Join Our WhatsApp Group

UWAR MUGU Complete Hausa Novel Document by UWAR MUGU


UWAR MUGU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 32370



UWAR MUGU

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 175.05 kb

File Type: txt

Views: 592+

Download: 352+

Last download: 31 minutes ago

Description/Story: UWAR MUGU-01

Daga Littattafan Nazir Adam Salih.

*KIBIYAR AJALI*
*ME YAFI KUDI*
*TA LEKO TA KOMA*
*BIRNIN SARAUNIYA*
*MUTUWAR KASKO*
*NAIRA DA KWABO*
*ACI BULUS*
*ALAKAKAI*
*WA NA KAMA*
*HINDU*
*RUHINA*
*DARE DA RANA*
*KARYA LINZAMIN SHAIDAN*
*CUTA TA DAU CUTA*
*ISKA MAI KADA RUWA*
*BINDIGAR KWALI*
*DAMISAR TAKARDA*
*AZIZA*
*TSOHON ALKAWARI*
*KAI DA JINI*
*ALJANI YA TAKA WUTA*
*KUDI DA MACIJI*
*KISAN BOKO*
*KURA DA KAN RAGO*
*MURMUSHIN ALKAWARI*
*ZAYYANA*
*ZABIYA*
*MUGUN JI*

DON ABOKINA
Engr Auwal Sani Kabo.

UWAR MUGU
Copyright © Nazir Adam Salih 2010
Hakkin Mallaka (h) Nazir Adam Salih 2010

TARIHIN DABA'INSA
An fara Buga shi a Kamnas Publishers Dakata
Kano A shekarar 2010

GARGADI
Ba'a yarda wata kungiya ba ko wani mutum ya juya wani bangare na wannan littafin ta hanyar wasan kwaikwayo da majigi ko kuma wani abu daban saida tabbataccen izinin marubucin.

ADIRESHI
Abubakar Saddik Islamiyya Dakata Kano.
Akwatin Gidan Waya 4792.

UWAR MUGU
Nazir Adam Salih
(Nas)

BABI NA DAYA
ALIYA na zukar sigarin dake hannunta saita dafe makogoro cikin kaduwa sannan tafara tari kufur kufur nan da nan jikinta ya dauki rawa. Cikin sauri ta fice daga da'irar yan matan dake gaban makadin takoma can gefe guda sannan tafara nazarin su daya bayan daya tana mai addu'ar Allah yasa dai babu wanda ya lura da ita ballantana ma har ace tayi abin kunya ita dai ta sha fadi cikin zuciyarta cewa wannan abu ba dadinsa take ji ba mutum yayi ta hurawa cikinsa hayaƙi makoshinsa ya shake kamar zaka mutu amma don masifa sai an sha tunda yazama al'adar duk wata karuwa dake gurin abin kunya ne a ganki ma baki iya busa hayaƙi sama ba don haka wannan gudun abin kunyar shiyasa Aliya tafara busa hayaƙi sama amma ba wai don tana so ba.

Aliya ta tofar da yawu sannan tayi jifa da guntuwar tabar dake hannunta gamida ajiyar zuciya daga inda take tsaye tana iya hangen samari da yan mata dakuma dattijai masu budurwar zuciya sunata cashewa agaban DAN INDO wani dattijo dan duniya sanye da katon wando buje da dogon gemu kamar saman jinka ga tarin gashin baki kamar ciyawa yana tsakiya da mataji a hannunsa ana kida yana rawa lokaci guda kuma yana taje gemunsa da matajin yan duniya na ta watsi da Nairori a kansa kai ka rantse da Allah babu sauran talauci acikin kasa.

Mafi yawan daga cikin matan sanye suke da kaya iri daya sunyi Asin-da-Asin musamman don wannan ajo na FATI ZAFI ZAFI yan tsirarin karuwai masu rangwamen gata da wadanda ta karewa sune kawai suka fita zakka a cikinsu harda Aliya duk kuwa da cewa tafi duk wata karuwa dake gurin kyawun sura nesa ba kusa ba amma halayyar na tayi-da-fasawa ita ta ja mata shiga halin bakin talauci a halin yanzu talaucin daya hana mata ankon ajon kawarsu fati zafi-zafi.

Aliya ta dubi agogon kan fuskar wayar dake hannunta karfe biyu saura na dare. Adaidai lokacin ne dan indo yafara hada kayansa da komotsansa yan duniya suka fara kama gabansu suna shiga cikin garin TAFA domin cigaba da cin kasuwar dare.

Wannan shagali anyi shine cikin wani katon fili na wasan kwallo kafa dake bayan garin Tafa. Tun farko ita fati zafi zafi wadda ta shirya bikin ajon domin tara masu gidan rana bahaka taso ba taso ne ace acikin farfajiyar wata kayatacciyar otal aka yi bikin to amma sa'ar data lalubi aljihunta taji babu tudu saita ga batada zabi illa ta tara mutane a cikin katon filin a cashe akalla dai tayi imani ko mai zaije yadawo sai ta sami RIBA.

Daga filin kwallon kafan idan ka dubi bangaren kudu babu komai sai tarin bishiyoyi da kuma ciyayi gamida wani tsohon gidan mai wanda ya jima a rufe ba'a sayar da komai acikinsa sai beraye ne ke ta gada aciki.

Adab da inda wannan gidan mai a tsugunne yayi tagumi sanye d kaya dukun dukun kamar anyi barin mota dashi wani saurayi ne ya zurawa dandalin bikin idanu yana kallon jifa jifan mata da maza nan da can ana ta hira ana karawa sararin samaniya hazo.

Wannan saurayi yafi sa'o'i shida zaune agurin yayi zuru kamar mujiya yana kallon duk shagalin dake faruwa agurin dayawa daga cikin yan duniyar dake kai kawo a filin sun dauke shi ne amatsayin tababbe.

Tsakanin inda saurayin dake tsugunne zuwa inda Aliya take tsaye baifi taku goma ba.
Aliya ta dubi saurayin dake tsugunne agurin kana ta dauke kai cikin tausayi a zuciyar ta tana cewa.
Mutane dai basuda kirki gashi dai kyakkyawa da kuruciyarsa amma sai da aka samu wani marar imani ya haukata shi Aliya tayiwa kanta murmushi adaidai lokacin da wasu kawayen ta suka nufo inda take ta sake duban saurayin ta dauke kai.
Yanzu haka shaye shaye ne tace da kanta adaidai lokacin da su LARABA suka karaso inda take.

Laraba na karasowa saita dubi Aliya a yatsine
Kedai wallahi kinji kunya Shikenan don kawai bakiyi dinkin anko ba sai ki wani koma gefe kamar wata marainiya?

Aliya ta Harare ta.
Ke banza bakya ganin gurin ya cushe da kyar ake numfashi shiyasa na koma gefe na sha iska.

ASABE ta fashe da dariya shegiya Aliya akwai ki da iya kwana kamar mota to meye in baki yi anko ba akanki aka fara?

Aliya ta tafa hannu tace oh Ni Aliya na shiga uku to wai ina ruwan ku ne? Zan fa ci uban yarinya Wallahi ta dube su a fusace.

Laraba ta fashe da dariya Haba ƙawata ke baki san wasa bane?

Toh Ai ku ne da abin haushi Aliya tace sannan ta sake duban agogon dake wayarta

Laraba ta turo dankwalin ta gaban goshi sannan ta lalubi aljihu jakarta ta dauko karan taba ta cinna masa wuta ta busa hayakin sama kana ta dubi Aliya tace.

Kai gaskiya zafi zafi ta sami kudi yau anya kuwa ni ma ba ajon nan zan shirya ba.?

Kin rigani afili na riga ki a zuciya kinga yanda shegen nan alhaji DAN ABU yayi ta lika mata yan dubu dubu? Yafa taba nemana amma saboda yanzu yaga sabuwar fuska sabon jini ko kallo ban ishe shi ba. Asabe tace tana zazzare idanu.
Laraba ta Busa hayaƙi sama tabi shi da kallo.

Kedai abar tone tone kawai Amma in wannan ne Nima yataba nemana kuma har......UWAR MUGU-02

Kedai abar tone tone kawai Amma in wannan ne Nima yataba nemana kuma har... Tayi shiru bata karasa ba sa'ar data ji motsi abayansu cikin sauri ta juya sannan ta rike numfashi Sa'ar data ga saurayin nan dukun dukun tsugunne abayansu.
Laraba ta dube shi a wulakance ta tabe baki tace

Oh Ni Laraba nashige su!
Wannan kuma wanene kamar an tono shi daga kabari?
Asabe da Aliya suka juya lokaci guda suka dubi saurayin

Asabe ta tabe baki... Wayasan masa uban naci tun magariba yake nan yana rarraba idanu kamar dillalin kaji dube shi dukun-dukun wannan in ba asararriya ba wacce karuwa ce zata kula shi? Ta tsartar da yawu.

Laraba ta dube ta tace kika sani ko.... Tayi shiru sannan lokaci guda ta juya a tsorace sa'ar data ji ana ja mata riga ta baya.

Mutumin nan ne a tsaye a bayanta.

Yan matan..... Don Allah acikin ku wata ta taimaka min mana da dan abinci da gurin kwana kafin safiya.

Kawar Laraba ta Harare shi ta daka masa tsawa tace Kai! Kada ka dauki karuwa yar iska mana bayan tanada sana'a. An fada ma a caca aka ciyo mu da zamu dauke ka haka dukun dukun mu kai ka har daki ina abin yake wai maye yaci jariri. Ta zare masa idanu malam don Allah kama gabanka wannan ai sai ka sa a raina mu.
Ta juya sannan takama hannun Laraba tace zo mu tafi kawata kada wannan yasa jinina ya hau.
Suka juya suka fara tafiya sannan ne Laraba ta sake juyowa ta dubi Aliya cikin mamakin ganin ta tsaya bata biyo su ba.

Aliya.... Zo mu tafi mana
Aliya ta girgiza kai kuje Ina zuwa ni sai anjima zan karaso.

To Wallahi kidai bi ahankali kada wannan dan dukununun ya sure ki ta fashe da dariya sannan ta rataya hannunta a kafadar Laraba suka bace acikin duhun daren.

Aliya tayi ajiyar zuciya bayan sun bar gurin sannan ta sake nazarin katon filin da aka gana cashewa babu kowa a filin duk jama'ar sun watse sai yan daidaiku acikin duhun tareda Masoyan su suna kuskus.

Aliya ta juya ahankali ta dubi saurayin dake bayanta adaidai lokacin da wani mai tsohon mashin yazo wucewa ta kusa dasu. Aliya tayi nazarin fuskar saurayin na yan dakiku acikin hasken fitilar mashin din daya gifta taji gabanta yafadi ras meke damuna ne? Ta tambayi kanta tabbas Kodai tasan saurayin awani waje kokuma tasan wani mai kama dashi.

Aliya ta sake nazarin saurayin akaro na biyu sannan ne to ta fahimci abunda yasa gabanta faduwa da'ace bata riga taga gawarsa ba kafin a binne shi da babu Abunda zai hanata cewa saurayin dake tsaye yayanta ne AMADU ba duk dayake akwai duhun dare sai da kamar ta bayyana karara kamar su daya sak Haba gaskiya fa Naji gabana ya fadi ta sake fadi cikin zuciyarta. Acikin dan takin lokacin da taga fuskarsa cikin hasken fitilar mashin din daya gifta ta lura yana cikin tashin hankali domin taso ta ga wani abu mai kama da hawaye ko kuma busashshen jini a gefen fuskar sa wannan shiyasa har ta juya zata bi bayansu Laraba saita tsaya ta sake juyowa ta dubi saurayin kana ta matsa kusa dashi kadan a tsorace.

Sannu... Malam....
Saurayin yayi mata murmushin yake yauwa Sannun ki dai ya dan yi shiru sannan saiya dubeta yace bakya tsoron zan iya cutar dake kika tsaya dani ke kadai?

******* ******** ******** ******** ***********

Tsawon lokaci Aliya na tsaye tana dubansa a tsorace cikinta ya duri ruwa a zuciyarta tana cewa yau na gamu da gamona karambani na ya janyo min da nasani dana bi su Laraba sannan sai ta Dake zuciyarta ta dube shi cikin duhun daren tace don ne zanji tsoro kana mutum ba dodo ba?

Saurayin ya saki wata shakakkiyar dariya irinta wanda ya sha wahala yace. An gaishe ki mace mai kamar maza... Na dauka ai zakiji tsorona kokuma ki raina ni kamar yadda yan uwanki sukayi min ya dan yi shiru yana dubanta.

Kasan kowa da irin tunaninsa nasu tunanin kenan ta gyara tsayuwa tana dubansa hakane.

Ya sake yin murmushi yana kallon ta sannan sai yayi kasa kasa da murya yace idan zaki iya zan so ki taimaka min da dan abinci... In kuma da hali harda makwanci kafin gari ya waye nayi gaba don wallahi ina cikin matsala kanwata.. Kinsan in ba dole ba babu abunda zaisa na nemi irin wannan taimako.
Ya shafi fuskarsa da tafin hannunsa na dama yaci gaba da kallon ta yana jiran yaji abunda zata ce.

Aliya ta shiga rudani abinda yace ya jefa zuciyarta cikin wasi wasi tariga tasani ba karamin ganganci bane ta dauki mutum irin wannan dukun dukun dashi takai shi dakinta cikin wannan uban daren duk da dai cewa tasha saukar mutane iri daban daban abaya to amma su sunada kyawun gani ba kamar wannan ba dake gabanta amma duk da haka lokacin da ta sake dubansa sai taga bazata iya juya masa baya ba domin kamar ta isa sak kamar MARIGAYI AMADU.

In kuma kina ganin da takura to ki bari kawai KANWATA.... Bana son matsalata ta shafe ki... Nagode da tsayawar ma da kikayi har kika saurare ni yayi mata murmushin yake.

Wannan shiyasa Aliya ta dube shi sannan ta girgiza kai tace BAKOMAI YAYANA ZAN TAIMAKA MAKA...... AMMA FA.....UWAR MUGU-03

Wannan shiyasa Aliya ta dube shi sannan ta girgiza kai tace BAKOMAI YAYANA ZAN TAIMAKA MAKA...... AMMA FA abincin dake dakina ayanzu sai ahankali kuma shi kansa dakin nawa ma ba wani haduwa yayi ba don haka in kana ganin zaka iya maneji to zo mu tafi.

Saurayin ya dubeta da murmushi yace in banda abinki kanwata maroki ai ba shi da zabi nagode sosai.

Aliya ta dubi kayan dake jikinsa cikin damuwa ta ce to Shikenan mu tafi.
Saurayin ya kura da irin kallon da takeyi wa kayansa don haka saiya dube ta yace kayana ko? Ni kaina abunda nake tunani kenan domin nasan muna shiga cikin gari zan iya zama abin kallo ya danyi shiru ina ganin ko gaba zakiyi sai na bi ki abaya basai mun jera ba ko?

Aliya ta juya ahankali tayi nazarin jerin gidajen dake fuskantar katon filin da suke ciki sannan tayi ajiyar zuciya ta juyo ta dubi saurayin.
Ina ganin ma ai ba matsala nuna iya tafiya tare ashe na an dauke wuta tana gama fadin haka saita juya tafara tafiya.

Saurayin yayi jim na yan dakiku sannan saiya bi ta abaya cikin sauri na mamaki Idan akayi la'akari da irin yanayin dayake ciki koda ya karasa kusa da ita sai ya dube ta yace kafin mu karasa inaso na roke ki wata alfarma ta karshe.

Aliya ta dan tsaya kana ta dube shi cikin mamaki.
Alfarmar me?

Idan zai yiwu bana son wani ko wata ya shigo yau sameni cikin dakin ki.

Aliya ta dube shi cikin kaduwa
Kana nufin ko da ƙawata bazan bari ta shigo dakin ba?

Saurayin ya gyada kai eh gaskiya haka nake nufi indai zai yiyu.

Ganin tayi shiru a tsorace saiya ci gaba da cewa cikin sauri kiyi hakuri nazo miki da tsarabobi amma ina son ki sani cewa ina cikin matsaloli ne masu yawan gaske wadanda bazan so mutane su gane fuskata ba ayanzu... Kiyi hakuri kinji kanwata sannu ahankali zaki fahimci abunda nake nufi.
Aliya ta dube shi dogon kallo na yan dakiku sannan sai taci gaba da tafiya
To ni dai nayi niyyar taimakon ka bansan ko kai wanene ba bansan daga ina kake ba bansan abinda ke tafe dakai ba koma dai kai wanene ni nayi niyyar taimaka ma duk abunda kayi niyya saidai ka yi min.

Taci gaba da tafiya.
Kanwata saurayin ya kira ta a tausashe.
Aliya ta juyo ahankali ta fuskance shi.
Bazan cutar dake ba kinji.
Aliya ta yi masa dogon kallo kana tayi ajiyar zuciya.
Akwai wani abu a muryarsa dayasa ta amince da abinda yafada mata alokacin tabbas muryarsa ma tana sauti kusan daya da na marigayi Amadu.

***** ***** ****** ****** ******* ****** *******

In ka dauke wani dan siririn farin haske na fitilar kwai yar Cana da yayi wa kansa hanya ta karfin da yaji ta tsakankanin labule da rufaffiyar wata Munafukar kofar daki duk farfajiyar gidan cikin duhu take hakan ya farantawa Aliya rai wacce Daman tun da suka shigo gidan duk da dai dare yayi Aliya tasan wata sa'ar Abokanan kwanan ta basa dawowa sai Asuba to amma tasan wata sa'ar a farfajiyar gidan suke shimfida idan babu wuta sai su kunna fitilar kwai su sa karta agaba suyi ta caca watarana har sai gari ya waye don haka ayanzu da suka shigo taga farfajiyar gidan cikin duhu sai tayi ajiyar zuciya.
Cikin sauri ta lalubi saman asabarin dake kofar dakin ta dauko dan makullin sannan ta juya akaro na farko tun sa'ar da suka shigo gidan tayi masa murmushin yake.
Munyi sa'a ba kowa sai wancan dakin ta nuna kofar dakin nan da hasken yake ratsowa ta kofar sa da baki.

Saurayin yayi nazarin farfajiyar gidan dakuna uku ne agidan har na Aliya farfajiyar gidan ba wani abin Kuzo ku gani bace domin kuwa sau uku yana tuntube...


Read / Download UWAR MUGU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album