Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR UBA Complete Hausa Novel Document by MATAR UBA


MATAR UBA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51602



MATAR UBA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 04, Apr 2025

Author: Fadeela Yakubu Milhat ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITERS ASSOCATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 272.58 kb

File Type: txt

Views: 9+

Download: 54+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ο»ΏπŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

```CHAPTER 1```
Zaune na gansu a Kan sallaya da alama sun idar da sallah ne. Yara ne Mata Wanda baza su haura shekaru Sha hud'u a duniya ba.

Bangaje kofar tayi ta shigo tana huci Tace "Ke Asiya don ubanki Ni sa'ar kice da d'azu mijina Yana min magana Kika sa Mana Baki?"
Wacce aka Kira da Asiya sai rarraba Ido take ta kasa cewa komai idanun ta sun yi jajir cike da tsoro da fargaban abinda zata Mata,finciko ta tayi tana jaaan kunnen ta Tace "Daga yau idan Ina magana da mijina Wanda ya auro Ni a matsayin matar sa Yana min magana Kika sa min summan Bakin ki" tana maganar tana Jan bakin ta.
"Kar na Kuma ji ko gani kin fad'a Masa cewar bana kyauta ta muku kina jina?" chan Ciki ta amsa da "Eh" maruka masu kyau ta shafa Mata sannan Tace "Kice Ni yar banzar yarinya ce" cikin kuka Tace "Ni Yar banzar yarinya ce" hankad'e ta tayi ta fad'a a kan gado, da sauri ta karaso inda take tana kokarin d'aga ta.
"To Munafuka Meyasa kike rike ta da alama Kema Marin kike bukata,kina hauka ne? Da nice na haifi kamar biri kamar ku da na dad'e da kashe ku" ba b'ata lokaci ita ma ta karb'i nata marukan guda biyu.
"Mahaukatan banza mtwwws" sai tayi ficewar ta.

"Anisah ki daina kuka kinji? Inda sabo ai mun Saba,tashi mu cigaba da addu'ar mu" hannu ta sa ta sharewa kanwar ta hawaye sannan suka koma suka zauna a Akan sallaya, Anisa ce ta d'aga hannu sama Tace "Ya Allah Kaine Allah ka ga abinda matar uban mu take Mana ya Allah ka Kare mu daga sharriin ta" anisah ta amsa da ameen.
Tashi sukayi, sukayi addu'ar bacci sannan suka kwanta.

*WASHE GARI*
Zaune take a parlor tana kallon TV hannun ta rike yake da remote ko me ta tuna sai ji nayi ta kwala Kiran sunan "Anisah!!! Asiyah" shiru ba su amsa ba ta sake Kiran sunan su a Karo na biyu jiki a sanyaye suka fito jikin su a sanye yake da Riga da Wando jeans yayi matukar karb'an su sannan ko Wacce tasa ribbon kalar rigan ta tayi parking gashin ta, sunaa da tsawon gashi, gashi Baki Kirin.


Zuwa sukayi suka tsaya a gefen ta, kallon su ta Shiga yi daga sama har kasa sannan tace "Bakin ku ciwo yake da Kuna ji Ina Kiran Ku baku amsa ba, maza kuyi kneel down Ni sa'ar kuce da za ku Zo ku tsaya min a Kai?" Ba musu sukayi kneel down.

Tsaki tayi Tace "Daga gani cikin ku biyun Nan akwai mayya" tana nuna su da Yar yatsan ta akwai Wacce take kawo Mana matsala a gidan na rashin kud'i gashi Kun sa mun Fara Shiga talauci, ko kud'in da mijina yake kashewa a makarantar ku ma ai asara ce ban ga amfanin ta ba sabida haka na yanke shawara daga yau Kun daina makaranta a gidan Kar ku kuskura naji Kun ambaci sunan makaranta ko da dawasane" ganin tayi shiru suka tashi a tsawace Tace "Don uwar ku wa ya ce ku tashi maza ku koma kneel down, raise up your hands and close your eyes" a tsorace sukayi yanda tace sun dad'e a haka Kan tace "babu abinda kuka iya sai Kama gashi da ribbon zan Baku shawara gara ma kuje ku koyi sana'ar d'inki ko salloon Yan iskan Yara kawaii tashi ku bani guri" cikin sauri suka Mike suka bar gun.

Bayan Mahaifin su ya dawo daga aiki Yana zaune a parlor suka shigo suka tsaya a gaban TV idan ya karkata kansa sai su tare sunyi hakan kusan sau uku sannan yayi Murmushi yace "To naji naji me Daddy yayi wa little angels d'insa Kuma wanna karon?"
Anisah Tace "Daddy Meyasa kace zaka cire mu a makaranta?"
Kallon su yayi d'aya bayan d'aya sannan yace "Na cire ku a makaranta? Me zai Sa na cire ku a makaranta?"
Asiyah Tace "Mummy ce tace Mana za'a cire mu a makaranta"
Cikin rashin fahimta yace "Meyasa?"
Anisah Tace "Cewa tayi babu kud'i Yanzu ana cikin marra"
Murmushin gefen baki yayi yace "Haba duk talauci na bazan ki saku a makaranta ba Kuma Alhamdulillah muna ci muna Sha babu abunda muka rasa, maybe mummyn naku Wasa take muku ko Kuma Bata San me take fad'a ba"

Anisah Tace "Allah yasa dai bata San me take cewa bane" ta Maida kallon ga Asiya Tace "Asiyah Zo mu tafi" d'akin su suka haura suka barshi zaune Baki a bud'e yace "Ikon Allah, wato dai Baraka baza ta canza ba" Kiran Sa akayi a waya Yana wayar ya haura saman su inda ya Samu tana zaune gaban mirror tana taje gashin kanta jikinta Kuma sanye yake da sleeping dress iya gwiwa yellow ne aka Masa flowers da jaan color, sai da ya gama wayar da yake sannan tace "Naji kana maganar tafiya"
Murmushi yayi yace "Eh tafiya xanyi zuwa London next week insha Allah"
"Masha Allah tare zamu tafi ko?"
Yar karamar dariya yayi yace "tafiyar Nan na office ne Kuma sai naje dake? Idan na tafi dake wa zai kula da yaran?"

Tashi tayi a tsawace Tace "Ni fa matar kace ba baiwar su ba, ko Kuma ka auro Ni ne don na Zama baiwar su?"
"Haba Baraka Kar ki manta Kan na auro ki kin San da zaman su Kuma kin tabbatar min da ba matsala Zaki kula dasu Amma Yanzu kiji abinda kike cewa 'ya 'yan ki ne fa?"

A tsawace Tace " 'ya 'yan ka dai zaman ka nakeyi ba nasu ba ka gane ko? Kuma da kake cewa sai da na amince Kan akayi auren do you expect me to refuse your proposal?"
"No no Baraka ba haka nake nufi ba" wayar ta tasa hannun ta d'auka sannan ta nufi hanyar fita Tace "Sai Kuma kayi ai."

"Baraka!! Baraka!!!" Bata tsaya ba bare ta saurare shi.
'''CHAPTER 2'''
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
........... Zaune take a Parlor ta d'aura kafa d'aya Kan d'aya tana kallon TV, ji tayi a na kwankwasa kofa tashi tayi ta bud'e ganin mijin taneΒ  yasa tayi Murmushi da saurin ta rungume shi had'e da sumbatar sa a kumatu, ganin mace a bayan sa hannun ta rike take da Ghana most go yasa tayi saurin sake shi Tace "who is she?"
Murmushi yayi yace "Sunan ta maijiddah, na d'auko tane sabida ta Rika Taya ki aiki"

Cike da mamaki take kallon sa Tace "Yar aiki a gidan Nan?"
Ya amsa da "Eh"
Tace "Na d'auka kace baka son yar aiki a gidan ka Kuma ya akayi ka canza shawara?"
"Gani nayi kina wahala sosai da aikace aikacen gidan Nan don gidan babbane Kuma Kinga zata Rika Taya ki kula da yaran Nan"

Murmushin gefen baki tayi Tace "Okay idan na fahimce ka karfin d'auko ta da ka yi shine don ta Rika kula da yaran ka ko?"
"Eh Haka ne"
Rai a b'ace tace "To Ni yaushe zaka Fara yin Abu sabida Ni a ko da yaushe maganar 'ya 'yan ka kake, sau nawa nake rokon ka da ka d'auko min Yar aiki Amma kaki? toh ban yarda ba ka maida ta inda ka d'auko ta" tana Kai Nan ta bar gun Yana Kiran ta Amma Bata kulashi ba cikin sauri ya bi bayanta sannan ya dawo yace "Maijiddah ki jira ni anan ko? Ina dawo wa"
Ta amsa da to.

Yana yafiya ta Fara kalle kalle tayi Nan tayi chan har ta hango wani kofa tana Shiga Ashe kofan kitchen ne ga mamakin ta taga Yara biyu suna aiki d'ayar na girki d'ayar kuma na wanke wanke hard'e hannu tayi tana kallon su a zuciyar ta Tace "Ikon Allah kananun yaran Nan da aiki haka har da girki abun tausayi?"

"Haba Baraka meyasa kike min haka ne ya kamata ki fahimce ni ki gane dalili na, Kinga idan Zaki fita yanzu Baki da wata matsala akwai Mai kula da su Kuma Kar ki manta idan na dawo daga London zamu tafi yawon shakawata a Saudi kin ga zai Zo Mana da sauki ko?"

Murmushi tayi Tace "To
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR UBA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album