Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DOCTOR HASSAN Book 1 Complete Hausa Novel Document by DOCTOR HASSAN Book 1


DOCTOR HASSAN Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 107766



DOCTOR HASSAN Book 1

Reading Time: 8 Hours

Added On: 03, Jul 2024

Author: Rasheedat Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08147537180.

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 591.5 kb

File Type: txt

Views: 677+

Download: 757+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [8/27, 9:25 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romantic and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni yanzu ma gani tafe da Hatsabibiyar da tafi INDO sheɗanci.

*Bazan taɓa manta alherin ku gareni ba masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin littafin RUƊANIN ZUCIYA BIYU gaskiya naji daɗin ƙaunar ku gareni, domin kuwa kun sayi wannan littafin fiye da yanda nake zato to yanzu ma gani tafe da sabon labari mai rikitar da mai karatu.*


Ku dai ku kasance dani mu tsunduma cikin wannan labarin.🖊️📖



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 1 to 2*

*_____________________________________*


Alhamdulillah ala kulli halin, na godewa Allah daya bani damar sake dawo muku da sabon book ɗina, wanda nake da tabbacin zaku samu nishaɗi a cikin sa, tare da tsantsar darasin zamantakewar Rayuwa mussaman zama irin na babban gida Soyayya tausayi cin Amana ban dariya, ɗan uwa ƴar uwa ina kike maza taho mu haɗe dake cikin wannan labarin mai matuƙar zaƙin zuma tare da garɗin madara taho domin kema a dama da ke nidai fatana na kawo muku Abunda zai amfane ku.

Wannan labarin yana tafe ne da salo na mussaman .

Please idan kina da interest akan wannan book ɗin ki fara binsa tun yanzu kar sai nayi nisa kice min daga farko.




Sharhin ku shi nake buƙata.



*Mu kafta* ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️


*BABBAN BIRNIN MAIDUGURI BARNO STATE*

Jihar da ta tara Barebarin Asali birnin kanuri.



*Unguwar GRA*



____________Fitowa yayi daga tollet ƙugunsa ɗaure da towel, ɗaya kuma ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan jikin sa, dressing mirro ya ƙaraso ya jawo table ɗin dake wajen ya zauna yana cigaba da tsame ruwan jikin sa, sanda ya tsame ruwan tas sannan ya ajiye towel ɗin a hanun bed, lotion ya jawo mai ƙamshin gaske ya fara mulke jikinsa dashi, sannan ya hau gyara gashin kansa shima da mayuka masu ƙamshi sanda ya mulke ko ina na jikin sa da lotion sannan ya ɗauki body spray ya dinga feshe jikinsa dasu sanda ya fesa kala uku kafin ya miƙe tsaye ya je drower ya buɗe ya ɗauko set ɗin kayan sa Blue Black ɗin wandon jeans ya saka tare da rigar suit fari yasa tare da ɗauko ribin dark blue ya ɗaura a wuyan rigar gyara kwalar rigar yayi sannan ya ɗauko suit ɗin ya saka , komai cikin nutsuwa yake yinsa sannan ya ɗauko takalmi sau ciki zama yayi bakin bed ɗin ya sunkuya yana ɗaura igiyar takalmin.

" Assalamu alaikum"

Yaji sallamar ta, shuru yayi ba tare daya amsa mata ba ya cigaba da ɗaure igiyar takalmin, Sau uku take sallamar amma yayi banza da ita kamar baiji ta ba ya cigaba da abunda yake yi, sai a na huɗun ne ya amsa mata can ciki kamar wanda baya son Maganar nan ma sanin darajar Sallamar yasa ya amsa mata idan ba kana kusa dashi ba bazaka ji ya amsa sallamar ba, ita kanta ganin da tayi bakin sa yayi motsi ya sata fahimtar sallamar ya amsa mata, ƙarasowa tayi har gaban sa ta tsaya jikinta a sanyaye ta sunkuya tare da saka hanu zata karɓi igiyar takalmin ta ɗaure masa, yayi saurin bige hanunta yana cigaba da ɗaure wa, cikin sanyin jiki ta masa magana da Sweet voice ɗin ta tace.

" My Doctor breakfast is ready."

Shuru Yayi Still bai kulata ba, kuma sarai yana jinta sai ma ƙara haɗa fuskar sa da yayi tamau babu alamar annashuwa cikinta, ɗagowa yayi tare da ɗaukar agogon sa ƙirar gucci ya fara ƙoƙarin ɗaurawa a hanunsa, a karo na biyu ta ƙara cewa.

" I Say Doctor breakfast is ready please jiya ma fa haka ka kwana babu abunda kaci ko ruwan tea baka sha ba, haka ka kwana ya kamata kafin ka fice kasa ko da ruwan tea ne a cikin ka bana son kana fita da yunwa bana jin daɗin hakan."

Ɗago lumshashshun idanunsa yayi masu kama dana mai bacci fuskar sa kuma a matuƙar ɗaure ya dubeta sannan ya fara magana cikin Slow VOICE ɗinsa da kuma faɗa faɗa.

" Wai meyasa ke mayya ce kam *FALMATA*!!!!, Meyasa kika addabi rayuwata ce, nace miki na tsaneki ki daina damun rayuwata ki daina shiga Cikin lamari na, Wallahi Falmata na miki tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam shiba, na tsaneki na tsani iyayen ki ina Zaune dake ne a dole Saboda kin zamo min ƙarfen ƙafa ba yanda zanyi dake, Banza ƴar Mayya, dan Allah ki fita a cikin rayuwata, nace bazan ci abincin ki ba ko ana dole ne Get Out of my room Mayya!!!!."

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙofa, hawaye ne suka gangaro daga daradaran idanunta, ta ɗago tana kallon mijin nata cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, sunkuyawa tayi ta durƙusa da gwiwowin ta ta fara magana cikin rawar murya mai cike da alamun kuka.

" Karka min haka mijina Please ka daina hukunta ni da laifin da ba nawa ba, asali ma bani da hanu ciki, kana azabtar dani da yawa Doctor, kaine duniya ta, bani da wani farin cikin daya wuce naka, meyasa sanda ka koya min Soyayyar ka sannan zaka juya min baya, Ka ji tausayi na ka cire ni cikin *LAMARIN GABAR CIKIN GIDAN MU TABBAS AN ƁATA ZUMUNCI* amma ni meye nawa ciki da zaka juyawa Soyayyar mu baya, *INA SOYAYYAR DA KACE KANA MIN, KAINE FA KA ƊAUKA MIN ALƘAWARIN CEWA BAZAKA TAƁA RABUWA DANI BA, KOMAI TSANANI KOMAI WAHALA KANA TARE DANI MEYASA YANZU KA TSANENI LOKACI GUDA* ina sonka MIJINA kaji ƙaina?"

Ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, tunda ta fara Maganar ya zuba mata Lumshashshun idanunsa yana mata kallon tsana da kuma tausayi sanda ta dire maganar tukunna Yaja tsaki mai sauti sannan ya sunkuyawa ya ɗebi wayoyinsa dake bedsite drower da key ɗin motar sa ya juya da niyar ficewa ba tare daya tanka mata ba, yaji ta riƙe ƙafafunsa, Runtse idanunsa yayi sanda yaji hanunta a jikinsa, Yana jin wani abu na yawo tun daga babbar yatsar sa har cikin kansa tsayawa yayi cak.

" Please My Doctor ka taimaki Rayuwata ka tausaya min, Ka dawo da Soyayyar mu ka ji ƙaina, Wallahi zuciyata ciwo take min, karka bari na mutu ta sanadiyyar ka kaine gata na, kaine rayuwata ina sonka DOCTOR."

Cin jin wani ƙarin tsanarta ya saka ƙafarsa ya naushe ta da ƙarfi sanda ta bige kanta da jikin bed ɗin, da sauri ya saka kansa ya fice daga cikin bedroom ɗin, kanta ta riƙe tana jin yana mata zafi, hawaye kuwa wani ne yake bin wani saman fuskar ta, sosai take kuka harda shashsheƙa, takurewa tayi a gefe tana cigaba da kuka zuciyarta kuma cike take da baƙin ciki, Duniyar gabaki ɗaya ji take ta isheta, kullum baƙin ciki shine abokin hirar ta, ta rasa farin cikin ta tun sanda wannan mummunan ƙaddarar ta afku tsakanin mijinta d iyayenta, mijinta mai tsananin ƙaunar ta wanda ada baya son ɓacin ranta wanda kullum shine abokin hirarta shine amininta, shine mai share mata hawayenta amma yanzu shine mutumin daya fi kowa tsanar ta, shine ya maida ita ABOKIYAR GABAR sa, Tabbas rayuwa ta juya mata ba tunda har ta shiga tsakanin ta da mijinta, sanda taci kukan ya isheta sannan ta tashi ta goge hawayenta, ta faɗa saman bed ɗin nasa tana ajiyar Zuciya, rigarsa daya cire ta rarumo ta rungume a ƙirjin ta, tana shaƙar ƙamshin turaren sa, ji take tamkar shi ta rungume, sai famar ajiyar Zuciya kawai take, tana nan rungume da rigar har bacci ɓarawo yayi nasarar sace ta tana sauƙe ajiyar zuciya."

Shi kuwa yafi 30 minute yana zaune cikin motar ya ɗaura kansa jikin matuƙin motar pictures ne ɗan ƙaramin elagment a ajiye cikin motar, Sosai yake ƙarewa pictures ɗin kallo kafin yasa hanunsa ya shafa sa hawaye ne yake tsiyaya saman fuskar sa, *AUNTY JALILA DA UMMAN SA* sune kawai suke masa yawo a cikin zuciyarsa shikenan ya rasa *AUNTYN SA DA ABBAN SA* anbar *UMMAN SA* kuma cikin jinya, taya zai iya yafe musu bayan ya rasa farin cikin sa duk ta sanadiyyar su, ya daɗe
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DOCTOR HASSAN Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album