Join Our WhatsApp Group

KISAN BOKO Complete Hausa Novel Document by KISAN BOKO


KISAN BOKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 32650



KISAN BOKO

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Unknown

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 178.15 kb

File Type: txt

Views: 483+

Download: 181+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: KISAN BOKO-01

Nazir Adam Salih (Nas)

TABA KA LASHE

Wani tela ya auri wata Masifaffiyar mata mai fadan tsiya kamar karya. Ance basu fi shekara da aure ba amma fadansu yakai sau saba'in da doriya

Don me zakice na auri aminiyar ki?
Sanin kanki ne duk duniya babu wacce nake kauna kamar ki shin bazaki aureni bane? Saurayin telan ya tambayi Uwargijiyarsa.

Zan aure ka mana. Amma kana da wani aibu.
Aibun da babu mai wanke ma shi har sai ka auri babbar aminiyata NADIYA. Kafin ni nasamu kwanciyar hankalin da zan aure ka daga baya...............

NAZIR ADAM SALIH (Nas)

DAGA NAZIR ADAM SALIH
KIBIYAR AJALI✅
ME YAFI KUDI✅
TA LEKO TA KOMA✅
BIRNIN SARAUNIYA✅
NAIRA DA KWABO❌
ACI BULUS✅
MUTUWAR KASKO✅
ALAKAKAI✅
WA NA KAMA?❌
HINDU✅
RUHINA❌
DARE DA RANA✅
KARYA LINZAMIN SHAIDAN✅
CUTA TA DAU CUTA✅
ISKA MAI KADA RUWA❌
BINDIGAR KWALI✅
DAMISAR TAKARDA❌
AZIZA⭕
TSOHON ALKAWARI✅
KAI DA JINI❌
ALJANI YA TAKA WUTA✅
SAI MUTUWA❌
KUDI DA MACIJI✅
KISAN BOKO✔️
MURMUSHIN ALKAWARI ✅
KURA DA KAN RAGO.✅

DON
Abokina Muttaka (Baggio) Gwammaja.
Da
Abdullahi Musa Madda
Da
Assadik Muhammad
Wanda ya taimaka wajen gyara littafin.

KISAN BOKO
Nazir Adam Salih (Nas)

Copyright © nazir Adam salih (Nas) 2006
Hakkin mallaka (h) Nazir Adam Salih NAS 2006

TARIHIN DABA'INSA
An fara buga shi a kamfani KAMNAS PUBISHERS DAKATA A SHEKARAR 2006 (1427)

GARGADI
Ba'a yarda wata kungiya ba ko wani mutum ya juya wani bangare na wannan littafin ta hanyar wasan kwaikwayo da majigi ko kuma wani abu daban saida tabbataccen izinin marubucin hakanan duk wani abu dayayi kama da halin wani mutum acikin labarin nan don Allah gafarce ni akasi ne kawai aka samu domin labarin kagagge ne NAGODE.

ADIRESHI
Abubakar Saddik islamiyya dakata Kano
Akwatin waya 4792.

KISAN BOKO
Nazir Adam Salih
(NAS) 2006

BABI NA DAYA 1
Awata kasa awata jiha awata unguwa awani katon gida acikin wani faffadan dakin shakatawa dake kallon lambu wata mata ce zaune tayi tagumi haka nan ta zurawa katuwar akwatin gilashin idanu wacce ke dauke da dan karamin teku da wasu yan kananan kifaye kirar nasara sunata wasa abinsu kai kace masu rai ne ba robobin wofi ba azahiri idan ka dubi matar saika rantse da Allah dan karamin tekun bogin dake gabanta take kallo amma a badini bashi take kallo ba hakanan ba kawar ta dake zaune kusa da ita take kallo ba zuciyarta na can cikin duhu tana ta lalube.
Laluben abinda take zargin kanta da cewa Meyasa bata lalube shi ba tunda sauran haske?

Kai NADIYA meyayi zafi haka kikayi jugum kamar anyi miki mutuwa? Irin wannan tunani haka tunda kuruciyar ki kawar ta ce ke magana.

Nadiya ta mike tsaye akwai alamun damuwa karara a fuskarta ta nufi wani dan karamin firji dake dab da tekun Tangaran din ta bude shi kana ta dauko wani dan karamin kofin Tangaran da wani abu aciki ruwa ruwa ta dan kurba ta runtse idanu kadan kamar mai hadiyar magani saita ta mayar da kofin cikin firjin ta rufe lokaci guda kuma ta nufi gindin katuwar tagar gilashin dake kallon lambun alfarmar dake bayan gidan tafara girgiza kai cikin takaici.

Haba AMIRA wacce irin kuruciya kuma ga matar datayi shekaru talatin da uku aduniya?
Amira ta dubeta cikin mamaki tace
Kina nufin kenan kice dani ke tsohuwa ce?

Nadiya ta girgiza kai.
Bahaka Nake nufi ba Amira abinda nake son ki fahimta shine a irin shekarun da muke ciki ayanzu mun fi karfin a kira mu da yan mata masu kuruciya saidai ko iyayen mata shekara talatin da uku fa Amira! Ayanzu haka halin da ake ciki ya'yan sa'annin mu sun isa aure amma mu gamu nan.... Tayi shiru bata karasa ba.

Kodayake gara ma ke Amira kin yi sa'a kin sami miji bara nayi miki murna wallahi da auren da kikayi Amira ta tura baki gaba tace.
Eh to yafi babu amma meye wani abin murna ga auren tsoho?

Kinyi sa'a ma ke da kika auri tsohon Amira ta harari Nadiya sannan saita fashe da dariya.

Bana son iskanci nadiya meye abin sa'ar a auren tsoho? Sanin kanki ne da inada tarin dukiya da kayan alatun duniya kamar ki babu abinda zaisa na auri tsoho Nima wallahi kudi na bi ta danyi shiru alamun damuwa suka dan bayyana a fuskarta.

Ai ke Nadiya da sauki ma damuwar ki kadan ce dubi fa yanda kike gidanku akwai kudi kema da kudi yan uwanki da kudi mahaifiyar ki da kudi mahaifin ki Allah ya jikan sa shima cikin kudi ya mutu to yanzu in banda abin ki Nadiya me kika nema rasa da har zaki bi ki uzurruwa kanki abanza?

MIJI shine abunda na nema na rasa amira wannan shine kawai ya rage min MIJI ba. Shekara talatin da uku aduniya babu miji.
Amira ta girgiza kai lokaci guda kuma ta bude jakarta ta dauko wani dan karamin mudubi mai shan zuciya tafara kallon fuskarta a jiki.
LALLAI shekaru sun fara ja tace cikin zuciyarta sa'ar da ta kalli fuskarta taga ta dan fara tauyewa cikin sauri ta ajiye Mudubin cikin damuwa ta dubi Nadiya tace.
ME KUDI BASHIDA HAUSHIN KOWA.

Nadiya idan kikaga dama kina iya auren kowane irin mutum ne tunda dai kinada kudi ko dan dole basai kin takura shi yayi auren jari dake ba Wallahi Nadiya idan nice ke ina iya auran yaro dan shekara ashirin. Amira tayi shiru tana duban fuskar Nadiya. Lokaci guda kuma tana kokarin taga ko abunda tace yayi tasiri.

Can sai Nadiya tayi ajiyar zuciya sannan saita baro jikin tagar ta matso kuwa da inda amira take zaune ta zauna ahannun kujerar tace da ita a tausashe.

Gaskiya ne duk abunda kika fada amira tabbas in har ina son auren jari zan iya yi dan ayanzu haka ma a asibitin danake aiki akwai wani saurayi daya nace min amma na rigaya na san karya yakeyi bani yake so ba kudina yake kauna.

To Meyasa ke bazaki aure shi ba yaro ne ko tsoho? Amira ta tambaya. Nadiya ta dubeta wani irin tsoho kuma saurayi ne Wallahi na ma girme shi domin nasan yayi da yawa shekara talatin.

Indai hakane ashe da gangan kike ta uzzurawa kanki da tunane tunanen banza ba sai ki aure shi ba kawai tunda saurayi ne ko mummuna ne?

Nadiya ta girgiza kai tace.
Kyakkyawa ne amira kyakkyawan gaske wanda hakan shiyasa bana son hada wata alaka dashi domin na tabbata da bashi da labarin arzikina babu abinda kyakkyawa kamar sa zaiyi da babbar mace kamar ni......KISAN BOKO-02

Nadiya ta girgiza kai tace.
Kyakkyawa ne amira kyakkyawan gaske wanda hakan shiyasa bana son hada wata alaka dashi domin na tabbata da bashi da labarin arzikina babu abinda kyakkyawa kamar sa zaiyi da babbar mace kamar ni.

Haba Amira dubeni fa da kyau yadda na lalace kyawuna duk ya gushe jikina ya saki wallahi akwai sa'ar danake jin kunyar kallon Mudubi domin tun hoda tana rufa min asiri har itama ta gaji ta bari.

Nadiya tayi shiru idanun ta sukayi Rau Rau suka cicciko da kwalla kamar zatayi kuka.
SO nake na sami wanda yake kaunata tsakaninsa da Allah Badon kudina ba..... Zuciyarta ta karye muryarta tafara rawa.
Kuma zan so ace saurayi ne.... Ba.... Tsoho ba amira.... Wallahi kullum na tuna da auren babban mutum sai inji duk duniyar tayi min zafi domin tun ina karama sosai budurwa yar shekara sha bakwai nake mafarkin auren saurayi domin jin dadin aure yafi tabbata idan budurwa ta auri matashi dan uwanta sai gashi Rudin zamani yasa na makara.

Nadiya tafara zubar da hawaye sannan taci gaba da cewa lokacin ina sakandire Amira... Inada wani saurayi TIJJANI babu yadda baiyi ba akan ya aure ni naki bakiga wulakancin danayi masa ba saboda naga ya mace akaina nace dashi ni bazanyi aure ba sai na gama karatuna na likita.
bazan taba mantawa ba amira da daddare ne acikin lambun can da kike hange daga nan. Kinga fararen kujerun can guda biyu anan ya durkusa gabana yana rokona harda kwalla yana neman na hakura muyi aure yayi min alkawarin cewa idan na aure shi zai kyale ni na cigaba da karatuna amma fau fau fau naki... Nadiya ta fashe da kuka.

Haba Nadiya me yayi zafi haka harda su kuka wannan idan da maza zasuji mu ai ba karamin abin kunya bane shi aure ai nufi ne na Allah idan yaso saiki ga kin sami saurayin da kike so wanda ke kaunar ki tsakaninsa da Allah ya aure ki.

Nadiya ta share hawaye ta girgiza kai tace.
Anya kuwa amira yanzu kina ganin yadda nake din nan kuwa akwai wani saurayi da zai iya kaunata tsakani da Allah.? Ban ki ta taki ba dai idan akace zai so ni don abun hannuna amma haka kawai ya so ni ni kadai.....
Kai abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa amira ta bude baki kamar zatayi magana sai kuma ta fasa domin bata san abunda zata ce wa kawar Tata ba tarigaya tasan cewa duk Abunda Nadiya tafadi gaskiya ne domin ita kanta abun na da sauki da babu abunda zai sa ta auri tsohon nan.

Kawayen biyu sukayi shiru na yan dakiku kawunan su a sunkuye sannan sai Nadiya tace
Ni Daman tun muna jami'a amira jikina yafara bani cewa zamu sha wahala kafin mu samu irin mazan da muke so suke son mu. Amira ta dubeta cikin mamaki..
Meyasa kikace haka.?sabdoa wata magana danaji wasu samari suna fada a shekarar mu ta karshe a jami'aKISAN BOKO-03

Meyasa kikace haka.? sabdoa wata magana danaji wasu samari suna fada a shekarar mu ta karshe a jami'a

Me suke cewa? Amira ta sake tambayar nadiya akaro na biyu idanunta akan fuskar nadiya.

Abinda suke cewa shine wai mun yi musu tsufa su yanzu sun fi son suyi kawance da yan mata yan aji daya sabbin dauka.

Wannan zancen banza ne Amira tace da kawar tata a fusace.
Mata nawa ne a lokacin namu da suka sami mazan aure a acikin mazan ajinsu? Ai ba zasu kirgu ba nadiya.

Amma kuma zancen gaskiya amira idan kika lura zakiga duk kusan matan da suka sami maza Awannan lokacin sunfi mu kurciya nesa ba kusa ba domin sun shiga jami'a ne tun suna da kananan shekaru kuma karatun su bashida tsayi kamar namu ki tuna fa aikin likita na karanta kusan shekaru shida zuwa bakwai kai sun kai takwas ma harda yajin aiki amira tayi shiru na tsawon lokaci bayan da nadiya ta gama dogon bayanin ta sannan saita Mike tsaye domin wannan dogon bayani na kawar tata duk ya gama gundurar ta.

To Allah ya kyauta tace sa'ar data mike tsaye sannan saita dada da cewa
Wato yanzu dai a takaice kina son kice dani ke kin yanke kauna da samun miji saurayi kenan?

Nadiya ta dago kai ta dubi amira sannan saita saki wani bushashshan murmushin yake akaro na farko tun sa'ar da suka fara hirar takaicin.

Amira kenan wallahi idan kina wani zancen sainaji kamar ba dake mukayi zaman jami'a ba ke abunda baki gane ba shine wannan yan banzan samarin masu tsabar iya sa riga da wando da muke burin aura sunyi bala'in raina mu kullum hankalin su yana kan kananan yan mata shin bakiji ba har wani sunan shegantaka suke kiran mu dashi ba?

Suna kuma kamar yaya wane suna ne wannan? Nadiya ta dubi amira sannan saita rufe idanunta ta fashe da dariya.
Nima wallahi amira kunyar fadar sunan nake yi.

Ke kinga bana son iskanci dan Allah fada min kinji nadiya.... Dan Allah fada min wane suna suke kiran mu dashi? Nadiya ta dubi amira sannan tayi kasa-kasa da murya tace wai KISAN BOKO suke cewa irin mu amira ta rike baki cikin kaduwa.
KISAN BOKO? Mune kisan bokon? Nadiya ta mike tsaye ta matsa kusa da amira haka suke kiran mu amira saidai hakuri wallahi basuda kirki....

Basuda mutunci zakice amira tace a fusace yan iska suma ai kisan bokon ne.

Kwarai kuwa nadiya tace sannan ta dubi amira ta dada da cewa.
Yanzu daga nan ina zakije gida zaki koma kokuma shagon dinkin naki zaki koma? Amira ta girgiza kai sannan ta dubi agogo.

Kinsan nafi zuwa da rana lokacin da suke tsakiyar aiki amma yanzu gida zan koma kina ganin har shida ta kusa amira tabi kan tattausan kilishin dake dakin ta nufi kofa kafafun ta kamar zasu nutse aciki saboda taushi.
Kamata yayi ma ace muje ki ga shagon dinkin nawa nadiya. Amira taci gaba da cewa nadiya ta bita abaya tana kada dan makullin mota a hannu.

Muje to na mayar dake gida idan zamu wuce ta bakin kasuwar basai ki nuna min inda shagon yake ba ko ba'a bakin kasuwa yake ba? Amira ta harari nadiya tace.
Bangane in zamu wuce na nuna miki shi ba kina nufin ganin nesa zakiyi wa shagon nawa?
Amira ta girgiza kai tace.
Bazata yiwu ba nadiya nifa Daman neman taimako ne yakawo ni gurinki ta danyi shiru.

Ki shirya tunda gobe Lahadi bazaki je aiki ba sai mu tafi da rana ki ga yadda tsarin shagon yake domin agaskiya nadiya.... So nake ki karamin jari kinga yanzu kekunan dinki bakwai ne aciki so nake na kara guda uku su zama goma kenan gaba daya sai na sake karo madinka kuma inda hali ma inason nafara sayar da shaddodi da atamfofi a shagon amira ta sake yin shiru sannan saita tausasa murya tace.
Bafa dole bane nadiya kiyi min kawai abunda zaki iya... Mijin nawa ne baya banbaruwa tauri ne kamar naman kai nadiya ta fashe da dariya sannan sai kuma ta zubawa tsohuwar kawar tata idanu lokaci guda kuma irin taimakon da kawar tata tayi mata a zamanin zaman su na jami'a ya fado mata tabbas ya kamata ta agaza mata.

Haba amira don dan wannan ma kin tsaya kina ta wani dogon bayani ai da tun zuwan ki ma kin fada da sai mu wuce banki na baki duk abinda kike bukata ta dan yi shiru tana duban agogo
Kinga yanzu har shida tayi abunda zamuyi shine idan kinje gida yau saiki yi lissafin duk abinda kike bukata idan nazo gobe sai mu je shagon Naki na gani sannan na baki cakin in yaso ranar (Monday) saiki karɓa nan da nan fuskar amira ta washe.

GODIYA Nake nadiyata bansan abunda zanyi aduniya ba idan babu ke nagode nagode Allah ya saka da alheri.

Bakomai amira menene amfanin zaman taren idan ba'a amfani juna ba? Muje na kaiki gida.
Kawayen biyu taka ahankali suka fice daga dakin suna hira cikin raha sannu ahankali suka tattaka takan wata yar karamar matattakala ta farin dutse wacce gefen ta ke dauke da jerin sahun shuke shuke ma'abota fure mai kamshi suka nufi inda filin ajiye motoci na gidan yake daga inda suke tafe suna iya hango wasu dirka dirkan jiminoni suna zagayawa a farfajiyar gidan zakalan-zakalan abinsu suna mika dogon wuya.

Nashiga Uku amira tace sa'ar da taga daya daga cikin jiminonin ta nufo inda suke Nadiya ta fashe da dariya.

Ke ba abinda zatayi miki ina ruwan ki da ita jiminonina ne wannan me zuwan sunanta ZANKALA waccan kuma dake jikin bishiyar can sunanta SANTALA amira ta rike baki cikin mamaki lokaci guda kuma ta rike kafadar nadiya a tsorace.

Oh su nadiya manyan gari in banda rigima irin taki ina ke ina irin wannan zankala zankalan halittu dubi fa wuyan ta idan ta mike shi kamar zai taba sama.

Nadiya ta fashe da dariya ta mari kafadar amira tace shegiya har yau...


Read / Download KISAN BOKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album