. Dakta Sadi likita ne a asibitin
JUMARE MEMORAL HOSPITAL.
.
Ku Biyoni Don Jin Cigaban Labarin Wannan Somin Tabi
Ne
.
Salon Rubutun Yayi Kokuwa Yayi Yawa A rage Yawan
shi ????
BINDIGAR KWALI--> 2
...Dakta Sadi likita ne a asibitin
JUMARE MEMORAL HOSPITAL.
Tun sa'ar da ya gama makaranta ya yi
dace aka daukeshi aiki a
matsayin likita a asibitin. Yau
shekararsa hudu kenan yana aiki
a asibitin. Tun da yake bai taba
ganin mace da kyawun halitta
kamar Zainab ba. Ba kuma
kyawunta ne kawai ya rudeshi
ba, akwai wani abu daban dake
jikinta wanda a kullum yake hana
Sadi barci. Da zarar ya rufe
idanunsa sai ya ga fuskartatana
yi masa murmushi. Dan haka tun
sa'ar da ya kyalla idanu ya dora a
kanta. To amma a lokacin da aka
ce dashi Zainab matar mai
asibitin ce, sai duk maitarsa ta
narke a cikinsa. Ya fitar da rai, sai
dai kuma duk sa'ar da ta kawo
ziyara to shi ke kan gaba yana
nunnuna mata gurare da ci gaban da aka samu a asibitin.
Sannan kuma idanunsa akan ta
kamar maye.*****
Alhaji Hamisu Jumare shi ne mijin
kyakkyawar matar kuma shi ne
mai asibitin na jumare Memorila
Hospital, ko kusa Alhaji Hamisu
bai damu da zama gida Najeriya
ba, manya yawan harkokinsa ya
fi yinsu a kasashen ketare. Sai ya
yi wata shida yana zazzaga
kasashen ketare. Sai ya yi wata
shida yana zazzaga kasashen
duniya kamar wani tauraron dan Adam.
Mutum ne da kullum yake cikin aiki babu hutu kamar
zuciya. Ya fi damuwa da kudi fiye da komai a rayuwarsa,
mutane na kusa dashi kan yi mamakin abin
da ke sashi barin
wannan zukekiyar mata
Zainab ya yi tafiyarsa ba zai
koda waiwayeta ba sai bayan wata shida koma fiye da
haka. Zainab ta dade da
gajiya da
irin wannan halayya ta mijinta.****
"Bai kyautu ba abin da kake yi, ka tafi ka bar ni a
gida ba ka ko tunanin hakkina a
kanka, ka tuna
fa so da kauna ce ta sa ka aure ni, amma dubi shekara
biyu kawai da auren ka yi
fatali da ni kamar ma ni ba
matarka ba ce." Ta ce dashi wata
rana suna zaune.
"kada ki damu zainab, ni
mata basu fiye damu na ba,
kuma in ban da abin ki ma
me ye na damuwa da
rashin zamana ?? Ga kudi nan ki yi
abinda kika ga dama,
ki shakata abin ki, ga kuma asibiti na nan kina kula
dashi." ya dafa kafadarta
ya ce. "Haba Zainab meye na damun
kan ki ma ??"
Tun daga ranar Zainab ta daina yi masa zancen.
To sai dai kuma shedan ya yi halinsa. Ba ta dade da
fara zuwa asibitin ba, sai ta hango Dakta Sadi, nan da
nan sha'awa da kaunarsa ta lillibe zuciyarta ta ga
babu wanda take sha'awa ya zo kusa da ita in ba Sadi
ba. Dan haka sai ta fara gayyatar sa gida ta hanyar
sashi ya kawo mata wasu
bayanan asibitin marasa
dalili zuwa gidanta. Da
farko Sadi bai saki jikinsa
da ita ba, to amma da ya fahimci
abin da take nufi sai
ya ga abin da ya kamata
kawai shi ne shima ya saki
jikinsa ya sha gara.*****
Yau kusan wata uku kenan da kulla huldar masha'a
tsakaninsa da Hajiya Zainab Jumare, sau da yawa ma a
gidan yake kwana yau wata biyar kenan da tafiyar Alhaji
Hamisu Jumare, ba shi kuma da ranar
dawowa.
A daren litinin din ne to suka sami rashin fahimta
tsakanin Dakta Sadi da
Hajiya Zainab Jumare,
saboda wasu kudi da ya nuna
mata yana son ya
handame. Ba zai yiyu ba, Hajiya Zainab ta ce da shi.
Ya ya ma zata yiyu haba
Sadi miliyan uku fa!!
Kai baka gode Allah ne ka tuna fa
duk yan kananan
kudin da kake cinyewa a
asibitin bana cewa da kai komai, amma duk da haka
kuma kake son daukar
miliyan uku, kanka ya tabu ne ?? Ta
tambayeshi.*****
"kaina bai tabu ba, kuma da kike zancen ina cinye
kananan kudin asibitin ai
wannan kamar biyana kike
yi tun da dai ni nake taya ki jin
dadin rayuwa a asirce, ba tare da mijinki uban
gantali ya sani ba".
Hakan shi ya bata mata rai
ta fatattake shi, ta ce kuma
kada ya sake shigo mata gida,
fitarsa ke da wuya sai
ta kifa kai ta fara kuka, domin ita ba zata taba iya
rayuwa ba sai da da namiji, to gashi kuma mijinta bai
damu da ita ba, idan ta nemi ya
saketa kuma ta tonawa
kanta asiri, domin babu
sauran jin dadi in ta rabu
dashi, ba kudin kashewa,
ba kuma za a sake
girmamata ba tun da daman duk
girman da
mutane suke bata na kudin ne. Dole ne na sami wani
sabon masoyin da zai ke biya min bukatuna a asirce ta ce
da kanta.*****
Wannan ita tasa
safiyar
litinin din ta zo mata cikin
mawuyacin halin tunani.
Kamar dai kuma dan
kyakkyawan saurayin,
itama in ba dan tana son kai yar
karamar yarta
Zuhuriyya makaranta ba, to da babu abin da zai sa ta
fito cikin wannan ruwan.
A daidai lokacin da take
tukin motar ne, to tana tunanin
abin da ya faru a
daren jiya tsakaninta da Sadi, ta hango dan
kyakkyawan saurayin a gefen titi yana tafiya cikin
ruwan. Ga dukkan alamu kuma
makaranta zai tafi,
wani abu ya yi yar! Kamar tafiyar kyankyaso a cikin
jijiyoyin jikinta. Kai
wannan yaro da kyau
yake ta ce a zuciyarta. A daidai lokacin ne ta Hango..........
ME HAJIYA ZAINAB TA HANGO KUMA ???
BINDIGAR KWALI--> 3
.
Kai wannan yaro da kyau yake ta
ce a zuciyarta. A daidai
lokacin ne ta ga iska
ta wafce lemar sa ta yi jifa da ita.
Nan da nan ta taka
birki a gabansa ta sauke gilashi
ta ce.
"Makaranta za ka ne ??" Dan
kyakkyawan saurayin ya dubi
kyakkyawar matar kirjinsa na
harbawa
kamar dakikar agogo,
sannan kuma ya dubi yar
karamar yarinya dake bayan
motar bata fi
shekara uku ba, tana wasa da
dan karamin mutum-mutumin
karen roba gashi
kamar na gaske. Sannan
kuma a gefenta bindigar roba ce
akan kujerar
motar.
"Makaranta za ni".
Hajiya Zainab ta yi
murmushi sannan ta kashe
idonta na hagu ta ce. "Wace
makaranta kake
zuwa saurayin ya dubeta cikin
mamaki, sannan ya ce. "JUMARE
PRIVATE SCHOOL"****
Zainab ta dubeshi cikin mamaki
tana murmushi.
"JUMARE ?? Amma kuma ban taba
ganinka ba, ai kusan
kullum sai na kai yarinya ta
makarantar" Ta dubi
zuhuriyya dake zaune a bayan
motar.
"Shigo to mu tafi na rage ma
hanya" Saurayin ya
bude motar ya shiga
sannan ya ce.
"Ai ba dole bane ki ganni, tun da
ke bangaren
(Nursery School) din kike zuwa"
Hajiya zainab ta dubi
saurayin ta kyalkyale da wata irin
daddadar dariya mai
kamar busar sarewa a kunnen
saurayin ta ce. "Ai makarantar
miji na ce,
ni ce Hajiya Zainab Jumare ba ka
taba jin sunana bane ??
Ta sake murmushi. Saurayin ya
dubeta cikin mamaki da kaduwa
ya ce
bakinsa na rawa.
"Daman ke ce ?? Na sha jin sunan
ki amma ban taba
ganinki ido da ido ba, mijinki dai
na taba gani"
Hajiya zainab ta dubeshi
cikin sha'awa. Ba ta taba ganin
kyakkyawa
kamarsa ba, shin ko
wannan yaro zai iya zamowa
canjin SADI ? Ta tambayi
kanta.*****
"Wannan yar ki ce ?" Zainab ta yi
murmushi har
hakoranta suka fito,
sannan ta karawa motar gudu ta
ce.
"Oh! Zuhuriyya, ya ta ce". A daidai
lokacin ne to
Zuhuriyya ta turo mutum-
mutumin karen robar ta
tsakanin kujerar motar ta ce da
saurayin. Kana son wannan?"
saurayin ya yi mata dariya,
sannan kuma ya yi
mamakin irin kamar da suka yi
da mahaifiyarta, kamar an tsaga
kara.
"Ashe tana magana". Ya ce da
Zainab.
"Lah!! Wace, ai surutu ne da ita".
Zainab ta ce tana murmushi.
Zuhuriyya ta zuro bindigar robar
ta zunguri kunnen
saurayin ta ce.
"Wa na kama?" Zainab da
saurayin suka fashe da
dariya gaba daya.
"Na tuba zuhuriyya kada ki
harbeni". Saurayin ya ce yana
satar kallon fuskar
zainab, Zuhuriyya ta fashe da
dariya ta ce.
"Kai ba ta gaske ba ce,
BINDIGAR KWALI ce!" Zainab ta
fashe da dariya kamar zata
saki sitiyarin motar.
"Shashashar banza,
bindigar roba za ki ce ba ta Kwali
ba."****
Dan saurayin ya fito daga cikin
motar ya dubi agogon dake
hannunsa, tara saura
minti goma, tuni har dalibai sun
fara shigewa tangamemen ajin
da aka tanada don zaman
jarrabawar.
Ya dawo da hankalinsa gurin
Hajiya Zainab wacce ke ta faman
kallonsa kamar zata hadiye shi.
"Sha daya da rabi". Ya amsa yana
dubanta.
"Ban san kuma sunanka ba". Ya
dubeta da lallausan
murmushi ya dauke kansa kadan
ya ce.
"Sunana Hilal... Hilal Aliyu". Ta yi
murmushi ta ce.
"Hilal sunan larabawa ne". Suka yi
dariya gaba daya,
sannan sai zainab ta miko masa
Naira ashirin-ashirin
sababbi fil. Hilal ya dubeta cikin
mamaki yace.
"Hajiya wannan na mene ne?"
Ta yi murmushi.
"karbi mana, ai ba ka na yi,
kyauta ce, kada ka maida
hannunta baya." Halil ya
karba. "Na gode. Ni zan tafi na ga
an fara shiga aji".****
Zainab ta dubeshi ido da ido ta
ce. "To Hilal Allah ba da sa'a."
Ta dan yi shiru tana
dubansa, sannan sai ta ce. "In ba
ka damu ba, ina gayyatarka"
Birthday Party" bikin haihuwar
Zuhuriyya
ranar Asabar din
nan mai zuwa." Hilal ya yi
murmushi.
"Ba damuwa Hajiya." ya dubi
zuhuriyya.
"Shekara nawa za ta cika"
"Shekaru Hudu kenan a duniya,
Ina fatan dai zaka
zo bari in baka adireshin gidana......"*****
Ta laluba ta dauko biro daga jakarta ta
dubeshi ta ce. "Ba ni littafin ka daya in
rubuta maka, dan bana jin ina da takarda a motar nan,
wannan rigimammiyar
kuma ba ta barin a yagi littafinta". Ta dubi Zuhuriyya.
Hilal
ya mika mata littafin. Zainab ta saci
kallonsa, ta dan kara
littafin a kirjinta, sannan ta ajiye shi akan cinyarta ta
rubuta masa adireshin. "To Hajiya
ni zan tafi lokaci
ya yi sai na zo din".
"To... Hilal sai na ganka". Mutanen biyu masu kusan
shekaru daya suka dubi juna, idanun kowa ya aika da
sakon dake zuciyar
kowa izuwa gurin kowa sannan sai suka yiwa juna
murmushi. Hajiya Zainab ta ja motar tana daga masa
hannu, ta nufi bangaren da (Nursery) makaranta
kananan yara take. A
fuskarta akwai wani
tattausan murmushi na gamsuwa. Ko shakka ba ta
yi akan lamarin ta san Hilal ya yi
masifar kamuwa
kamar yadda itama ta
kamu Koda ta karawa
motar wuta, sai tunanin mijinta Hamisu Jumare ya
fado mata shin ko yana ina? Ta
tambayi kanta.****
Lokacin da ya zo rubuta sunansa akan littafin amsa
jarabawar sai ya yi
mamakin ganin kalmar farko da
alkalaminsa ya yi
kuskuren rubutawa ita ce (Z)
Hilal ya rikice saboda dalilai da dama. Wasu daga cikin
dalilan rikicewarsa sune abin da
ya gani a idanun
Zainab. Kauna ce a gareshi ba ya ko shakkar hakan.
To yaya za ta yi wannan abu kuwa ya yiwu ai bashi
yiyuwa kwabar kasa da Cokali, yaushe!! Ya ya ma za a yi
ace matar babban
mutum kamar Alhaji
Hamisu Jumare ta kaunace shi, bayan kuma har yanzu
da aure a tsakaninsu. Sai kuma gayyatarsa da ta yi da
sunan wai za a yi (birthday) shima ya jefa shi
cikin tunani, domin ko shakka ba ya yi ya san ba bikin
haihuwar yarinyar ba ce kawai ya sa ta
gayyaceshi ya san akwai wani abu daban, musamman da
ya dubi cikin
kwayar idanunta
murmushinta, dariyarta, kallonta,
kai hatta motsinta
duk suna nuni ne da abu daya wato So, to amma
zuciyarsa ta kasa imani da
hakan. Lokacin da aka tashi daga
makarantar sai ya ji bashi da ra'ayin magana da kowace
budurwa da ke
ajinsu, ballantana ma namiji,
zuciyarsa babu komai a ciki sai fatalwan murmushin
kyakkyawar fuskar Zainab ne ke kai kai kawo cikin
zuciyarsa, wata zuciya ta ce dashi kada ka je (birthday)
din nan. To amma ya san babu abin da zai hana shi sake
ganin kyakkyawar
fuskar shi ya san ba daidai bane hulda da matar wani
musamman ma idan ka ga kamar wani abu na shirin
shiga tsakani*****
To amma duk da
haka zuciyarsa bata iya jurewa sai ya sake ganinta.
A daidai lokacin ne to ya ji an taba kafadarsa.
Hilal ya juya firgigit! A farfajiyar makarantar. "Tunanin
me kake yi ne?"
Rukayya ta ce dashi tana dubansa fuskarta a hade.
Ta dade tana bata lokacinta akan kaunarsa, amma shi
bai ma san tana yi ba. Duk da yake dai da yawa daga
cikin yan matan ajinsu suna
mutuwar sonsa, to amma babu wadda maitarta ta
fito fili kamar ta, Hilal ya dubeta. "Ni ba tunanin da nake"
"Ya ya jarrabawar ta yi sauki?" Rukayya ta tambaya. Hilal
ya yi
dum dashi
yana kallon gabansa bai bata amsa ba.
"Na ce da kai tunani kake ka ce a'a."
Rukayya ta ce tana dubansa.
"Me ya sa ne kika cika damun mutum?"
Rukayya ta dubeshi a yatsine ta ce.
"Wace ce wannan dazu ta kawo
ka a mota?" Hilal ya dubeta a fusace ya ce.
"Kin cika shiga harkar da ba ta ki ba, wata rana za ki yi
dana-sani." ya juya a fusace
ya nufi kofar makarantar. Har ya
kai daf
da rumfar masu gadi bai juyo ba,
to amma jikinsa ya fada masa cewa
idanun Rukayya a kansa suke suna
kallon bayansa. Koda ya kawo ga kofar
makarantar sai ya yi ido biyu da
sunan
makarantar
"JUMARE PRIVATE SEC. SCH."
Gabansa ya fadi ras!! Daga nan
ya san cewa duk inda ya ga sunan sai
gabansa ya
fadi domin ganin sunan kamar ganin
ZAINAB ne.*****
Kusan duk wadanda ta gayyata gurin
bikin haihuwar ya karaso in ka
dauke mutum daya. Wannan mutum shi
ya fi muhimmanci fiye da duk wanda
ya halarci
bikin a gurin Zainab.
Tun kusan karfe hudu ta caba
kwalliya,
duk jikinta sheki yake, bugu da
kari kuma
ga kayan adon da ta caba reras a
jikinta
suna ta kyalkyali kamar amaryar
indiya.
Da yawa daga cikin mutanen da
basu san
me ake ba a gurin idan suka kalli
kwalliyar
da ta caba sai su dauka bikin
zagayowar
ranar haihuwarta ne ake, ko
kuma ma
bikin aurenta baki daya. Yawa-
yawa bakin
da ta gayyato gurin duk yan
uwanta ne
mafi yawa samari ne, yan kasa da
shekaru
ashirin, wasu kuma ashirin da
biyu, sai
kuma yan mata wadanda su
kuma mafi
yawan su malaman asibitin
mijinta ne.
Tuni an jera tebura da guraren
zama, a
gaban kowa dake farfajiyar
gidan ga
kayan shaye-shaye da romo nan
wasu ma
mutum bai ko taba ganin irin su
ba
ballantana ma ya dandana. A
tsakiya
kuma wani dan madaidaicin
teburi ne
lillibe da farin kyalle na leshi
wanda aka
kawata jikinsa da kayan ado
masu
kyalkyali kamar ruwan lu'u-lu'u.
Akan
kyallen a tsaye kamar mutum-
mutumi,
wani zungureren (cake) ne da
aka yi shi
da madara, da sauran dangogi
ma'abota
zaki da sa kunnen duk wanda ya
shasu mikewa tsaye.*****
Zuhuriyya na
zaune akan
wata yar karamar kujera wace
aka kawata
da ado. Ita ma zuhuriyya ta sha
ado
kamar dai mahaifiyarta Zainab.
Zuhuriyya
na zaune sai ta dubi wannan ta
yi
murmushi ta dubi wancan ta yi
fari da
fararen idanunta, yan samari da
yan
matan dake gurin suka dubeta
cikin
sha'awa kowa so yake ta matsa
kusa
dashi ya dauketa, ko kuma ya
rike
hannunta kawai.
Abin kuma da yafi burge kowa
da ba da
mamaki shi ne irin yadda ta yi
tsananin
kama da mahaifiyarta, hancinta,
idonta,
bakinta, girarta, kunnenta, shan
fuskarta,
kallonta, murmushinta kai hatta
tafiyar
Zuhuriyya irin ta Zainab ce.
Duk abin nan da ake Zainab bata
zauna ba,
sai zagaye-zagaye take tana
dube-dube,
amma har yanzu bata ga koda
alamar
Hilal ba. Misalin karfe hudu da
rabi ta gaji
da jira, tuni mutane har sun fara
shaye-
shaye da ciye-ciye. Tun karfe
hudu
Zuhuriyya ta yanka (cake) dinta
da wata
yar karamar wuka ta azurfa
mutane suka
dauki sowa da tafi.****
Hajiya Zainab ta gana yanke
kauna da
zuwan Hilal dan haka sai ta koma
cikin
mutanen ta fuskance su zuciyarta
cikin
kuna sannan ta dafa kan yar ta
Zuhuriyya
ta fara yi wa jama'a bayani da
godiya. Nan da nan gurin ya yi tsit.
Zuhuriyya na tsaye gaban mahaifiyarta
tana rike da bindigarta ta roba,
hannunta
daya kuma rike da katuwar
balam-balam,
kwatsam sai ta bata shirun, ta
dauki sowa
ta kwace daga hannun
mahaifiyarta, ta
nufi bayan inda mutane ke
tsattsaye da
gudu tana sowa tana cewa.
"Sai na harbe ka da bindigar kwali na
durum!!" Tace tana kumbura
baki.
Hilal ya yi sauri ya dauke ta yana
dariya.
Duk mutane suka juya suna
dubansa cikin
mamaki.
Zainab ta yi sororo tana duban
Hilal dauke
da yarta Zuhuriyya cikin mamaki.
Zuhuriyya ta dubi mahaifiyarta
tana
murna ta ce.
"Mama ga SHILAL ya zo!".*****
kusan rabin wadanda suka zo liyafar sun
tafi sai yan tsiraru da ke can da
can su da
yan matansu suna neman gindin
zama.
Zainab da Hilal zaune a kusa da
jerin wasu
yan dukus-dukus din fulawowi
masu
kamar lema. Har yanzu Zuhuriyya
na kan
cinyar Hilal tana wasa da
bindigarta.
"Haba Hilal ya ka yi min haka?"
Hajiya
Zainab ta ce tana dubansa kamar
ta
hadiye shi.
"Ki yi hakuri Hajiya, wallahi
mahaifiyata ce
ta tashi jikin ba dadi". Zainab ta
dubeshi
cikin tausayi.
"Ayya Allah ya sawwake me ke
damunta
ne? Hilal ya dan yi shiru yana
wasa da
gashin kan zuhuriyya.
"Hauhawar jini ce ke damunta, ta
dade da
cutar dan tun ina dan karami
nake jin
labarin cutar"****
Zainab ta dube shi cikin
tausayawa.
"Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya,
idan dai
ka ga cutar ta dawo sai ku wuce
da ita
asibiti ni kuma ka zo ka fada
min". Ta ce
tana dubansa
"To na gode Hajiya" Hilal ya ce ba
tare da
ya dubeta ba.
"Me ya sa kake son kirana da
Hajiya?
Kamata ya yi kana kirana kawai
da sunana
Zainab kamar yadda nake
kiranka da
sunanka Hilal." Ta yi masa
murmushi ta
kashe idanu sannan ta ce da
Zuhuriyya
"ke sauka daga cinyarsa, ki tafi
gurin su
Anti Zaliha ki gaida su"
BINDIGAR KWALI--> 4
Zuhuriyya ta sauko daga kan
cinyar Hilal sannan ta dubeshi ta
ce.
"Ina zuwa Shilal yanzu zan
dawo". Ta tafi gurin wasu mata
dake can gefe guda na farfajiyar
gidan wanda Hilal yake
tsammanin a nan Anti Zalihar da
Zainab take fada take.
Zainab ta dubi Hilal cikin sha'awa.
Hilal ya yi sauri ya dauke kansa
bai iya yarda sun hada ido ba,
domin duk da kasancewarsa da
namiji sai ya sami kansa yana
mai kunyar hada idanu da
zainab, kansa a sunkuye gabansa
yana dukan uku-uku. Hakika ya
san ya kamu da masifar kaunar
matar da ba tasa ba. Bai kuma
zargi kowa ba sai kansa, domin
kuskure ne da ya yarda har
matar da ba muharramarsa ba ta
rage masa hanya, domin shedan
na iya yin galaba akan duk
macen da namijin da suka
kadaice, kuma babu aure a
tsakaninsu.
Shirun da ya yi a yanzu zuciyarsa
na bugawa, sai ya gane cewa
tuni shedan ya yi galaba a kansa,
domin kuwa ya san ya kamu da
matsananciyar kaunar matar da
ba muharramarsa ba.
"Hilal..." Ta kira sunansa muryarta
na rawa "Tunanin me kake yi". Ta
tambayeshi Hilal ya dago kansa,
sai ya ji gabansa ya sake faduwa
a karo na biyu, domin koda ya
kalli idanunta, ya san itama ta
mace a kansa kamar koma fiye
da yadda shi yake kaunarta. Irin
kallon da take yi masa shi ya tona
sirrin dake Zuciyarsa. Domin Hilal
ya sha ganin irin kallon a cikin
idanun Rukayya, kallo ne dake
isar da sakon macewar Zuciya
akan abin begenta.
"Zainab..." Hilal shima ya kira ta a
sanyaye. Zainab ta tashi tsaye
sannan ta rankwafa a kan Hilal
wanda ke zaune akan kujera ta
dubeshi cikin kwayar idanu. Hilal
ya ji hucinta na bugun fuskarsa,
hakan shi ya sashi dimaucewa
jikinsa ya fara rawa kamar
mazari, domin tun da yake wata
ya mace bata taba kusantarsa ba
kusa-kusa haka.
"Zainab... Mene ne?" Ya ce
bakinsa na rawa.
"Ka fi ni sanin ko me Hilal, dubi
idanuna ka karanta sakon dake
cikin zuciyata Hilal..." Ta yi shiru
tana dubansa, idanunta suka yi
rau-rau kamar za su zubar da
kwalla.
"Ban fahimce ki ba zainab, na
kasa...." Ta katse shi.
"Ka da ka zolayi kanka Hilal. Haba!
Kada ka zama dan karamin yaro
mana, kai ko makaho ne Hilal in
ka shafi fuskata ai dole ne ka
fahimci sirrin dake zuciyata".
Hilal ya dubeta cikin kunya ya
buda baki zai yi magana sai ya
kasa. Zainab ta dada rankwafawa
kamar za ta hada fuskarta da
tasa ta ce.
"Fadi mana Hilal, ai na san kaima
kana kaunata, in ma kuma ba ka
sona to bari ni yau na warware
ma sirrin dake zuciyata ni
kaunarka nake yi Hilal!!".
***
Kaunarka nake yi!!
Amsa kuwwar kalamanta na
karshe ya sake dukan dodon
kunnen Hilal, tamkar mari da
kususun roba akan gadon baya.
Duk da yake dai ya dade da sanin
cewa Zainab son sa take, to
amma abin da ta ce ya girgiza
shi, domin bai taba tsammanin
ma za ta bayyana sirrin dake
zuciyarta ba a gareshi.
"So na?" Ya tambayeta a
shashance baki bude.
Hajiya Zainab ta zauna tana
dubansa.
"Abin da na ce kenan Hilal, kuma
ina nufin hakan har can cikin
autar zuciyata." Hilal ya yi shiru
yana tunani. Tabbas ya san ya
jefa kansa cikin hadari.
Ya san cewa wannan matar dake
zaune gabansa, tana daya daga
cikin matan manya masu fada a
ji. Yanzu idan Alhaji Hamisu
Jumare ya dawo ya ya zai yi da
rayuwarsa? Na farko dai ya san
idan mijinta ya dawo babu shi ba
sake koda ganinta in ba a hanya
ba. Na biyu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment