Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SONKI NE ƘADDARATA Complete Hausa Novel Document by SONKI NE ƘADDARATA


SONKI NE ƘADDARATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15804



SONKI NE ƘADDARATA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Batul Kamba ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 101.35 kb

File Type: txt

Views: 452+

Download: 272+

Last download: 1 day ago

Description/Story:

💋 *SONKI NE ƘADDARTA*💋

ʂƚσɾყ&ɯɾιƚιɳɠ
Ⴆყ
Fateemah Abdullahi
/Ⴆαƚσσʅ ƙαɱႦα/

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·

_______

Wannan Labarin ƙagaggen labari ne. Wanda duk yaga ya yi dai dai da rayuwarsa ya yi hakuri a kasi Marubuciyar ta samu Please.



*Page 1&2*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Niamey, Niger.

Babban gida ne mai ɗauke da manyan Bedroom's.
Ba kowa a tsakar gidan kasancewar safiya ce kuma ana iskan hunturu sosai.

Wata matashiyar Budurwa ce zaune daga gefan pampo, ga wani uban tarin wanke wanke daga gefenta, gyan-gyaɗi take yi.
Da ka gan ta kasan baccin wahala ne take.
Duba da yanda fuskar take yamutse, babu alamar walwala.

Wata Ƴar Dattijuwa wacce ta fito daga cikin wani ɗaki.
Butar dake tsakar gidan ta ɗauka da alama banɗaki zata shiga, wucewa tayi ta gaban Budurwar sam bata ma lura da ita ba, har ta fito zata sake gifta wa, sannan ne ta lura da mutum a wurin.

Kiran sunanta ta fara yi cikin mamaki

"Maryam.!

Maryam..."

A hankali ta fara buɗe manyan fararren idanun ta, ta sauke su kan Dattijuwar.

"Maryam ki tashi, kin san duk mutanen gidan nan suka fito baki kammala aikin nan ba, tabbas kin san menene zai biyo baya."


Da sauri ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin dai-daita tsayuwar ta kasancewar tana jin jiri sosai.

Cikin tautsayi Dattijuwar ta kalle ta tana faɗin

"Hala dai baki ci abinci bane ko?."

Gya ɗa ma ta kai ta yi alamar "E," girgiza kai ta yi cikin jin wani sabon tautsayin Maryam sannan ta ce

"Ki kammala aikin kizo ɗakina ki ci abincin kin ji."

Nan ma gyaɗa kai ta yi ta fara ƙoƙarin fara wanke wanken cikin ƙarfin hali, sai da ta kammala ba wanda ya sake fitowa, hakan ya ma ta daɗi sosai, da hanzari ta nufi Ɗakin Dattijuwar.

Bata kai ga ƙara sawa ba ta ji wata murya mai amo da rikita duk wani bakon da bai saba jinta ba, duk da ta saba jin muryar hakan bai hana wani tsoro game da tashin hankali shigar ta ba

"Ina zaki je?."

Wata mata da ta fito ɗaya daga cikin ɗakunan ta tambaya tana mai kafe tada ƙananan idanun ta

"Am dama iya ce taki rani Shshh..."

Wani ban zan kallo tayi ma ta. Bata bari ta ƙarasa ba, ta katse ta da cewa

"Uwar me zata miki?."

Shiru tayi hadi da sadda kan ta kasa, wata tsawar ta sake daka ma ta

"Ba tambayar ki nake ba?."

Cikin rawar jiki ta fara magana, hankalin ta idan ya yi dubu ya tashi.

"Yi hakuri Mamma, Allah wallahi yunwa nake ji zan je ne na ci abinci ne, Ƴan hanjina kamar zasu fito waje."

Kallon baki da hankali tayi ma ta sannan cikin kumbar baki take faɗin

"Dan uwarki wa zai miki sharar da sauran ayyukan?."



"Zan yi, Insha Allah, wallahi yunwa nake ji sosai."

"Idan kin kammala aikin sai ki je, muddun baki kammala ba, kika shiga wani Ɗaki a gidan nan billahil azim sai na lahira ya fiki jin daɗi..."

Tana kai nan a zancen ta ta koma ɗakinta. Fuuu kamar zata tashi sama tsaban bala'i.


Da shigar ta Ɗakin ta fara tashin ƴaƴanta dake nannade cikin bargo, ta shin su ta fara yi kasancewar ko sallar asuba ba wanda ya yi a cikinsu kuma tana sane da hakan.

"Lafiya dai Mamma?."


"Lafiya Qlau ku tashi magana zamu yi, waccen matar tana son ta ɓata mana shiri."

"Kamar ya?. Wai kina nufin Iya ko. Hum hum dama nasan wannan munafukar tsohuwar ita zata kawo mana cikass a tsarin mu wallahi."

Cewar ɗaya daga cikin Ƴan matan, a masifance.

"Ni yanzu bama wannan ba, ku tashi bana son Papan ku ya same ta ita ɗaya tana aiki.
Sannan Bance ku taya ta ba, amma ku fita wajen da kun ji alamar shigowar sa ku fara wani abin ta yadda zai dauka tare kuke yin aikin."

Kallon kallon suka shiga yi a tsakanin su Ƴan matan

"Kursiya ki tashi ni dai Allah ya san ba inda zanje wallahi."

Wadda aka kira da Kursiya cike da bala'i take cewa

"Ni ma babu inda zanje, cikin wannan iskar haba dan Allah."

"Kuyi hakuri Ƴan albarka ku je kar ku ja min masifar Papan ku."


Cike da rashin kunya da tsaban ji da tashen balaga, suka mimmiƙe suna zuzzunɓura baki suka yi wajen.
Koda suka fita har ta kammala shara ta fara ɗiban ruwa tana zubawa a manyan robobin dake tsakar gidan.

Akai kaice suke kallon ta dukkanin su biyun babu wanda ya yi alamar daukan bokiti da niyar kama ma ta sai ma harare hararen da suke yi har ta kusa kammalawa ba wanda ta kalla daga cikin su.

F🌹A🌹K Batool Kamba
✍️αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσϝι🤙

Follow this link to join my WhatApp group


https://chat.whatsapp.co💋 *SONKI NE ƘADDARTA*💋

ʂƚσɾყ&ɯɾιƚιɳɠ
Ⴆყ
Fateemah Abdullahi
/Ⴆαƚσσʅ ƙαɱႦα/

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•

💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦



________________________✍️
Kallonta iya tayi tana mai faɗin

"Kiyi haƙuri Maryam Papan ku yana iya ƙoƙarin sa, amma haryau shiru kakeji Allah yasani ina tausaya miki sosai, domin wannan matar batada tausayi ko kaɗan, kanta kawai tasani sai kuma yaranta."

Share kwallar idanunta tayi.

"Iya ban san menene yake damuna ba. haryau nakasa sanin ni wacece?.
Wai dama mutum yakan manta ko shi waye?. A'ina ya fito?, suwaye danginsa? Hatta mahaifiyata nakasa tunawa fa."

Ta ƙarasa maganar tana mai sake fashewa dawani sabon kuka
mai cike da ƙunar zuciya. 😓

*Abuja, Nigeria*

Zaune yake a gaban Dressing Mirror
yazu bawa wani katafaren zane da akayi na Art kyawawan idanun sa.

Kallon zanen yake yi yana zubar da zafafan kwalla,
magana yake tamkar wani zautacce.



"A'ina kike ne?, me yasa kika min hakan,
Shinko kin san wani kalar raɗaɗi nake fama dashi a silar rashin ki?,
Me yasa biki yi tunanin irin halin da zan shiga ba, a dalilin rashin ki?..."

Kai duba na nayi kan fuskarsa kyakkyawan Namiji mai cikar kamala da kwar jini ma abucin
kyawun fata dana fuska, fuskar tasa zagaye
da siririn gemu irin na gayun wannan zamanin. 🥰

Duk da cewar a zaune yake hakan bai hanani gano tsayin da Allah ya hore masa yana da tsayi
dai dai misali, ƙara duban sa nayi sai yanzu nagano wai ashe yanada tabon sallah ago shin sa. 😘

Yanda yake magana zaka ɗauka tare yake da wani ko wata a Bedroom ɗin, duba da yanda yake kallon gefe ɗaya.

Turo ƙofar akayi tare da sallama,
ko motsawa bai yi ba yadai amsa sallamar sanin muhimmancin ta.


Macece matashiyar tsohuwa mai ki manin shekaru Arba'in a duniya.

Kallonsa ta tsaya yi nawasu Ƴan mintuna sanna ta ƙaraso kusa dashi, dafa kafaɗar sa tayi.
hakan yasa ya juyo ya kalle ta bata ce masa komai ba ta fara share masa hawayen fuskarsa.
Har ta kammala bai yi magana ba. cikin muryar rarrashi ta fara magana.

"Marwan kayi haƙuri mana kaza ma Namiji mai juriya mana. Tabbas na sa ni abin da ciyo, amma ya zamuyi da hukuncin Allah?.

Insha Allah za'a ganta kaji, nan bada jimawa ba.
Kasan Doctor yace 'Ka ra ge tunane tunane sosai,
Please karka ja mana ciwon ka yatashi zamu wahaltu sosai."

Kallon mahaifiyar tasa ya yi cikin karayar zuciya Yake faɗin

"Momy juriya fa kika ce?,
Zan iya juriyar komai a duniya tabbas, banda rashin ta. Bazan iya jurewa ba. Haƙuri Momy taya zan yi haƙuri?,
Zuciyata ba za ta ɗauka ba ji nake kamar zan yi hauka Momy.
Please Momy ki gaya min inda ake cire soyayya, naje a cire min soyayyar ta daga zuciyata, wata ƙila zan samu sassaucin abin da na ke ji.."

jin yadda yake magana yasa Momyn fashewa da kuka ita ma cikin tausayawa ta ce

"Haba Marwan dan Allah kayi shiru mana kasan baka da wata isasshiyar lafiya, so kake ciyon ka ya tashi ne?."

Cikin zubta kwalla mai zafi ya girgiza kai
"A'a Momy nakasa jure wane kawai."

"Kayi hakuri Marwan taka kalar ƙaddarar ke nan."

Rarrashin sa ta ci gaba dayi har tasa mu ta shawo kansa ya daina kukan
da suru tanda yake yi, ta fita ranta na mata suya.

Kasan cewar Ranar Friday ne yasa shi miƙewa yanufi toilet.

A kalla yashafe one hour kafin ya fito
ɗaure da towel.
A wurin da ya tashi a nan ya koma zauna, nan ya fara shafe jikin sa da Body Lotion na maza masu matuƙar tsada da ƙamshi dama shiɗin ma'abocin ƙamshi ne, yakai kusan twenty minute's yana abu ɗaya kafin ya miƙe ya nufi zuwa Closet ɗin sa yaciro wata arniyar Shadda Golding color.

Kama daga Takalman ƙafafunsa A gogonsa, Hularsa duk Golding color's ne..

Sai da ya kammala feshe jikinsa da daɗa-ɗan Turare masu ƙamshi, sannan ya kalli kansa a Mirror idanun sa suka ciko da
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SONKI NE ƘADDARATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album