Join Our WhatsApp Group

Mage Complete Hausa Novel Document by Mage


Mage

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 254167



Mage

Reading Time: 21 Hours

Added On: 04, Apr 2023

Author: Sajida ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Taurarin Marubatan Niger

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 1.52 mb

File Type: doc

Views: 3769+

Download: 5216+

Last download: 16 hours ago

DOWNLOAD
Description/Story: *MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß>ØÕÝ<Øûß

Na

*SAJIDA*


1


Zaune suke baki d'ayansu cikin fada, a kasa suke su dukansu saman tankadaden reran (kasa fara tas) dake tsakiyar fadar baki daya ba saman tabarma ba

Su dukansu sun tantankwashe kaffafuwansu tun daga datijon dake zaune har zuwa yar karamarsu

Kamaninsu du iri daya ne, sun kwaso kamar mahaifinsu wanda ya haife su wanda yake zaunen cikin shigar shada ruwan toka mai cike da kamala
Sai matarsa dake zaune gefensa fara tas matashiya domin sam bata kai shekarunsa ba bayanta da goyo tana dan jijiga yarinyar dake dauke da wani irin gashi mai kyau a kanta wanda sun gado shi ne daga wajen mahaifinsu da yake bakin balarabe

Manyan malaman fadar ne zazaune kusa da kujerar alfarma wace sarki ke sama zaune ya kura masu ido daya bayan daya yana kallonsu
Dogarai ne hudu biyu gefe da gefen sarki, daya rike da wata irin bullalar dorina irin ta dukan rakumin nan murdadiya mai taurin gaske sannan mai lauyewa wace idan aka tsulawa mutun take zagaye jikinsa ta dannu da zafin gaske, dayan kuwa yana tsaye rike da wata jakar fata wace ke dauke da alkur'ani mai girma ya masa kyakyawan riko

A hankali sarki ya dan daga kansa ya dan juya kan nasa hakan ya sa baban malamin da ya fi aminta da shi sannan ya fi kowa tsufa a fadar ya gyara cikin nutsuwa ya ce" Allah ya ja da rai, Allah ya jibanci lamuran sarkin garina, Allah ya huci zuciyar matashin sarkina mai cike da kamala, na miko gaisuwata ina kara jinjina da adu'ar gamawa da duniya lafia

Sai da ya numfasa kafin ya ci gana cike da jin nauyin maganar da zai yin duba da abin na cikin gida ne ya ce"
Yaran nan ne suka shigar da karan da ka bada rana yau a zo gabanka zaka wanzar da shara'a kwana biyu da suka shige

Baki daya aka kwashi gyara kimtsi, sarki mai adalci, sarki mai zartar da hukunci a kan dukan wanda aka cuta

Sai da ya lumshe idannuwansa cike da wani irin jan aji da wani irin cika da kamala sannan da jin kunyar datijon dake zaune wanda ke tafe da iyalinsa baki daya sun zo a masu shara'a kafin ya daga yan yatsunsa yana kallon baban yayan yaran da suka kawo karar mahaifinsu da kuma matarsa kan a saka masu alkur'ani a masu shinge kan aikata mugun abu a tsakani kama daga maganin asiri , zagon kasa dai da sauransu dukan abinda zai zama na cutarwa ne

Da dan yatsansa ya yi nuni kan baban yayan nasu wanda kansa ke kasa yana cike da kunyar sarkin domin ya tabata ya shaka kuma a kansa zai sauke dukan haushinsa

Da sauri na kusa da shi ya fadi cewa" Sarki ya baka damar fadin abinda ke tafe da ku a matsayinka na ja gabansu

Sai da ya sada kansa sannan ya dago ya sauke ajiyar zuciya, shi kansa kana ganninsa ka ga jinnin sarautar domin maganar da zai yi sai da ya ringa motsa bakinsa kafin da kyar ya buda bakinsa ya ce" SUNNANa *DAYABU BINE MUTALAB,* mun kawo karar matar mahaifinmu ne wato MUTALAB da kuma matarsa MARDIYA domin muna so a yi mana shari'a ta adalci hakan ya sa muka nufo gidan adalci

Gaskiya ne jangori, gaskiya ne yaro jangori a nan adalci shi ke janye da ragamar komai

Ajiyar zuciya ya sauke ya ci gaba da fadin" ba wani abu ne ya kawo mu nan ba sai bukatar a yi mana tsakani da matar mahaifinmu wanda take uwa a wajenmu kan zamantakewar yau da kulun, kwarai muna fuskantar abubuwan dake gifata mana kala daban daban wa'inda suke saka mu a halin rashin nutsuwa da fadace fadace tsakaninmu da ita
Mun zo gidan nan ne dan kaine uban kowa kuma mai zartar da hukuncin da ya dace bisa tafiar adinni,
muna so a yi mana tsakani da ita kan maganar magani wato asiri, kar ta shiga tsakaninmu da mahaifinmu, kar ta shiga tsakaninmu da yan uwanmu, kar ta shiga hurumin aikinmu, ko matayenmu ko kannenmu kar ta hada su da lamari na rashin samun miji, a takaice dai dukan wani shinge da ake yi a gidannan mun zo da kokon bararmu kan a mana shi tsakaninmu da *Su* muma a yi masu tsakani da *Mu* koda wani ta ji zai yi idan bata tona ba, koda wani muka saka ya mana ya ci mu!

Wasu kai suke jujuyawa, wasun kuwa cike da mamakin yau shara'ar ta cikin gida ce aman suka yarda ake yinta a fili gaban kowa, Jangori ne da kansa sai y'ayansa duda aun kasance fitatu kuma sananu a duniyar rigima sai dai abin ya bada mamaki gannin ya amsa kira shi dinma da kansa
nan da nan labari ya fara fita waje harma yan jarida suka fara garzayowa suka cika kofar gidan sarki kowa na jiran fitowarsu domin komai abinka shara'ar gidan sarki baka isa ka fitar da ita waje ba sai dai ka tsinci abinda ka tsinta a waje

Murmushi mahaifinsu ya yi a lokacin da DAYABU ya gama magana kafin ya dago jajayen idannuwansa da suka rikide sukai ja sakamakon bacin rai ya kali y'ayan nasa daya bayan daya sannan ya ce" *Na yarda nima a min tsakani da iyalaina, Sai kuma ya rage muryarsa a hankali ya kalli sarki ya ce" Aman banda soyayarmu, ina nufin ni dai ta min na fuskana wanda zamu ci gaba da zama lafia*

Gaba daya aka shiga kallonsa, da yawa suka shiga sada kansu cike da kunya, wasun suka saki baki da jin abinda ya fada, matarsa kuwa ta rausaya kanta tana sakin murmushi tana jujuya kaffafuwanta
A lokacin ne itama ta dago kanta da wani irin sauri ta kai dubanta wajen mahaifinsu
Hannunta na hagu ta dago ta kai wajen bakinta da sauri tana mai ruruko manyan idannuwanta masu zagaye da kwalin kajal ta ce" *lah*

Sai kuma ta maida dubanta wajen sarki wanda ya sauke mata kallon da zata iya kira kallon tsana wanda kwannan duniya ita rayuwarta bata san me ta masa ta tsare masa ba ya tsaneta yake kuma kan tsanarta kamar ya fida mata rai , ba wani haduwa suke da shi ba sai jifa jifa ko idan shara'a ta kawota ko ta rako wani aman daga irin kallon kyamar da yake jifanta da shi ta tabata da ace mai magana ne shi ko mai zage zage da ya mata zagin da bata taba jin irinsa a duniya ba

Kanta ta yi gagawar mayarwa ta sada

Sarki ya dan yi gyaran murya yana mai duban dogari mai rike da dorina a hannunsa, sannan a zuciyarsa ya ayanna" *Dama yaya za'a zo wajen fitina banda ke ke dai kin saka kanki a uku, mai yiwuwa yanda fatarki keda baki haka aniyarki azaluma kawai!*

Da sauri mai rike da bulalar nan ya dagata ya mata wani irin duka a jikin wajen da na yi tunanin garu ne, ashe ba garu bane an masa wani irin tsarin shafa penti ne ya hade da garun

Karan da abun ya yi ne ya saka baki daya mutanen wajen sada kansu sunna masu nutsuwa harma da hade kafafuwansu sunna kara kimtsa zamansu

Sai da ya kuma dago kansa ya kara bin y'ayan da kallo lafin ya maida wajen mahaifinsu da kuma matarsa
Su su goma sha uku ne, cikinsu ba wanda suke uwa daya kowane da uwarsa sai dai wani ikon Allah kamaninsu baki dayansu ya zo daya sai dai daga fata ne wani ya fi wani haske
Kanta ya sauke dubansa, yanda take wasa da yan yatsunta kanta sade tamkar saliha
Haka ya kuma furtawa a kasan zuciyarsa kafin ya maida dubansa wajen mai rike da alkur'annin

Hannunsa ya nuna kansa

Da sauri ya buda alkur'annin ya ciro shi
Baki daya wajen suka kwashi kabara hakan ya sa du wanda ke wajen tsigar jikinsa tashi tana yam yam yam masu saurin hawaye kuwa suka shiga sharewa

Kanta ta dago a hankali ta kai dubanta wajen alkur'anin
Kafeshi ta yi da ido, har idannuwanta suka nuna mata abinda take zargi

Da sauri ta kalli yayansu, sai kuma ta maida dubanta wajen mahaifinsu wanda shima ita din yake kallo ya zabga mata harara domin cikinsu ba wanda baya jin haushi, su dukansu suun cira bata nuna ba kuma daya bayan daya sai ya rama!

Dan jan abin da ta ganni ne ya sakata tabe bakinta ta maida dubanta wajen sarki wanda ya gama hada gabas da yama kudu da arewa ya hade rai hakan ya tsoratar da dukan wani wanda ke zaune a wajen itama da gagawa ta sada kanta tana dan bubuga kafafuwanta kasan zuciyarta kuwa fadi take " *Azalumi mai wata fuska*

Baban malamin dake zaune ne ya gyara zamansa cikin kamala ya shiga koro bayanan saka layar wanda du idan ya yi magana wajen sai an dauki kabara

Irin abubuwan da aka gindaya habaici da baki ne kawai aka cire ciki kuwa harda duka aka saka hakan ya sa jikin DAYABU yin wani irin sanyi nan da nan dana sani ta ziyarce shi yana kallon kannen nasa da ya yi imanin du sai sun mutu ko sun kuturce a kan layar duka da aka saka masu dan wasu irin jarababun y'aya ne masu fadan balaki, domin idan ta hadoka da su har kirari suke yiwa kansu na idan baka jiyata mutumen ba kai ba jinnin MUTALAB bane!

Cike da tausayi ya ajiye dubansa a kanta, ya tabata itace gawar fari domin kaf cikin kannensa babu wace ta kaita fada , a haka kuwa kamaninta sam bata da siffar mafadaciya, sam *Kamaninta basu yi nuni da wace zata iya yiwa wani illah ba*

Ana gamawa wajen ya kwashi wani irin shiru,
Sai da ya kuma jifan DAYABU da kallon zamu hade sannan ya gyara rawaninsa hakan ya sa suka gane zai mike ne, domin dama wannan shari'ar ita ta fitar da shi, ita ta tsayar da shi, baya kananun shari'a sai idan baba ce ko wace ta shafi ahalinsu

Kowa kansa na kasa sakamakon tashin da zai yi
A hankali ya sauko kafarsa ta dama mai dauke da takalmin fata irin na jinnin sarauta aman yana da kalar fukafuken dawissu bayan ya yi adu'a a kasan zuciyarsa

Sai da ya gama sauke kafafuwansa sannan ya mike da wani irin isa da takama
Yana mikewa da sauri sauran dogaran da suka karu suka shiga gyara masa rantsatsiyar suturar da ya saka ta yau wace sak irin fukafuken dawisu ne, harta da rawanin da ya sha wani irin rawani ne da akaiwa adon dawisu hakan ya sa baki daya ya dauke hasken wajen

Da sauri suka lallayu shi kuwa ya shiga takawa a hankali yana bi ta tsakiyar mutanen da suka layu

Kanta dake kasa hakama idannuwanta tana kallon kasa
A lokacin da ya kawo kafarsa daidai ita ta kasan gilashin dake fuskarsa mai hasken fari ya ga yar igiyar abin sauraron kidan da ta saka a kunnayenta tana sauraro, hakan ya sa ya dan jima a tsaye a kanta har sai da ta yi saurin dago da dubanta sai dai bata karasa kallon fusakarsa dake lulube da rawani da gilas ta yi saurin sada tsumamun idannuwanta da kanta tana kallon takalminsa da ya tafi da imaninta baki daya

Wata ajiyar zuciya mai zafi ya sauke yana ayanna tabas idan tana tunanin ta gagari kowa zai taka mata birki, a kulun ya hadu da ahalin gidansu yana mamakin irin zubin Halitar salihan mutane da akai masu sai dai tarin jaraba dake ciciyarsu, bare ita dake dauke da irin idannuwan nan masu lumshewa da wani irin lumtu lumtu masu tudun gaske da wani irin kumbura

Kwafa ya yi a ransa ya ayanna: ita har ta isa ta saka abin sauraron kida a lokacin da take zaune a gabansa?

A hankali ya kuma daga kafarsa ya ci gaba da takawa har ya bar wajen wanda barin wajen kadai sai da ya dauki kusan minti talatin tashinsa zuwa tafiarsa

Sai da ya shige sannan dogarin ya shaida masu summa iya daga kai

Kanta ta dago hade da harara ta sauke a fuskar dogarim wanda yake ta lulube kujerar sarki baima san tana yi ba

Yayansu na mikewa suma du suka mimike , mahaifinsu kuwa ya duka sunna magana kasa kasa da malan

Cike da bacin rai ta fara fita
Tana fita ta saka dogon takalminta fari kal mai tsinin gaske ta rike tsatsonta tana girgiza

Yayanta da sauran kannenta ne suka fito sai matar babansu a bayansu dauke da yarinyarta a goye

Da wani irin sauri ta zagaye ta koma kusa da ita ta kama goyon da sauri ta kunce hakan ya sa suka shiga kokowar kar ta kunce mata goyonta ita kuwa sai da ta kunce shi ta yi sauri ta damkawa yayarta mai dan sanyin cikin nasu wace ke fadi" ke meye haka? Ki rufa mana asiri da laya tsakanninmu

Bata tsaya ta saurari abinda take fada ba ta juya da sauro ta karasa kusa da matar mahaifinta wace ke tsaye da yan uwanta suma dangin balaki ta daga hannu ta wankawa matar mari da wani irin masifa ta aniya shigarta da duka

Yan uwan matar babansu na gannin hakan summa suka shigeta da dukan domin ai laya tsakaninta da su aka yi ba da yan uwanta ba
Yan uwanta na gannin hakan summa suka kasa hakuri domin familynsu wata irin family ce mai wuyar fasara, a tsakaninsu sunna cin kansu kamar me sai dai koda wasa basa bari a cuci dan uwansu idan kuwa aka yi gigin hakan sunna iya haduwa su lalasa mutun

Wata irin kokowa ce ta kaure tsakanin dangin matar mahaifinsu da kuma su hakan ya saka baban yayansu dora hannayensa saman kansa a fili furta" shikenan, yau dai karshenmu ya zo, shikenan ta halakamu baki daya

Da sauri ya karasa ya shiga janyo kannen nasa du wanda ya yi gardama kuwa hannunsa yake dagawa ya wankawa mutun mari nan da nan sai mutun ya bar fadan, mutane kuwa sunna kallon ikom Allah basu shiga ba domin kana iya shiga dan rabiya abin ya juye kanka su kuwa basa fatan fada da wannan ahali

Yana damkar hannunta itane ta karshe sai da ya kaita kusa da motarta ya saketa
Tana ta maida numfashi bata ankara ba ya daga hannunsa ya dauketa da gigitacen marin da ya sakata jin wani irin kauuu har kunnayenta suka yi kamar sun rufe tsabar saukar marin da zafi

Cike da fada ya ce" kin kashe mu! Kin kashe mu! Ubanme ya kaiki marinta bayan yanzu aka mana tsakani da laya a gabanki aka dagata?

A firgice sakamakon zafin marin da ya dada mata da dago shanyayun idannuwanta masu matukar haske da girma ta kale shi, kamar an mintsineta ta...


Read / Download Mage

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album