Join Our WhatsApp Group

ABADAN Complete Hausa Novel Document by ABADAN


ABADAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 176236



ABADAN

Reading Time: 14 Hours

Added On: 07, Oct 2023

Author: Safiyya Abdullahi Huguma ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 970.72 kb

File Type: txt

Views: 1170+

Download: 1040+

Last download: 17 hours ago

Description/Story: Muhammad kabir
Documentation work shop
08160112181

[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺 *DA 'IMAN*🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺 *written by safiyya Abdullahi musa huguma*
💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺
🌺



⏯1⃣



A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al'ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah


sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta


babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi


ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’
‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan
hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki
''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba''
''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa''
cike da masifa hauwa ta qwalalo ido
''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?''



ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto''haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?''
duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu


sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki


bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana'ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu
''hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka''
''kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace 'yarsu?,ai dole su maisheta jari''
''hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za'a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa''


duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu


isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace''haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankali?''
baki ya murguda ya galla mata harara
''eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida''
ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin
''ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi 'yan kallo dake wallahi''


bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin
''kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne''
gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin gidan
''kai kai lafiya?''
''yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi yarranmu?''ya katseta da fadin
''to yanzu me kuma ya faru?''
''wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da kaina''


''kai isyaku me yasa haka''
''baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama''
''ke *maryam* bashi haquri''
babu yadda ta iya haka tace kayi haquri
shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura
hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah


ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji maman tace
''na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne cikin gidan nan''wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin
''mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehaving,yanzu mama kamar isyaku fa qanin bayana mama?''
''ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke bane''
cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa lamuranta ga Allah
''to mama''shine abunda ta fada a sanyaye



*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖 *ABADAN*💖
🌺💖🌺💖🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺


*assalamu alaikum masoya,xaku ga nun canzs sunan littafin mu zuwa ABADAN,haka ya faru ne sakamakon yin wani littafi a baya mai wannan sunan,ina muku fatan alkhairi*



▶2⃣


Hundatu ce tayi sallama ta shigo rumfar sanye da unifoam ruwan tsamigaye riga da zani sai farin hijabinta kafadarta rataye da jakar makaranta fara,tana cire takalminta hade da socks tace
''anty maryam ya na ganki yau a gida da wuri?''
dan dafe kanta tayi kadan tace''yau da wuri na kammala aikin ne shi yasa,kuma dama bana jin dadi sosai''
cikin nuna damuwa ta zauna saman kujera
''sannu antin mu,ko na karbo miki magani?''
murmushi tayi har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
''idan banda abun hindu wanne me chamist za'a samu da uwar ranar nan?''
ta dage gira''haka ne fa anty''
''ki duba locker kusa da gadona akwai paracetamol ki dauko ki sha,tuntuni da kika shigo baki gayamin ba har kika tsaya fada da mutane ko?''


ta karyar da kai ''ayyah maman mu ba haka bane,sallah kinga muka gama yanzun ai''
''dawa antin tayi fada mama?,wannan maras kunyan ne isyaku ko?''
''shine mana''
a fusace ta miqe zata fita maman ta yi kiranta
''ina kuma zaki?''
''mama don Allah ki barni naje naci uwar yaron nan don Allah,yayi matuqar raina yaya maryam,dan iska mara kunya kawai''
''ko da wasa naji kinje gurinsu sai na sabarmiki''
ba haka taso ba amma babu yadda ta iya haka ta wuce daki tana kumbure kumbure ta sauyo unifoam dinta ta dawo dan kitchen dinsu wsnda daki ne gudun tashin hankali suka maida shi kitchen ta zubo musu shinkafa da miya da salad da maman tayi a faranti daya,duka suka sa hannu


hindatu tace''dama zamu samu ruwan sanyi yadda ake zabga ranar nan wlh''
''ai insha Allahu da na dauki albashina,zan siya mana qaramin firji''
cike da doki hindatu tace
''eh wlh yaya''
mama ta dubi maryam din''yanzun maryam ba zaki yiwa kanki fada ba?,bama zancan aure kike ba zancan siyan firji kike ki saka mana,duk yadda mutane ke maganganu tamkar ma ke din baki damu ba maryam?''


duk sai taji abincin ya fice mata a ka,ta sunkuyar da kanta,Allah ne kadai yasan abinda take ji a zuciyarta,itakam tasan ba domin mamanta bata sonta take mata wannan fadan ba,tana yine sabida qauna,ita din ma da za'a tona zuciyarta tabbas babu dadi


🎄🎄🎄🎄🎄🎄

Zaune take cikin rumfar tasu wadda ke da madaidaiciyar yalwa,kujeru ne one sitter two sitter da kuma three sitter masu dan sauqin farashi,falon malale yake da tyles ruwan madara da labulaye suma ruwan madara masu sauqin kudi,sai kayan kallo da suka hada da t.v ta xaune da d.v.d,komai na falon madaidai cine dai dai talaka wanda albashin maryaman ne da qoqarinta ya kai falon ga zama haka


kusan kaf gidan babu muhallin da yakai tsaftar nan,ko yaushe zaka sameshi a goge qal yana qamshin turaren garwashi ko na tsinke,hakan ke qara haddasa qiyayya da kishi mai zafi tsakanin mama *amina* da sauran abokan zamanta


sanye take da pakistan riga da wando wanda rigar tasa ta kai mata har gwiwa,dan kwalin pakistan dinne daure a kanta,duka hankalinta ta tattarashi kacokam kan wayarta da tayi googling din wasu sabbin girke girke,shirun da dakin da ma gidan baki daya da yayi shi ya qara mata nishadi da fahimtar abunda take karantawa,


sallamar da ta jiyo anayi cikin tsakar gidan ita ta ja hankalinta,ta sauke wayar tana amsawa tare da cewa ''a shigo''
mai sallama ta sake maimaitawa lokacin da take shigowa rumfar tasu,da sauri maryam ta sauke wayar a gefanta fuskarta dauke da murmushin farinciki wandayayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta ta miqe
''radiya..saukar yaushe kenan mutanen south africa?''
harara wadda aka kira da radiyan ta cilla mata
''hmmm,babu wani nan,wlh baki da abinda zaki kare kanki da shi,yanzu ma ni ba gunki nazo ba,mama na kawowa jikanta ta ganshi''
''oh ni maryama,laifi baya qaremin,me kuma nayi''ta fada cikin murmushi da dafe kai
harararta dai ta sakeyi''kinfi kowa sanin laifinki maryam,sati na guda da dawowa qasar nan amma ko mai kama da ke ban gani ba,ina dira nigeria kece ta farko da na fara yiwa tex amma ko matsayin reply ban samu ba''


''yanzu dai yo haquri don sonki da annabi ki zauna tukun,don mama bata nan ta tafi kitso''ta fada tana karbe kyakkyawan baby boy din dake sabe a kafadarta,tare suka zauna idon maryam na kan yaron''masha Allah laquwwata illa billah fadil''yana kan kadarta ta shiga kitchen din su ta dauko mata ruwa da lemon sobo cikin fridge din da daqyar ta shawo kan mama da dadin bakin hindatu aka siyoshi suke lemon siyarwa a kuma fita kunyar baqi idan anyi


''bismillah''tace da ita bayan ta tsiyaya mata lemon
''bani dana kawai na wuce''
''haba sister,kada fa ayi mana dariya a ganmu a rana''
''ke kika jawo hakan ai''
''kinsan Allah banga saqonki,ki yarda dani bani da lokaci wallahi yanzu isashshe idan ba weekends ba saboda aiki''
da qyar ta samu ta shawo kan radiya bayan ta mata alqawarin zuwa mata a wannan weekend din wanda daga nan suka fada hirar duniya


radiya ta ajiye glass cup din bayan ta kalli maryam
''maryam har yanzu dai batun aure shiru?''sakin ajiyar zuciya tayi sannan ta tabe baki
''hmmm,barni kawai radiya,samun miji na gari yanzun ya zamo wuya,mazan yanzu duka 'yan garari ne,yawancinsu ba aure ke kawosu gurinki ba''
''anya maryam,bana manta fa yawan samarin da kike da su tun muna school''
''radiya kenan......manta da wannan,na fada miki yawa yawansu ba don Allah suke sonki ba,sun lallabo ne kawai su kwashi abunda suka kwasa na rasa wannan masifa kamar hadin baki?kamar ni kadai sukewa haka,ke dai ki sani kawai a addu'a radiya''ta qarashe maganar muryarta na dan rawa alamun kuka keson zuwa mata
''shikenan maryam,insha Allahu na miki alqawari ba zan fasa sakaki cikin addu'o'ina ba,komai yayi farko yana da qarshe''


a hankali suka fada wasu hirarrakin nasu a haka maman ta cimma su,tunda ta dauke fadil bata dawo da shi ba sai da zasu tafi,sabulai ta bawa radiyar sinqi biyu da turare,hannu biyu amsa tayi mata godiya sannan maryam ta amsheshi ta biyo radiyan qofar gida don raka ta
''ke da nasir fa muka zo''
cikin mamaki take kallin radiyar''amma baki da mutunci,ki bar bawan Allah a mota duka lokacin nan yana zaman jiranki''
fuska ta yatsina''rabu da shi,fada mukayi da shi sulhu yake nema shi yasa''
''Allah ya shiryeki radiya ''abunda ta samu ta iya fada kenan don sun qaraso gaban motar''


gidan gaba ta shige ta dora mata fadil saman cinyarta suna gaisawa da nasir din
''munfa yi fushi maryam gaskiya''
sassanyan murmushinta tayi''to ayi haquri tunda na wanke kaina next week ina tafe insha Allahu ranan sunday''
''to Allah ya nuna mana''
sallama sukayi ta koma cikin gidan radiyan na jaddada mata ta cika alqawari fa




tana cusa kai gidan suka ci karo da *BINTA*
dauke da botikin awara zata fita inda aka fi kaurin,maryam dince ta fara ja da baya don tasan bata qi ta bangajeta ta wuce ba,duk da hakan ma dai bata tsira ba daga tsaki da harar da qanwar bayanta ta saba jifanta da su ba koda zasu hada hanya ne sau miliyan


ta rasa me ra tsarewa yaran da iyayensu,gaba daya anbi an cika zukatansu da qinsu,qannenta ne duka amma babu daya dake ganinta da gashi,saidai duk da haka rashin mutunci wani yafi na wani
ga tsantsar rashin tarbiyya da qin karatu da aka dasawa zucoyoyinsu,ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa suka zabawa kansu,da wannan tunanin ta qarasa falonsu ta zube saman kujera tana rowon Allah daukinsa kan halin da take ciki



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖 *ABADAN*💖
🌺💖🌺💖🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖🌺
...


Read / Download ABADAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album