Join Our WhatsApp Group

RAYUWAR BAHIJJA Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR BAHIJJA


RAYUWAR BAHIJJA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 59213



RAYUWAR BAHIJJA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 23, Oct 2023

Author: Safiyya Mrs J Moon ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 344.13 kb

File Type: txt

Views: 1146+

Download: 510+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [9:51AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [12:30PM, 7/1/2017] mrs j moon: *RAYUWAR BAHIJJA*
Didecated to mumm Abdul *(bebeelo)*

Dasunar Allah mai rahama maijin qai.

*01*
"Queen queen!! Shine kiran da wanani matashin saurayi keta ta fad'a da qarfi amma wacce yake kira tayi kunnin uwar shegu dashi.
Da sarsarfa ya sha gabanta yana qare mata kallo fuskansa d'auke da murmushi. Taja gyefen hijabinta ta rufe fuskanta tana dariya qasa qasa.

Ya dungure mata kai "kunyar qaryane wannan kikeji queen, kinaji ina ta kwallamiki kira amma kikayi banza dani ko?
"Uhmm yaya bilal kenan, ta yaya xan ansa maka irin wanna uban kiran akan hanya. Tana fad'an haka ta rabe ta wuce da sauri yabita suka jera taja ta tsaya ta kafeshi da idanu shima kallonta yakeyi.
Cikin muryanta mai sanyi tasoma magana "don Allah yaya bilal katafi abinka sabida ba girmanmu bane yin hakan, ko kamanta kaid'in dan gidan sarki ne ni kuma 'yar gidan liman. To inkamanta natuna maka yanzu, yin hakan ba girmanmu bane don haka na had'aka da Allah kabar biyoni kana tareni. Ta juya tana mai gyara ruqon littafan islamiyyarta tayi tafiyarta batare da ta ko waigoba.
Sututi yayi yana vin bayanta da kallo yana ayyna dirinta tare da surarta aransa. Ahankali ya furta"lalai inkin girma za asami shamshaqiyar budurwa, ya cije babansa na qasa tare da sosa sumar kansa wanda ke nannad'e sai kyalli keyi irin na fulanin usul 'yan daji.

Ya juya xuwa majalisarsu ya zauna shiru batare da yacewa kowa qalaba, tunanin maganganun qaramar yarinyar ke mishi yawo a brain sosai take bashi mamaki intana magana cikin natsuwa da hikima, kuma komi tafad'a mai amfani ne yaja ajiyar zuciya tare fa cewa " 'yar baiwa bahijjata. Duk suka xuba mishi ido alokaci daya kuma sukasa dariya hara ya watsa musu yaja tsaki ya bar musu wurin
[1:35PM, 7/1/2017] mrs j moon: Da sallama tashiga gidan, gwagwgo bintu ce ta amsa. Taqarasa kusa da ita tad'an russuna tace "barka da yammaci gwagwgo ya jikin nana? "Barkanmu bahijja, nana tasami sauqi har na aiketa. "Madallah Allah yaqara lafiya "Amin kedai 'yar albarka. Murmushi tayi tare da qarasawa ciki.

Bataga gwogwgo lanti ba don haka ta tube kaynta tasa na aiki ta soma cika randunar da ruwa sanna tasoma haramar d'ora sanwar dare.
Cikin qannanin lokaci ta dai daita wata qatuwar tukunya amurhu sannan tayi sanwar wata madai daiciya da alama ta miyace babbar kuma ta tuwo.
Tana tankad'en gari Nana ta iso cikin fara'a tace "sannu adda bahijja da aiki "yawwa sannu kema, ya qarfin jikin naki? "Nawarke ai.
Ta dubeta ta girgiza kai "anya Nana ba rashin lafiyar qarya kikayiba kuwa? Darita saki tare da matsowa kusa da kunnen bahijja cikin rad'a tace ban iya qarin siran da akayi ba shi yasa nace cikina na ciwo sabida tsoron dukan malam mamunu. Dan qwashin kanta tayi tasaki qara zata gudu ta damqe hannunta tace "don Allah dakamin kubewan can daxan kad'a "angama maa.
"Ina gwagwgo taje? "Taje wurin magani, wai tanaganin adda hindu mayu sun kamata. "Toh fa aina ta had'u dasu? Oho mata, kinsan dai halin gwagwgo da iya habbaka bala'I, komi yasameta tace jifanta akayi ba aciwon Allah d'akinta sai da sanadi don kawai rashin wada taccen imani.
"Uhmm to Allah ya kyauta, yakuma bata lafiya "Amin dai kam.

Tana tuqin tuqin tuwo gwagwgo lanti tadawo tare da hindu.
Tana yimata sannu da dawowa tayi banza da ita tashige d'aki fuuuu Nana ta tabe baki tamiqe tashige lungunsu.

Tsaf tagama aikinta ta nemo gwagwgo bintu ta kwashe mata domin baza ta iyaba kuma tasn kotakira gwagwgo tasan baxa takulataba.

Aguje hindu tafito tayi baki rariya tasoma sheqa amai bahijja ta tai maka mata ta d'auraye bakinta tana tajera mata sannu wanda bata amsa ko d'ayaba.
Ta ratayo jikkanta ta leqa "gwagwgo sai na dawo. Cikin kumfar baki ta amsa"kada Allah yasa kidawo lafiya, shegiya mai baqin hali, mai kama da aljannu kawai bacemin dagani ko intaso in dakaki. Da sauri tafice tana sharan kwallah.
Awaje ta had'u da malam ya cire mai hansin yabata yayin yabama nana ishirin suka russuna kakayi mishi godiya.

Yauma ita da nana suke ta kicikicin d'ora abincin dare duk sunyi zufa sakamakon itacen ruwa ba bugeshi yaqi kamawa kuma gwagwgo bintu batanan, sai hawaye suke na shaqan hayaqi. Hindu na zaune tana kallonsu ko sannu takasa ce musu sai qorafin hayaqi ya isheta qaurins zaisa mata ciwonkai.

Malam ya shigo hayaqi yayi masa maraba tuni yasoma tari ya hango su nana cikinsa suna ta fifitawa ga kuma hindu zaune ta hard'e qafafu.
Cikin zafi yasoma kiran "lanti lanti!!! Tafito d'aki tana gyara d'ankwali alamar barci takeyima.

Wani kallon banza yawatsa ma yace "aikin mikikeyi kikabar yra na aiki cikin wannan hayaqin? Tasoma sosa kai narashin gaskiya ganin takasa kare kanta ya d'ora da cewa to na soke sa su girki irin wannan mai yawa daga yau. Ya juyo yana kallon hindu yace "tashi muje chemist adubamin ke. Ahankali ta miqe tasanyo hijab.

"Kufito waje nace ya umurci su bahijja, suka fito idanu duk yayi ja sai xufa suke sharewa. "Inbanda rahin imnai irin naki lanti mi yara 'yan shekaru 12 xasuyi miki a kitchen? Kai Allah yashiryaki dai.

Sallamar gwagwgo bintu yakatsema malam bambamin fad'ansa.
Ya amsa sallamar yayin da su nana suka rungumeta suna murnan ganinta. Malam yace
"Yaewwa bintu tafi da hindatu chemist ayi mata gwajin bitsari da jini muji mike damunta "to malam. Ku kuma kuzo muyi bitan karatunmu najiya suka amsa da"toh atare.


*BARKA DA SALLAH TO YOU ALL*🙋🏻🙋🏻🙋🏻 Allah SWA ya amsa ibadarmu amin.


*mrs j moon*
[9:51AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [8:55AM, 7/3/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*

©Safiyya

*02*

Ad'akin malam sukayi sallar magriba, sabida gudun fad'an gwagwgo. Amma duk da haka basu tsiraba domin tanajin fitan malam xuwa masallaci taxo qofarshi tayi tayin ruwan bala'I ita kad'ai kamar wata karya. Sai da tagaji dan kanta tayi shiru amma bini bini xatace iskancin banza da wofi.

Sai bayan isha'I su hindu suka dawo. Gwagwgo bintu sallah tayi haramar gabatarwa batare da bata lokaciba.

Kururuwan ihun hindu yaja hankalin al ummar gidan duk suka taru sukayi cirko cirko suna sonjin dalilin ihunta wanda taqi bari alaman dukanta akeyi.

Gyaran muryan malam yasa mutanen suka watse.
Bakin qofar lanti ya ja yatsaya tare da cewa "lanti ba kya da imani ne daxaki tasa yarinya kina bugu alhalin kinfi kowa sanin batada lafiya, ko so kike ki kasheta ne? Tafito duk ta had'a xufa ta hankad'o hindu ta fad'I qasa faf.
Cikin d'aga murya tace "malam gatanan tafada maka uban da yayi mata ciki agarinnan kuma wallahi babu ruwana cikin lamarin domin bansan ta inda ta kwaso wannan abin kunyarba.
Wani kallon tuhuma malam yawatsa mata atake ta sunkuyar da kai narashin gaskiya. "Bintu! "Na'am ta amsa tare da bitowa hannunta riqe da tasbaha tana ja, ta durqusa gefensa tace "gani malam.
Ahankali yace "minene sakanakon gwajin da akayi? Tamiqa mishi takardu guda biyu tare da cewa "ayi haquri bisa lamarin abi komi asannu. Bai amsa takardunba yace "fad'amin abinda ke ciki inji, caraf lanti ta amshe "ai da kaduba dakanka dayafi tunda ita ba...."ke!!!!! Waya sakoki bakin ki ciki da zaki ki tsoma? Malam kenan ya katseta cikin tsawa. Taja da baya tana aunawa bintu harara kamar idonta zaigad'o qasa.
"Ina sauraronki bintu. Ahankali tasoma magana "malam ayi haquri tare da dangana domin wannan abu qaddarace da ga Allah, taja numfashi tacigaba sakamako dai baida dad'in ji domin antabbatar da hindu na d'auke da juna biyu na tsawon watanni uku da sati biyu, kusan watanni hud'u kenan.

Innalillahi wa inna ilaihin raji'un!! Abinda malam yayi tananatawa kenan yana sharce gumi dama yayi xargin hakan zaifaru sabida ganin yawan amai datakeyi ako da yaushe inya tambayi mikedamunta ace malaria da shawara.
Ya sauke dubansa kan hindu da sauri ta ja dabaya tana rawan jiki tasoma cewa"Allah malam sharrin shaid'anne da kuma matsawan gwagwgo akan sai na saida talla tas ko ina zanshiga inje in saida shi, amma don Allah malam kayafemin bazan qaraba wallahi natuba, tafashe da kuka ma tsanani tana cewa "kin cuceni gwagwgo banyi dacen uwaba kaicona.

Malam xuciyarsa kamar wuta yaja dabaya yafice batare dayace komiba.

Lanti da watsama hindu wani lafiyayyen mari wanda saida ta fad'I tasaki qara tace "wallahi kuma sainafad'a gaskiya komi zakimin. Tako soma dukanta baji bagani ta ko ina tana zaginta "shegiya 'yarbanza ina ruwana don nasa miki tallah sai kice nace kibi maza, ita bahijja bata zuwa tallan ne dabatayo gantaliba saike uwar jarabara, to wallahi ahir dinki naqarajin sunnana abakinki tam, ta tureta tashige d'aki tana zage zagen banza tare da ajama gwagwgo bintu Allah ya isa wai ita tayima hindu asiri tabi maza har ta kwaso abin kunya.


*mrs j moon*
[11:49AM, 7/3/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*

©Safiyya

*03*
Gwagwgo bintu bata kulataba taja su bahijja suka shige d'aki wanda duk jikinsu yayi sanyi. Xuwa can hindu tashigo dakin gwagwgo bintu ta duqa agefen qofa ta sunkuyar da kai tasoma magana cikin muryan kuka "don Allah gwagwgo kitai makeni malam yayafemin kada ya koreni, nasan inkinsa baki zai huce.
Asannu bintu tasoma da cewa"hindu baki kyautama rayuwarkiba sam kinbata wayonki kuma kinzubarma da gidanku qima a idon al umma kam, "nasan bayiwa rayuwata adalciba amma ina roqonki da ki taimakeni ki mance rashin kunya dana riqa yimiki abaya wallahi duk gwagwgo ke sani amma yanzu natuba na daina Allah. "To madallah Allah yashige mana gaba, kuma insha Allahu malam zai d'au abin asannu. "To nagode gwagwgo "bakomi tafi kije ki kwanta tamiqe tafice jiri na d'aukanta.

Arba tayi da malam tare da qaninsa aguje ta juya d'akin gwagwgo bintu, arazane ta tareta tana tambayarta "ke da waye kuma? Bata bata amsaba malam ya shigo ya fizgota yayi waje da ita gwagwgo bintu ta biyoshi tana cewa haba malam kabita asannu mana, inrai yanaci hankali ke nemosa, don Allah kada ka doketa. Bai kulataba ya isa wurin inda qanninsa suke tsaye yatura musu ita yace "ku casamin ita har sai tafad'a muku gaskiyan wanda yayi mata ciki. Ciki!!!!!!! Kuma malam? Suka tambayeshi atare, bai amsa musuba ya shige d'akinsa a fusace.

Faruqu sarkin zuciya tuni yasa qafa yyi ball da ita ya xare belt yasoma xuba mata ta ko ina yana cewa yau saidai uwarki ta haifi wata mara tarbiyan amma kedai yau sunarki marigayiya.
Ihu takeyi tana fad'in "natuba baba xan fad'a dogari ilyane kuma gwagwgo ta sani ita tasani in nemo mata kud'I ko ta halin qaqa, afusace gwagwgo lanti tafito tayo kanta tana cewa sharri xakiyimin komi? Faruqu dai dai yadaga belt zai xubawa hindu yaga zuwa lanti aiko ya dage ya lafta mata a mazaunai tasaki qara tayi baya tana sosawa.

Dakyat gwg bintu tayi nasaran tsaida faruqu ya bar dukan hindu ganin xai yi kisan kai.
Ta taima mata ta kaita d'aki ta roqi lanti da kada taqara bugunta don Allah, cikin ruwa bala'I ta amsa "to kanwa uwar gami 'yar baqin ciki munafuka burinki yacika sai kimaza kiqarawa bokanki kud'I tunda aiki yayi kyau 'yata tabi maza, itadai gwg bintu tayi shiru tana kallonta xuwacan tajuya zatafice taji gwg lanti tace "kuma banyafemikiba Allah yasakamin akan 'yarki Nana, insha Allahu ita har qanjamau zata d'auko domin kuwa burina taxama magajiyar karuwai.
Ahankali gwg bintu tadawo daf da gwg lanti cikin matsanancin bacin rai tasoma magana "ba Amin va lanti, baqin baki yayi ta koma miki kanki da yardan Allah kamar yadda yanzu ya koma miki gashinan 'yarki d'auke da abin kunya duk don sakamakon mugun fatanki akan marainiyar Allah Bahijja, kinta kurawa rayuwarta kin hanta saqat kullum burinki mugun abu yasameta, alhalin tana cikin gatanta kika rabota dashi, to ta Allah ba nakiba lanti, baqin bakinki yasami bishiyar tsamiya kuma aniyarki tayi tabinki har yauma tanadi, taqarasa da fad'in axxaluma kawai mai mugun nufi, tafice tabar gwg lanti baki bud'e cike da mamaki wai yau bintu ce ke fad'a mata magana haka bako jin shakkanta, uhm lallai gobe sammakon zuwa gidan 'yar goje yakamani in zana mata abinda ke faruwa domin samo mafita.

Washe gari malam nadawowa masallaci yatara kowa na gidan a dakinsa.
Bayan an gama taruwa yayi sallama tare dayin gyaran murya sannan yasoma da cewa "duk kanmu munsami labarin iftik'in da ya affawa rayuwarmu na samuwar cikin jikin hindatu ta gurbatacciyan hanya, to abisa da haka ni malam yusufu na soke talla agidana akan kowani yaro na gidannan kuma in nasami wani yaqi bin wannan umurnin to za agamu da bacin raina, dafatan anjini suka amsa "eh.
Yacigaba "hindatu kuma zata haife cikin jikinta in Allah yaso sannan bazamu tuhumi dogari ilya akan maganarba sabida ba fyad'e yayi mataba da kanta kaje don haka inta haihu sai abashi d'ansa ko 'yarsa inyana so.
Kowa yayi shiru yana jimani sai sautin kukan hindu ke fita ahankali mai tsuma zuciyan mai saurare.

Tararrafa gaban malam tace "kayimin rai malam ka yafemin natuba kuma ka taimakeni acire cikin don Allah wallhi bana sonsa bazan haifi shegeba wallahi banyafema gwagwgo ita da ilya. Afusace gwg lanti ta fallmata mari bata maida nunfashiba malam ya sauke yatsunsa biyar afusknta saida yayi mata maruka hud'u masu kyau sannan yace "lanti zan tsige igiyata akanki in har baki shiga hankalinkiba, cikin zubar hawaye tafice dakin.

Malam ya dubi hindu yace "baxa axubda cikinba sai kin haifeshi, shine hukuncin daxan miki ta fashe da kuka tana fadin na bani na lalace.


Qauyen kwara kwara qauyene mai tarihi sosai to anan garin malam yusufu ke zaune da iyalansa kuma shine limamim garin gaba daya.

Yana da mata biyu lanti da bintu. Baya da 'ya'ya da yawa su hud'une duka duka lanti uwar gida keda uku bintu nada daya itace nana.Ado d hindu da musa yaran lanti.

Bahijja kuwa 'yar yayan lanti ce tunda babanta yarasu ta taho da ita tuntana 'yar shekara bakwai yanzu takai shekaru biyar ahannunta kuma taqi kaita ganin mamanta ko sau daya sannna sukuma tayi musu surkulle sunkasa zuwa ganinta sam.

Lanti jaraba laqabinta aqauyen.
Kowa yasanta da masifa amma sosai take shakkan mijinta malam domin tasan bai d'aukan iskancinta.


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: [10:50AM, 7/5/2017] mrs j moon😊: *RUYUWAR BAHIJJA*
Deducted to mumm Abbadul *(Bebeelo)*

©Safiyya
*04*
*BUKAR LAMI'DO LGEA PRIMARY AND SECONDRY SCHOOL*
Makarantace daya tilo dake hanyar shigowa garin kwara-kwara, qauyen dake cikin egabi local government ta...


Read / Download RAYUWAR BAHIJJA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album