Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

NI DA FATALWA Complete Hausa Novel Document by NI DA FATALWA


NI DA FATALWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10166



NI DA FATALWA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 06, Apr 2025

Author: King Boy Isa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08096831009

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 52.67 kb

File Type: txt

Views: 122+

Download: 39+

Last download: 2 days ago

Description/Story:  ↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {1}

@KINGBOY ISAH



NOTE:
IN KASAN KANA/KINA DA TSORO KARKA/KI KARANTA. DOMIN LABARI NE MAI CIKE DA ABUBUWAN TSORO DA NA DARIYA. IN KUWA KA KARANTA KAYI MAFARKIN FATALWA BA RUWAN KING.LOL


"Habib da gaske wai fita zakiyi ka barni ni kadai? Wallahi na gaya ma akwai fatalwa a gidan nan, ni fa na ganta da idanuna dan Allah in dai fitarka ta zama dole to ka barni in tafi gida da yamma in ka dawo daga wajen aikin sai ka biya ka dauko ni kaji angona tsoro nake ji". Tsaki naji yaja abunda bai taba mun ba tun kafin ma muyi aure balle yau da na zama amaryarsa yau duka kwana takwas nayi a gidan nasa. "Khadija naga alamun so kike ki bata mun rai kuma nima in bata miki. Wai ku mata me yasa komai sai kun canfa shi ne? Shegen tsoro ne ya miki yauwa amma ba wani fatalwa a gidan nan, ni a rayuwata kwata-kwata ma ban yarda cewa akwai fatalwa ba. Ni zan tafi kuma wallahi in kika yarda kika sa kafa kika fita daga gidan nan ko? Zakiyi mamakin hukuncin da zan yanke". Yana fadar haka ya shige motar sa ya fita sannan ya dawo ya rufe get din. Da sauri na karasa bakin get din na zukulkula kubobi hade da kule get din. Zuciyata cike take da tsoro amma ya na iya? zaman aure ya ja mun. Shima Habib sai da nace ya nema wani gidan- ya nema wani gidan amma yaki gida kusa da makabarta ai dole ma fatalwa ta takura ma. Tsaye nake tsakar gida ni kadai nake zancen zuci. Ta wutsiyar idona na hangi kamar wani farin abu ya shigar mun daki. Hakan tasa na nufi dakin a tsorace na bude labule. Sai da na leka ko'ina a falon naga ba kowa sannan na sauke ajiyar zuciya. Domin bana mantawa sau biyu naga fatalwar nan kuma fararen kaya ne a jikinta. Jikin socket ma naje na ciro wayata na bude data na kwanata kan kujera sofa, na shiga whatsapp na fara chat da kawayena domin shi ne kadai nake tunanin zai deben kewa. Message naga ya shiga na bakuwar number nayi saurin shiga hoto ne aka turo ba sallama ba komai. Na sa hannu na danna kan hotan don ya bude. Ihu na kwada hade da yin wulli da wayar. Domin kuwa hotan wannan fatalwar ta jiya ne na gani. Da gudu nayo waje daga cikin dakin. Fitowata yayi dai-dai da sallamar wata mata. Turus na tsaya ina maida numfashi ina kare mata kallo wani dogon farin hijabi ne dogo a jikin matar gata doguwa. Girman idanunta kadai abun tsorone gata dattijuwa. Cikin tsoro muryata na rawa na amsa sallamar. Sai ji nayi tace "Sunana Indo ni makwabciyar ki ce ga gida na nan gaba da gidan ki. Gani nayi an kawo amarya yau har kwana takwas nace bari na leko mu gaisa". murmushin karfi da yaji nayi cikin karfin hali nace "Bismillah to mu shiga ciki". Gabana ne ya fadi da na tuna cewa na fa kulle gidan nasa kubobi da jamuluck amma ta ina matar nan ta shigo anya kuwa ba fatalwar bace? na tambayi kaina da kaina tambayar da bata da amsa. Sofa na nuna mata nace ta zauna ni kuma na daukko mata juice a cikin kofin glass a tsorace na kawo gabanta na ajiye sananan na koma Can kuryan falon kan archair na zauna domin a matukar tsorace nake da matar nan. "Amarya banga angonba ko ya fita ne". abunda matar nan tace kenan da muryarta marar dadin saurare. "Eh dazun ya fita office". Na bata amsa. "Kina nufin ke kadai aka bari a gida? bakisan akwai fatalwa a gida nan ba". Tuni tsoro biyu suka farmake ni. Ga tsoron matar nan ga kuma ta kara tabbatar min da zargina."Fatalwa kuma Inna Indo? ashe da gaske akwai fatalwa dama sau biyu ina ganinta na fadawa Habib amma yace wai tsorata nayi". "Ba tsorata bane bari kiji na baki labarin gidan nan". Na kara gyara zama hade da mika hankalina gare ta, ta fara da cewa, "gidan nan gida ne mai hatsari nan baya da shekara biyar aka gida shi. kinga ai katanga daya ta raba ku da makabarta ko". Nayi saurin girgiz kai Alamun eh. "To da nan gidan da kike ciki makabarta ne an taba binne wata mata ce a saitin gidan nan. Matar nan kuma itace take fatalwa taki barin a zauna a gidan nan. Fatalwar nan tana da matukar hatsari gata da siffofin tsoro na tabbata mijinki ma bai san cewa haka gidan nan yake". Wani sabon tsoro ne ya sake ziyartar zuciyata lokaci guda, na daga kai ina kare wa gidan kallo. A raina nace ko habib yana so ko baya so wallahi sai ya canza min gida. taya zan zauna a gida Ni da fatalwa?...................

Autan writers ne...

https://www.facebook.com/groups/1232550283531628/







↫ NI DA FATALWA! ↬

{gajeran labari}

Part {2}

@KINGBOY ISAH

note;
Mai tsoro kar ta karanta!...

Maganar matar nan ce ta dawo dani daga tunanin da nake, "Shin kinsan me ya faru da matar da ta fara zama a gidan nan kuwa?". Na kada kai alamun Aa. "Itama amaryace kamar ki tun ranar da aka kawo ta gidan nan fatalwa ta fara firgita ta. Wata rana da daddare mijinta baya nan ya tafi wajen aiki bai dawo ba har dare wajen magariba. Tana zaune a falo ita kadai tana kallon tv kawai sai gani tayi wuyar dakin ta dauke, nan take fanka ta fara wulwulawa da karfi. Yarinyar nan tsoro ya kamata kawai gani tayi TV ta kawo ciki kuwa wata doguwar mata ce mai dogayen faracina domin farcen ta na hannu har kasa yake tabowa gashin kanta kuwa baki ne wulf amma yana da tsayi sai hakora zako-zako abun tsoro". Ina jin haka tuni na makalkale kafafuna kan kujera na kame waje daya kamar ni ce naga fatalwar. "Kina ji nan take sai fatalwar nan ta cikin TV ta kyalkyale da dariya mai firgitarwa yarinyar nan ta kwalla ihu ta yunkura zata tashi amma sai taji kamar an daure ta. Fatalwar nan ta daka mata tsawa tace "Ina zakije? ko ina zaki ba zaki guje mun ba sai kin gaya mun dalilin da yasa kuka shigo mun gida. Yarinyar nan ta fashe da kuka tace "Dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan nan gidan ki ne ba" fatalwar nan ta bushe da dariya kawai yarinyar nan sai gani tayi fatalwar ta zuro hannu daga cikin TV zata kama ta kawai sai ta sulale kasa a sume". A firgice nace "Wayyo Allah na Fatalwar ta kashe ta?". Matar tayi murmushi tace ai ita bata kashe mutum sai dai ta basa wahala domin tana ganin yarinyar nan ta suma sai ta barta. shi kuma mai gidanta wata rana yayo dare karfe goma ya nufo gida sai sauri yake domin shi kanshi tsoron unguwar yake kasancewar dare yayi ga kuma duhun dare. yana cikin tafiya kwatsam sai ganin wani abu yayi fari tass a gaban shi. Da ya lura da kyau sai yaga kamar mutum ne a kwance cikin fararen kaya hakan yasa ya tsaya cik ya fara cewa "Waye a nan? waye ne". amma sai yaji shiru hakan tasa ya dan rabe da nufin yabi ta gefe ya wuce bai sani ba ashe fatalwa ce, Ya kusan wucewa kenan ta mirgina ta rike masa kafa a lokacin ta dago fuskarta abun tsoro da gashi baja baja ta fashe da dariya marar dadin saurare. suna hada ido kuwa ya kwallah ihun neman agaji amma ina ba wanda ya kawo mai dauki domin kowa yasan halin unguwar nan ba a zuwa da dare daga bakin isha'i duk wanda ya fito to ba shakka sai ya hadu da fatalwar nan". Ai tuni jubi ya kwaranyo min. naji tsoro ya dabai baye ni. Nace "To Inna Indo ya kike ganin za'ayi domin nima na ganta wata abun tsoro mai fararen kaya jini na zuba a idonta". Wata irin dariya naji Inna ma'au ta kyalkyale da ita wacce har sai da ta ban tsoro ma. "Kwarai yarinya kin ganta domin nima ina ganinta sosai jarumta nake kawai ina nuna mata rashin tsoro. Yanzu dai mafita daya ce ku tattara ku bar gidan nan in ba haka ba komai zai iya faruwa daku kullum kina cikin tsoro ne da fargaba. Yauwa yar nan ni bari na tashi na shiga gida gobe ma zan zo in dan debe miki
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download NI DA FATALWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album