Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*KARUWAR GIDA*






*STORY WRITEEN BY✍*

*_AMENAT KABER KIRU_*



*I'M BACK 🤒DUNIYAR MARUBUTA SALAMU ALAIKUM* *ina yiwa d'aukacin Al'umman musulmi na duniya baki daya barka da sallah muna fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu .👏*

*SADAUKARWA:*

_*WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA HJY ZALIHA YOLA(MMN AHMED)*_


*GODIYA*
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji talikai wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba,salati da daukaka da aminci ka qarasu ga dan Amenatu manzo tsira wanda babu tamkarshi,alaye da sahhaban gidanshi tsarkaka._

*TSOKACI*

*wanna labarin bai shafi wata ko wani ba na rubuta shine domin gani yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamanin duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zu'katan mu, ba nayi ne dan yad'a bad'ala ba,a'a zanyi ne saboda na zakulo wasu halaye da suka shiga gidajen aure. Duk wanda yaga abinda bai masa ba yana da kyau ya bude dogon shafin zagina kofa a bude take domin karbar hakan daga ko waye,zagi danzagawa ne nasan baya tabo🤷‍♂Azagi kowa normal ne🤪*




*PAGE🅾1⃣*


Da sauri Mariya ta juya ta kalli mahaifiyar ta wacce ta ke 'kokarin fita daga 'karamin dakin nasu ta kira sunanta a hankali tace UMMA dan Allah ki saurareni mana" kallon yar tata tayi galala wacce bata wuce shekara goma sha d'aya a duniya ba, tare da fad'in ina jinki, nisawa tayi da cewar UMMA ina zaki tafi a wannan daren ki barmu bai kamata ki tafi ki barni nida ANAS a wannan halin ba. daka mata tsawa tayi hadi da cewar ni zakayiwa nasiha?" Girgiza kai MARIYA tayi hadi da cewar A'a UMMA kawai naga tunda kika dawo dazu ko magani baki bashi umarnin ya tashi yasha ba gashi zaki 'kara komawa..... katse y'artata ta 'karayi da cewar naji ke din tunda har kinfini sanin abinda ya dace ki tasheshi ki bash mana. tana fad'in haka ta kad'a kanta tayi waje ko sauraren MARIYA bata 'karayiba duk da tasan MARIYA gaskiya ta gaya mata amman ta kasa tsayawa ga yaran nata, ita kuwa tunda mahaifiyar tata ta fita ta koma kusa da inda kaninta yake kwance ta dagoshi da cewar ANAS tashi kaci abinci ka sha magani,da kyar yaron ya dago daga kwanciyar da yayi yace toh yaya, amman ina UMMA?" Kwallace ta fito daga idon MARIYA sannan ta amsa da cewar ta sake fita yanzu, kad'a kai kawai ANAS yayi duk da 'kan'kantar shi a matsayinshi na karamin yaro yace kai UMMA kai UMMA mai kikeson zamane adacan idan ance UMMA zata iya fita nan da k'ofar daki ta barmu zanyi mamaki amman yau mune UMMA take gudu a matsayinta na mahaifiyar mu. kafin ya karasa maganarshi tuni kuka yaci karfinshi daga shi har yar uwarshi watau MARIYA hakuri ta shiga bashi da rarrashin qanin nata. Sai da sukayi kuka mai isa,sannan ta mik'e ta dauko abinci ta Zuba musu, ta fita waje ta dauko roba da ruwa ta umarci kaninta daya tara hannunshi ya wanke a cikin robar, bayan ya gama ta dauki robar da ruwan ta fita dasu itama ta wanke nata hannu sanna ta dawo sukaci abinci tare"bayan sun kammala ne ta dauko magungunanshi ta bare ko wanne ta bashi ta qara gyara mishi gurin kwanciyarshi sannan ta fita ta dauro alwala ta dawo daki,tayi sallah tare da kara gyara nata makwancin hadi da yin addu'a ta shafejikinta ta kwanta amman ta kasa bacci sakamakon tunanin ina mahaifiyar tasu take zuwa babu dare babu rana?" Juye juye tai tayi tana tunanin sauyin halayyar da suke gani a tare da mahaifiyar su, A dan tsakanin nan. Sabida karancin shekarun MARIYA bata iya gano amsar komai ba a haka dai taita juyi har mahaifinta ya shigo jin shigowar tashine yasa ta mike tsaye zumbur daga kwanciyar da tayi hadi da cewa sannu da dawowa ABBA" a ciki ya amsa hadi da cewar ina ZAINAB ta tafi ne?"bata damu da rashin nuna ko in kula da mahifin nata yayi ba tace yanxu ta fita babu dadewa,kwafa yayi da cewar toh,kawai ya nufa inda abinci yake a ajjiye ya dauko ya ajje shi daga gefe hadi da umartar MARIYA data dauko mishi abin zubawa"mikewa tayi ko tsoro bataji domin idan da sabo ta saba da halin mahaifin nata,na rashin tausayi ko jin k'ai a garesu ita da qanninta fita tayi ta hado komai tazo ta ajje masa komai sannan ta koma gefe ta zauna tana ta kallonshi yana muzurai haka ya zuba abincin ya fara ci ko wanke hannu bai fita yayi ba,ya fara ci kenan MARIYA tayi farat da cewar au ABBA na manta ban gaya ma jikin ANAS ya kara tashi ba. Wurga mata ido yayi hadi da kai lomar hannunshi baki yace toh sai akayi yaya? ZAINAB ce ta ce ki gayamin haka da zarar na fara cin abinci ko? dan ku hana zuciyata sukuni toh bari kiji sabida ku wallahi bazan kashe kaina ba'" girgiza kai MARIYA tayi hadi da cewar A'a ABBA, tare da matse kwallar da ta rufe idonta,tsawa yayi mata hadi da nuna mata makwancita da ta tafi ta kwanta, tashi tayi a hankali ta nufi shinfidar ta ta kwanta cikin kunar zuciya,da mamakin anya kuwa ABBA shine ya haifesu ita da qaninta?AMMA ce mai tausaya musu tai musu komai amman yanxu itama ta sauya a yan tsakanin nan bata san menene yake faruwa a tsakanin iyayen nasu ba, a haka bacci yayi awan gaba da ita, Ita kuwa ZAINAB tun fitar ta bata zame ko ina ba sai gidan kawarta Hajiya Rukaiyya tayi sallama tayi aka amsa mata daga ciki ta karasa tayi sa'a Hajiya ta dawo ba kamar dazu da tazo tai ta faman jiranta bata dawo ba,da fara'a Hajiya Rkaiyya ta karbi ZAINAB da cewar kawata kece a yanzu haka?"amsawa ZAINAB tayi hadi da zama kan daya daga cikin kujerun falon, kawata da cewar ai nazo daxu bakya gida UMAR bai gaya miki ba?" Har yace bakiyi nisa ba"nan nayi ta zaman jiranki da naga rana tayi sosai shine na koma gida na daurawa yara abinci na danyi aikace_aikacen gida, yanzu ma harsashe nayi da cewar duk inda kika tafi kin dawo gida tunda yace ance min ba dadewa zakiyi ba,dariya Hajiya Rukaiyya tayi da cewar hakane qawata kuma da na dawo nayi kamar nima na bi ta gidan naki sai kuma dai naji nagaji na bari da safe kamin na fita na shigo ta gidan na duba ANAS da jiki, murmushi ZAINAB tayi da cewar ai yanxu ma matsalar jinkin nashice ta tasoni shine nazo na sanar miki hadi da qarin neman taimakonki akan dan Allah qawata ki tallafi rayuwata ki qara taimakamin da aron kudi zan kaishi asibiti, murmushi Rukaiyya tayi da cewar ai kawata tunda na ganki a wannan lkc nasan damuwa ce ta kawo ki gareni Amman dan Allah ina RABI'U yake ne da yabarki kike ta fakan2 din neman kudin kai yaro asibiti? "Murmushi ZAINAB tayi da cewar ai tunda ya fita sallah asuba bai kara dawowa gidan ba har na fito din na" nisawa Hajiya Rukaiyya tayi da cewar gaskiya ZAINAB baza rufeki ba kin sakarwa mijin ki fuska da yawa har ya samu damar wulakantaki haka, amman babu komai sai ki cigaba da hakuri da shi haka nan tunda da yara a tsakanin ku, mikewa tayi daga falon ta shiga dakinta, ta dauko naira dubu biyu ta mikawa ZAINAB tace mata gashi ba ranta miki nayi ba, zanzo muje asibitin tare da safe sai muga yadda Allah zaiyi ko kawata" toh ZAINABA tacewa Hajiya Rukaiyya" ta amsa da babu komai amman yana da kyau kije ki sanarwa da iyayen ku halin da kike ciki keda mijinki,shawara na baki bawai dan na gajiya da baki wani abu nawa ba,toh ZAINAB taqara cewa qawarta hadi da yi mata godiya sukayi sallama ta kamo hanya tayo gida.Koda tazo kofar gidanta sai ta tarar har mijinta ya rufe kofar gida nan ta hau bugun kofa, takai kimamin mitin talatin tana bugun kofar kamin yazo ya bude mata a fusace ya bude yana faman hucin da cewar daga ina kike,?" Shiru ZAINAB tayi kamar bata ji ba ta wuce ta barshi a tsaye ta shige ciki abinta" mayar da kofar yayi shima ya rufe ya bi bayanta hadi da kara tambayar ta daga ina take?" Amman shiru jin bata da niyyar amsawa yasa shi ya kara bude murya ya shiga zazzaga masifa a wannan dare ko kallonshi batayi ba bare ta tanka mishi haka dai yai ta zagi da gori da jifanta da bakaken maganganu amman tayi shiru, ta shiga daki ta cire hijab dinta sai kuwa ya hango k'yalin kudi nan fa ya kara gyara sai ya shiga rarrashita da cewar ai baki gaya min zaki fita bane shine dalilina, na yi miki fada amman kiyi hakuri ZAINABUWATA ai nasan bazaki wuce gidan Hajiya Rukaiyya ba toh ya kika barta?" Shiru ZAINAB tayi kamar bataji abinda yace ba hadi da waye kudin ta dauresu a ha6ar zaninta sanna ta nufi gado ta kwanta, biyo bayanta yayi shima ya kwanta gefe, yana jiran yaji abinda zata ce masa amman shiru, tashi yayi ya cire kayanshi ya dauko wata dukunku_nanniyar jallabiya ya saka kana ya qara hayowa gadon ya kwanta yana faman huci," haushine ya kara kama ZAINAB ta kara juya mishi baya ta kama bacci, bata farka ba sai ji tayi zakara na chara, sauri tayi ta mike tsaye tayi waje ta dauro alwala tayi sallah shi kuwa gogan naka ai bata farka ta ganshi a d'akin ba tuni ya fice, tashin MARIYA tayi dacewar taje tayo alwala, da sauri MARIYA ta mike ta bi umarnin mahaifiyar tata da cewar to" tayi waje ta d'auro alwala tazo tayi sallah.

Bayan ta idar ta gaishe da mahaifiyar tata " amsawa ZAINAB tayi cikin kulawa tace mata lfy qlu" mamaki ne ya kama MARIYA duba da yadda taga mahifiyar tata kwana biyu bata sakar musu fuska sai tayi tsammanin ko wani abu tayi mata," murmushi ZAINAB tayi ganin yadda yar tata har ta saki jikinta a wannan lkc, ta qara muskutawa gefe ta kwanto zanninta da zata bawa MARIYA kudin da tasamu jiya ta sayo musu gasarar koko a ciki ta shafa babu su,ta juya ta koma kan gadon bata ji su ba, shiru ta yi hadi da zubar hawaye da sauri ta goge kar MARIYA tagani,duk da haka yarinyar ta fuskancin chanji da tagani daga mahaifiyar tata, sai tace mata UMMA tunda bakiga kudin ba ai ABBA ya rage abinci jiya ki barshi kawai maci haka. Toh kawai ZAINAB tace ta koma gun da ANAS yake kwance ta daga shi tayi waje dashi ta sashi yayi fitsari kana ta wanke masa bakinshi ta dawo dashi daki ta fita ta hada wuta ta dumama musu abincin sanna ta daura musu ruwan wanka. Bayan sun gama cin abin tayiwa ANAS wanka ta hadawa MARIYA nata ruwan wanka ta kaimata" sanna ta dawo ta gyara ko ina sanna ta debi nata ruwan wanka" tana fitowa sai ga kawarta Hajiya Rukaiyya ta karaso gidan kamar yadda ta al'qarta mata, tana shiga MARIYA ta gaisheta,Sai ta tashi ta fita tsakar gida, tabar mahaifiyar tata suna gaisawa da kawarta,bayan sun gaisa ta tambayeta jikin ANAS ta amsa da yaji sauki,can tace toh ki shirya muje asibitin ko, shiru ZAINAB tayiwa Hajiya Rukaiyya hadi da zubda kwallah tace ai babu damar zuwa" amsawa Hajiya Rukaiyy Tayi da cewar kamar yaya, RABI'U ne ya hanaki zuwa kai yaron asibiti?" Girgiza kai ZAINAB tayi da cewar A'a,mamaki ne ya kama Hajiya Raukaiyya tace toh menene?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar ai ya sace kudin da kika bani jiya" ta6e baki Hajiya Rukaiyya tayi tana mamakin wanne irin sauyin yanayin ne yazowa ZAINAB haka?" Ace mijinta shine yake neman tagaiyyarata ci gaba tayi da tafe hannu tayi ta kara tambayar ZAINAB sata fa?" Daga mata kai ZAINAB kawai tayi, ta cigaba da kukan da takeyi duk maganar da sukeyi MARIYA na tsakar gida tana jinsu,a sanyaye itama Hajiya Rukaiyya tacewa ZAINAB toh kiyi hakuri ki barshi kizo mu tafi kawai mu kaishi ai baza'abar yaro hakaba" toh ZAINAB tace ta dauko hijjab hadi da rungumo ANAS ta rufo kofar dakin nata"suka rankayo har MARIYA sai da ta sakashi cikin motar kawar tata, sannan ta juya tace mata bari nayiwa makofciyata sallama" toh Hajiya Rukaiiya tace mata kawai ta bude mota ta shiga tana jiranta" , juyawa tayi da saurinta ta cewa MARIYA muje gidan su Haiidar ko nayi musu sallama,ta shiga ta bayar da ajjiyar MARIYA hadi da yi musu sallama,ta dawo ta bude motar kawar tata ta shiga,ita kuma taja mota suka dauki hanyar asibiti, sai da sukayi nisa sannan Hajiya Rukaiyya ta dan nisa ta kalli ZAINAB da cewar wai yaran nan duk sun daina zuwa Makaranta ne?"murmushi ZAINAB tayi da cewar yace bazai iya biya musu kudin makarantar ba, ta gwamnati ya mayar dasu,ita madin ya daina biyan komai nasu nice nake biya toh nima yanxu ta ritso banida kudin shine dalilin da yasa basa Makaranta,wallahi kawata banida jari jarina duk ya kare banida yadda zanyi,shine dalili, ko jiya da kikayimin maganar na saka manya cikin maganata da babansu nayi nayi,abin yakiyi Ke kisan yadda nake da shi a dacan ban taba tsamanin zai min abinda yake min a yanzu ba, daga ni har yarana,amman babu yadda zanyi da halayyar da ya sauya min, naje na sami iyayenshi akan suyi masa fada,wallahi goya masa baya ma sukayi da cewar ai bashida sarari wanda ni nasan ba haka bane son zuciya ne irin na wasu iyayen mijin, da na dawo na sake yanke sahwarar naje na sanarwa da nawa iyayyen domin su shigo cikin lamarina amman abin duk yaci tura sun kirashi dan jin abinda nake masa yace babu komai, anyi mana fada gaba daya kamar zai gyara amman ya sake komawa kan halinshi wallahi kawata yanxu tsakanina da BABAN ANAS babu abinda ya sani nawa sai bukatarshi zuwa gareni,kinga kuwa dole zan fita hayyaci na,duk lokacin da naje gida hakuri ake bani, ace na dawo kan yarana ,nima duk lkc da so mu rabu idon yaran nake kallah sai naji na kasa tabuka komai a kanshi Amman yanxu tausayin yaran ya fara gushewa daga zuciyata domin bansan me zanyi ba, matukar hakan ba hakuri ne ba,kawata" nisawa hajiya Rukaiyya tayi da cewar kawata babu komai kedai ki cigaba da hakurin da ake cewa kiyi ai baya karewa, shiru ZAINAB tayi hadi da goge kwallar da ta cika mata ido ta amsa da cewa insha Allah kawata zanyi komai kike cemin,a haka dai suka cigaba da tafiya har suka zo dai_dai inda danja ta tsayar dasu suka tsaya nan fa ZAINAB ta dan bude glass din gefenta sakamakon dan zafin da aka fara na dagawar hantsi tana budewa taji ana kiran Sunanta daga motar da take gefenta takara lek'o da kanta tayi domin ta tabbatar ita din ake kira ko wa? Tana dubawa sai ta hango mai kiran nata hakan yayi dai2 da basu hannu da danger tayi domin su wuce, da sauri ta cewa Hajiya Rukaiyya kisan mai kirana kuwa?"A'a tace mata hadi da cigaba da tukin motarta tana kallon gabanta,"ZAINAB tace ai HAFSAT AL'AMEN ce a motar, kaminta karasa maganar tuni ta zo saitunsu ta yi ma Hajiya Rukaiyya nuni da su sami guri suyi parking nan fa suka dan tsaya a gefen hanya suka gaisa hadi da tambayar su ina zasu?"ZAINAB ce ta amsa mata da cewar zamuje kai yaron wajena asibiti ne"da sauri HAFSTA ta leqa sit din dake baya motar ta gano ANAS da yake a kwance yana ta faman bacci, kallo daya HAFSAT tayiwa ZAINAB ta tabbatar ko ba'ace mata komai kanta ba tasan tana cikin wani hali komawa tayi cikin tata motar ta dauko jakar hannuta ta bude ta debo kudi masu yawa ta mikawa ZAINAB hadi da kara jajanta mata rashin tafiyar ANAS din godiya tayi mata, a lokacin Hajiya Rukaiyya itama ta kara saka baki a maganar tasu tayiwa HAFSAT godiya, har sun juya zasu koma mota ta kira sunan ZAINAB hadi da tambayar ta number wayarta tace ko dan sanin halin da kike ciki Sosa k'eya ZAINAB tayi da cewar ai banida waya a hannu na yanxu,mamakine ya kara kama HAFSAT da cewar toh bari na baki card dina duk duk lkc da kika sami dama sai ki kirani ta miqa mata, ZAINAB ta karba ta rike hadi da kara yi mata godiya, sukayi sallama ta shiga motar ta suma suka koma tasu suka dauki hanyarsu ta zuwa asibiti. Basu wani kara bata lkc ba suka karasa wani karamin clinic wanda suka shiga suka karbi kati a inda suka wuce sunga likita ya duba ANAS da kyau inda ya sanar musu cewar ba wani ciwo ne mai tsanani ba, garkuwar jikinshi ce tayi laushi sakamakon rashin samun wadatacan abinci mai gina jiki, hakan shine yasa yake yawan zazzabi mai zafi, cikin kwarewa Dr ya rubuta musu magunguna karin jini da na cin abinci da basu shawara akan su ringa bashi abinci mai gina jiki,suka amsa hadi da yiwa Dr godiya suka fito gurin zama Hajiya Rukaiya ta nuna ma ZAINAB da cewar ta zauna ta jirata taje ta sayo magungunan da Dr yayi umarnin su saya......


*Comments dinku shi zai sa insan kuna son Inci gaba da rubuta muku wannan labarin*








~AMENAT KABER KIRU~





*KARUWAR GIDA*



*STORY WRITEEN BY✍*


*AMENAT KABER KIRU*

*SADAUKARWA GA:*

*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*



*TSOKACI*

*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.Duk wanda yaga abinda bai masa ba yana da kyau ya bude shafin zagina k'ofa a bude take domin karbar hakan daka ko waye zagi d'an zagawa ne nasan baya tabo🤷‍♂azagi kowa normal ne🤪*


*🅾2⃣*



Amsawa ZAINAB tayi da toh, ta sami d'aya daga cikin kujerun da suke gurin ta zauna hadi da rungume ANAS," ita kuwa Hajiya Rukaiyya pharmacy dake cikin asibitin ta nufa kai tsaye domin sayo magungunan da aka rubuta musu," tafiyarta kadan ZAINAB ta fada duniyar tunanin baya yadda rayuwar ta kasance tsakaninta da mijinta uban 'ya'yanta wanda take kallon a matsayi sanyin idon ta a wancan lkc ba yanxu ba,tunawa tayi da irin soyayyar da ta nuna mishi had'i da bashi kulawa haka shima daga nashi 6angaren sam baya son abinda zai bata mata zuciya,rayuwa ce mai ban sha'awa mai cike da kaunar juna tunda ZAINAB ta auri RABI'U bata taba kai k'ararshi ba haka shima bai taba kai tata k'arar ba sai lkc da ta sami cikin MARIYA ne aka fara samun matsala domin kuwa cikin yazo mata da wani irin yanayin laulayi mai daga hankali komai taci sai ta amayar dashi,aman yakan zo matane a ko wanne yanayi babu dare babu rana,wannan ce tasa RABI'U ya fara tsanarta da hantarar ZAINAB a ko wanne lkc hakan ce tasa duk abinda ZAINAB ta ta6a RABI'U baya iya amfani dashi ga k'yara da hantara a duk lkc da ta fara amaye_amayenta haka zai tsallake ya barta babu tausayawa ya fita , tun abin baya damunta, har ta fara tsangwamar kanta da cewar ko RABI'U ya daina sonta ne? take ta k'aryata zuciyar ta akan abin da take zargi" duk abinda ZAINAB tace tana marmari a matsayinta na mai ciki bazata samu daga gareshi ba, tun tana iya tashi tayi komai da kanta har hakan ta gagara wannan hujjar ce tasa ZAINAB ta nemi izinin RABI'U da ya barta ta tafi gida tayi jinya acan" Katseta yayi da wani wawan mari hadi da daka mata tsawa na cewar ai daman ba d'aureki nayi ba ko an gaya miki cewar zamanki anan yana da wani muhimmanci a gareni ne?" Dafe kumatu ZAINAB tayi hadi da kallonshi cikin mamaki duba da irin yadda ya rufe ido yake ta faman masifa kamar bai san da wacce yakeyi ba ya fice ya barta anan tsugunne kan gwaiwuyinta ,can kuma sai ta tuna ai dole zaiyi masifa duba da yadda ta saba masa da mi'ka mishi jikinta a koda yaushe, kamin cikin ya samu, tayi iya yinta itama wajan taga tana iya jure masa a duk lkc da yaso hakan amman abin yak'i domin kuwa duk lkc da RABI'U yazo kwanciya da ita ji take yana mata wani irin wari wannan ce take k'ara sa ambaliyar amai da zarar ya nemata" shi kuwa sai yake ganin ai ta raina shine hadi da wulak'anci shi yasa ko tausaya mata baya yi a duk lkc da yaganta a irin wannan halin. tashi tayi da k'yar Ta mike ta goge hawaye da yake fuskarta ko wanka batayi ba ta sake kaya ta dauki kudin mota ta nufi gidansu,"tun daga sallamarta mahaifiyar ta tabbatar ba lfy ba, duba da yadda taga ZAINAB cikin tashin hankali hakan ne yabata damar tambayar ZAINAB ko lfy?" Asmwa ZAINAB tayi jiki a san yaye da cewar lfy qlu MAMA, ta tsuke bakinta daga haka ta k'arasa dakinsu inda k'anneta suke, duk suka tashi da murnar ganin yayar tasu"ta amsa fuska babu walwala ta nemi gefen gado ta kwanta ba tare da ta kara cewa kowa komai ba a haka bacci yayi awan gaba da ita." Sanin halin mahaifin ZAINAB da mahaifiyar tata tayi ne yasa ko bin ta kanta bata

Please Login or Register in order to submit comment