Join Our WhatsApp Group

BOYAYYEN ALAMARI Complete Hausa Novel Document by BOYAYYEN ALAMARI


BOYAYYEN ALAMARI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41293



BOYAYYEN ALAMARI

Reading Time: 3 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: SeemaLuv ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 227.28 kb

File Type: txt

Views: 1499+

Download: 393+

Last download: 1 day ago

Description/Story: BOYAYYEN AL'AMARI
Na SEEMALUV
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
T


‎khaleesat haiydar hausa novels*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_*Bismillahir Rahmanir Rahim...Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin K'ai...*01*A zaune Safna take saman tabarma rik'e da razor a hannun ta tana cire kumban k'afar ta, Sai Umma wacce take ta kara kaina a tsakar gida ' sai kuwa k'an nanta guda biyu Rumaisa da Anisa wad'an da suke wasan guje guje a tsakar gida.Safna ita ce babba a cikin su ' don kuwa zata kai kimanin shekara 20 cir, Rumaisa kuwa shekaran ta 17 Anisa 10.Safna, Rumaisa da Anisa marayu ne ' Mahaifin su yarasu sakamakon rashin lafiyan da yayi mai tsana ni.Hakan yasa karatun Safna ya tsaya cak tunda ta gama secondry school ' bata samu damar zuwa gaba ba, Kasan cewar matsalar rashin kudin da sukefama dashi.Rumaisa da Anisa kuwa ' a makarantar Primary suka tsaya, ba tare da sun cigaba ba ' sai makarantar allon da suke zuwa anan k'ofar gida.Rumaisa ita ke fita k'ofar gida tana suyan wara, A haka har tayi ciniki susami abinda zasuci.Ita kuwa Safna aikatau take zuwa mak'otan su, wani lokaci haka zata gama aikin ranar baza'a bata abinciba.Umma ce keta d'awainiya dasu da dad'i babu dad'i, Hakan baisa tayi wani auren ba ' wani lokuta ma 'yan uwanta ke d'an harhad'a mata kayan abinci."Safna ya kamata ki tashi ' ki tafi wajen aikin ki rana nayi".Inji Umma."Umma ranar ma tayi wallahi ' yanzu ina zuwa fad'a zasu rufeni dashi, Suda basu da uzri"."Baki da wani uzri ai lafinki ne ' bakison zuwa da wuri, Yanzu dai ki tashi ki d'auki hijabin ki ki wuce"."To shikenan Umma".Safna ta fad'i haka tana k'ok'arin tashi."Safna zan biki".Cewar Anisa."A'a kiyi zaman ki gida".Safna na fad'in haka ta mik'e tare da janyo hijab d'inta maroon colour dake saman k'ofa, Ta sanya ta fice.Haka ta kama hanya ' harta isa kusa da gidan ta had'e da k'awar ta tana fitowa ciki."Sumayya ya garin ne".Cewar Safna.Harare hararen da Sumayya takeyi ne ya d'aure ma Safna kai."Lafiya kuwa"."Lafiyar ta kawo haka!"."Tooo! Allah ya baki hak'uri sai anjima".Safna tana fad'in haka ta k'arasa cikin gidan, Kai tsaye ta wuce d'akin hajiya domin su gaisa.Bayan ta shiga ne Safna ta iske suna magana da babban d'anta.Haka ta zuk'unna har k'asa ta gaishe ta, Bayan sun gaisa ne ta tashi zata fita Hajiya ta tsaida ita."Safna tsaya tukunna"."To".Ta fad'a tare da komawa ta zuk'unna, Hajiya bud'e jakarta tayi ta ciro kudi kimanin dubu 2 ' ta mik'awa Safna, Haka Safna ta mik'a hannu ta amsa ba tare da tasan na menene ba."Safna ' wannan kud'in sallama ne, Bakison zuwa dawuri kuma bakison wanke mun kwanoni da kyau ' saboda haka na yanke shawarar cenja ki" ."Subhanallah! Hajiya don Allah kiyi hak'uri ki dawo dani ' wallahi Allah ina miki aiki dakyau, Yaune kawai na makara".Tana fad'in haka hawaye na zubo mata a ido."Nifa ba kuka nace kimun ba, Saboda haka tashi ki fita"."Hajiya kiyi mata afuwa mana".Cewar d'anta."Bana son iskanci kaji ko?"."Allah ya huci zuciyarki".Safna kuwa ganin bata da niyyar hak'ura ne yasa ta tashi ta fita, Harta kama hanyar fita taji motsi a kitchen alamar ana wanke wanke."Bari inga wacce aka cenja".Ta fad'a a zuciyar ta.Tana k'arasawa wajen taga mahaifiyar k'awarta wato sumayya, Mamaki ne ya cika Safna ' hakan yasa ta juya da sauri tabar wajen.Haka Safna ta baro gidan cikin wani hali ' tafiya kawai takeyi tana share k'wallar dake idon ta, Har ta isa gida cike da sallama a bakin ta.Umma ta iske ita kad'ai a tsakar gida tana surfa dawa."Wa'alaiki-salaam Safna, Lafiya kika dawo?".Matso murmushi tayi ta sakar mata ' amma sam fuskarta babu walwala, Tukunna ta k'arasa kusa da Umma wacce tayi kasak'e tana kallon ta."Am... Umma ga wannan inji Hajiya".Safna mik'awa Umma kud'in tayi, Umma ta lura idanun ta cike suke da hawaye."Tooo Kud'in aikin ki aka biyaki da wuri haka?"."A'a Umma, Kud'in sallama ce".Nan gaban Umma ya fad'i tayi sauri ta jinginar da tab'arya jikin bango, Gami da dafe k'irji."Uban me kikayi? Iyi Safna wane laifin kika aikata? Sata kikayi mata?".Jin an abaci sata ne ' yasa Rumaisa fitowa daga d'akin su cikin sauri, Ita kuwa Safna hawaye kawai ke mata zarya a fuska."Haba Umma! Ya za'ai kici taimata sata? Bayan kinsan halayen Yaya Safna kaf...".Idanun Umma ne suka ciko da k'walla, Rumaisa tasahannu ta sharewa Safna hawaye tare da janyo tabarma suka zauna."Yaya Safna meya faru?".Nan Safna ta fad'awa Umma duk abinda ya faru, Umma waje ta samu ta zauna cike da ajiyar zuciya."Yanzu abunda Hajiya zatai mun kenan?"."Umma karki damu ' insha Allah zan fita in nemi aiki,Kuma insha Allah bazamu tagayyara ba"."Rumaisa ina Anisa?".Inji Safna."Tana Bacci".Mik'ewa Safna tayi idon ta akan Umma wacce duk damuwa sun bayyana a fuskar ta."Umma ki bani koda dubu d'aya ne cikin kud'in, Domin zan hau adaidaita sahu ' inshiga cikin gari"."Hm... Yanzu idan kinje ina zaki nufa?".Cewar Umma."Umma manyan kanfanoni(Companies) zan fara bincikawa ' ni koda share share ne su bani"."Hm... Meyasa baki tunanin k'asa da wannan? Meyasa baza kije gidaje ba? Safna ina ganin kamar neman aiki a kanfanoni zaiyi maki wahalar samu".Rumaisa ce tayi saurin kutsa baki cikin maganar."Haba Umma fatan alkairi kawai zamuyi mata"."Hakane Rumaisa".Umma na gama rufe baki ' ta zari dubu ta mik'awa Safna, Ta karb'a sannan tasa kai ta bar gidan cike darashin sanin inda zata fara nufa.Bayan Safna ta fito ne ' tayi sa'a tasami adaidaita ta shiga."Ina muka nufa?"."Cikin gari zamu shiga ' kawai kaita kewaye da wajajen manya manyan ma aikatun nan".Haka mai adaidaita sahu yaja napep d'inshi Safna na ciki, Har suka isa cikin gari.Mai napep zagaye ya dunga yi da ita ' tana k'arewa kowacce ma'aikata kallo kasancewar Garin babban gari ne ba k'arya. Safna wani k'ayataccen company ta hango cikin garege d'inshi motocin ma'aikata ne birjit iyakar ganin ka.Hakan yasa Safna yin saurin tsaida mai adaidaita sahun."Bawan Allah mu tsaya anan, Nawa ne kud'inka?".Tayi tambayar tana k'ok'arin saukowa daga napep d'in."Gaskiya malama bisa adalci ' dubu d'aya zaki bani"."Haba kaikuwa? Har dubu d'aya? Ina laifin d'ari ukku? Kaga fa dubu d'ayan nan ita kenan mun, Kuma wajen nan zan iya kaiwa yamma"."Shikenan kawo d'ari biyar ' gaskiya iyakar abunda zan iya ragewa kenan".Inji mai Napep.Safna mik'a mashi dubu d'ayan nan tayi, Shi kuma ya bata cenjin d'ari biyar sannan ta juya ta doshi cikin company d'in.*DEDICATION..._My Family!_*....*....B'OYAYYEN**AL'AMARI**2-3**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_**2-3*Safna tafiya takeyi tana kallon yanayin Company d'in, Har ta isa bakin k'ofar shiga ciki ' jitayi ana."Hey! Hey!!!".Hakan yasa ta tsaya cak ' cike da fargaba, Wasu securities guda biyu sukayo kanta."Madam! How can we help you?".Nan bakin Safna ya hau rawa ' kasan cewar turancinkad'an kad'an take iya maidawa."Am... Sunana Safna ' nazo neman aiki ne a job".Nan securities d'in suka fara dariya tare da k'are mata kallo."Madam, ba'a d'aukan aiki anan, saboda haka ki tafi ki nemi wani wajen".Cewar d'aya daga cikin su."Don Allah koda shara ne zanyi muku ' sai ku rik'a biya don Allah".Tana gama fad'in haka suka rufe security door d'in, Hakan yasa Safna juyawa ta matsa daga wajen ' ta nemi waje ta zauna tana k'arewa motocin da ke wajen kallo.Bata ankara ba taji iskar hadari ta taso ' hakan yasa tabarin wajen cikin hanzari, Ta shige cikin wani garden wanda aka k'ayatar dashi matuk'a.Safna kujera ta samu ta zauna ' tare da d'aura kanta saman table, Haka akaita tsugaga ruwan sama ita kuwa tuni bacci ya kwashe ta a wajen.*35 MINUTES LATER*Safna taji ana buga table d'inda ta d'ora kanta akai, Hakan yasa ta farka daga baccin tare da d'ago kai domin taga waye.Wani Mutum ta gani sanye da suit a jikin shi ' Chocolate colour, Zubin masu kad'i."Who are you?".Nan nefa Safna ta kauda kanta daga kallon da take mashi ' ta koma kallon sama don duban hadari."Ashema angama ruwan!"Shima juyawa yayi ya dubi sama."Oh yes angama, and am advising u, koma wacece ke kibar wajen nan ' kafin nakira securities".Ai nan Safna ta mik'e tsaye gami da zaro ido."Don Allah ka taimaka mun! Wallahi aiki nazo nema ido rufe, Sir koda Shara ne zanyi muku sai ku biyani".Kujera yaja ya zauna, sannan yace."Hope kina da takaddun ki a hannu?"."Eh dasu nazo".Miko mata hannu yayi ta bashi takaddun nata ' ya duba tsaf sannan ya mik'a mata."Kamata yayi kije ki cigaba da karatun ki ' inyaso saiki dawo mu baki aiki"."Sir nidai a taimaka mun insamu da secondry schoolcertificate d'in"."Well... Is ok if that's what you want, Ammm are you good in making Coffee?"."Coffee?"."Yes Ruwan bunu"."Amm.. A'a...".Bata kaiga k'arasawa ba ya katseta da cewa."Then saikije ki koyo ' domin shine zai zama aikin ki dazaki rik'ayi a wannan Company"."OK! Na gode"."Am KAMAL ABUBAKAR ni ne mataimakin mai wannan Company ma'ana (P.A), You can call me Sir Kamal Ok?".Ta d'aga mashi kai alaman To."Sir, Yaushe zan fara aikin?".Murmushi yayi mata ' ganin ta cika sauri."Ai zaki fara ' har saikin gaji"."Hmm"."Yanzu tashi zakiyi ' ki biyoni mu shiga Office d'ina, Domin insamu wasu informations a tsanake.""Har ina ne wajen?".Kamal sauri yayi ya d'ago kai ya kalleta."Office d'ina mana!"."Hmm... Nidai da dai zamu iyayin komai anan"."What!? You are not serious!, Look inada aiki sosai a gaba na ' so ki tattara inaki inaki kibar wajen nan".Kamal tashi yayi cikin b'acin rai zai bar wajen tayi saurin rik'o gefen rigar shi, Gami da zubewa k'asa."Sir Kamal! Am sorry, ka taimakamun don Allah ' na yarda muje cikin office d'in naka amma kuma inaso ka rik'e Allah ya zuciyar ka"."It's Ok".Haka Safna ta bishi suka shige cikin ma'aikatar securities da sauran ma'aikatan kallonta kawai sukeyi, Ita kuwa Safna wurga idanu kawai takeyi tako ina har suka isa cikin Office d'in.Kamal a kujerar shi yaje ya zauna ' gami da zaro takarda, Sannan ya d'auki pen daga desk d'in shi, Zaifara rubutu kenan ya ankara ashe a tsaye take har yanzu."Madam!".Ta d'ago kai ta kalleshi tare da cewa."Sir!"."Zaki iya zama".Safna waje ta samu ta zauna ' sannan ta maida kanta k'asa Kamal
ya cigaba da rubutu.Sai da ya kammala ne ya d'ago kai ya kalleta tare damik'a mata takaddan."Am..ansa wannan ' zaki dawo ranar monday! Wannan takaddan itace zaki nunawa securities idan kinzo, Understand?"."Yes"."Good! But before then, Ya kamata inji sunan ki ' infact you have to introduce yourself to me now!"."Ok, Sunana Safna Habib! Ina zaune ne ana k'auyen GATORIYA, Kuma ni marainiya ce mahaifina ya rasu' sai mahaifiya ta wacce take d'awainiya damu..."."Ya Salaam! Allah yaji k'anshi"."Amin"."Insha Allah zaki sami aiki Safna ' Zanyi magana da Ogana kinji?"."Nagode"."Shikenan! Zaki iya tafiya yanzu".Safna tashi tayi rik'e da takaddan ta ahannu, Tabar Office d'in cikin hanzari tana fita suka ci karo da wani har suna bangazar juna.Wani Handsome guy ne ' mai kamala shima cikin suit, Fari ne zubin larabawa ' da bloothode d'in shi sanye a kunne, Matashi ne d'an kimanin shekara 30."Whattaaa!!!".Abunda taji ya furta kenan tajuyo cikin tsoro ta kalleshi."Kayi hak'uri don Allah"."What? Are you blind? Wacece ke? Daga ina? And who gave you the permission to...".Bai k'arasa ba tayi saurin katseshi da cewa."Ha'a bana baka hak'uri ba? Hmm".Tana gama fad'in haka ta juya ta wuce.Mamaki ne ya cikashi ganin yadda ta juya ta wuce without begging."Wace yarinya ce wannan? She don't even have manner, i will surely find out ' mtsww".Yana fad'in haka ya juya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya wuce.*DEDICATED TO MY FAN'S**....B'OYAYYEN**AL'AMARI**4-5**_Pure Moment Of Life writers_*© ```Written```By*_Seemaluv_**4-5*Safna tana fita daga company d'in ta tsaya bakin titi domin samun abun hawa, Bata wani b'ata lokaci ba ta tari mai keke napep tai mashi kwatancen inda zai kaita ' kasancewar K'auyen su da cikin garin bashidanisa.Farin ciki ne cike ranta ' don kuwa ya kasa b'oyuwa afuskarta."Bawan Allah d'anyi sauri mana".Cewar Safna.Haka tasa mai keke-napep ya karawa keken shi gudu, Ita kuwa sai godewa Allah takeyi da k'osawa taga Umman ta.*AROUND 5:00PM*Safna ta isa gida ' nan ta sallami mai keke-napep sannan ta shige gida, Safna shiga tayi d'auke da sallama a bakinta ta iske Rumaisa tana jan ruwa a rijiya.Jin sallamar yasa Rumaisa d'ago kanta ta kalli Safna, Cikin jindad'i da nuna farin ciki Rumaisa ta aje gugar a gefe tayo kanta."Yaya Safna, sannu da dawowa ' Allah dai yasa antaki sa'a".Murmushi kawai Safna tayi gami da cewa."Umm! Ina Umma take?"."Umma tana d'aki tare da Anisa"."Ok".Safna da Rumaisa d'aki suka shige cike da sallama Umma ta amsa."Alhamdulillah Safna ya hanyar?"."Umma hanya lafiya k'alau, yana barku?"."Lafiya k'alau Safna, Allah dai yasa anci nasara!"."Insha Allah Umma".Cewar Safna.Bakin gado ta samu da zauna ' sannan ta cire hijab d'inta ta aje gefe, Tukunna ta cigaba da cewa."Umma! Kinga wannan takaddar?".Tayi mata nuni da takaddar dake hannun ta."Eh k'warai"."To mataimakin Ogan wajen ne yayi mun rubutu aciki ' yace kuma indawo ranar litinin da takaddar tabbas zan samu aiki"."A wane waje kika nema?".Cewar Umma."Umma a babbar ma'aikata ce (Company)"."Kinga Safna banason abunda zaije yajawo matsala?".Rumaisa ce tayi sauri ta shiga maganar."Haba Umma? Insha Allah babu wata matsala!"."To Shikenan! Allah ya shige mana gaba"."Amin"."Umma? Ina abinci na don nadawo da yunwa wallahi".Cewar Safna."Tuwo ne da miya gayacen ' ki d'auko kwano ki d'iba".Tashi Safna tayi gami da cewa To ta nufi wani d'an d'aki wanda anan ne suke aje kwanoni, Nan ta d'aukikwano ta dawo d'aki ta zuba tuwon taci.Bayan ta gama ne Umma tace."Safna?".Ta d'ago kai ta kalleta tare da cewa."Na'am"."Wai wannan ma'aikatar ta mecece?"."Umma ma'aikar tumatirin gwangwani ne"."To Allah yasa adace!".Rumaisa wacce ke gefe tana kallonsu ta amsa da amin.Safna suna cikin haka ne aka kira sallar magrib, Cikin nutsuwa gaba d'ayan su suka tashi sukayo alwala sannan sukayi sallah.Bayan sun idar ne Rumaisa ta tada Anisa domi itama tayi sallar.Atak'aice dai basu kwanta bacci ba saida sukayi sallar isha'i tukunna.Haka rayuwa tacigaba da juyawa ' da dad'i babu dad'i haka Safna da Umma ke fad'i tashi don ganin rayuwarsu ta inganta.*3DAYS LATER...*Yau take lahadi, Safna da Rumaisa tunda sassafe suka tashi suka fara aikin cikin gida ' kamar yadda suka saba, Sannan Umma ta tashi ta had'awa Rumaisa waran da zata sayar a k'ofar gida domin susamu su sami abinda zasu ci.B'angaren Kamal kuwa zaune yake cikin Office d'in shi yana danna laptop kira ya shigo cikin wayar shi, Ganin Oga ne yasa shi yin saurin d'agawa."Sir?"."Yes come to my office right now!"."Am on my way Sir".Kamal yana gama fad'in haka wayar ta yanke hakan yasashi tashi cikin hanzari ya nufi office d'in Oga.Kai tsaye ya shiga ciki ' ya sameshi a zaune saman kujerar shi ya juya baya."Sir, Am here".A hankali ya juyo ya kalli Kamal."Good! Zaka iya zama".Kamal zama...


Read / Download BOYAYYEN ALAMARI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On BOYAYYEN ALAMARI
avatar
shafaatu-9

8 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album