Join Our WhatsApp Group

HINDU Complete Hausa Novel Document by HINDU


HINDU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21220



HINDU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 118.08 kb

File Type: txt

Views: 613+

Download: 221+

Last download: 8 minutes ago

Description/Story: HINDU - 01
.
Hindu. Nakara kiran sunanta. Shiru bata amsa ba sai amsa kuwwar muryata acikin duhun daren.
Na lalubi makunnar lantarkin na kunna dakin ya gauraye da haske babu alamar HINDU.
Na fara waige waige gumi yafara diga akan fuskata. Hatta dan lullubin da aka kawota dashi na AMARCI babu shi babu alamarsa.
Hindu idan wasa kikeyi min don Allah kifito fili ya isa haka..... Shiru bata amsa ba!
NAS
.
LITTATTAFAN NAZRI ADAM SALIH.
1- Kibiyar Ajali
2- Me Ya Fi Kudi?
3- Ta Leko Ta Koma
4- Birnin Sarauniya
5- Naira Da Kobo
6- Aci Bulus
7- Wa Na Kama ?
8- Iska Mai Kada Ruwa
9- Alakakai
10- Cuta Da Dau Cuta
11- Kudi Da Maciji
12- Kai Da Jini
13- Bindigar Kwali
14- Karya Linzamin Shaidan
15- Dare Da Rana
16- HINDU
17- Damisar Takarda
18- Mutuwar Kasko
19- Sai Mutuwa
20- Aziza.
.
SHIMFIDA
Na Ragewa Tsohuwar Motar Hajiya Ba Duwawu Giya adaidai lokacin dana fara hangen dandasheshen gidan mai kama da aikin budar ido. Na dan dada mika wuyana domin kaiwa daidai da inda madubin dake makale a saman motar yake. Nayi nazarin fuskata akaro na bakwai tun bayan sa'ar dana baro gida.
Abunda nagani ajikin madubin na daga surar fuskata bai dadamin wani kwarin gwiwa ba to akalla dai nasan koda tanada kananan kannai dai bazan tsorata ba.
Amma duk da haka dai fuskar tawa babu yabo babu fallasa kafin nabaro gida saida na shafe sama da awa guda da rabi inata wanka kamar agwagwa haka nan na shafe sama da mintuna talatin da biyar ina zaben suturar da yakamata nasa duk saboda wannan muhimmiyar tafiya. To amma har yanzun nan dana fara hango gidan zuciyata bata gamsu da shirin danayi ba.
.
Na rage gudu adaidai lokacin dana fara gabato kofar ina kusantarsa bugun zuciyata na karuwa. Na sake kallon fuskata ajikin madubin akaro na tara abinda nagani shiya dada sa wani sassanyan gumi barko min domin duk fuskata a tsorace take gashi ta hada gumi sharkaf sai naso nake yoi kamar kaskson tuyar awara,
Bi ahankali dan saurayi. Nace da kaina duk kabi ka rufe menene ne na tsorata da fargaba? Ba itace da kai duk lokacin dakayi niyya kazo ba? To gaka ai kazo din ko banza dai ai baka fadi ba dan samari tunda dai kyakkyawa ce fara sol tana sheki kamar tsada, tauraruwa acikin taurari masu haskakawa....
Wannan tunani shiya dan karfafa min gwiwa don haka saina na dafe sitiyarin tsohuwar hajiya ba duwawun da hannun hagu sannan na lalubi aljihuna na dauko kyalle na share gumin dake fuskata sannan na dada duban kaina jikin madubin akaro na goma. Nayiwa kaina murmushi.
Ko kaifa dan samari ai da kunya ace kaje gaban dalibar ka duk a rude a firgice kamar zomo a burma, bana son ko yin kwakkwaran motsi da jikina domin gani nakeyi kamar karin gugata zai dukunkune...
Gashi dai sa-ar dana baro gida yunwa nakeji cikina sai kugi yakeyi kamar goge amma sa-ar dana kai abincin baki sainaji dandanon sam-sam babu dadi kamar ina dandana ruwan allura.
Ahaka na taho cikina najin yunwa amma tunaninta da zumudin samun cikakkiyar kadaicewa da ita a karo na farko ya gusar min da yunwar.
Tun kafin na karasa tafkekiyar kofar shiga gidan na fara kokarin take burkin motar domin bayaji sosai. Dakyar da taimakon Allah dana wani gwabjejen dutse na samu motar ta tsaya kadan ya rage in karawa kofar.
Shiru na dan lokaci babu wanda yako da leko ballantana yayi kokarin bude min kofar. Na kosa da jira dan haka saina fara danna hon din motar nan da nan ya fara bada wani irin sauti tsut-tsut kamar ana matse balin balam-balam mai iska.
Mintuna biyu suka shude ba'azo an bude min kofar ba. Nan da nan sainaji zuciyata ta dada sake karaya tsoro da fargabar danakeyi tun ahanya suka fara dawowa.
Ka cika karanbani wata zuciya tace dani daman in banda abinka ina kai ina yargidan H. MAHDI.
na share gumin dake kwarara tun daga kan fuskata har gefen wuyana awannan laron ban ko damu danasa kyalle ba da tafin hannuna nayi amfani. Adaidai lokacin danake kokarin sake danna hon din motar ne wani dan motsi daga bakin kofar yaja hankalina dan haka sai nabar hannuna akan hon din motar batareda na danna ba.
Wata farar mage ce mai bakar jela ta fara lekowa sannan sai wani dan durkurkushin kare mai yawan jan gashi ya biyota abaya yana lasar baki. Ahaka suka tsaya bakin kofar suka kura min idanu banyi mamai ba domin babu mamaki tunda Allah ya kawosu gidan basu taba ganin mota Hajiya ba duwawu ta zuciyar gidan ba.
.
Suna nan tsaye muna kallon kallo sai naji wani motsin ba'a dade ba sai wani busasshen maigadi mai busassun idanu yafito sanye da shudiyar riga da tsangalelen wando kafi shanu wuya. Dan siriri ne mai dogon wuya da siririyar fuska dogon hancin daya tankwara kamar baka akan godon hancinsa shiya sa shi kama da AKU.
Ciki zaka shiga ne? Ya tambaya da wata malalaciyar murya gamida daga girar idanunsa dugujejiya mai kama da tsutsar dole dole. Na dube shi sa'ar daya karaso daf da tagar motar sainaji haushi ya kashe ni saboda irin kallon biyu ahun dana gani karara a fuskarsa.
Ko Ba ciki zaka shiga ba?
Ya sake tambayata akaro na biyu cikin daga murya.
Nasan bahaka yake tambayar duk mai motar da yazo shiga gidan ba amma dana dubi mota ta.........HINDU - 02
.
Ko ba ciki zaka shiga ba?
Ya sake tambayata akaro na biyu cikin daga murya. Nasan ba haka yake tambayar duk wanda yazo shiga cikin gidan da mota ba to amma sa'ar dana dubi mota ta sai naga ko kusa ko alama bashida laifi.
Ko malam bayaji ne? Yasake cewa
inajinka.... Ina jinka bawan Allah... Mamaki ne yakamani shiyasa kaga nayi shiru hakan da nace shi yasa shi dubana cikin mamaki.
Mamakin me? Ya tambayeni
mamakin ganin cewa haryanzu masu gadi basuyi wayewar da zasu bambance wanda yazo kallon kofa ba dakuma wanda ke son shiga gida.
Maigadin ya dubeni fuska a yatsine na dan lokaci daga karshe dai me yiwuwa zuciyarsa ta amince cewa ba tabuwa nayi ba sai yace
shiga dai kenan kake son yi?
Kwarai kuwa kasan dai ai kallon kofa bazai kawoni nan ba koda kuwa kofar zinare ce ballantana ta karfe.
Ka iya bakinka dan samari alhaji bazai so kalaman ka na karshe ba. Maigadi yace lokaci guda kuma yafara kokarin bude kofar saida ya kusan minti biyu yana jan kofar dakyar kamar me jan mushen rakumi. Sannan ya samu ya budeta.
Nasawa motar giya sannan na harba zuwa cikin farfajiyar gidan aguje batareda na sake dubansa ba. Koda na wuce kofar sai na juyo domin ganin halin dana bar maigadin to saidai kuma farin hayakin dake fita daga motar ya rufe bayana ruf kamar hazo lokacin hunturun sanyi.
Akwai tafiya mai yar tazara daga kofar gidan zuwa ainihin inda gine ginen alfarmar yake haka nan tun daga kofar gidan har zuwa cikinsa ko ina shuke shuken furanni ne da bishiyoyin dabino sunyi sahu sahu sunata rangaji acikin iskar yammacin.
Filin da aka tanada dan ajiye motoci acan arewa da gine ginen gidan yake. Tun daga nesa na hango motoci biyar aciki suna ta sheki acikin dan abinda ya rage na daga hasken yammacin.
Nasami can gefe guda na kara tsohuwar motata. Sannan na dubi agogona karfe biyar da mintina biyu. Na bude kofar mota ahankali na fito sannan saina fara waige waige ina tunanin abinda ya kamata nayi ga mamakina sainaji kafafuna suna rawa gidan yayi tsit bakajin motsin komai sai na kukan tsuntsaye dakuma sautin almakasan hadiman gidan dake can cikin shuke shuken sunata yiwa fulawowin da suka cika tsayi kwas kwas.
Nayi tsaye ina ta nazarin farfajiyar gidan da gine ginensa. Hakika gidan ya keru daidai da yadda kowane gida keru in har aka kashe masa milliyoyin kudi na nufi bangaren gine ginen alfarmar kafata na rawa ba ita kadai ma ba hatta hantar cikina kadawa takeyi. Bayan dan lokaci nakai ga fuskata ga ginin abu na farko daya fara daukar hankalina shine kofar gilashin dake fuskantata wacce sainabi ta kan wata mattakala ta sarrafaffen dutse zaka kai ga kofar. Adaidai lokacin da gumi keta wanke min gadon baya ina muzurai.... Sai idona yakai ga abinda yasa zuciyata harbawa. Amakale agefen kofar gilashin daga hagu magannin kararrawar sallama ne.
Daman tun sa'ar dana kawo ga kofar ginin zuciyata keta dawurwuri tana neman abinda zan farayi. Shin kwankwasawa zanyi? Ai kuwa abu ne mai wuya aji sautin kwankwasawar awannan gida mai kamar gari. Ko kuwa na kwada sallama?
To wa zaijika? Wata zuciya tace dani. Dan haka ganin kararrawar ayanzu shiya bani mafita?
Na lallaba jikina na bari kamar sabon barawo na mika hannuna na latsa kararrawar ina matsawa kamar daman alabe yake abayan gilashin yana kallona sai kofar ta bude. Wani tankwareren tsoho mai dogon gemu fari ya dubeni gamida daga min girar idanu alamar tambaya.
Malam lafiya? Ya tambayeni
*** ** **
Tsahon lokaci muna tsaye muna nazarin juna nida shi.
Tsohon dogo ne wankan tarwada tsufa ya sashi tankwarewa daga tsakiya kamar baka. Sanye yake da doguwar riga da wando farare abinda zai hanaka kuskurensa amatsayin masinjan ma'aikatar ilmi shine rashin jar dara.
Sabanin hakan hular dake kansa habar kadace shudiya.
Atsammanina zaiyi kimanin shekaru kusan tamanin aduniya abinda yafi bani mamaki shine duk tsufansa anutse yake tsaf babu alamar rudewa atattare dashi.
Akauye sune irin tsofaffin da zaka tarar kullum kwanan duniya zaune a karkashin bishiyar chediya ko maina suna tufka igiyar kaba a birni kuwa sune irin tsofaffin da zaka tarar akullum kwanan duniya zaune agindin ganuwa kokuma akofar masallaci suna jan charbi tun asuba har zuwa talatainin dare.
Lafiya kalau baba. Nace dashi cikin girmamawa azuciyata nayi mamakin ko wanene shi duk da yake dai idan ka dube shi da kyau zakaga zama cikin arzikin ya taimaka wajen tsaftace shi to amma da zarar ya dubi farin gemunsa zuwa ga tsukeken bakinsa gamida kananan idanuwansa dake jiyawa wuri wuri kamar na barawon akuya zakasan tabbas duniya bata kyautata masa azamanin kuruciyarsa.
Wani kake nema? Ya tambaye ni akaro na biyu yana nazarin suturar dake jikina aciikin takaici nasan abinda yake tunani me yiwa fata yakeyi inama ace yanada halin sauya min suturar da bazata taba tozarta kyakkyawan gidan ba me yiwuwa kuma wani tunani ne can na daban yakeyi. To koma dai menene babu alamar farin ciki ko bakin ciki a fuskarsa.
Eh... Wani nake nema... Uhm wata nazo nema
nace dashi harshena yana sarsarkewa.....HINDU - 03
.
Eh wani nake nema.... Uhm wata nazo nema. Nace dashi harshena yana sarsarkewa.
.
Tsohon ya shafi farin gemunsa sa'annan ya karkata kai gefe guda kamar zakara yace.
Wa kenan? Nayi shiru na dan lokaci tambayarsa ta fara isata.
HINDU...nake son gani
daman kunyi da ita zaka zo ne? Na girgiza kai.
Bamuyi da ita zanzo ba yau ba to amma munyi da ita cewa duk sa'ar da naso na iya ziyartarta.
Tsohon ya sake gyara tsayuwa akofar gilashin kamar wanda ke tsammanin zan banke shi in shiga ciki aguje
In dai bakuyi zaka zo ba to ina mai fargabar sanar dakai cewa bazata iya ganin ka ba. Wani zazzafan gumi ya keto min. Hakika na tsunduma kaina acikin tekun ruwan zafi domin yan kwanakin da mukayi da hindu ta gama shiga raina gashi kuma na fahimci kamar hindu ba ajinmu daya ba.
Ka...ce da ita ISMA'IL ne... Malam isma'il na JAMI'AR SARAUNIYA..
Nace dashi cikin karfin hali tsohon ya girgiza kai cikin takaici
Yallabai kada ka wahalar da kanka domin hindu bata san yawan surutu in ma naje mata da wannan labarin dana fara fada kalma guda zata takamin burki hakan dayace shiya tabbatar min da cewa Hadimin gidan ne shi ma.
Amma idan kanada kati ko wata alama da zan iya nuna mata ta ta fito kana iya bayarwa in kai mata domin ga al'ada ta gwammace ta karance shafi ashirin da rubutu fiyeda ace ta saurari jumla guda ta magana.
Nayi ajiyar zuciya sa'ar danaji abinda yace Hannuna na rawa na lalubi aljihuna na zaro kati na na shaidar gurin aikina na mika masa ina cewa.
Gashi ka bata wannan.,. Kaikuma abinda kayimin nagode baba
ga mamakina sainaga ya saki lallausan murmushi akaro na farko tun sa'ar da muka fara muhawwara dashi.
Kada kayi gaggawar godiya haka tun da wurwuri kabari har sai idan na dawo tace tana son ganinka sannan saika gode na dubeshi nima da murmushi.
Kada ka damu zama ta ganni tun kafin na gama bayanin ya juya da sauri ya rufe kofar gilashin a fuskata nayi ajiyar zuciya gamida share gumi. Zuciyata na wasi wasi gamida zargin kaina da wautar zuwa gidansu wannan daliba tawa. Koda yake dai abin da ido ya gani zuciya ta yaba... Bat sake hutu da tunaninsa har sai ta mallake shi.
Ina nan tsaye bakin ginin alfarma jikina na bari kamar tsohuwar data kama kwarto a karkashin gadonta. Banyi aune ba ban kuma san da dawowarsa ba sai dana ji gyaran murya sannan na juyo firgigit.
Yallabai tace wai ka shigo yace dani awannan karon harda rusunawa cikin girmamawa.
Biyo ni mu shiga. Nabishi abaya simi simi kamar batacciyar tunkiya muka shiga kawataccen dakin shakatawar da tun da nake ban taba ganin irinsa amafarki ba. Ballantana har na shiga. Sannu ahankali muna tafiya sai da muka wuce dakunan shakatawar har guda uku kafin mu tsaya.
Dakin da muke tsaye acikinsa fankadeden gaske ne kujerun alfarma sun yi sahu sahu akan tattausar kilishi mai numfashi acan gefe guda daga bangaren arewa wani dan karamin tekun gilashi wasu irin kifaye koraye nata wasa aciki hakanan duk dakin kamshi yakeyi kamar dakin amarya akasar hausa.
.
Na dade ina mafarke mafarke na banza da wofi wasu a barci wasu ko a farke wani sa'in sai nayi mafarki wai gani nan na zama sarki ga dogarawa da jakadu duk an zagaye ni anata fadanci gami dayi min fifita. Wata sa'ar kuwa sai inyi mafarkin wai gani nan na zama babban attajiri gani nan zaune acikin mani'imacin gida da kayan karau na kawa...
Wasu kuwa mafarke mafarken nawa azuciya nakeyinsu wani sa'ar sai in hau gado ni kadai in kwana gashi dai idanuwana rufe amma sam-sam ba barci ba nakeyi lissafo irin rayuwar da zanyi nake yi in har na zama attijiri haka kawai dan shirme sai inyi ta ayyanawa zuciyata wai gani nan nayi kyautar tsohuwar motata hajiya ba duwawu na sayo sababbin motoci guda biyar... Uku shida kai goma dai.... Gani nan zaune cikin dakin ma'abocin kayan alatun duniya.
Dan haka sa'ar danayi tsaye ina nazarin kayan alatun da ke dankare daya kawai daga cikin dakunan shakatawar su Hindu sai na fahimci duk acikin mafarkin da nakeyi ban tabayin na kyawawan daki kamar wannan ba.
Ina nan tsaye sororo ina kalle kalle kamar sauna sai tsohon yace.
Yallabai zauna anan ka jirata. Nayi tsaye ina kokarin zabar kujerar daya kamata in zauna daman gani nakeyi kamar duk wacce na zauna akanta laifi zanyi daga karshe na zauna akan kuryar daya daga cikin kujerun. Naji nayi kasa Luuuuu! Kamar zata hadiye ni ina nan zaune zuciyata nata sake sake dakyar nake motsi akan kujerar wata sassanyar iska da ban san daga ko daga ina take ba sai fifitani takeyi gwanin dadi.
Wani dan motsi ya dauki...


Read / Download HINDU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album