Join Our WhatsApp Group

ALJANACE KO MUTUM Complete Hausa Novel Document by ALJANACE KO MUTUM


ALJANACE KO MUTUM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16542



ALJANACE KO MUTUM

Reading Time: 1 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Nusnim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 806 448 1931

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 98.15 kb

File Type: txt

Views: 1026+

Download: 185+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: ALJANA CE KO MUTUM
littafin Nusnim
Ebook created by Shuraih 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng




[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*ko*
*MUTUM*
*BY* *Nusnim*

*Assalamu* *Alaikum* *ya ayyuhal* *Muslim in*, *ina* *mika* *sakon* *gaisuwata* *ga* *dukkan* *yan* *uwana* *musulmai*, *dafatan* *zaku* *kasance* *dani* *acikin* *sabon* *novel* *dina* *mai* *suna* *ALJANA* *KO* *MUTUM*, *Wanda* *nida* *kaina* *nakin* *kira* *labarin* _Allah_ _yabani_ _ikon_ _Isar_ _da_ _sakon_ _dake_ _ciki_.
1⃣ &5⃣
kwance yake saman makeken katifarsa dataji lallausar zanin gado' sai juyi yake ya kasa bacci, tunani yake ina zai sake ganinta? ina zai sake tozali da wannan kyakkyawar fuskar dake hana zuciyarsa sukuni dare da rana? wani irin haske yaziyarci idanuwansa, wanda yayi sanadiyyar saurin runtse idanun don hasken yayi yawa, jiyayi ance bude idanunka mosoyina, gani nazo gareka don insanyaya maka zuciya tareda sanyata nishadi" saurin bude idanunsa yayi sukayi ido hudu da kyakkyawar fuskarta, yayi saurin tashi zaune cikeda jindad'in ganinta' don Allah kada kisake tafiya kibarni, ina matukar sonki, inason kasancewa tare dake' inason mukasance a inuwa guda (aure)

tace" kayi hakuri mosoyina inasonka, amman banajin zamu iyayin aure yanxu kusa' saboda wasu dalilai' na farko baka sanni ba' baka san koni wacece ba, akwai babban hatsarin dake tattare da arayuwata' banason wani mummunar abu yafaru da rayuwarka' hawaye yaji ya siraro a idanunsa, ya dafe saitin zuciyarsa dake baraxanar faso kirjinsa sbd tsabar sonta dayakeji' wani irin had'arine? wani irin had'arine arayuwarki dazai hana mana mana kasancewa da juna?
jiyayi ance cikin tsawa ina ruwanka da rayuwarta, inaso kafita hanyar wannan yarinya' inba haka ba rayuwarka zata salwanta, ke kuma yau saikin d'and'ani azaban da baki taba sha ba arayuwarki, ba an hanaki zuwa wajan wannan mutumin ba? afusace matar ta fizgo hannunta 6at suka 6ace'
wani irin zazzafan hawaye ya gangaro a kuncinsa" meyasa zuciyata zatamin haka? meyasa zata fad'a soyayya da wacce ba jinsinmu guda ba? meyasa zataso wacce ba mutum ba, ohh Allah" hannunsa ya d'aga sama yana cewa ya Allah ka kawo min agaji arayuwata' kacire min son abunda bazai ta6a yiwwa ba. tashi yayi yaje ya dauro alwala don gabatar da sallan raka'atanin fijir, kasan cewar ansoma kiraye2n sallah farko.
bayan ya dawo daga masallaci ya dauko book da kanwarsa ta kawo masa jiya daddare don yayi mata assignment, yana gamawa ya kwanta bacci har 9am na safe *NAWWAR* bai tashiba.
mami hafsat ce zaune a parlo tana breakfast, yar autar tace tashigo me suna *mimi* zama tayi kusada maminta tareda gaisheta" mami hafsa tace autana har kin tashi baccin? eh mami nah natashi, gashi duk jikina ciwo yake min wlhy, ayya sannu ga abincinki can keda yayanki idan kikaci sai kisha magani" yau naga shima bai fito da wuri ba, ko lafiya?jeki ki duboshi, to mami, ta tashi ta nufi hanyar dakin shi, abakin kofa sukaci karo.


TAKU UMMU RUMAN
*nusnim*
*phyar*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*ko*
*MUTUM*
*BY* *Nusnim*
5⃣&1⃣0⃣

Abakin kofa suka ci karo shima yafito cikin shiri, yace a'a autar mami ya akayi? lafiya lau hamma nah, mami ce tace inxo in dubaka, yau baka tashi da wuri ba?
eh wallahi assingment din kine ya hanamin bacci da wuri, saboda wannan *nahawun* yad'an bani wahala, kai hamma" kai da ka haddace nahawul wadi shine zai baka wahala? nikam ban yarda ba? dariya yayi yace autar mu baki da dama.
suka karasa wajen *mami hafsah* duk suka zauna kusa da ita, *Nawwar* yagaisar da maminsa cikin girmamawa, ta amsa tare da cewa nawwar yau lafiya baka tashi da wuri ba? ko bakajin dadin jikin ne? a'a mami lafiyata kalau.
kawai assignment din wannan autar naki ce ya hanani bacci da wuri, mami tace dafatan dai kagama mata? eh nagama, cikin murna mimi tace yauwa hamma nah nagode sosai, kace yau ni zanyi ta d'aya a ajinmu, murmushi yayi yace aah nibance ba" kika sani ma koban rbt dai2 ba? fuska ta yamutsa cikin shagwa6a tace mami kina jinsa koh? wlhy kabari aka sakamin ziro saina gayama abba, dan nasan ka iya nahawu sosai' idan naci xiro nasan kana sane kamin' kuma mami kicema hamma yadaina min fatar cin zero' ta karashe mgnr tana turo baki" dariya sukayi gaba d'aya
mami tace rabudashi autana jeki kawo muku breakfast kuyi kuci kutafi lkc na wucewa, to"
mami ta gyara zamanta da kyau ta kalli Nawwar tace kaima yakamata ace zuwa yanxu kafitar da matar aure, tun kafin baban ku yaza6o maka matar da bakaso, tunda ya dade yana baka lkc.
wani irin faduwa gabanshi yayi, sai gumi yasoma hadawa a goshinsa' yayin da zuciyarshi ke har bawa, saboda tuno abar sonshi, shiru yayi"mami sai magana take amma kamar hankalinshi bai jikin shi, data gama maganar ne tayi shiru ta zuba masa ido, shi bai ma san tayi shirun ba.
hankalin shi gaba daya ya tafiga tuno masoyiyarsa' kafad'arsa mami hafsa ta dafa , yayi saurin sauke ajiyar zuciya, ya dago kai ya kalleta, idanunshi har sun kada sunyi launin "JA" , mami hafsa duk ta tsorata da ganin yadda yanayinshi ya sauya cikin dan lkc, cikin damuwa tace lafiya *nawwar*? daga maganar aure har yanayinka yacanza, shin bakada lafiya ne ko aurenne baka so? ajiyar zuciya ya sauke tare da karnto addu'ar nutsuwa, a hankali ya riko hannun mami dake kan kafad'arsa' yace wlhy mami nikam tsinci kaina a cikin tashin hankali da damuwa aduk lokacin da akamin maganar aure, sai inji zuciyata tana suya, cikin raunanniyar murya yace mami nah please kitayani da addu'a babu wacce tafi cancanta na fadama damuwata sama dake,
akwai wacce nake matukar so tana yawan zuwa min a mafarki da zahiri sai dai kuma ba mutum bace, mami tazaro ido waje, yace wallahi mami ina tsananin sonta jinake bazan iya rayuwa babu ita ba.
dayar hannunsa yasa ya goge hawayen daya gangaro a idanunshi, sosai mami ta tausaya ma danta, itama tuni hawaye yaciko a idanunta' tace wannan wace irin masiface? ina nata6ajin anyi syy tsakanin *aljana* da *mutum* ta jinjina kanta tace Allah mai iko.
*nawwar* kaci gaba da addu'a insha Allahu nima zantayaka dayin addu'an Allah ubangiji yacire maka son abunda bazaiyu arayuwarka ba, amma gaskiya naji tsoro, ba jinsin mu daya ba, meyasa zasu Shiga rayuwar d'ana? meyasa ita wannan aljanar tazabi tayi soyayya da kai alhalin tasan kai ba jinsin su bane? gsky bata kyauta mana ba, insha Allahu addu'ah itace magani, kaima nasan kayi sakaci da addu'ar ne shiyasa'
mimi da ta dade da kawo musu breakfast tazauna tanajin abinda mami da hammanta suke tattaunawa,itama ta tausaya masa kuma taji mamakin al'amarin, tace *hamma* nah kamar yadda mami tace maka addu'a itace magani, toh ita zaka dingayi nima zantayaka kaji hamma nawwar, murmushi yayi yace nagode autar mami.
yaji dadin yadda mahaifiyarsa da kanwarsa suka fahimceshi tareda kwantar masa da hankali, da kuma nuna masa muhimmancin addu'a" nan sukayi breakfast dinsu, bayan sun gama mimi tayi saurin saka kayan islamiyarta don nawwar ya sauketa a makarantarsu, tare suka fito farfajiyar gdan mami hafsa tarako su tana daga masu hannu har suka fita gidan.


TAKU UMMU RUMAN
*nusnim*
*phyar*
*EID* *KUM* *MUBARAK*
*TAQABBALALLAHU MINNA WAMINKUM*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*
*BY* *Nusnim*
1⃣0⃣&1⃣5⃣
nawwar ya ijye Mimi a islamiya" shi kuma Yakama hanyar zuwa hospital dinshi, yana tafe yana tunanin maganar da sukayi da Mami, yana cikin tunani wani abu ya diro mishi kan motar shi, yayi saurin J'an burki" tare da kifa kanshi kan sitiyarin motan yana maida numfashi, dago kan dazaiyi " yayi ido hudu da wannan matar da dauke mashi abar sonshi lokacin data zo mai, yayi saurin zabura tare da karanto *innalillahi* *wa'inna* *ilaihiraji'un*, da sauri ya rufe glass din motarsa" gani yake kamar zata shigo.
itako tana tsaye tana kallon abunda yake yi, tasaki wani irin gitattaccen dariya, tare da nunasa da dan yasa" cikin babban murya, tace *Nawwar* nazo maka gargadi ne kafita Daga rayuwar *sameeratun* *nawwara* idan kuma ba haka ba , kai da'ita zaku fuskanci" mummunan tashin hankali arayuwar Ku, don baza mu kyale kowani bil adama ba yashiga cikin rayuwar mu.
yanxu haka *sameeratun* *nawwara* tana can tana fuskantar mummunar hukunci, saboda tasaba mawa dokar mu, *nawwar* yayi saurin cewa don Allah Ku kyaleta karku" mata komai, ta daka mashi tsawa tare da cewa, kai har ka isa kafada mana abunda zamuyi, ina kara gargadin ka" akaro na biyu, Daga fita Daga cikin rayuwar da bata shafe ka ba, Idan kunne yaji Gangar jiki yatsira.
zai yi magana kenan wuf ta bace mai, ya sauke ajiyar zuciya tare da hawaye mai radadi dake gangaro mai, zuciyarshi sai har bawa take kamar zata fito, sboda tsananin zafin dayake mai.
jikinshi duk ya mutum kamar Wanda akamai duka, dakyar ya iya Jan mortar sa zuwa hospital" lokacin dayayi parking din mortar sa alokacin abokinsa shima yayi parking din nasa" nawwar ya bude mortar zai fito yakasa ganin halin dayake ne yasa abokinshi me suna awwal" ya karaso wajan da Sauri cikin kidimewa, yana fadin nawwara lafiya naganka haka? meke damunka? cikin karfin hali nawwar ke nuna mawa awwal zuciyar alamun ita ke mai zafi, amma yakasa magana" awwal ne ya taimaka mashi suka karasa cikin hospital din.
dayake shi doctor be a fannin zuciya, ya kwantar dashi kan gadon sake office dinsa ya dubasa da kyau, tare dayi mashi allura da bashi magani" har bacci yayi awon gaba dashi" awwal ya zauna shiru yana tunanin wani irin damuwa ne abokinshi yake ciki" da har ciwon zuciya takamashi, Allah sarki nawwar, Allah ya yaye maka koma menene.

***************
tun lokacin da sameeratun nawwara tabar gun nawwara ake gallaza mata azaba aduniyar su ta aljanu" don ta taka dokan da aka mata, daure take jikin wani bishiya ta tsafi duk kaca ne jikinta, yayin da wasu irin halittu ke jibgarta da bulalan wuta, tana ihu saboda tsananin azaban zafi.
gefe daya kuma wani mutum ne azaune cikin kayataccen kijera ta alfarma irinta sarauta da alamu shine shugaba" sai dariyan keta yakeyi, irinta ta mugaye.
yana kallon yadda ake wahalar da sameeratun nawwara, saida da ya bari tasha wahala sosai har bata motsi sannan yace adakata" ya karaso wajanta dai dai fuskarta yasa hannunshi yadago fuskarta, yace haryanxu, kina cikin bakanki na kin" aure na, tayi karfin hali tace eh, bazan aureka ba, ba zan aureka ba, koda zan rasa raina ne , kamar yadda " kuka rabani da farin cikin to kuma har abada bazaku taba samun naku farin cikin ba, don nawwar shine mijina, na har abada, *Ambar* yayi saurin ja da baya yana cewa, cewa karyanki ne kija dani sameeratun nawwara, sai kinzama tawa, banga wani bil adaman daya isa yashiga gonata ba , mahaifinki shi yaja miki sameeratun nawwara" ni nan *ambar* sai na mallake ki, duk cikin tsawa yake maganar nan, kuma sai naga bayan wannan nawwar din, tanaji ya ambato nawwar dinta , itama cikin Daga murya tace karya kake ambar , indai INA da sauran numfashi baka Isa ka halaka nawwar ba, don yafi karfinka" ji tayi an wurgo mata wani katon dutse dai dai saitin bakinta" har Saida hakorarta yafadi, ta dafe gun tare da juyowa" taga wanene , ido hudu sukayi da kanwar ambar, me suna *kiyara* tana dariyar mugunta.
cikin tsawa tace baki da hankali kike fada mawa shugaban mu magana " saina koya miki darasi, cikin iska tazo da gudu zata shake" wuyan sameratun nawwara, sai taji ansha ke nata wuyan, bataganin Wanda, yashake ta" saboda wani irin guguwar iska ce" ke tashi, *kiyar* da *ambar* sunshiga rudu saka makon ganin wannan halittar, cikin yaransu wannan halittar take cewa " duk da na mutu baza kubarni na huta ba, sai kun binci koni.

TAKU UMMU RUMAN
*nusnim*
*pyar*
[1/11, 4:39 PM] ‪+234 806 448 1931‬: *ALJANA*
*CE*
*KO*
*MUTUM*

...


Read / Download ALJANACE KO MUTUM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album