Join Our WhatsApp Group

DAULA BIYU Complete Hausa Novel Document by DAULA BIYU


DAULA BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 262821



DAULA BIYU

Reading Time: 21 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Mai Dambu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.39 mb

File Type: txt

Views: 796+

Download: 1291+

Last download: 5 days ago

Description/Story: [5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1018349125?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=p2YTjw4PS2qpjrTn042i27PbQ7pe7tatfB7muSQqjA9gUEzeMYU0Byrn1sxsLB59Bib4pHQOjkRuhTdYZ8v%2FVGLh2TPrLFa1eWMLQDVO3Yth5Qw268jk0kPY0Y%2B%2Bctix

*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*

   _The Historical_
~BOOK ONE~

Bismillah Rahamani Raheem

*Sadaukarwar taki ce! Maman ABUNA! Kince na rage masarautan Jordan ko💝💞🤩 Uwata ga book dinki sukutun da guda na baki domin ke*

'''Tukwaici gareku
Batul Ghana And Mom Sayeed
My Juwairiya Nasir And Mom Ases And Maman Khadijah da Sadeeq
   Har abada kuka raina💝

Gaisuwarki ce Aunty Safiya Danjuma Jos 💞'''

Page 1..
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama... Ya rasu a shekara  632 ran takwas ga wata june,(malaman tarihi zaku iya min karin bayani idan nayi kuskure ba laifi bane 💞)

         Bayan rasuwar shi Asahaba suka shiga tattaunawa, inda aka daura Sayyiduna Abubakar, bayan shekara biyu Allah yayi mishi rasuwa sakamakon zazzabin da yayi fama dashi. Bayan shi sai aka bawa Sayyiduna Umar wanda yayi shekaru biyar zuwa bakwai, ya rasu. Lokacin Sayyiduna Usman yana kasar damascu na syria ya tafi fatauci. Aka bashi bai sani bashi khalifancin. Wato Amirul Muminina kenan.

      Shima bai jima ba, Allah ya amshi rayuwar shi aka bawa Sayyiduna Ali shima ya rike na wani lokaci kafin ya rasu, amma har zuwa lokacin gwamnatin Musulunci bata fad'adda ba. Iyakarta jazziratul Arab ce, wato yankin. Madina, macca, da wasu sassan jazziratul Arab. Bayan wasu lokuta. Aka bawa Khalifancin Rashidu. Lokacin khalifancin yayi da'awa amma shi bai kafa daula ba, yayi dai lokacin da inda wasu daga cikin ayarin shi suka yi ta kama karya tare da zalinci.

      Sannan shi ya shigar da al'adun larabawa zuwa ga maguzawan larabawa.

   Daga nan Umayyad ta kafa daular ta, daga shekarar 661, 750 Umayyad itace daular musulunci da tayi fadi da tsayi, domin tayi girman ban mamaki, Umayyad ta mamaye yankin jazziratul Arab baki daya. Idan muka duba inda Ta mamaye sune.
*Makka*
*Madina*
*Damascu na ƙasar Siriya*
*Kuifa*
  *Istanbul*
  *Carboda*
  *Falasɗinu*
   *Kairomam*
    Da wasu yankunan jazziratul Arab,
    Sannan bata samu damar shiga Farisa da Girka ba, a wannan lokacin khalifancin Umayyad ba a takura wanda ba Musulmi ba, asalima tsarin su ya banbanta da na Khalifancin Rashidu. Haka ya janyo hankalin wadanda ba musulmi ba shiga addinin Musulunci.

   Zunzurutun karfin mulkin Umayyad tasa aka fara rade radin zai d'aga hedkwatar musulinci da yake Madina zuwa damascu, tilas yasa shi dawowa Madina gudun faruwar juyin juya halin Musulunci.

            Dan haka sai ya zamana an sami hedkwatar musulinci guda biyu, daya a damascu daya kuma a Madina, wanda haka yaso tab'a kimar musulinci a lokacin.
                Shekara 750- 1258 Abbasiyyah ya kafa tashi daular lokacin wafatin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, yana da shekaru daular abbasid yayi rolling.
  Wanda shi kuma ya mamaye yankin guf baki daya har zuwa nahiyar Turai. Daga cikin yankin da Daular Abbasid suke mamaye akwai.
*Farisa*
*Andulus*
*Hindu*
*Asia*
*Iraq*
Da wasu sassan kasar Afrika, ita ba su libya, Morocco, Algeria, da tsallaken kogin blue nel. Sannan musulinci ya tsallako har bakin gabar tekun maliya, zuwa sudan kenan. Daga nan kuma ya karaso sauran yankunan kudancin Afirka da sahara. Wanda ya shigo har kasar Masar.

        ---- Babban hedkwatar Abbasiyyah tana Baghdad, a Lokacin wadanda ba muslmai ba, suna biyan haraji me suna  jizyah,2.5% wanda dashi ake raba charity. (Ban san me zan ce da Hausa ba! Amma ana kiran shi da haddaya da larabci)

              Tsarin sarrafa mulkin daular abbasid yayi wani irin karfi wanda shi da Umayyad aka ce sune mafi girman daular musulunci daya shekara dubu daya da dari hudu da ashirin da biyar.

       Sannan daga baya wasu daga cikin dangin Umayyad, sun koma Andulus inda suka kafa daular Larabawa a gurin, wasu kuma suka kafa daular Ottamah A Istanbul na kasar Turkiyya.

    Shi kuma Abbas ya kafa daular Abbasid a tsakanin. Daga baya wasu daga cikin mukararaban Abbasid sun dawo Samanid da wasu bangare na yankin suka kafa daular Abbasid a gurin.

         Mafi girman Daular da ta gagari kowa a lokacin, tana da dinbin dakarun soji, sannan a lokacin ta hana kowani harshe sai labarci, bayan haka an yi sarakuna shida a cikin Daular.

Bayan Abbasid da kuma wasu mabiyan shi.

     Sannan sai ana cikin shekaru ba 1355 Hijrah Manzon Allah daga Makka zuwa Madina, Turawan Mulkin Mallaka suka shigo cikin lamarin daular Larabawa.

         Suka dagula musu lissafi, inda suka nuna musu mace tana da damar yin mulki, kamar yadda yake faruwa a wasu nahiyoyi kamar kasar hindu, ana samun magajiyar sarauta, sai kasar Sin, suma ana samun magajiyar sarauta, a turance(Empress, a larabci kuwa ana kiranta Sultanah)

       Wato ita (Empress) ana samunta ne sakamakon kasancewar matar Sarki ko Kwarkwarah sarki, ko kuyangar sarki, sannan matsayin da yake kaita zuwa Empress haihuwar d'a namiji.

            Sanan ba a damu ba, koda kuwa matar sarki ce ta ta samu wannan damar, burinta kawai ta sami d'a namiji, wanda zai zame mata garkuwa.

    Daga lokacin da aka ce matar sarki ta samu juna biyu, toh akan Nimo duk wani me maganin cikin masarautan ya bincika lafiyarta, idan kuma kuyanga ce. Toh zata kasance a killace. Gudun kar a bata guba ko abinda zai kashe d'an cikin ta.

         Tunda turawa suka basu wannan tsarin ya zamana, an sami sarakuna, suka shiga mutuwa, basa cika shekara daya za a wayi gari sarki ya mutu, ko a samu matar shi itama ta mutu ko idan tana da d'a namiji ya mutu.

   Sai da ta kai daular Samanid manyan mutanen cikin gidan sarautar kowa gudun mulkin yake, kuma wani abun da yake damun crown prince, sun fara tsoron zama a matsayin Sultan a cikin daular.

           ^^^
Abdus Samad bin Hubaish bin Aamaan al Muktum.

            Shine Sultan na tara a daular Samanid, kuma ya rayu tsawon shekaru goma sha biyar,  Yana auren Yar daya daga cikin crown prince na masarautan wato Fazilatul nisa, mahaifinta  me suna.
     Hood bin Abdul munaf bin Basra, almuktum yana cikin jerin manyan masu jiran gado,  dan haka lokacin Sultan Abdus Samad yana shekara biyar a karagar mulki, ya hada shi aure da yarshi duk da Sultan din yaƙi, sabida tsoron kar ta samu ciki a kasheta.

Tunda daular ta zama kamar akwai cultist curse. Koda aka aura mishi ita, babu abinda ya tab'a hadasu asalima Sultan kauracewa yayi tare da dauko balagoron dole zuwa kasar Carboda, inda a can ya hadu da wata baiwa me suna. Hoyam,

  Ya daukota har daular a boye, daga shi sai narmin baiwar shi ce, a hannunta ya taso, lokacin da ya kawo mata Hoyam. Yarinya ce da bata wuce shekara goma sha shida ba, dan haka ya manta da ita, sai bayan wasu shekaru marasa rata.

      Ya tuna da ita, lokacin yana fama da rashin haihuwa, dan da farko bai damu ba, sai daga baya da aka matsa mishi musamman sultana Fazilatul nisa, abin ya d'aga mishi hankali.

              Har zuwa wani lokacin da ya nemi Hoyam, tunda Sultan ya nemi yarinyar nan ya daina niman Sultana. Hankalinta yayi mugun tashi san haka tana da wani amintattun bayinta me suna Shairah da Narjis, ita Narjis mace ce Shairah kuma namiji ne wato d'an daudu. Duk wata mace baiwa da take cikin masarautar shi yake shayarda ita maganin gyaran jiki, tare da mata duk wani abinda zai gyarata.

            Narjis kuma itace ke tare da Sultanah duk abinda za a aikata da saninta itace kashin bayan dukkanin aiyukan Sultana,

    Yawo take a tsakar d'akinta sanye take da wani shegen gown, me dauke da duwatsun jauhari, kanta da wuyarta dauke yake da kambun lu'lu'u.
Shafa wuyarta tayi sannan cikin wani irin yanayi me cike da mugun mulki tare da Izzar da suka tattaro a cikin idanunta tace.
"Taya aka yi Abdus Samad ya ajiye baiwa a cikin masarautan nan ban wani ba?"

      Zuɓewa suka yi akan gwiwar su, tare da kaskantar da kansu, suna faɗin.
"Mun tabbata asararru marasa albarka, tunda zaman mu a gare ki bai zama me amfani ba, Sultana mun bayarda kawunan mu da gangan jikin mu sadaukarwa ga b'acin ranki kinsaka takobin ki, ki.sare kawunan azzalumai irin mu!"

Wani irin iska taja, kafin ta juya musu baya tace..
"Narmin!"
Jikin Narjis na rawa taficce da sauri, har shashin bayi wanda yake can hanyar fita cikin masarautan. Ta buga kofar Narmin.
A tsora ce ita da Hoyam suka kalli juna, sannan ta  juya ta boye Hoyam, kafin ta bude kofar.

     Turata dakarun da suka taki Narjis suka yi sannan suka shiga duba d'akin, cikin tsananin bincike suka samota sakamakon atishawar sa tayi. Wani iri daraja kan Narmin, dan haka aka sako su a gaba, babu wanda yace kala.

         Lokacin da suka isa shashin Sultanah, zuɓewa suka yi akan gwiwar su. Tana kishingide akan wata kyakyawan darduma, tare da wasa da tufar hannunta. Kusan rabin awa, kafin ta kalli Shairah. Cikin wani yauki ya kalli Narmin.
"Toh azabar Allah ya tabbata akanki. Da cin amanar da kika yi! Yau naga abinda ya hana mata gemu yaba maza!"
"Hmm!" Sultanah tace,
"Toh ai sai ki tashi ki bar mana nan domin Sultanah zata yi magana da abinda kike b'oyewa!"

     Mik'ewa tayi kanta a duke sannan tace.
"Kaina da gangan jikina, mallakar Sultan Abdus Samad ne, haka ma Hoyam mallakar shi ce,.ina niman afuwar Sultanah da karta cutar da Hoyam. Yarinya ce da bata san kome ba."

    Sake tufan da yake hannunta tayi, sannan ta juya tana kallon Narmin. "Ni zaki koyawa abinda na taso a kai?" Sake zuɓewa tayi akan gwiwar ta, zata yi magana aka bankad'e kofar shiga d'akin. Aka shigo,. sanye yake da doguwar riga, me ruwan goro sai gashin da ta sauka har gadon bayan shi. Kallonta yayi cikin nutsuwa. kowa fita yayi daga dakin aka bar Hoyam da take durkushe gaban Sultanah da ta hasala.
"Abdus Samad! Meye nufinka da wannan kaskantacciyar baiwar? Shin tafini nasaba ne? Nawa ka saye ta na fanshe ta."

Mik'ar da Hoyam yayi yana kallon Sultanah, sannan ya d'aga haɓɓar Hoyam wacce take kuka kamar ana yagar namar jikinta dan ta gama tsorata.

             "Bar kuka gani nan a tare dake! Kinji ki fita Narmin tana jiranki." Ya faɗa mata.
   A hankali ta janye jikinta tare da barin d'akin, ta nufi hanyar waje, tana shashekar kuka. A bakin kofar tafi ta gamu da Narmin, ta riko hannunta suka fara tafiya,.harsuka iso shashin kuyangi. Kallon su tayi sannan ta sunkuyar da kanta sakamakon irin kallon da suke mata, suna magana kasa kasa. Akan itace sultan mafi soyuwa a zuciyar shi.

Kishin ta yi kama su, sosai musamman da suka ganta sanye da tufafi masu kyau irinta kasar yamma. Haka yana nufin Sultan yana ji da ita kenan. Tunda suka isa dakin su, take kuka cike da tsoro.
"Narmin ina jin tsoron kar su, kuma zuwa."
"Karki damu Sultan ya san da batun ba zai tab'a barin a cutar dake ba, domin yana sane dake. Ki bar kuka;"

   Gyada mata kai tayi, sannan ta kalle ta cikin damuwa.
"Me yasa takira mu?"
Banza da ita tai tana hada kayan da aka wargaza d'azun.
"Baki ce min kome ba?"
"Sabida har yanzun daular nan babu wanda yake da yakinin Sultan zai samu d'a namiji, tunda har Kwarkwarorin shi ba haihuwa suke ba, sannan na hore ki da karki yarda wani ya baki abu kici.

      Domin cin abu a hannun wani tashin hankali ne, karki yarda wani ya shayar dake wani abu, yin haka hatsari ne."
"Sabida Me yasa kika min doka?"
"Sabida zasu iya samun damar saka ki cikin jerin mutanen da ba zasu sami haihuwa da Sultan ba.  Duk ranar da kika samu ciki da Sultan ranar zaki daina amsa sunan baiwa ko kuyangar sarki, sai dai magajiyar sarauta, isa wannan matakin kuma shine rayuwa da mutuwa, domin.".

Buga kofar dakin aka yi, da sauri tazo ta bude. Sultanah ce tana huci tare da kallon Narmin.
"Ina munafukar take? Wani tsafi kika yiwa Sultanah da yake cewa kinyi mishi ya zab'e ki a matsayin kuyangar shi, ki gaya min nawa ne zan biyaki!"

"Sultanah! Kuyangi suna jinki karki bada mata, zasu samu abin gulmatawa!" Shiru tayi tana kallon Narjis gyada mata kai Shairah yayi tare da cewa.
"Sultanah!"
A fusace ta juya tare da barin gurin, tana isa shashin kuyangi, tace.
"Shairah ka dauko min Hoyam, nan."
Da sauri ya kalli Sultanah. Kafin ya juya inda suke, aka tawo da Hoyam. Tana kallon Yarinyar cikin tsana da tsangwama tace.
"Zan shayarda duk wacce Sultan ya keb'e da ita, duk wacce Sultan ya gayyaceta turakar shi bata gaya min ba, sai na shayar da shi nono mahaifiyar shi a karo na biyu."
          Huci tayi sannan ta kalle su, ta juya bayanta, tare da d'aga hannunta.
"Darda, ka zane mana Hoyame!"....
*Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641 Insha Allah 13/2/2021 xan cigaba da Posting*
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: https://www.wattpad.com/1019331921?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=EhMWxWcs3%2BXBPmJ9Mx4VmYNMNPNLwAtXfRCgGgL0YhnfgfEGgGb%2BS6%2FL2PAUJxT95YPPst3m3dR%2FtnwJ0kHvOKhC0Kwru7g1GiqVx5gpeoIWEc8eNdkpZWokeVl8WEgB

*_ᎠᎪႮᏞᎪᎻ BIYU_*

   _The Historical_
~BOOK ONE FREE~

Bismillah Rahamani Raheem
Page 2....
Kamar wacce aka aikowa wahayi ta juya tare da dakatar da Darda, ta tako har gaban Hayom. Tana huci musamman da taga yadda yarinyar take mata kallon kurilla.

         Dauketa tayi da mari, tana tuno abinda yace mata.
--- "me ka ɗauke ni? Ka maida Ni wata bita can, mmm sultan yaushe rabon ka da ka gayyace Ni turakar ka? Ashe ka ajiye wata a can gefe ne, ka saba duk macen da zaka nima a cikin Kwarkwarorin ka kana turo min a shirya maka su, ashe ha'intana kake? Meye na rage ka dashi da zaka boye yar wannan yarinyar?"

          Karamin murmushi yayi sanan yace mata.
"Idan kin gama zan fita?" Ya gaya mata hankalin shi yana kan zoben hannun shi, a rikice tace.
"Sultan!!!"
Juyawa yayi tare da tura kofar zai fita.
"Meye na rage ka dashi?"
Cak ya tsaya kafin ya juya yana kallonta, sannan yace.
"Ke zab'in Kawuna ce! Ita kuma abinda zuciya ta ke so ce, dan haka koda ban bata gurbin Matana ba, zan ajiye ta a matsayin Kuyangar da nake so! Kuma na rantse da Allah, wani abu ya same ta, dole na rage miki matsayin ki daga Sultanah zuwa Ameerah."
    Sake baki tayi tana kallon shi har.
         Yana gama fadar haka, ya fice abinshi daga d'akin, ihu ta saka tare da zuɓewa a gurin. Bayan fitar shine ta fito domin cikin mutuncin Hayom.

         "Sultanah, karki yanke hukunci cikin sauri, ki barta a sannu zamu yi maganinta, yanzun kuma kika yi haka tankar zubda kimar ki ce, kuma kuyangi na kallonki, kiyi nazarin abu mana." Inji Shairah,

     Juyawa tayi tare da barin gurin, ranta a b'ace, tana shiga turakarta ta shiga watsi da kome na dakin, hatta mudunin dakin. Cikin...


Read / Download DAULA BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album