Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SIHIRTACCEN IKO Complete Hausa Novel Document by SIHIRTACCEN IKO


SIHIRTACCEN IKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9271



SIHIRTACCEN IKO

Reading Time: 0 Hours

Added On: 28, Jun 2024

Author: Khadija Muhammad Shitu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 911 744 0993

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 48.47 kb

File Type: txt

Views: 1551+

Download: 671+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: [6/8, 11:51 AM] ~Siyama.♥️: 
©®2023-K_shitu🦋
Khadija Muhammad Shitu
Arewabooks: Kshitu
Hikaya: Kshitu
Wattpad: Kshitu
K_shitu Multimedia.

*SIHIRTACCEN IKO!*
(Al’ajab).

📕K _ S H I T U

*Page 1&2*

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Mafarin Ƙaddarar ya fara ne tun sanda Kakata ta ɗauki tulun ta fasa! tun daga wannan lokacin ba mu sake samun salamar Rayuwa ba, Shaiɗanu ke bibiyar Rayuwarmu.
Sihirtaccen Iko! Ya zame mana fitina a rayuwarmu, Sheɗanu sun yi nasarar Hallaka Kakata amma har yau babu tabbacin tana raye ko ta mutu, sannan mahaifiyata itama an samu nasarar hallakata ta bar wannan duniyar ke nan har abada.
A hankali na sauke Ajiyar zuciya mai ƙarfi, na mayar da idanuwana kan Ruwan da muke tafiya saman shi daga inda nake ina iya hango yanda ƙananun kifaye ke shawagi hankali kwance.
Na zurfafa sosai cikin duniyar tunani, ina ta saƙe-saƙe da maganganu cikin Raina, Har ban san lokacin da muka ƙaraso Yankinmu ba, mutane har sun fara fita, amma ni na yi shiru, na yi zaune.
Kiran sunana da na ji an yi ne har cikin ƙwaƙwalwata, ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi.
Har lokacin Idanuna a rufe suke ban buɗe su ba, Kamar a mafarki na kuma jin An kira sunan nawa,
"Zoya! Zoya.!!" A ɗan firgice na buɗe idanuwana.
Rungume juna muka yi ni da Ariya cike da murna da kewar juna, Sakina ta yi tana ƙare min kallo tana ƴar dariya "Zoya kina nan dai yanda kike baki ƙara komai ba, sai fari da kika yi amma kina nan ƴar siririya." dariya na yi ina hararta na ce,
"Na dawo ke nan zaki fara samin ido, ko ina Kaka da Anum, har da baba aka zo tarba ta?"
Jan hannuna tayi, tare da faɗin, "Oho! ke fa kin iya tambayoyi, idan kinje kya gani da idonki."
Harar ta na yi, sanna na biyo bayanta muke fice daga cikin jirgin ruwan, Tsaitsaye na gansu alamun ni da Ariya suke jira. Da gudu na nufi Kaka ina murnar ganinta zan rungumeta.
Saurin kaucewa tayi tana dariya, har na kusa faɗuwa Baba ya riƙo ni yana murmushi, "Wato Kaka kaɗai kika gani ko Zoya ni bak..". ban bari ya ƙarasa zancensa ba na rungume shi ina dariya, na ce "Baba yi haƙuri na so na fara zuwa gurinka amma Tsohuwa ta ɗauke min hankali."
Mun daɗe muna gaggaisawa da Ahalina, cikin farin ciki, da walwala, Kafin Baba ya ce mu tafi gida haka nan, Amalanken shanu muka shiga guda biyu, muka kama hanyar gida, Babban gidanmu muka ƙaraso mai kyau wanda kallo ɗaya zaka masa kasan ko a ɗan garin Muna da wadata sosai da Arziƙi.
Tun da na fito na tura gate ɗin gidanmu na shiga nake aikin ƙwalawa Kawu kira, "Kawu, Kawu! ka fito yau na dawo na dinga takura ka, me ma yasa baka zo tarbata ba, Kana ina kawu ka fito mana Zoyarka ta dawo..". haka nayi ta surutu ina ƙwala masa kira, Daga ɗakinsa ya amsa min "Ke Zoya kin dawo ke nana! shi ke nan ba zan sake samun sukuni ba zaki yi ta haddasa min ciwon kai."
Fitowa ya yi daga ɗakin yana kallona, "Barka da dawowa Zoya, yanzu dai ya kamata ki je ki ci abinci da kuma wanka".
Sauran ƴan'uwana dake parlourn suka shiga hidima da ni, tare da tambayata ya na baro yayana, ni kuma ina ta amsa musu da lafiya lau, shi ma yace yana nan tafe.
Agogon Hannuna na kalla tare da, Miƙewa na ce "Ƴan'uwa zan shiga na yi wanka, na ɗan huta, idan na gama zan fito."
Akwatin kayana Ariya ta biyo ni dashi, tana aje min itama ta fice dan ta bani guri na huta.
Mintuna Sha biyar tsakanin shiga ta wanka da fitowa ta, nayi wanka na fito na shirya cikin doguwar riga Blue da mayafinta fari, sannan na jawo Akwatin kayana na janyo na fara fito da su ina jerawa, inda muke ajiye kaya nida da Ariya, Wani littafina ɗauka Na SIHIRTACCEN IKO! na ajiye bisa gadon, sannan na ci gaba da kimtsawa, sai da na gama duk abin da ya dace sannan na hau gadon na janyo littafin na buɗe shafi na farko na fara karantawa.
Abin da na fara gani a farkon shafin ya sanya ni natsuwa sosai da son karantawa, dan fahimtar komai da kyau.
Shafain farko abin da na ga an rubuta Shi ne SIHIRTACCEN IKO! da wani jan rubutu kamar jini, kafin na ci gaba da karantawa na soma ƙarewa bangon littafin kallon ba wani hoto bane a jiki ko adon wani abu, littafin ƙarami ne mai baƙin bango, sai wani jan abu wanda yafi kama da jini a farkon littafin, daga ƙasa wani rubutu ne wanda ban san da wane yare aka yi shi ba, ban kuma iya karantawa ba, bayan ma Rubutun ne dai.
Tunani na fara akan tsohon da ya mallaka min da littafin, Chan kuma na soma magana a bayyane, "Anya shi ɗin ya kasance jinsin mutum kamar ni? ko dai na yi kuskure a bisa karɓar wannan littafin, to me yasa ƙwayar idanunshi fara idanun kuma suka kasance baƙaƙe ƙwayar idon kawai ce fara Anya kuwa ban yi kuskuren yi masa kyautar zinare mai daraja sannan kuma ai tun a ranar da abin ya faru har ya mallaka min littafin ban sake ganinsa a jirgin da muke tafiya. kuma na san babu inda muka tsaya, taya kuma ya san sunan kakata da mahaifiyata? sannan ya ce a duk sanda na buƙaci ganinsa na buɗe littafin akwai hodar Sirrin da zan gano shi da ita mu gana! Anya kuwa zoya ba ki yi wauta ba?"
Ajiyar zuciya na sauke wannan karon tsoro ya fara shigata, amma na daure na janyo littafin na fara karanta bayanin.

SIHIRTACCEN IKO! Abun da aka rubuta shi ne; Sihirtaccen Iko! ya kasance ƙwaya ɗaya tak amma yana da sassa uku na iko, wato mahaɗinsa, Ɓarin ikunan sun kasance ƙwaya uku, duk wanda ya yi nasarar mallakarsu zai samu ƙarfin sihirin da babu mai shi kaf faɗin duniyoyin da muke da su.
Duk Wanda ya yi nasarar Mallakar Sihirtaccen iko! zai iya mulkar duniyoyin manyan matsafa da aheɗanu har abada, zai zama shugaba ga kowa da kuma ko wane jinsi da halittun da ke akwai a duniya!
Ɓarin Sihirtaccen ikona farko, ya kasance Wani Narkakken Ruwan lu'u-lu'u ne, mai cike da sihiri marar misaltuwa wanda zai iya shafe tarihin duniyar mutane. Sannan ya kasance ba ko wane jinsin halittu zai iya taɓa ɗan tulun da yake ciki.
Numfashi na sauke da ƙarfi sannan, na buɗe shafi na gaba.
Cikakken bayani da kuma mamallakin Ɓarin Sihirtaccen Iko har sauri na ke wajen jefa ƙwayar idona kan rubutun da yake ƙasan bayanin, amma abin takaicin wannan rubutun ne da na gani a ƙasan bangon littafin wanda ban san ko da wane yare aka yi amfani wajen rubuta shi.
Takaici ne ya sanya ni buɗe Ma'adanar kayayyakinmu na saka littafin, tare da miƙewa na fice daga ɗakin bakiɗaya.
Ɗakin kaka na nufa dan ina kyautata zaton Ariya na chan.
Kwance na same ta tayi ɗaiɗaya bisa gadon Kaka tana cin Gyaɗa, faɗawa na yi nima bisa gadon ina faɗin, "Ash na gaji Riya!" Dariya ta yi ta ce "Yanzu fa nake son zuwa na tashe ki kin huta da kika kawo kanki."
Hannu na sa na ɗibi gyaɗar na murza sannan na watsa a baki ina taunawa a hanakali, "Wai ina tsohuwa ne?" na tambaye Riya ina sake bajewa bisa gadon.
"bata ma jima da tafiya kasuwa ba, ta ce tana son yin siyayy ne ta miki girki mai daɗi.
Ɗibar gyaɗar na yi na murza da dukkanin hannayena ina faɗin "Zan ci girkin tsohuwa mai daɗi."
Na ƙarasa faɗa ina watsa gyadar a bakina.
Wani irin na ji ɗanɗanon gyad'ar ga kuma kaina da ya sara lokaci guda kuma na soma jin zufa na tsiyayo min daga cikin gashin kaina zuwa gadon bayana.
Ni kuwa bam sani ba, ashe na yi mummunan kuskure na cin wani abu ba tare da na wanke hannayena da ruwa mai tsarki na taɓa littafin Sihirtaccen iko.
Idanuna na ji sun min nauyi ba na jin surutun da Ariya ke min, kawai idanuna suka lumshe, jikina ya sake na soma barci....
**PaidBook 300 Vip500 2329557913 UBA Evidence of Payment via 09117440993.*

(Ina godiya sosai wa masoyana, Littafin kuɗi ne na yi muku sauƙi no complain 300N masu son VIP 500)

09117440993
[6/8, 12:10 PM] ~Siyama.♥️:
*SIHIRTACCEN IKO!*
Arewabook@Kshitu.



*Page 3&4*

Tun da na fara barci ban farka ba saida duhu ya fara sannan Anum ta soma tashi na, da ƙyar na iya buɗe idanuwana na sauke su kanta, "Zoya ki tashi wannan barci haka tun wajajen safe, yanzu fa duhu ya
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SIHIRTACCEN IKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album