Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MAKOTAN JUNA Complete Hausa Novel Document by MAKOTAN JUNA


MAKOTAN JUNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 108480



MAKOTAN JUNA

Reading Time: 9 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Sadnaf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 590.24 kb

File Type: txt

Views: 699+

Download: 1108+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ๏ปฟ[21/07, 03:12] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: *M๐Ÿ…ฐK'OT๐Ÿ…ฐN JUN๐Ÿ…ฐ*


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *P.M.L*



*Written by*

๐Ÿ’…๐Ÿ’…๐Ÿ’… *SADNAF*๐Ÿ’…๐Ÿ’…๐Ÿ’…


*HAPPY SALLAH TO OLL MUSLIM UMMAH AM BACK AGAIN INSHA ALLAH WITH MAH SHORT WRITE UP I REALLY DO HOPE U GUYS WILL ENJOY IT OLL I NEED IS UR PRAYERS I DID NOT PROMISE U GUYS TO BE SEEING MY POST EVERYDAY WEN EVA AM LESS BUSY U GUYS WOULD SEE MY POST HAPPY READING FANS*



*page 1*




Adnan a tsaye yake a gaban mudubi yana gyara zaman hular kansa sanye yake da Ash d'in shadda mai bak'in surfani shaddar ta dace da kalar fatarsa kasancewarsa baki mai d'an kyau

Agogon hannunsa yake sawa Aliya ta fito daga band'akin tana gyara zanin jikinta sanye take da wani bakin less mai torches d'in pink ya bala'in amsarta kasancewarta fara kyakyawa ce ba laifi Dan baza'a sata sahun munana ba.


Wardrobe d'inta ta bud'e ta d'auko wani mayafi pink Wanda ya dace da kalar kayanta ta fara k'ok'arin yafawa akanta

Adnan da tunda ta fito daga band'aki yake binta da kallo ganin ta d'auko k'aton mayafi zata yafa akanta ne yasa ya juyo yana ajiye turaren dayake fesawa yace

"Ke mai haka"?

Aliya da mamaki tace " kamarya fa" ta cigaba da gyara zaman mayafin akanta

"Ba dai haka kike tunanin zaki bini dinner abokina ba"?

A hankali Aliya ta ajiye hannunta jiki a sanyaye tace "mai aibun shigar danayi"?


Tsaki adnan yayi yace "u must be joking idan kina tunanin ahaka zanje wajen dinner abokina dake gwara ki sha zamanki Dan babu yanda za'ayi abokaina suga matata ahaka sai kiyi ta Abu kamar ba wayayya ba ji wani katon mayafin da kika d'auko kamar gidan mutuwa zaki haba Aliya wai meyesa kike hakane yaushe zaki waye ki daina zama cikin duhu gaskiya kina kwapsa min Aliya Dan Allah ki dubi neighbour d'inki wayayya 'yar gayu bata kai ki kyau ba amma ta bala'in iya dressing ke kuwa kamar 'yar kauye wlh
gaskiya ki canja kayan jikinki completely ki samu skirt haka ko fitted gown ki samu medium size Vail ki yafa mu tafi amma kam idan dai bazaki canza shigar nan ba ki sha zamanki gaskiya"


Aliya a hankali ta cire mayafin jikinta ta koma kan gado ta zauna ta buga tagumi tana kallon Adnan daya d'auko well polished cover shoe d'insa yana sawa yana 'yan wake wakensa a k'asan zuciyarta tana mishi add'uar shiriya Dan idan yana wani Abun kamar wanda bashi da addini


Adnan k'ara juyowa yayi yana kallonta yace " au da ki canza shigar jikinki gwara ki hakura da zuwa kenan"?


Rai a d'an b'ace Aliya tace "bazan canja shigar jikina ba indai sai na canza zaka tafi dani kayi tafiyarka kawai tunda baka kishin matarka Adnan yanzu so kake a matsayina na matar Aure na dame jikina in fito da surar jikina sabida kawai ka burge abokanan ka suce kai wayayye ne idan kai Baka San darajata ba bakasan martabar Aure ba ni na sani bazan iya tallatawa abokanan ka jikina ba"



Adnan d'aga kafad'unsa yayi in I don't care manner ya nufi hanyar fita daga d'akin yana "ai ke kanki a tukunya yake some times I do regret how comes some one like me get married to you u are not civilized at all"


Aliya bin bayansa tayi da kallo har ya fice wasu siraren hawaye na zubo mata a k'asan ranta tana mamakin halin Adnan


Adnan wajen da yayi parking motarsa ya nufa adai dai lokacin da Zara ta fito daga b'angarensu sanye da kananan kaya ba ko dankwali tana tauna cingum

Adnan sakin baki yayi yana kallonta sabida yanda ta masifar tafiya da imaninsa haka yake so yaga Aliya na shiga amma ina idan tayi shigar ma sai ta d'auko wani k'aton Hijab ta saka

Sirirrin muryar Zara ne ya doki kunnensa "Hi" tace tana d'aga masa Hannu a dai dai lokacin da take wuce shi tare da nufar b'angarensu


Shima hannu ya daga mata kamar wani soko yace "hi" da idanu ya rakata har ta shige ya sauke wani nannauyan ajiyar zuciya sabida tafiyar ma da ta ringa yi is something else


A hankali yaja kafafunsa ya nufi cikin motar tare da barin harabar gidan


Zara kuwa ko sallama batayi ba ta tura k'ofar ta shige aranta kuwa tana admiring d'in Adnan Dan ba karya gayen ya had'u haka take so Amir d'inta ya ringa gayu amma ina ba shida wayewa ko kad'an Abu d'aya biyu sai ya hau wa'azi ita kuwa arayuwarta tana balain San wayayyen mutum

Ganin bata ga Aliya a palon ba yasa ta nufi bedroom d'inta

Tura k'ofar tayi ta shige a kwance ta Tarar da Aliya still da kayanta a jikinta dankwallinta kawai ta cire ta ajiye a gefe idonta a lumshe tana d'an karkad'a k'afa shigowar Zara d'akin ne yasa ta bud'e idonta



"Ya baku tafi dinner tare ba na ganki a kwance"?

Cewar Zara a dai dai lokacin da take zama a gefen gadon


Aliya kuwa mik'ewa tayi a hankali fuskarta d'auke da mamakin shigar da Zara tayi duk da ba Yau ta saba ganin Zara da wanan shigar ba amma na Yau ya bata mamaki a matsayinta na matar Aure da kuma tasan basu kadai bane a gidan Dan wani wando tasa 3qtr sai wani matsassen top daya bayyana surar jikinta Kanta kuwa ba dankwalli


Zara kuwa comfortably ta cigaba da tauna cingum d'inta tana wani irin Abu da ido


"Zara kina da hankali kuwa kinga yanda kika fito fa amatsayinki na matar Aure and kuma kinsan ba ke kadai ce a gidanan ba yanzu da kun had'u da Adnan fa"



Zara tsaki tayi tace "kina da matsala wallahi Aliya mai aibun shigar danayi so kike Nima na ringa jibga kaya a jikina yanda kike jibgawa bazan iya bafa shikenan Dan ina da Aure sai na takurawa rayuwata wlh bazan iya ba ina mamakin ke da Amir bakuda wayewa ko kad'an wlh haka kawai a wanan zamanin kayi gayu ma ya ka kare ballantana ma ace kana zaune haka"?


Aliya girgiza kanta tayi kawai Dan tasan Zara tayi nisa bata jin kira


" Hmm Zara kenan gaskiya ce dai bazan fasa gaya miki ba wanan ba wayewa bace halaka ce bance karki yi gayu ba kiyi daga ke sai mijinki
Dan shi ya hallata yaga kwalliyarki ba wani ba amma bai kamata kiringa wanan shigar kina fitowa ba al halin kinsan bake kadai ce a gidan ba Dan kinga bai kamata Mijina da ba muharraminki bama yaganki da wanan shigar ba Dan haka nidai Dan Allah ko Dan mijina kidaina fitowa ahaka ya kamata kiringa darajar Auren dake kanki kiringa taya mijinki kishin kanki"


Dariya Zara ta kyalkyale dashi harda rik'e ciki tace


"Aliya kenan aure bazai hanani rayuwar Dana Riga na saba dashi ba babu wani aibu a shigar danake yi babu ruwan wani da rayuwata batun kuma mijinki ni ina ruwana dashi naga nima ina da nawa mijin idan ma yaga irin shigar danayi ya burge shi ke kika jawo Dan kece bakya masa irin shi"


Aliya kallonta kawai take tana hango tsantsar rashin ilimi da rashin hankali a tattare da ita girgiza kanta kawai tayi tace "Allah ya shiryeki Zara nidai kidaina yawo haka sabida bake kadai ce a gidanan ba mijina zai iya ganinki da wanan shigar"

"Na nawa kuma yama gani dan yanzu ma daya zo fita mun gaisa ina ruwanshi dani ke da bazaki ringa masa kwalliya ba ai sai kiyi ta zama ahaka Dan Allah ji wani kaya da kika saka haba Aliya wai yaushe zaki wayene dazu kikace min tare zakuje dinner abokinsa hala sabida wanan manyan kayan da kika sa yak'i tafiya dake kashhh I wish ni nake samun opportunity da kike samu wlh ko hmmm ba a magana"


Aliya tsaki tayi ta koma ta kwanta Dan taga alamar Zara bata da cikakken hankali ahaka Zara ta karaci surutunta sai da ta jiyo horn d'in Mijinta Amir ta mik'e ta fice Aliya kuwa ta bita da add'uar shiriya.




Adnan kuwa awajen dinner 'yan mata kawai yake bi da kallo Dan rabinsu surorinsu awaje yake nonuwan nan luhum luhum kamar zasu huda Riga su fito sai lashe lebb'e yake wata kawar amarya meera ce ta balain tafiya da imaninsa Dan mazaunanta manya manya ga hips tommynta very flat shape d'inta yafita sosai duk da bata kamo Aliyarsa a kyau ba amma fa ta tafi da imaninsa sosai


Ahaka ya ringa monitoring d'inta da ido idan ta shiga filin rawa sai ya tashi ya mata
Liki sai yanzu yake godewa Allah da Aliya bata biyo shi ba


Meera kuwa tuni itama taji Adnan
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MAKOTAN JUNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album