Join Our WhatsApp Group

DUKAN RUWA Complete Hausa Novel Document by DUKAN RUWA


DUKAN RUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 96585



DUKAN RUWA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 03, Apr 2023

Author: Rufaida Omar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 479.04 kb

File Type: txt

Views: 11789+

Download: 6673+

Last download: 18 minutes ago

Description/Story: ba za su kai ba. Wani lokacin idan sun gifta bukkokin jama'ar wani yankin, takan yi murmushi cike da al'ajabin ta yadda mutum ƊAN ADAM ke iya rayuwa a wannan wuri. Tun tana kallon har dai ta zame ta gyara zama gami da lumshe idanu, bacci ke ƙoƙarin ɗaukarta tana yakicewa. Babu abin da ta tsana sama da bacci a hanya, hanyar ma da ko a mafarki ba ta taɓa ganin za ta bi ba,  zuwa Nijeriya daga Nijar.
Ajiyar zuciya ta saki tamkar wacce ta ci gudu, lokaci guda nannauyen tunanin da take ƙoƙarin kaucewa na ƙara yi mata saukar aradu a kwakwalwa. Idanunta ta sauke akan matar dake kusa da ita, baccinta take haiƙan har carbin da ke riƙe a hannunta tana ja, ya faɗi. Sai dai duk da baccin da ta lula, hakan bai sa ta saki yaronta ba, yana rungume a kirjinta ɗam! Kai ka ce wani ne zai ƙwace mata shi. Juya kai tayi ta koma kallon hanya da murmushi ɗauke saman fuskarta. Soyayya da shaƙuwar dake tsakanin ɗa da uwa na daban ne, a kowane yanayi, a kowace rana burin kowace uwa ganin gudan jininta cikin walwala da annashuwa, ba ta fatan wani mugun abu ya same shi. Shakka babu duk wanda ya rayu da uwa ya more.
  Sai kuma kewa ya lulluɓe ta dalilin Dada da ta tuno, watanni biyar kenan da rasuwarta amma jin sa take a rai tamkar jiya-jiya. Kullum mutuwar kakarta kamar sabo ne fil a wurinta, mace mai hakuri da dattako, ta yi namijin kokari wurin ba ta kulawa daidai gwargwado da kuma tarbiyyar islama. Ba ta shaƙu da kowa ba sama da ita sai ko Kawunta ɗan uwan Mamanta, Kawu Umaru. Shi ma ba ta jin za ta manta da irin namijin ƙoƙarin da ya yi a kanta, koda dai dama barewa ba ta yi gudu ba ɗanta ya yi rarrafe, wannan kyawawan ɗabi'un Dada ne suka kwaso. A wannan irin namijin ƙoƙarin ne a yau Kawunta ya tashi haiƙan suka bi wannan doguwar hanyar kawai don ya sada ta da mahaifinta, mutumin da tun da ta buɗi ido ba ta taɓa ganinsa ba. Hatta a waya ba su taɓa koda gaisawa ba.  Duka wannan bai sa ta riƙe mahaifinta a zuciya ba domin kuwa ya samu kyakkyawar shaida a gurin Dada da Kawu. Ko sau ɗaya ba su taɓa kawomata kushensa ba, asalima sun ce yana sonta sosai, kuma acewarsu ya sha zuwa ganinta tana ƙarama, su ɗin ne suka ƙi amincewa ya tafi da ita bisa dalilan da su kaɗai suka bar wa kansu sani. A yau kuma da aka wayi gari babu Dada, Kawunta ya ɗauki ɗamarar cika wasiyyar da Dada ta bari na cewar ya sada ta da Mahaifinta idan har rai ya yi halinsa.

  Ɗan girgizar da motar ta yi sakamakon taka wani ɗan tudu ne ya sa ts ji saukar ruwa a saman leɓɓanta, sai lokacin ta gane kuka take. Kukan kewa da damuwa ne, Dada ta tafi, tafiya ta har abada, ta tafi wajen da ba za ta sake ganinta ba sai ko idan nata ajalin ya iso, ta je ta tarar da ita.
  _"Kar ki taɓa bakin ciki da zuwa wurin Mahaifinki Shatu, mutum ne nagari mai sanyin hali, za ki yi farin ciki da ganinsa. Yana sonki sosai Shatu."_

Kalaman Dada suka faɗomata a rai, ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, lokaci guda ta ciza leɓɓanta na ƙasa tana ƙara murmusawa karo na barkatai. Ya mahaifinta yake? Da wane ido za ta ɗaga ta kalle shi ya kalle ta? Dagaske tana kama da shi ko kuwa dai Kawu ya faɗi ne don ta ji dadi? To an ce yana da wasu yaran, su ma tana kama da su ko aa?

Duka waɗannan tambayoyi ne da ta hargitsa lissafin kwakwalwarta da su alhalin babu mai ba ta amsa. Haka dai ta yi ta saƙe-saƙenta har suka fita gaba ɗaya daga Nijar suka nufi bodar Nijeriya.
Nan ɗin ma bayan kammala cike-cike da duba kayyakinsu, suka gangara cikin Nijeriya, ta baza ido tana kallon yanda cikin iko da hukuncin Allah, shuke-shukensu ya sha bamban da na ƙasar da ta fito.

***

"KATSINA" Ta karanta sunan a hankali, sannan ta dinga bin garin da kallo tana ƙarewa bambance-bambancen garin da nasu. Tunaninta ya katse sa'ilin da direba ya  tsaya a gefen hanya domin ba su damar gabatar da sallar la'asar. Mazan duk suka riga su sauka, su ma suka sauko. Kawu ya dube ta.

"Ki bi su ku yi sallah kar ki je ko'ina kin ji ko?"
Ta gyada kai ta amsa da toh, tana rungume da ƴar ƙaramar jakarta ta hannu haka ta dinga bin matan su uku har zuwa wani ɗan wuri da aka katange, suka samu gefe guda da ba mutane, masu jin fitsari suka yi sannan suka ɗaura alwala. Bayan sun idar suka dawo motar, nan kuma kowa ya hau zuge jaka ya na siyan abin motsa baki. Tana nan zaune cikin motar Kawu ya kawo mata ruwa da lemu sai nama a leda, kaɗan ta ci bayan ta yiwa ƴan motar bismillah, sauran ta naɗe ya ajiye a gefe, lemun dai ta sha sosai.

Daga nan suka ƙara miƙa hanya har dai cikin hukuncin Allah suka ƙaraso cikin garin KANO.

Ta nanata sunan a kan harshenta jin wata Mata ta ambata, ta maimaita har sau uku, lallai idan ba ta mance ba shi ne sunan da Dada ke yawan ambata idan ta tambaye ta sunan garin Mahaifinta.  Nan da nan zuciyarta ta yi fari ƙal, ta kasa rufe bakinta, wannan karon murmushi take tun daga ƙasan zuciyarta har saman leɓɓanta don har siririn wushiryarta na bayyana. Sai da suka ƙarasa tasha suka sauka, daga nan ne kuma Kawunta ya ɗauki akwatin kayanta suka fito bakin titi. Suna hawa taji ya ce unguwar Gadon Ƙaya, daga nan direban ya hau tafiya ita kuwa tana ta kallon hanya har suka sauka. Sun yi ƴar tafiya a ƙafa sannan ta ga ya tsaya daidai bakin wani ɗan shago ya yiwa mai shagon sallama. Koda suka gaisa ya ce.

"Don Allah gidan Alhaji Isuhu Maiagogo nake tambaya."

Mai shagon ya gyada kai ya ɗan fito sarari ya hau yi musu kwatance da hannu. Ya yi godiya suka nufi inda ya ce.

Koda suka karasa wajen wani ƙaton gini ta ga ya tsaya cak a gaban ginin, ta bi ginin da kallo ta ji gabanta ya yanke ya faɗi lokaci guda, ba kuma don tasan dalili ba. Ta kasa kwakkwaran motsi har Kawunta ya taka zuwa ga kofar gidan yana tambayar wani dattijo ko nan ne gidan, amma ita kam ba ta dauke kai daga kallon ginin ba, gwuiwoyinta suka yi wani irin saki, ganin yanayin da ta shiga har zufa na tsastsafomata a goshi yasa ta dinga maimaita kalmar innalillahi.

"Shatu ke!"

Kiran da Kawu ya kwalamata ne ya maido ta hayyacinta, a hankali ta soma takawa har ta ƙarasa gefensa, ba ta kuma san dalili ba ya ji ta sa hannu ta riƙo nashi yatsun gam!
Hakan da tayi ya sanya shi dubanta, itama shi din take kallo, ya yi dariya.

"Tsoro gidan ya ba ki ne? To ki shirya yaƙar tsoron nan don nan ne gidan zamanki daga yau in sha Allahu."

Dattijon ya taya shi darawa kaɗan duk da bai fahimci komai ba. Amma ta lura da yadda yake ta kallonta har ya kasa hakuri ya tanka.

"Amma dai wannan ƴar uwar Alhaji ce ko?" Kawuna ya yi dariya ya amsa da eh kawai. Ita dai ba ta ce musu uffan ba sai sadda kai ƙasa da ta yi, ta na ji Dattijon nan na kara zuzuta kamanninta da Alhajin wanda shi ya sanya shi tankawa.  Suna nan dai  tsaye sai ga wani ɗan matashin yaro ya fito, ashe wai Dattijon ne ya aika shi gidan don a shaida wa Maigidan zuwansu.

"Ya ce maza ku shigo ciki. Muje na raka ku."

Daga haka  suka shiga ciki. Madadin faɗuwar gabanta ya ragu, sai ma ƙara hauhawa da ya yi, ta ci gaba da maimaita innalillahi har ƙarshe, sai ta ji gaba daya ta bar rawar ƙafar son haɗuwa da Babanta Isuhu.

   Koda suka ƙarasa cikin ƙaton falo, wani irin sanyi da ƙamshi mai dadi ne ya daki hancinta. Ta gefen ido take bin wurin da kallo tana so tayi ido huɗu da Babanta, sai dai kuma duk irin girma da daular da ke shimfiɗe a falon wanda ya ƙara ƙawatashi, babu rai ko ɗaya mai numfashi face su ukun da suka shiga.
Wuri ya nuna masu saman kujera suka zauna, ita kuwa ƙasa ta zauna gefen Kawu don ba'a ba ta tarbiyyar zama saman kujera alhalin manya na zaune ba. Matashin ya kara juyowa fuskarsa a sake.
  "Ku jira Yallaɓai nasan ba zai jima ba zai fito." Kawu ya amsa daga nan ya fice ya bar su a nan. Sun samu mintoci goma da sakanni, don gaba daya hankalinta yana kan ƙaton agogon da ta zauna saitinsa, kafin ta ƙarasa ƙirgenta suka tsinkayi sallama. Lokaci guda suka kai duba ga gefen da muryar ta ɓullo, baki da ido ta saki tana kallon mutumin yayinda shi kuma idanunsa ke kan Kawu, kallon mamaki da tsantsar farin ciki yake binsa da shi.

A gefenta kuwa halittar fuskarsa take ƙarewa kallo. Eh, tabbas suna kama, fuskarsa doguwa kuma siririya irin nata, yana da dogon hanci masha Allah, sai kuwa bakinsa daidai. Idanunsa manya kamar naya hatta da cikar halittar girarsa da gashin kai, duk kuwa da cewa shi nasa gashin ya yi fari fat na manyanta amma kamanninsu da shi sun fito fes har tsawon. Ba ta ƙara gani ba sai da ya saki dariyar farin ciki, anan kuma baki hangame ta ce. "Kai!" Ta furta a fili ba tare da ta shirya ba. Gaba daya suka juyo su na dubanta. Ta kama bakinta da sauri gami da ƙara sunkuyar da kai, mutumin ya matso ya durƙusa a gabanta, zuciyarsa ta yi wani irin nauyi, abubuwa da dama suka shuɗe a tsawon shekarun baya suka dawo mishi sabo fil. Ita kuwa kunya ce ta kama ta, bata ma gaida shi ba, ta gaishe shi a hankali don a zaton ta ma bai ji ba, amma ga mamakinta ya amsa.

"Barka da zuwa Mamana. Ki saki jikinki nan gidanku ne, gidan Abbanki, ba ki da inda ya fi nan kinji ko?"

Da ya fadi haka wai sai ta kalli Kawu, hakan da tayi ya ba su dariya. Kawu ya gyaɗamata kai.

"Idan eh kike so nace ko aa, toh eh Shatu, gidan mahaifinki kenan. Abin tunƙahonki."

Ta yi murmushi tana kara duban wanda ya kira kansa da Abbanta, sai nan da nan kwalla ta cikamata idanu. Wannan fargabar ta kau, so da kaunar suka dawo daga hutun da suka je, ta rungume hannunsa ta saki kuka sosai. Abubuwa da dama take tunawa, tabbas ta yi kewarsa a rayuwa. Koda ace ba ta rasa ci, sha da sutura ba daidai da kwana ɗaya a rayuwa, to ta rasa wannan kusancin na ɗa da mahaifi, shi din na dabanne. Ko ma dai tace ta rasa soyayyar iyaye gaba ɗaya.

"Kiyi hakuri Mamana, ba zan ƙara yin nesa da ke ba, wancan ma ƙaddara ne, amma wannan karon in sha Allahu ni da kaina zan miƙa ki ɗakin mijinki. Allah ya ji ƙan Mahaifiyarki da Hajiya Dada."

Suka amsa da amin. Nan kuma ya shiga jan ta da hira kadan har ta sake, waya ya zaro a aljihu ya danna kira, sunan wata ya ambata, Ummita, ya ce ta zo yanzu. Daga haka ya  juya ga Kawu suka yi ta hira yana ba shi labarin rashin lafiyar Dada har zuwa rasuwarta. Suna nan zaune ita kam ta kasa ɗquke ido akan Abban, suka tsinkayi sallamar wata ƴar budurwa da ba ta wuce sa'arta ba. Baƙa ce, irin baƙin da hutu ya ratsa, riga da wando ne a jikinta sai dai ba su ɗame ta ba, ta saka hijabi iyaka kafaɗarta. Ta gaida Kawu sannan ta maida hankali ga Abba.

"Yauwa Ummita, kama hannun ƴar uwarki ku je a ba ta abinci ta ci ta yi wanka. Ki kuma faɗawa Maminki ina da baƙo a shirya masa abinci kafin mu yi sallah. A kawo ruwan sha."
Ummita ta amsa da toh tana kallonta fuskarta a sake ta ce.  

   "Lah Abba wallahi kuna kama sosai."

Duk sai ta ba su dariya, Abba ya dubi Aisha Humaira kafin ya maida duba gareta.

  "Itama ƴata ce, ita ce mai sunan Umma."

"Abba ita ce wacce ka ce tana Nijar ko?" Wannan karon da wani irin zumuɗi ta yi tambayar. Ya amsa mata da eh. Ta kuwa karaso da sauri ba tare da nuna kyankyamin komai ba ta rungumeta tana fadin. "Welcome Sister." Ba ta gane me ta ce ba amma itama ta rungumeta tana mai jin kaunarta har can ƙasan ruhinta.
  Ummita kenan, tana daga cikin mutane masu girma da matsayi sosai a rayuwar Humaira, har abada Humaira ba za ta cire ta a tarihin rayuwarta ba, ta karɓe ta a yadda take, ƴar kauyen Maine. Ƙamshi take a yayinda ita kuwa ba ta ma sani ba, ƙarnin kifin da ta ci a mota take yi ko kuma naman da ta ci ne. Kai ko ma mene ne, ta sani Ummita ba ta irin wannan ƙarnin, ƙamshi ne a jikinta, amma ba ta duba komai ba ta rungumeta. Ta tabbata tana daga cikin masoyanta na haƙiƙa. Ta kama hannunta ɗayan hannun kuma ta ɗauki akwatin kayanta wanda duk ya ci gidansu, akwati ne irin na da da aka yi yayinsa, Dada ta ce nata akwatin tun na auren Mamanta ne.
  Suka nufi wata ƴar siririyar hanya suka fito wurin wani ƙaramin hanya nan ma gefensa duk shuke shuke. Wurin ya burge Aisha Humaira sosai, a daidai ƙofar shiga wajen ma, shukoki ne sun kewaye jikin ƙofar da bango sun ba da zane mai kyau. Ummita ta ci gaba da tafiya har suka nufi wani ɓangaren, baranda ne sai kuwa wata ƙofa, suka shiga Ummita ta shiga kwala ihun kira.
"Mami! Mami!! Fito ki gani!"

Ihun da take tana kira ya sa sauran mutanen dakin suka fito. Maza da mata wadanda sun ɗan girme ta sai ko yara.

"Wai Ummita me ke damunki haka? Tun ɗazu bakinki ya ƙi..."

Aisha Humaira ta lura haɗa idanun da suka yi ne ya sa sauran kalaman bakin matar suka maƙale. Kallonta take kamar a razane, ita kuwa kallonta take tana so ta ga ta inda suka yi kama da Ummita don ko kaɗan ba su yi kama ba. Ummita baƙa ce, wannan kuwa ta tsaye a gabanta da alama ma buzuwa ce. Gashinta a tufke a baya, ta kai duba ga wasu a cikin yaran, su ma farare ne ƙal, kyawawa da su.

"Wace ce wannan?"
Ɗaya daga...


Read / Download DUKAN RUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

5 Comments On DUKAN RUWA
avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

hhh

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
daiy drop

1 year ago

Reply

sss

avatar
north

12 months ago

Reply

hhhhh

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album