Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

LIFE PARTNER Complete Hausa Novel Document by LIFE PARTNER


LIFE PARTNER

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 71239LIFE PARTNER

Reading Time: 5 Hours

Added On: 07, Apr 2023

Author: Fatima ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zamani Writers

Author Phone : 08103810398

Book License : Paid

Category: Horror novels

File Size: 368.89 kb

File Type: txt

Views: 3167+

Download: 1773+

Last download: 21 minutes ago

Description/Story: https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: _...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_1~2_
*Thanks to Almighty Allah for giving me the ability and chance to start the book SHARIK HAYATI {My life partner}, Special greetings to the whole members of ZAMANI WRITERS ASS. Ina maku fatan alkhairi da kuma gamawa lafiya, My Ilham, Fatima (Baby), My Zee Auwab and Luvly KK can't luv u less sisters. Members of my groups are not excluded too, ina sanku sosai wallah 🥰 Finally my fans, Ina maku gaisuwa irinta addini aduk inda kuke, billah nima ina yinku over and over ❣️*

A firgice ta mike tana kallan agogan dake manne a bangon dakin, ta zare manyan
idanuwanta waje ta ce"What!!! Past 8". Quickly ta janye duvet din dake jikinta ta shige bathroom hankalinta a tashe, bayan 6 minutes ta fito daure da towel ta nufi gaban mirror, comb ta dauka ta fara combing gashinta, nan da nan ta gama ta dauka ribbon tayi packing smooth hair dinta waje daya, daga nan ta fara robbing body lotion shap-shap. Cikin few minutes ta gama ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga baki ta saka kafin ta dauko veil dinsa ta yafa ta jawo side bag dinta dake jikin bag hanger sannan ta fice a dakin, daidai shoe rack ta tsaya ta dauka flat shoe sannan ta kama hanyar stairs cikin sauri ta fara saukowa. Ba kowa a falon sai TV dake kunne sai karan standing fan, hakan yasa ta wuce kitchen da gudu tana fadin "Ummi! Ummi!" Kafin ta karasa shiga kitchen din Ummi ta fito rike da warmer, kana kallanta kaga mahaifiyar yarinyar saboda tsantsar kama da suke. Ummi ta mata wani irin kallo ta ce"Are u ok? What's the essence of running" ta ce" Ummi ina da appointment a clinic yau fa" ta karashe maganar in a hurry, Ummi ta dalla mata harara ta ce"Wa kika gayawa to?", a hankali ta dan gyara veil dinta ta ce"I'm sorry Ummi, jiya da doctor hisham ya kirani kin riga kin rife kofa, and i didn't woke up early today". Ummi ta ajiye warmer din hannunta akan dinning ta ce"Kije Mustapha ya kaiki, i think i don't have to go,". Silently ta ce "To saina dawo" daga haka ta fice a kitchen din ta nufi kofar fita.
Babban gidane na gani na fada, yana dauke da shuke shuken flowers all over, part guda biyu ne daya na kallan daya sai kuma BQ daga gefe sannan parking lot a tsakiyan apartments din wanda ke dauke da motoci 6. Da sauri ta karasa jikin motar tana kallan Mustapha ta ce"Na makara fa Musty, kuma cewa yayi he's leaving the country today" ta karashe maganar tana shiga back seat, Mustapha ya rife kofar ya zagayo cikin hanzari ya shiga driver seat ya kunna motar yana fadin "Yanzu zamu isa Hajiya Karama, aini inasan shiga asibitin nan kodan ina ganin turawa, ance nasu nema asibitin ko?". Murmushi tayi me kyau ta ce"Sure, amma ai mutanenmu na nan suna aiki a caan" Mustapha ya washe baki ya ce"wa yake ta bakar fata Hajiya karama, ai turawan sunfi dadin gani, kaii Allah yayi halitta, farare kal kal dasu kamar ka bigesu jini ya fito, nifa ban ta6a ganin turawa ido da ido ba a garin kano sai a asibitin nan" ta ce"To menene abin san gani a jikin bature Mustapha, sai wani zuzutawa kake" cikin sauri ya ce"Ai wallahi Hajiya karama bature abin a ganshi ne, aini dana zauna kallan bakar mace gara a kaini gaban tsohuwar baturiya naita kallanta ina maimaitawa", dariya sosai tayi kafin ta ce"Wato dai Mustapha bakasan ganinmu kenan, kace baturiya zaka nemo" zaro ido yayi ya ce"Na isa ince banasan ganinki, ai wallahi dana fara ganinki na zata bakyajin hausa sai larabci" dariya ta fashe dashi tana girgiza kai, duk drivers din da suke yi a gidansu tafi san Mustapha saboda idan yana mata hira yana sata nishadi, ko bata da lafiya inya shigo gaisheta sai yasan yadda yayi ya sata murmushi. Yana parking ta fito a motar tana kallansa ta ce"To zan shiga Mustapha, ga turawa nan aita kallansu, idan na fito ka fadamin wacce ka za6a" bata jira amsarsa ba ta wuce ciki saboda sauri da take.Kamar me counting steps ta shiga clinic din very gentle, office din dake gefenta by d left ta nufa ta fara knocking a hankali, ta ciki aka bata izinin shiga sannan ta bude kofar a hankali ta shiga, Doctor hisham kawai take kalla tana murmushi ta karasa ciki ta ce"Morning Dr" ya mayar mata da murmushi ya ce"Morning Fatima, how are u?" A hankali ta ce "I'm fine Dr, i though u are leaving now". Dr hisham ya kalli wristwatch din hannunsa ya ce"I have 1 hour left, have a seat" ya karashe magana yana nuna mata kan sofa, juyawa tayi a hankali zata zauna ta ce"But Dr pls i don't want injection this time around i need just dru... " shiru tayi tana kallan Mutumin dake zaune kan sofa yana danna waya, saam bata kula da mutum a wajen ba, and his face look very familia, ta dan hade gira in a very low voice ta ce"Morning" ba tare daya dago ba ya ce"Same" daga haka yaci gaba da danna wayarsa, ta juyo tana kallan Dr dake rubutu ta ce"Can i have them now?" Ya ce"Yes wait a minutes, how is Abba?" Ta zauna kan hannun kujeran ta ce"He's fine". Very gentle mutumin gefenta ya tashi ya ya karasa wajen Dr Hisham ya mika masa hannu ya ce"Dr I'm going, thanks for all" Dr yayi murmushi ya ce"Alright friend Allah ya sauwake" zame hannunsa yayi cikin na Dr ya mayar cikin pocket dinsa ya ce"Ameen" daga haka ya nufi kofar fita a office din. Doctor Hisham ya mika mata takardar daya rubuta mata magunguna ya ce"Gashi, idan kika siya a pharmacy zasu miki explaining just like they used to" ta kar6a takardan ta ce"Thank u, and when are u coming back from cairo?" Ya ce"I'm spending just 5 days, idan akwai matsala u can meet Dr Aryan zai maki komai" ta ce "To nagode", daga haka ta fita a office din ta wuce pharmacy.
Still mutumin nan yana tsaye a wajen, ta samu gefensa ta tsaya tana kallan fuskarsa daya hadeta ko walwala babu unlike ranar daya taimaketa. Kallan magungunan da aka masa packaging kawai take, sak irin nata wanda take sha, kenan shima irin ciwanta gareshi? Abinda ta fada cikin ranta kenan. Mika nata takardar tayi bayan an sallameshi ya bar wajen, cikin few minutes itama aka mata packaging nata ta biya kudin sannan ta bar pharmacy din cikin gaggawa saboda bataso mutumin ya mata nisa. Tana shan kwana ta ganshi a zaune ya limshe idanuwansa kamar me bacci, ta karasa a hankali ta tsaya a kansa ta ce"Assalamu alaikum" ya bude manyan idanuwansa cikin cool and sweet voice ya ce"Wa'alaikum salaam" ta danyi murmushi dan batai tinanin zai amsa ta ba, wasa ta farayi da ring din hannunta ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ce"Thank u once again for helping me the other time, lokacin dana farka Salma tace min ka tafi, sai yau Allah ya hadamu, thank u so much" kallanta kawai yake yana sauraronta since she started talking, ya sauke kansa kasa ya ce"Ba komai, ki dinga kula" ta ce "Insha Allah" daga haka ta juya zata tafi ya ce"Your name" ba tare data juyo ba ta ce "Fatima Rafi'ah" ya mike tsaye yana kallanta ya ce"I'm Yusuf Muhammad" sai a lokacin ta juyo ta ce"Nice to meet u, thanks much" daga haka taci gaba da tafiya tanajin ta sauke wani babban nauyi na masa godiya da tayi.Ta bayanta taji ya ce "Rafi'ah" ta tsaya caak sai kuma ta juyo tana kallansa, da alama binta yake a baya, ya karaso wajenta yana folding hannayensa ya ce"Can u pls pretend as my girlfriend?"
Zaro ido tayi tana kallansa ta ce"What!" Ya gyada mata kai looking into her eyes ya ce"Yes, pls do help" cikin sarkakkiyar murya ta bude hannayenta tana kallansa ta ce"But why?" Hannayensa duka ya saka a pocket dinsa ya ce"I will explain ltr, just go...


Read / Download LIFE PARTNER

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album