Join Our WhatsApp Group

KARO DAYA Complete Hausa Novel Document by KARO DAYA


KARO DAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20341



KARO DAYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Fatima Rabiu Ummu Affan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gawurtattu Biyar

Author Phone : 08104335144

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 109.31 kb

File Type: txt

Views: 769+

Download: 160+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: *KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU._🤟


01

Dukkansu zaune suke a ɗan madaidaicin parlournsu suna cin abincin rana, mahaifiyarsu Malama Rabi da suke kira da Umma sannan babban Yayansu Ma'aruf wanda bai daɗe da shugowa ba sannan ƙannansa guda Uku Muwaddat Zulfa'u sai ƙaraminsu Dawud.
Kallo ɗaya zakawa fuskar Muwaddat ka gane kamar akan dole take cin abincin, haka ne kam amma ba wai girkin ne bai mata daɗi ba a'a. Kawai tana can duniyar tunanin masoyinta wato Sadik wanda ya kira wayarta cewar tazo yana son ganinta. Ita kuwa takan bawa komai nasa muhimmanci domin irin tsananin ƙaunar da ke tsakaninsu.

Wata dubara ce ta faɗo mata kallon Umma tayi ta ce"Yawwa Umma na fa manta Salma ta ce mini yau Mamarsu zata fita wai naje na tayata aikin gida, saboda aikin zai mata yawa." Sanin yadda Muwaddat da Salma suke wato awaye kuma aminan juna, yasa Umma cewa,
"To amma fa karki daɗe domin kin san halin Babanku idan ya dawo bai iske ki a gida ba." Cike da farin ciki ta amsa da "Ba zan daɗe ba in sha Allahu Ummana."
Da sauri ta miƙe tare da zura hijabinta har ta doshi hanya Yaya Ma'aruf wanda tun ɗazun yake dubanta ya ce"Amma duk wannan zumuɗin na zuwa gidansu Salma ne?"
Ya tambaye tacike da tuhuma.

Sanin halin Yaya Ma'aruf yanzu zai iya ɓata mata shiri yasa na daidaita na tsuwarta,
"Nasan tana ta jira na ne yanzu."
Da sauri na fice, shi kuwa bin ta ya yi da kallo sam bai yadda da ƙanwar tashi ba, wacce ta ke marainiya a hannun iyayensa, tabbas Muwaddat tana cikin wani hali da ya kasance mara tsari da san ambata, babbar matsalar iyayen nasu sun yarda da ita sosai gashi son da suke mata tare da tausayin rasa iyayenta da tayi tun tana ƙarama yasa ba sa ganin laifinta.
Girgiza kai kawai ya yi amma dole ne ya yi wani abu a kai domin ada ba haka halinta ya ke ba sam.

Muwaddat Kuwa tana fita kai tsaye gate ɗin gidansu Yaya Sadik ta tura, ta gaishe da Maigadi tare da cewa"Salma tana ciki kuwa?"
"Eh ranki ya daɗe." Ya amsa mata, hanyar cikin gidan ta nufa har ƙafafuwanta na hard'ewa saboda sauri.

Kai tsaye part d'in *Sadeeq* ta wuce,bayan ta waiga taga ba kowa dake kallonta.

Zaune ya ke akan d'aya daga cikin kujerun dake parlourn,yana sanye cikin Boxer da singlet,center table a gabansa da cup wanda coppee ke ciki lokaci-zuwa-lokaci yana kur6a.

Jin an bud'e k'ofa yasa shi d'ago rikitattun idanuwansa masu matuk'ar kyau da haske gasu manya a ko da yaushe yanayinsu kamar na mai jin barci,murmushi ne kwance saman fuskarta yayin da shi kuma babu alamar fara'a a tasa fuskar,ganin haka ta k'araso da sauri tare da zama gefensa tace" Yaya *Sadeeq* me ya faru?" bai ce mata komai ba,cike da damuwa ta jawo hannayensa ta rik'e k'am a nata tace"please Yayana wallahi abinda yasa ban shugo lokacin da ka kirani ba Yaya *Ma'aruf* yana gida kuma sarai kasan halinsa."

Fincike hannayensa yayi daga nata yace"to sai me?akan wannan wawan Yayan naki yana gida musaki wanda lafiyar ma bata ishesa ba kika k'i amsa kirana a lokacin da ya dace" Runtse idanuwanta tayi da k'arfi domin bata ji dad'in *MUSAKI* da ya kira Yaya *Ma'aruf* d'in ba, cikin Cool Voice d'inta tace"am very sorry dear hakan bazata sake faruwa ba" d'ago shanyayyun idanuwansa yayi ya zuba mata yace"da gaske" "yes" ta basa amsa.

Jawota yayi jikinsa yace"ok yayi kyau amma kinsan bana so kina min maganarsa idan har muna tare" gyad'a kai tayi tare da k'ara kwantar da kanta bisa kafad'arsa tana jin wani irin sonsa na k'ara shigarta.

Yaya Sadeeq Yaya ne a gurin k'awarta kuma aminiyarta Salma wacce k'awan can nasu tun yarinta ne kamar yarda Soyayyar Sadeeq da Muwaddat ta ke tun yarinta,duk da Sadeeq d'in ya girme mata nesa ba kusa ba.

Ya mutsata ya farayi son ransa ita ma tana biye masa,domin tun bata saba ba yanzu har tasa ba dashi,tun tana k'iyawa amma yanzu abin ya zamo tamkar jikinta,tana son Sadeeq sannan tana son komai na jikinsa bata k'yank'yaminsa kamar yarda shima hakan duk da kuwa Sadeeq d'in yana shaye-shaye,sai-dai a gurin Muwaddat wannan ba komai bane domin son da take masa ya zarta misali.

Tun suna abu a parlour har ya kinkimeta zuwa cikin bedroom d'insa,nan ne dukansu suka manta da kowa da komai,har Allah dake sama yana kallonsu,sunyi nisa matuk'a cikin lamarin,tuni daman ya cire mata hijabi tun a parlour,hannu yasa ya zage zip d'in rigarta nan take komai na k'irjinta ya baiyana k'ara haukace mata yayi,gaba d'aya ya fita cikin hayyacinsa,yarda yake matsa boobs d'inta abin zai baka mamaki kamar wani mayun wacin zaki,hannu ya kai zai zare mata fant tayi saurin kai hannunta saman hannunsa tare da girgiza masa kanta.

Cikin wata irin mayen murya yace"Muwaddat me ye haka?tace"ban san me yasa duk ranar da hakan ta faru ba Yaya *Ma'aruf* sai ya gane,na rasa gane kansa" Mtsuww yaja tsaki yace"wannan ne zai hana muji dad'inmu?mance da kidahumin" nan yaji gaba da abinda yake,ganin da gaske fa yake *Muwaddat* ta rik'e hannayensa ta mau tace"Pls Yaya Sadeeq gobe sai muyi wllh yau Yaya Ma'aruf zaizo gidanmu" cikin murya mai kama da maye yace"Muwaddat yanzu akan wani wawa cen zamu 6ata wannan lokacin to hakan ba zai yuwu ba."

Fin cike hannunsa yayi sannan ya matse mata hannaye duka ya d'aura mata duka nauyinsa ta yarda ko k'wak'k'waran motsi bazata iya ba bare kuma tace zata k'waci kanta.

Hawaye ne suka wanke fuskarta domin a gaskiya abin na Yaya Sadeeq ya fara bata haushi akan me zai mata dole sannan ya d'aura mata nauyinsa duka gaba d'aya,haka ya fara aikinsa akan Muwaddat wacce saboda takaici ma ko motsin k'yirki ta kasa,ashe daman so ya kan zamo k'iyayya me yasa saboda Yaya Sadeeq ya ga duk wani so da kulawa ta damk'asa garesa yake mata hakan?tabbas tasan tana son Sadeeq fiye da tunanin mai tunani zata iya bawa Sadeeq duk abinda yake buk'ata koda menene saboda son da take masa.

Gashi babban abin takaicin ko me ya mata bata ta6a ganin laifinsa,kai koda bugunta zaiyi kuwa k'arshe kenan,wani irin so da k'auna take masa wanda k'watantasa ma 6ata baki ne.

Bayan ya gama budirinsa Bathroom ya fad'a,bin bayansa tayi da kallo tare da goge kuntun hawayen dake zubo mata.

Kusan minti talatin kafin ya fito,d'aure da towel wani kallon banza ya zuba mata da cewa"Wai Muwaddat me ma ya shugo dake part d'ina da kinsan ba farin ciki zaki bani ba?yanzu akan wani banza cen kike fad'amin maganar ta tazo bakinki?Ok na gane manufarki saboda shi ba zamuji dad'in rayuwarmu ba,to naji saiki tashi ki fitar min daga bedroom"

Sosai Muwaddat ta fara kuka jin maganar da ya ke,kana tace"haba Sadeeq kai kasan yarda kake a gurina amma wllh ina mamakin yarda Yaya Ma'aruf ke da saurin gano ni" yace"to sai me?shi kinsan abinda yake aikatawa a waje?ke bari kiji wllh irinsu sunfi munafunci da iskanci idan zama kiyi abinki gyara kiyi don yanzun babu wani da zaka yaba kowa shegen kansa ne."

Tace"shi kenan hakan ba zai kuma faruwa ba" kanne mata ido yayi da cewa"daman ni babu abinda naji d'azun yanzu sai ayi mai dalili" murmushi tayi har kumatunta biyu suna lotsawa tace"Nacewa Umma bazan dad'e ba,amma kayi hakuri anjima zan dawo" girgiza kai yayi tare da sake nufarta yace"no ban yarda ba ajiyar dani dadi tukun" haka ya sake afka mata wannan karon ta saki jiki sosai sukaji dad'i,kusan awa guda sannan suka fad'a toilet tare anan ma sun kwashi lokaci kafin kuma su fito,kayanta ta mayar da sauri jin ana kiran magrib tace"Yaya Sadeeq bari na wuce" d'aukarta yayi chak ya nufi hanyar waje da ita,suna zuwa k'ofar parlounsa tace"Please Yaya Sadeeq sauke ni anan na k'arasa"yace"ni dai har gate zan kai ki"idanuwa ta zaro da cewa"a'a wllh na gode."

Direta yayi yana murmushi,d'aga masa hannu tayi tare da saurin fita,ta nufi gate saiji tayi Salma na kiran sunanta ta baya,sosaoi k'irjinta ya fara bugu a rikice ta juyo,suka had'a ido da Salma...

Wani irin kallo Salma ke binta dashi wanda ya saka k'irjinta bugu ba sassauci,murmushin yak'e ta k'ak'alo da cewa"Salma daman...da sauri Salma ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu tace"Me ya kaiki Shashin Yaya Sadeeq a wannan lokacin?."

Ran Muwaddat ya d'an sosu tace"Salma me kike nufi da wannan tambayar bayan kin san tsakaninmu da shi" tace"da kin fara amsa min tambayata tukun" Muwaddat tace"Girki ya sani na masa shine na kaimasa."

Wata sanyayyar ajiyar zuciya Salma ta saki tare da cewa"Muwaddat ke k'awata ce,bana son wani mummunan abu ya sameki,wallahi jinki nake tamkar 'yar uwata" tace"Amma ai Yaya Sadeeq d'an uwanki ne me yasa kike tunanin zai min wani abu?k'ara sowa tayi kusa dani tare da dafa kafad'ata tace"Muwaddat duk inda namiji da mace suka ke 6ance to na ukunsu shed'anne,ni bana zargin Yayana ko ke amma zuciya bata da k'ashi kowa zai iya aikatawa" tafiya Muwaddat ta fara da cewa"ni dai na wuce gida kar Umma ta jini shuru" daga haka ta fice.

Maigadi wanda tun d'azun yake jin hirarsu ya k'ara so,har Salma ta juya yace"ai kuwa Hajiya wannan yarinyar tafi awa uku da shugowa wannan gidan,amma nayi mamakin jin hirar rakinku" k'irjin Salma ya buga da k'arfi ta dai daure da cewa"eh daman ai muna tare,yanzu rakota nayi" yace"to ranki ya dad'e."

Salma ta juya ciki zuciyarta na tafasa,sai yaushe Yayanta zai chenza hali,abin takaicin da k'awarta mafi kusanci da ita,k'awarta da take so take ji har cikin zuciyarta,da wannan tunanin ta k'arasa ciki.

Muwaddat tana tafe tana mitar"Wallahi Salmar nan kin fiye saka ido,kusan halinku guda da Yaya Ma'aruf. Umma ta dubeta bayan tayi sallama tace"Kyakkyawa naga kin dad'e ke da kika ce bazaki dad'e ba" da ya ke haka Umma ke kiran Muwaddat Kyakkyawa. Sosa k'eya tayi da cewa"Umma girkin ne mai wahala kuma ita bama ta iyashi sosai ma,nice ta mata kin san dai yarda DAMBUn shinkafa yake da wahala,kuma irin wanda kike mana na musu" (Muwaddat ko kunyar k'arya babu😂😂).

Umma tace"ayya hakan na da kyau kin kyauta ai" da haka ta k'arasa ciki, hijabinta ta cire sannan ta fito ta d'auki buta don yin alwala,ganin Umma ta shiga ciki da sauri ta bud'e tukunyar da ta d'aura ruwan zafin da zatayi wanka saboda ta ida girkinta,cika butar tayi da ruwan zafi ta shige bayi da sauri don karma Umma ta fito ta ganta,ta dad'e tana tsarkin domin tana jin dad'in ruwan zafin sannan ta fito taja ruwa rijiya ta d'aura alwala.

Idar da sallar isha'i Yaya Ma'aruf ya shugo gida,sosai k'irjin Muwaddat ya buga saboda tasan halinsa sarai na rashin mutumci domin bai raga mata,tana jinsa tayi saɗaf-saɗaf zata shiga ciki ya kira sunanta." Muwaddat " cikin muryarsa mai sanyi da matuk'ar dad'in sauraro,fuskarta d'aure ta juyo wani kallo ya ke binta dashi tun daga sama har ƙasa, nan take ƙafafuwanta suka fara rawa saboda kallon da yake mata,
"Kawo min abinci." da sauri ta nufi han yar kitchen har tana tuntuɓe ya bita da kallo cike da ƙaunarta, tabbas yana matuk'ar k'aunar k'anwar tasa sai-dai yana haukan banza me domin bata san yanayi ba, sannan ya daɗe da gano SON MASO WANI ne ƙoshin wahala domin ƙanwar tasa tuni tayi nisa a son waninsa wato Sadik wanda daga gidansu Sadik har nan gidan kowa yasan da soyayyar da ke tsakaninsu duk da an gano tamkar Muwaddat ce ke haukanta a yanzu tabbas a baya Sadik ya so Muwaddat tamkar me, amma a yanzu kuwa tamkar ita ce ke son sa domin abin nasu ya yi kama da Son maso wani ko da yake ganin har yanzu suna tare mutum ba zaiyi shaidar haka ba.

Abincin ta kawo masa, sannan ta tashi tayi shigewarta ciki, wayarta ta iske tana ɓurari da sauri ta ƙarasa ganin lambar Sadik jikinta har rawa yake ta ɗauka.
"Muwaddat kira na biyu fa kenan baki ɗauka ba? Bakinta har rawa yake wajen furta.
"Wallahi ina kitchen ne yanzu na shugo."
"Ina ƙofar gidanku ki fito yanzu ina jirankiwallahi ni kad'ai nasan abin da nake ji, kece kawai maganin matsalata." numfashi taja da cewa"Yaya Ma'aruf fa yana gida Sadik" Cikin ƙuluwa ya ce"Waini Muwaddat Ma'aruf ubanki ne ko ya? Kin ga ki fito ina jiranki domin a matse na ke,idan kuma tsoransa zai sa bazaki fito ba sai ki sanar da ni???"....
*KARO ƊAYA...!*


©UMMU AFFAN


_GAWURTATTU UKU 2023 🤟_


02

K'irjinta taji ya buga da k'arfi jin ya yanke kiran,wayar tabi da kallo hankalinta a matuk'ar tashe,saurin chenja kayan jikinta tayi zuwa doguwar riga ta atamfa sannan ta shafe jikinta da humra ta d'auko babban hijabinta ta zura tare da d'aukar jakar islamiyyarta tayi parlour.

Har lokacin Yaya Ma'aruf yana zaune yana cin abinci Baba ma ya dawo Umma na zaune gefensa tana zuba masa abinci,da sauri ta jube gabansu cikin sanyin murya tace"Baba sannu da shugowa" cikin sakin fuska da murmushi ya amsa da "Yawwa Muwaddatu" Umma ta kalleta tace"lafiya na ganki da k'aton hijabi kuma ga jaka a hannunki?" Sosai k'irjinta ya ke bugawa cikin karkarwar murya tace"da...dam..man namance ban sanar muku ba a islamiyya a za6emu a matsayin wad'anda za'a tura muhawara to nima na manta shine Salma yanzu ta kira ni wai nazo sun kunna jen muyi karatu saboda Muhawarar da zamuyi" sosai Baba da Umma suka fad'ad'a fara'arsu Baba yace"masha'Allah tabbas Muwaddatu ke yarinya ce mai k'ok'ari da matuk'ar hazak'a,Allah ya baki sa'a a dukkan al'amuranki ni nasan bazaki ta6a bamu kunya ba."

Wani murmushin samun nasara Muwaddat tayi tare da cewa insha'Allahu Babana" Ma'aruf kallonta kawai ya ke tun farkon fara bayaninta har zuwa idawarta,sam bai yarda da maganarta ba domin ance mara gaskiya ko cikin ruwa zufa yake.

Addu'a Umma ta mata sannan tace"kinga dare yayi don Allah kibi a sannu,idan kun gama kuma idan dare ya cika yi ki kwana kawai domin duk da mak'ota muke amma fita cikin dare bashi da dad'i" wani sanyin dad'i ta sakeji jin Umma ta yarje mata kwana da sauri ta mik'e da cewa"to Umma na gode,sai da safenmu" ta fice da hanzali.

Numfashi Ma'aruf yaja tare da kallon iyayen nasa,yace"Baba amma bai kamata kuna hakan ba Muwaddat amana ce a gare ku" da sauri suka dubesa,Baba ya kalli Umma ita ma Umma ta dubesa,sukayi musayar kallo dai Umma bakinta a bud'e tace"Ma'aruf kasan abinda kake cewa kuwa?mai kaga munawa Muwaddat" Baba yace"Ikon Allah kai kana ganin kamar bamu mata abinda yadace ne" numfashi yaja kana yace"Nasan matuk'a kuna k'aunar Muwaddat kuna nuna mata so da gatan da ko iyayenta ne iyakar wanda zasu nuna mata kenan,sai-dai maganar gaskiya tarbiyyar Muwaddat akwai gyara cikinta kuma...ai tun kafin ya idasa Umma ta fara tafa hannu da cewa"Ma'aruf me kake so kace?oh!nufinka bamu bawa Muwaddat tarbiyya ashe kuwa kaima bamu baka" Baba yace"tabbas kuwa idan Muwaddat bata da tarbiyya kaima kam baka da ita" zaiyi magana Umma tace"kaga don Allah tashi...


Read / Download KARO DAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album