Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KARUWAR GIDA Complete Hausa Novel Document by KARUWAR GIDA


KARUWAR GIDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 56716



KARUWAR GIDA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Ameenat Kabir Kiru (Maman Jabir) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 297.06 kb

File Type: txt

Views: 790+

Download: 1088+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: *KARUWAR GIDA*






*STORY WRITEEN BY✍*

*_AMENAT KABER KIRU_*



*I'M BACK 🤒DUNIYAR MARUBUTA SALAMU ALAIKUM* *ina yiwa d'aukacin Al'umman musulmi na duniya baki daya barka da sallah muna fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu .👏*

*SADAUKARWA:*

_*WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA HJY ZALIHA YOLA(MMN AHMED)*_


*GODIYA*
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji talikai wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba,salati da daukaka da aminci ka qarasu ga dan Amenatu manzo tsira wanda babu tamkarshi,alaye da sahhaban gidanshi tsarkaka._

*TSOKACI*

*wanna labarin bai shafi wata ko wani ba na rubuta shine domin gani yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamanin duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zu'katan mu, ba nayi ne dan yad'a bad'ala ba,a'a zanyi ne saboda na zakulo wasu halaye da suka shiga gidajen aure. Duk wanda yaga abinda bai masa ba yana da kyau ya bude dogon shafin zagina kofa a bude take domin karbar hakan daga ko waye,zagi danzagawa ne nasan baya tabo🤷‍♂Azagi kowa normal ne🤪*




*PAGE🅾1⃣*


Da sauri Mariya ta juya ta kalli mahaifiyar ta wacce ta ke 'kokarin fita daga 'karamin dakin nasu ta kira sunanta a hankali tace UMMA dan Allah ki saurareni mana" kallon yar tata tayi galala wacce bata wuce shekara goma sha d'aya a duniya ba, tare da fad'in ina jinki, nisawa tayi da cewar UMMA ina zaki tafi a wannan daren ki barmu bai kamata ki tafi ki barni nida ANAS a wannan halin ba. daka mata tsawa tayi hadi da cewar ni zakayiwa nasiha?" Girgiza kai MARIYA tayi hadi da cewar A'a UMMA kawai naga tunda kika dawo dazu ko magani baki bashi umarnin ya tashi yasha ba gashi zaki 'kara komawa..... katse y'artata ta 'karayi da cewar naji ke din tunda har kinfini sanin abinda ya dace ki tasheshi ki bash mana. tana fad'in haka ta kad'a kanta tayi waje ko sauraren MARIYA bata 'karayiba duk da tasan MARIYA gaskiya ta gaya mata amman ta kasa tsayawa ga yaran nata, ita kuwa tunda mahaifiyar tata ta fita ta koma kusa da inda kaninta yake kwance ta dagoshi da cewar ANAS tashi kaci abinci ka sha magani,da kyar yaron ya dago daga kwanciyar da yayi yace toh yaya, amman ina UMMA?" Kwallace ta fito daga idon MARIYA sannan ta amsa da cewar ta sake fita yanzu, kad'a kai kawai ANAS yayi duk da 'kan'kantar shi a matsayinshi na karamin yaro yace kai UMMA kai UMMA mai kikeson zamane adacan idan ance UMMA zata iya fita nan da k'ofar daki ta barmu zanyi mamaki amman yau mune UMMA take gudu a matsayinta na mahaifiyar mu. kafin ya karasa maganarshi tuni kuka yaci karfinshi daga shi har yar uwarshi watau MARIYA hakuri ta shiga bashi da rarrashin qanin nata. Sai da sukayi kuka mai isa,sannan ta mik'e ta dauko abinci ta Zuba musu, ta fita waje ta dauko roba da ruwa ta umarci kaninta daya tara hannunshi ya wanke a cikin robar, bayan ya gama ta dauki robar da ruwan ta fita dasu itama ta wanke nata hannu sanna ta dawo sukaci abinci tare"bayan sun kammala ne ta dauko magungunanshi ta bare ko wanne ta bashi ta qara gyara mishi gurin kwanciyarshi sannan ta fita ta dauro alwala ta dawo daki,tayi sallah tare da kara gyara nata makwancin hadi da yin addu'a ta shafejikinta ta kwanta amman ta kasa bacci sakamakon tunanin ina mahaifiyar tasu take zuwa babu dare babu rana?" Juye juye tai tayi tana tunanin sauyin halayyar da suke gani a tare da mahaifiyar su, A dan tsakanin nan. Sabida karancin shekarun MARIYA bata iya gano amsar komai ba a haka dai taita juyi har mahaifinta ya shigo jin shigowar tashine yasa ta mike tsaye zumbur daga kwanciyar da tayi hadi da cewa sannu da dawowa ABBA" a ciki ya amsa hadi da cewar ina ZAINAB ta tafi ne?"bata damu da rashin nuna ko in kula da mahifin nata yayi ba tace yanxu ta fita babu dadewa,kwafa yayi da cewar toh,kawai ya nufa inda abinci yake a ajjiye ya dauko ya ajje shi daga gefe hadi da umartar MARIYA data dauko mishi abin zubawa"mikewa tayi ko tsoro bataji domin idan da sabo ta saba da halin mahaifin nata,na rashin tausayi ko jin k'ai a garesu ita da qanninta fita tayi ta hado komai tazo ta ajje masa komai sannan ta koma gefe ta zauna tana ta kallonshi yana muzurai haka ya zuba abincin ya fara ci ko wanke hannu bai fita yayi ba,ya fara ci kenan MARIYA tayi farat da cewar au ABBA na manta ban gaya ma jikin ANAS ya kara tashi ba. Wurga mata ido yayi hadi da kai lomar hannunshi baki yace toh sai akayi yaya? ZAINAB ce ta ce ki gayamin haka da zarar na fara cin abinci ko? dan ku hana zuciyata sukuni toh bari kiji sabida ku wallahi bazan kashe kaina ba'" girgiza kai MARIYA tayi hadi da cewar A'a ABBA, tare da matse kwallar da ta rufe idonta,tsawa yayi mata hadi da nuna mata makwancita da ta tafi ta kwanta, tashi tayi a hankali ta nufi shinfidar ta ta kwanta cikin kunar zuciya,da mamakin anya kuwa ABBA shine ya haifesu ita da qaninta?AMMA ce mai tausaya musu tai musu komai amman yanxu itama ta sauya a yan tsakanin nan bata san menene yake faruwa a tsakanin iyayen nasu ba, a haka bacci yayi awan gaba da ita, Ita kuwa ZAINAB tun fitar ta bata zame ko ina ba sai gidan kawarta Hajiya Rukaiyya tayi sallama tayi aka amsa mata daga ciki ta karasa tayi sa'a Hajiya ta dawo ba kamar dazu da tazo tai ta faman jiranta bata dawo ba,da fara'a Hajiya Rkaiyya ta karbi ZAINAB da cewar kawata kece a yanzu haka?"amsawa ZAINAB tayi hadi da zama kan daya daga cikin kujerun falon, kawata da cewar ai nazo daxu bakya gida UMAR bai gaya miki ba?" Har yace bakiyi nisa ba"nan nayi ta zaman jiranki da naga rana tayi sosai shine na koma gida na daurawa yara abinci na danyi aikace_aikacen gida, yanzu ma harsashe nayi da cewar duk inda kika tafi kin dawo gida tunda yace ance min ba dadewa zakiyi ba,dariya Hajiya Rukaiyya tayi da cewar hakane qawata kuma da na dawo nayi kamar nima na bi ta gidan naki sai kuma dai naji nagaji na bari da safe kamin na fita na shigo ta gidan na duba ANAS da jiki, murmushi ZAINAB tayi da cewar ai yanxu ma matsalar jinkin nashice ta tasoni shine nazo na sanar miki hadi da qarin neman taimakonki akan dan Allah qawata ki tallafi rayuwata ki qara taimakamin da aron kudi zan kaishi asibiti, murmushi Rukaiyya tayi da cewar ai kawata tunda na ganki a wannan lkc nasan damuwa ce ta kawo ki gareni Amman dan Allah ina RABI'U yake ne da yabarki kike ta fakan2 din neman kudin kai yaro asibiti? "Murmushi ZAINAB tayi da cewar ai tunda ya fita sallah asuba bai kara dawowa gidan ba har na fito din na" nisawa Hajiya Rukaiyya tayi da cewar gaskiya ZAINAB baza rufeki ba kin sakarwa mijin ki fuska da yawa har ya samu damar wulakantaki haka, amman babu komai sai ki cigaba da hakuri da shi haka nan tunda da yara a tsakanin ku, mikewa tayi daga falon ta shiga dakinta, ta dauko naira dubu biyu ta mikawa ZAINAB tace mata gashi ba ranta miki nayi ba, zanzo muje asibitin tare da safe sai muga yadda Allah zaiyi ko kawata" toh ZAINABA tacewa Hajiya Rukaiyya" ta amsa da babu komai amman yana da kyau kije ki sanarwa da iyayen ku halin da kike ciki keda mijinki,shawara na baki bawai dan na gajiya da baki wani abu nawa ba,toh ZAINAB taqara cewa qawarta hadi da yi mata godiya sukayi sallama ta kamo hanya tayo gida.Koda tazo kofar gidanta sai ta tarar har mijinta ya rufe kofar gida nan ta hau bugun kofa, takai kimamin mitin talatin tana bugun kofar kamin yazo ya bude mata a fusace ya bude yana faman hucin da cewar daga ina kike,?" Shiru ZAINAB tayi kamar bata ji ba ta wuce ta barshi a tsaye ta shige ciki abinta" mayar da kofar yayi shima ya rufe ya bi bayanta hadi da kara tambayar ta daga ina take?" Amman shiru jin bata da niyyar amsawa yasa shi ya kara bude murya ya shiga zazzaga masifa a wannan dare ko kallonshi batayi ba bare ta tanka mishi haka dai yai ta zagi da gori da jifanta da bakaken maganganu amman tayi shiru, ta shiga daki ta cire hijab dinta sai kuwa ya hango k'yalin kudi nan fa ya kara gyara sai ya shiga rarrashita da cewar ai baki gaya min zaki fita bane shine dalilina, na yi miki fada
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KARUWAR GIDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album