Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

IDAN KA RAINA INDA KA KE Complete Hausa Novel Document by IDAN KA RAINA INDA KA KE


IDAN KA RAINA INDA KA KE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 122015



IDAN KA RAINA INDA KA KE

Reading Time: 10 Hours

Added On: 28, Jun 2024

Author: Sajida ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 629.6 kb

File Type: txt

Views: 446+

Download: 1451+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: *❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



1⃣


Na : *SAJIDA*

sadaukarwa wa *ummu lalla Fatumah sisna Hawwer*





Haba Aïsha, haba Aisha har yaushe zaki daina irin wannan mugun halin? Shin mai mahaifinmu ya rage mu da shi, daidai karfinsa yanai mana, du abinda muke bukata daidai gwargwadon iyawarsa yanai mana aman a kulun idan kika budi bakinki ba zaki yabi tarin alkhairan da yake yi mana na yau da kulun ba sai dai ki fadi wani wajen da ya gaza, a kulun ina fada maki ki daina kokarin hada rayuwarki da ta sabuwar kawar da kika yi.. kin ga iyayenta masu hali ne sannan samarinta sun tsaya mata...............ki........m

Wace aka kiraya da Aisha wace ta yi tsai tamkar tana daukan nasihar yar uwarta ta dago fuska a hade ta watsawa yar uwar tata harara ta ja wani uban tsaki ta ce" kinga malama ki saurara min haka, shin tambayar ki nai ki yi min kari a kan tarbiyar da kike ganni bani da ita ko mai? Ni ina mamakin idan kika sakoni gaba kinai min fada tamkar ke ce yayar tawa ni kuwa kanwarki,,, idan ke ita rayuwar nan ta yi maki sai ki je ki karata da talauci aman ni na fada maki idan baba ya nacewa FASKARE ni ba zan iya ba, ga ayuka nan barkatai a duniya aman shi ya nace sai dai faskare da shi ne zai ciyar da mu? To zan fada maki ko ta tsiya sai na shiga banban gida na hau babar mota domin Allah ya bamu halin auren nairar tunda ya kayatar da halitar mu.......
Ta gama tana mai juya dara daran idannuwanta ta zarce wajen dan karamin madubinsu ta zauna ta shiga fence fuskarta

Ta jima zaune tamkar ruwa ya cinyeta tana mai takaicin halayar yayarta, a hankali ta mike ta karaso kusa da ita ta dora hannunta na dama saman kafadar yayar tata ta marairaice murya ta sada kanta alamar zata bada hakuri ta ce" ki yi hakuri Autyna, ban fadi haka dan na bata maki rai ba idan na ga irin haka na faruwa ne sai hankalina ya tashi domin bana so ki fada *tarkon samarin zamani ne* inai maki son da ba zan juri ganinki a wani hali ba plz auntyna ki yi hakuri kar ki yi fushi da ni

A hankali Aisha ta juyo ta kamo hannun kanwarta wato *RAUDA* wace take yiwa kiranye da LALLA ta ce" *LALLANA* ki gane ni du abinda ya shafi talauci batan raina yake, ki duba fa ki ganni kulun Abanmu jalabiyarsa kwaya daya ya fice da ita da gatari ya tafi yawon anguwa anguwa kofa kofa yana neman itacen da za.a bashi ya faskara, bayan ya gama a hada shi da naira ashirin naira talatin baban samunsa naira dari watarana sai ya wuni bai samo komai ba ya dawo haka zasu yi ta samun matsala da mama sannan da wannan samun ne yake ciyar da mu ya siya mana atampa roba ya yi mana dinkin naira dari bibiyu, sai fa sallah ta zo bamu da kayan sallah dududu har muka yi yarinta muka gama hijabanmu hudu a duniya muna arawa juna muna canzawa...... makaranta litafinmu kwaya daya da shi kike rubutu nima da shi nake yi.... haba ko yaya na ga haske ai zan nufe shi shi ya sa nake fada maki yanzu mun taso mun kai mizanin yin samari muna jami.a dole mu so daukan wanka ko dan gudin raini , sannan samarin nan harin mu suke ina mai baki shawarar ki kula su tun suna kula ki ba sai su yarda ke ba ki dawo kina zubar da kwalah kina haukan neman su

Ajiyar zuciya Rauda ta sauke, kwata kwata magangannun yayarta banda caza mata kai ba abinda suke... a kulun adu.arta shine Allah ya katsewa yar uwarta irin wannan dogon buri na mahaifiyarsu tun kafin ya zame mata matsala, ita bata ga abin damuwa a rayuwarsu ba mahaifinsu yana nema tun karfinsa da shi yayi ta fafutuka wajen gannin sun yi karatu sun samu ilimin adini da na boko, da yake mutun ne mai tsayuwar dare mai fawalawa Allah lamuransa sai ya kasance duda makarantar gomnati suke yi sannan a jarabawa basu da mai kama masu sai Allah Ya tsaya masu suke tafe cikin nasara har Aisha ta samu shiga University sannan Rauda...... manema aurensu kuwa ta ko.ina fitowa suke sai dai idan har sunanka bai zarce ba Aisha Bata sauraronka ita kuwa Rauda tana saurare sai dai mahaifiyarta ta shiga ta fita ta kori mutun sannan ta....

Tunanin mai kike ne Lallana?
Muryar Aisha ya kashewa Raudat tunanin da ta fada ta zabura ta kakaro murmushi ta ce" ba komai Auntyna , Allah ya shige mana gaba

Aisha ta amsa da amin sannan ta juya ta ci gaba da gyara fuskarta dan zuwa makaranta

Haka suka fito Aisha ta gyara fuskarta tamkar zata je wajen biki Raudat kuwa banda kwali da ta dan furta a idannuwanta ko hoda bata shafa ba

Mahaifinsu ne zaune yana wanke hannunsa da gatarinsa gefe ya saka jalabiyarsa wace dan tsufa har yamutsewa take sai hularsa irin zigegen alhazan nan wace a kadan ta shekara hudu da aka yi masa kyautarta

Amsa gaisuwar yayan nasa yake cikin sakin fuska da basu mahinmanci sannan ya shiga laluben aljihunsa ya jawo naira dari da ashirin ya mikowa Aisha wace ita ce baba ya ce" Aisha ga wannan ba yawa sai ku sha ruwa a hanya

Aisha ta bi hannun mahaifin nasu da kalo naira darin ta yakune du a cicire hakama ashirin din ta sama ta kakaro murmushin yake ta ce" baba ai ka barshi kawai

Tana gama fada ta mike ta fice inda suka rakata da kalo jikinsu ya mutu murus

A hankali ya juyo da dubansa wajen Raudat ,

Saurin basar da abinda Aisha ta yi ta yi ta kakaro murmushinta mai kyau da tsari ta mika hannu biyu ta ce" Lah Abanmu ni dai ina so, bani naira ashirin din sai na kara da sauran canjin da ka bamu jiya bamu kashe su duka ba shi ya sa aunty ta ce bama so, tana son cewa ai da saura ne

Ta karasa maganar tana karbar ashirin din da iya kokarinta dan gannin ta mantar da shi dabi.ar yayar tata

Murmushi yayi ya sakar mata ta mike ta kama hanyar fita
Har ta daga kasarin da ya kare kofar mahaifinta ya ce" *Raudat*...

A hankali ta juyo tare da amsa kiransa

Cikin murya mai cike da nutsuwa ya ce" Allah ya datar da ku da dukan alkhairin rayuwa, ya daukaka ku, ya sanya farin ciki a cikin rayuwar ku, ya baku mazaje na kirki masu tsoron Allah da bin umarninsa ,

A hankali take amsawa da amin a dukan adu.ar mahaifinta har inda yake cewa" Allah ya shiryar da yar uwarki tun kafin dama ta kubuce mata, ya sa ta daina hangen na wasu ya kasance ta daina *raina inda take kar taje ta yi biyu babu domin mafi yawancin irin haka inda zasu ya raina su*

Saurin dago da kanta ta yi bata ce komai ba sai lumshe idannuwanta da ta yi ta mike ta kara gyara hijabinta ta juya tana sauri kar Aisha ta yi tafiyarta

Wani irin haushi da bacin rai ne ya turneke mata zuciya hango yar uwarta da ta yi tana kokarin shiga motar sabuwar kawar da ta yi mai suna Aminah

Dan tsayawa Aisha ta yi tana kalon Yannayin Raudat, dan haka ta hade fuska danma kar ta kawo mata wargi gaban Amina

Tana karasowa ta ce" mu je ko? Kin ga Allah ya kawo freind ba sai mun sha wahalar tafiya kafin mu hau bos ta sauke mu a bakin titi mu kuma yin wata tafiyar kafin mu karasa jami.a
Ta karashe tana dage gira dudan ta shawo kan Rauda duda ta san abu ne mai wuya ta yarda ta shiga dan ba shiga take yi ba

Rauda ta dan kakaro murmushi ta ce" ai kin san ina son tafiyar kafar nan ko dan na dan ringa mike kafana aunty ku je kawai sai na karaso

Tun kafin ta gama maganar Aisha ta daga kafadu irin ke kika jiyo ta bude gaban motar ta shige Amina ta ja da mugun gudu suka bar wajen

Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ta daga kafa ta nufi bakin titi dan shiga bos ta kaita makaranta

Lecture din awa hudu ne da ita a yau, haka ta yi karatun nan ba tare da ta saka komai a cikinta ba dan tana son kudin su isheta komawa gida

Karfe 2 na rana suka fito ta nufi bangaren su Aisha dan gannin ko basu sauka ba ta yi jiranta sai dai mai tana karasowa...


Read / Download IDAN KA RAINA INDA KA KE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album