Join Our WhatsApp Group

SIHIRTACCE Complete Hausa Novel Document by SIHIRTACCE


SIHIRTACCE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 26350SIHIRTACCE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Bala Anas Babin Lata ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 138.18 kb

File Type: txt

Views: 1005+

Download: 552+

Last download: 2 days ago

Description/Story: SIHIRTACCE-01

1895

BABI NA DAYA 1

Duk da basasa (Bashasa) ta kare Yusufawa sun rinjayi Tukurawa tuni ma har sarauta ta bar gidan Bello ta koma gidan Abdullahi amma tsugunne bata kare ba an sayar da kare an sayo biri. fitinu sai dada kunno kai suke yi daga gabas Rabeh ya cinye barno da yaki har ya soma shigowa Kasar Hausa.

Masauratar Kano na fuskantar yake yake daga kasashe irin su Damagaran da hadeja da Ningi haka nan ga rashin fahimtar juna dake tsakanin sarki alu da masarautar daular usmaniyya saboda basasa wannan al'amari dai ya faru tsakanin 1893 zuwa 1903 shekarar miladiyya wadda tazo daidai da shekarar Hijira 1314 zuwa 1324 wannan al'amari na yawan yake-yake yasa harkar cinikin bayi ta fadi.

Alokacin da Iro yaje gida ya ishe abokinsa JABIRU diyan sarkin baka ya same shi ne a zaune kamar babu lakka a jikinsa
Iro yayi masa sallama yayinda ya shiga harabar gidan.
Jabiru ya cira kai ya dubi Iro yayinda yayi masa sallamar.

Kaka na ganka tamkar mara lafiya Jabiru?
Iro ya tambaye shi yayinda ya isa gare shi.
Jabiru ya Mike tsaye yayi tari Iro lafiya lau me ka gani?

Naga ka zauna shiru ina fatan dai lafiya.? Kai da nake zaton tuni ka shirya tafiya kawai zamuyi.

Ai na shirya jakina kawai zan azawa kaya.
To don Allah ina waje ina jiranka.

Iro yafita waje inda ya baro jakin sa ya jira Jabiru lokacin da Jabiru ya koro nasa jakin yafito ya tarar iro na daure nasa kayan ya dubi iro ko kasan kuwa dazu tunanin wata yarinya nakeyi lokacin da ka shigo ka sameni.

Iro ya waiwaya daga aikin da yake yi ya dubi Jabiru. Ho dan nema ban sanka da irin wannan dabi'ar ba.

Kasan ni ma namiji ne komai dadewa dole ne hakan ta faru gareni.

Iro yace wacce yarinya ce wannan? Kaka sunanta?
Nan fa daya bansan sunanta ba anan kasuwar DAUSAYI nake ganinta.

To Allah ya saukaka.
Tunda nazo duniya bantaba gamuwa da 'ya macen data tsaya min Arai irinta ba iro? Ko barci fa bana iyawa saboda tsananin tunanin ta.
Iro yaci gaba da gyarawa jaki kaya yace to kai sai abkin zancen kaga budurwa kana so ance da kai wacece kaka sunanta kaki fadi shin me kake tsoro ne? Yarinya agarin nan ko da lu'ulu'u akayi ta bamaje muyi mata magana ba.

Jabiru ya girgiza kai ai a inda gizo ke sakar kenan ko alama ban san sunanta ba hasalima ganin da nayi mata duka duka baifi gani biyu ba.
Iro yayi dariya kai ma dai Jabiru agaishe ka in banda sakarci har sau biyu kana ganinta amma baka tanka ba? To ka bari in munje kasuwa yau daka ganta kayi min magana ai kace tana zuwa kasuwa ko?
Kwarai kuwa a kasuwar ma na ganta
To ka sha kurumin ka yau in munje kasuwar Nima zan nuna maka budurwata da nake son na aura Bafilatana ce.

Abokina ashe kace zamuyi sharo kenan
Iro yagama gyara kayan jakin kwarai kuwa indai akan masoyiya ta ne babu abinda bazan yi ba kai ko wuta akace na shiga kafin abani ita a shirye nake balle wata karamar alhaki tsabga.
Suka kada sukayi kasuwa suna tafe suna hira.

Kaka cinikin awakin nan naku kuwa na jiya an ce kun daidaita? Inji iro
Jabiru ya gyada kai kwarai kuwa ya biya keso biyar kudi hannu kuma la'ada waje.

Iro da Jabiru abokai ne wadanda sun shaku ainun kodayake dai suna yin sana'o'i ne mabanbanta da juna iro masaki ne hasalima gidansu saka ba haye bace gado ce Jabiru kuwa gidansu mafarauta ne tun daga kan kakansa na uku sarautar baka ta shigo gidansu saboda haka sunyi fice a fagen bayar da magungunan gargajiya matuka gaya ga jarumta da suka shahara da ita musamman a fagen yaki.

Sun gamu ne sun zama Abokai tun sunada shekaru sha hudu a makaranta acan Kasar Barno Allah cikin ikon sa sai ya jefa kaunar juna a zukatan su kusan zumuncin dake tsakanin yaran ya shahara a gidajen duk yan uwansu basa komai batareda shawarar juna ba.

Tare suke tafiya kasuwa duk ranar kasuwa tare suke shirya komai in sun tashi yi wannan ya samo asali ne tun suna makaranta a inda suka yi shekara da shekaru suna tare a gabas.
Lokacin Da suka isa kasuwar hantsi yayi tuni kasuwar dausayi ta soma cika da baki kowa na ta zuwa da kayan sa wasu a jakai wasu a takarkarai wasu kasuwar dausayi nasu kaya a rakunma sun ka azo.

Kasuwa ce wadda Allah ya albarkanta da yawan jama'a gami da yawan kaya.
Suka ratsa ta layin yan koli ya zuwa rumfarsu iro a inda ya sauke kayansa suka gaisa da makwabta sannan suka kada suka nufi rumfar Jabiru.
Da suka sauke kayan sai Jabiru Yakama jakinsa ya kai shi turke ya daure yakawo karmami da ruwa ya girke masa kana suka nufi wajen Fulanin nan suke don su sayo kindirmo.

Jabiru ne yafara hangota wannan karon ma kamar ganin dayayi mata abaya koma fiyeda zuciyarsa ta harba kunan bege da shaukin kauna ya motsa masa ya kura mata ido cikin daukewar numfashi.
Tana tareda wasu yan mata Fulani kawayen ta suma saukar su Kenan a kasuwar

Shi kuwa gogan iro hankalinsa na can wani waje bai lura ba har Jabiru ya bude baki zaiyi wa iro magana saiya ga ta kallo inda suke ta kura masa ido sannan yaga bakinta ya bude izuwa murmushin dayake jefa zuciyarsa abisa tafarkin bege.

Sannan ne abin mamakin yafaru Jabiru yaga kawai tayiwa sauran kawayen nata magana suma duka sun waiwayo sun kallo inda su Jabiru suke.
Kunya ya kama Jabiru Meyasa ta nuna shi ga kawayen ta? Ko kallon ta dayake yi ne.? Gaskiya baisan dalili ba tunda yazo duniya bai taba ganin yarinyar da ganinta ke karya masa zuciya ba kamar ta zaiji yana begen ta aransa alokacin da bai dora ido akanta ba har yaji yana zumudin ya sake ganinta aduk lokacin da bata kusa amma da zangar ya ganta saiyaji duk ta karya masa garkuwar zuciyarsa ganinta yakan dimautar dashi har yaji ya kasa magana in kuwa har ya yi yunkurin yin magana harshensa yakan sarke.

Ahalin yanzu harshensa ya sarke don kuwa ya kasa yiwa iro maganar alokacin daya dubi iro din sai ya ga shi wata mata dake sayarda fura ma yake yiwa magana..

Jabiru ya waiwaya ya sake duban inda yarinyar take yaji cikinsa ya kada numfashinsa ya dauke dayaga ta baro sauran kawayen nata ta nufo inda suke GABA GA-ƊISIHIRTACCE-02

Yaji cikinsa ya kada numfashinsa ya dauke dayaga ta baro sauran kawayen nata ta nufo inda suke GABA-GAƊI.

Ya sunkuyar da kai cikin jin kunya shin me ya taho da ita? Ko kallon dayake yi mata ne ya harzukata?

Wankar tarwada ce doguwa ba can ba siririya amma ba can ba tana da yalwar gashi mai siraran kitson Fulani ga idanu manya hanci har baka yan kananan laɓɓan kamar an keta da askar wanzamai in tana tafiya kamar reshen bishiyar da iska ta yiwa yawa ta daura wani zane sakakke a ƙirji.

Can dai sai ya dan cira kai don yaga halin da ake ciki watau ko ta iso babu shakka ta iso amna ina!
Ko alama ba wajensa ta taho ba ahalin yanzu tana tsaye ne agaban Iro suna magana me ke faruwa ne?
Allah shi tsare Allah yasa abunda ke zuciyata ba shine ke shirin tabbata ba Jabiru ya raya a ransa me ya kai ta wajen iro? Ko ta san shi ne ?
Amma kamar amsa ga hakan saiyaga iro ya waiwayo gare shi yana murmushi Jabiru zo ku gaisa da JARU itace masoyiyar tawa danake gaya maka.

Alokacin da Jabiru ya nufi wajensa ba'a cikin hayyacinsa yake ba saboda dimauta abinda kawai ya tuna shine yaji suna gaisawa da jaru yarinyar dayake masifar so a birnin zuciyarsa wadda ahalin yanzu ya tabbata tayi masa nisa ina shi ina son yarinyar da abokinsa ke so.?

Nan take Jabiru yaji jikinsa ya mutu kamar zazzabi zai lillibe shi ya soma nadamar zuwansa kasuwa yau. Duk tausayin kansa ya kama shi da ya tuna yadda rayuwarsa zata kasance batareda wannan yarinyar ba.

FARKON GANINSA DA ITA yafara ganinta tareda wasu yan mata kawayenta ne wadanda ya lura duk ta girmesu yayi al'ajabin yadda akayi duk Tsantsar kyau irin na jaru ta girma ta gandame batayi aure ba. Yasan dai amsar bazata taba zama cewa ta rasa ma'auri bane.
Aranar farko daya fara ganinta a kasuwa sun kawo kindirmo tareda sauran yan matan Fulani Jabiru bai iya jurewa ba aranar saida ya bisu a sace har zuwa rugarsu amma duk da haka ya kasa yi mata magana.
Wannan kwauron baki da yawa yake gashi iro ya riga shi yi mata magana.
To amma Meyasa iro bai taba yi masa maganar ta ba duk da mutunci da shakuwar dake tsakanin su?
Wannan tambaya ce da amsar ta batada wani amfani ga Jabiru ahalin yanzu.

A dalilin haka bayan Jabiru sun gaisa da jaru sai yace iro bari nakoma rumfa na zauna ji nake kamar zazzabi zai rufe ni.
IRO yace asssha Allah ya sauwaka Nima gani nan ba jimawa zanyi ba.
Komawar Jabiru rumfa bada jimawa ba saiga iro ya biyo shi ya same shi yana cikin tunani.

Jabiru kaka jikin dai?
Ya dubi iro. Da sauki ai ba zazzabin ne ya rufe ni ba tukunna dama dai alamun sa ne nakeji har jarun ta tafi?
Iro ya gyada kai Eh na sallame ta. Iro ya samu waje ya zauna akusa dai Jabiru kaka kaga wannan yarinyar Jabiru?

Agaskiya kayi dacen yarinya saidai nayi mamakin yadda akayi ka samu yarinya kyakkyawa irin wannan amma baka taba shaida min ba.
Iro ya gyara zama Haba Jabiru yaushe kake da lokacin hirar yan mata baka taba yi min zancen wata budurwa ba sai yau shiyasa ban Faye son na Dame ka da hirar su ba.
Jabiru yayi nazari saiyaga babu shakka hakane.

Bayan haka kuma iro yaci gaba halayyar jaru na daure min kai ta yadda har na kan karaya aduk lokacin dana gamu da ita na farko dai taki yarda nakai mata ziyara rigarsu nayi juyin duniyar nan ta gaya min dalili amma taki na biyu nayi mata maganar aure haryanzu taki yarda tabani amsa da zarar na tambayeta kuwa shin ko da gaske tana sona ko kuwa dai tana yaudara tane sai ta kan yi fushi tace bata taba zaton abinda nafada zai fito daga bakina ba kaji dalilin dayasa nake shakkar son da takeyi min.

Jabiru ya gyada kai ni kaina nayi tunanin haka iro agaskiya ruwa baya tsami banza nayi mamakin ganin yarinyar ta girma sosai amma haryanzu ba'a yi mata aure ba Allah yasa ba aljanu suka aureta ba.

Amin inji iro.

To amma iro me zai hana wata rana ka samu lokaci ka kai mata ziyarar ba zata inaganin in har kaje ka same ta acan rugar tasu zata iya yi maka bayani gamsashshe ga abubuwan da kake bukata kasani gameda da ita.
Iro yayi tunani zuwa wani dan lokaci sannan ya gyada kai kaga fa Jabiru maganar nan taka akwai Makama gareta saidai bansani ba ko zaka rakani.

Jabiru ya bushe da dariya Haba iro gwamma kayi tafiyar ka kai kadai kaga ni ba gwanin tadi da yan mata bane saidai kawai na taya ka da fatan alheri.

Iro yace wai ni ba haka ba ma shin ko ka ga yarinyar da kake min zance dazu kuwa? Ina nufin wadda kace kana so.?
Ya girgiza kai Banganta Ba me yiwuwa ma ba zan kuma ganinta ba.

Kada ka yanke kauna Jabiru indai har ka ganta kayi min magana sai muje wajen ta.

Babu damuwa indai na ganta zan maka magana sannan ya sauya Darasin bamu sayi kindirmo ba fa kada mai kyau ya kare.

Iro yace jaru ta taho min dashi mai kyau tace in anjima zata kawo min ta ce na wuri biyar ne na bata kudin amma taki karɓa.

Jabiru yayi murmushi. Allah yabar wannan soyayya taku....

BABI NA BIYU 2

Kwana Biyu Da cin kasuwar Dausayi iro ya kasa jurewa. shawarar da Jabiru yabashi tayi ta bijiro masa Arai har takai ya kasa daurewa
Babu shakka ya dace ya kaiwa jaru ziyara a rigarsu tun dawowar su daga kasuwa aranar yayi ta fama da tunane tunanen batun zuwa wajen jaru....

SAIDAI KASH....SIHIRTACCE-03

Tun dawowar sa daga kasuwa aranar yayi ta fama da tunane tunane kan batun zuwa wajen jaru.

A Rana ta uku ne ya shirya ya sayi kayan tsaraba yabar gida yatafi kauyen tun safe ya dauki hanya bai isa ba saida rana ta take bai sha wuya ba wajen neman rugar su jaru wadda aka fi sani da RUGAR BELLO.

Lokacin Da ya isa rugar Bello sai ya tarar da garkar shanun babu ko tururuwa baiyi mamaki ba don yasan lokacin suna wajen kiwo ya samu wasu yara yan mata su uku suna wasa awajen saboda haka saiya tambaye su Yan mata don Allah jaru nake nema.
Sukayi farat suka waiwaya suna kallonsa cikin mamaki malam jaru bata fitowa wajen samari.

Ya cika da mamaki Meyasa?

Suka dubi juna sannan daya daga cikinsu tace
TACE TA DAINA KULA SAMARI...

Iro yayi murmushi je to kice da ita IRO ne yazo daga birni zata fito.
Yan matan suka sake duban juna daga karshe daya daga cikinsu ta tafi bayan wani dan lokaci saiga su nan sun taho tare.

Jaru na gaba yarinyar na biye da ita.
IRO... Inji jaru me ya kawo ka rugar mu? Ya lura duk a tsorace take.

Menene ya tayar miki da hankali haka jaru?
Yanzu zuwan nawa bai faranta miki rai ba?

Ta kura masa ido haryanzu cikin fargaba... Zuwan ka nan kasada ce iro ban kai darajar da zaka sadaukar da ranka akaina ba.

IRO ya kasa fahimtar abinda take nufi Haba jaru wannan wacce irin magana ce kinsan ina sonki matsayin ki ya fice duk yadda kike zato azuciyata.

Tayi ajiyar zuciya cikin tunani da shakka sannan ta waiwaya ta dubi yan matan nan wadanda ke tsaye suna sauraron abunda suke cewa suna hada ido da jaru sai duk suka juya sum-sum Suka bar wajen bayan sun bace sai ta sake duban iro.. Amma daka dauki shawara da baka zo ba.

Kinga jaru ni fa nagaji da irin wannan halin naki da wane dalili zaki rika azabtar dani kina yawo da hankalina kin rigaya kinsan cewa ina son ki in har bakya sona ne me zaisa ki rika rufa min tsorona kikeji ko kuwa me ?

Ta sunkuyar dakai kasa batace uffan ba.

Ya matsa kusa da ita kigaya min gaskiya ko kinada wani tsayayye ne wanda yasha gabana?
Ta girgiza kai har yanzu bata cira kai ba ballantana ta dube shi.
Ko sona ne bakya yi kike rufe min?
Ta sake girgiza kai.
To Meyasa na taso nazo har wajen ki amma banga alamar walwala a fuskar ki ba?
Ta cira kai ta dube shi saboda inasonka.
Suka dubi juna zuwa wani dan lokaci
Saboda kina sona ne babu walwala a fuskar ki?
Shikenan jaru nagode. ya mika mata kullin daya taho dashi ga wannan ke na kawo wa.
Ta dubi kayan menene wannan?
TSARABA ce.
Ta mika hannu ta karɓa nagode Allah shi saka da alkhairi.
Amin Shikenan zan koma.

Ta dube shi haka da wuri?
Kin damu da zuwana ne? Bai tsaya ba bai waiwayo...


Read / Download SIHIRTACCE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album