Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa ZAINAB ta kashe duk kayan da RUKAIYYA ta bata da kudaden ta Adana, sanna ta shige d'akinta ta cigaba da aikin kukan da ya zame mata jiki, har yara suka dawo daga islamiyya ta basu ambinc tana ta kallon hanyar dawowar RABI'U amman shiru" haka dai ta sake zaman ba tare da ta runtsa ba har aka fara kiraye2 sallah asuba bata ritsa ba mikewa tayi ta tafi ta tafi ta daura alwala tazo tayi nafiloli, da baya ta mike ta kawo farillah bayan ta idar ta kwanta ta rintsa kadan ta fara baccin kenan taji ana bugun k'yauron kofar gida, a firgice ta tashi ta fito ta nufi kofar gidan,tana zuwa ta bude bata jira tambayar waye ba ta bude,ganin wanda yake a tsaye ne a kofar gidan bayan ta bude gidan yasata cikin firgice, domin kuwa shi kanshi a gigice yake lkc da ta ganshi ba wani bane sai UMAR dan mijin RUKAIYYA ne a tsaye ido jawur yace kuka ga murya ta disashe ya ce baki na wara yace AUNTY ......"amsawa ZAINAB tayi da cewar lfy UMAR?" Da kyar ya budi bakin cewar AUNTY na ce Allah ya karfi rayuwata, ko jira batayi ya kara fadeba taci kwallarshi da cewar karya kake wallahi RUKAIYYA ta bata mutu ba garin yaya zaka ce ta mutu menene ya Sameta ka gaya min gaskiya nace ka gayamin gaskiya!!!" ganin ta gigicene yasa ya cire hannuta daga kan kirjinshi, cikin kuka yace wallahi da gaske nakeyi ta rasu !!!!a dalilin bugawar zuciya da yasameta cikin daren jiya!! bayan nadawo daga gurin abokaina ne nashiga domin sake tayata harhade kayan da bata k'arasa hadawa ba shine na sameta akwance tana wani irin nishi da fitar da dafara daga bakinta ,nayi korin kiran likitan da zai dubata ta kamin yazo ta rigamu gidan gaskiya" koda likitan yazo shine ya tabbatar min da dalilin mutuwar tata,tun a daren aka sakarwa da kowa da kowa dangin na kusa da na nesa wasu tuni sun hallara a gidan, ganin ban ganki a gidan ba yasa na taso yanzu na zo gaya miki" wani irin kuka ZAINAB ta sake saki tare da ihu wanda hakan har sai da ya taso makwaftanta suka fito domin jin ihun kukanta, haka suka ringa bata hakuri da" shi kuwa UMAR tunda ya gama mata bayani ya juya gida domin komawa su yi Jana'izar RUKAIYYA( ALLHU AKBAR KABIRAN)." Komawa cikin gida ZAINAB tayi ta tashi su MARIYA tace suje makwafta su jirata zataje gidan rasuwa RUKAIYYA ce Allah ya karbi rayuwarta" su Kansu yaran da suke kananu sai da suka koka bisa maganar da sukaji na rasuwar aminyar mahaifiyar tasu." Amsawa sukayi da toh cikin kuka" itama ta shirya ta fita zuwa gidan rasuwa koda ta k'arasa kofar gidan ta tarar ya cika mak'il da jama'a da kyar ta sami hanyar da ta ra6a ta shiga cikin gidan tana zuwa ta tarra da gawar RUKAIYYA lallibe da zani a kwance a tsayar falon ta" tana budawa ta fada kan kirjita ta na wani irin kuka mai ratsa zuciya, hakika ZAINAB ta gigice da ganin gawar k'awarta ta sosai ta girgiza mutar ta domin kuwa gani take tamkar ita kade akayiwa mutuwar" nan fa mutane da yan uwan RUKAIYYA suka janye ZAINAB da kyar sannan a ka dauke gawar akayi mata wanka aka hada ta domin kaita makwancin ta,sai da aka dauke gawar aka fitar da itane ZAINAB ta k'ara yinkewa da maganar mutuwar RUKAIYYA gaskice domin da duk gani take tamkar mafarki take" wanna ne ya k'ara hasgitsa tunaninta da nutsuwarta domin gani take itama tata tazo k'arshe tunda ta rasa iyayenta bata kallon kowa a matsayinsu sai kawarta RUKAIYYA yau itama Allah ya amshi kayarshi," subatu ZAINAB ta riga yi mai ban tausayi babu wanda bai tausayawa ZAINAB ba a gidan mutuwar nan" domin kuwa kaiwa take tana kawowa tana surakatai tana juya hannu kamar wacce take shirin zarewa" ganin haka ne yasa wasu daga cikin matan da suke gurin suka kama ZAINAB suka zaunar da ita aka dinga yi mata nasiha da bata hakuri har ta ta lafa da subatun da takeyi" amman sam taki daina kukan da takeyi yaki tsayawa domin kuwa jinta take tamkar tsirara take a rayuwata ta duniyar yanzu" haka dai tacigaba da kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi matuka" ana ta bata bakin tayi hakuri"...............

~AMENAT KABER KIRU~



*KARUWAR GIDA*


*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*

*SADAUKARWA GA:*
*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*


*TSOKACI*
*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*

*GAISUWAR BAN GIRMA*
*_TA MANYAN HAMSHAK'AI MANDIYOYI BILKISU ABBAS SA'ID KIRU DA UMMU FATI MUTANE SAUDIYYA, BAN MATA DA KE BA UMMU ABDULLAHI KD,MMN AHMED KD (BAGOBIRA) MY SISTER UMMU MUHAMMAD, GA IRIN TAKU🤙_*


*1⃣1⃣*


Haka dai ZAINAB ta gaji har ta hakura. Tunda ta fara zuwa gidan karbar gaisuwa RUKAIYYA har sai da akayi sadakar bakwai da ita amman har a wannan lkc RABI'U bai dawo gida ba tun abin baya damuna har ya fara damunta haka tai ta rama da k'arewa a tsaye duka goma da goma" sai da RABI'U ya cika sati biyu Chif a waje ba tare da ya lek'o gida ba sannan ya dawo" koda ya dawo bai fasa halinshi ba haka zalika bai tausayawa ZAINAB halin da take ciki na rashin da ta shiga ba haka yayi ta kunsa mata taikaici na yau daban na gobe daban. Allah sarki duniya mai yayi haka ZAINAB ta kasance cikin rayuwar ban tausayi ga rashin kwanciyar hankali da miji"

Akwana a tashi RUKAIYYA ta cika wata hudu da mutuwa anan ne fa rayuwar ZAINAB ta k'ara tuzarta da wulak'anta domin kuwa idan ba kallon tsanaki mutum yayi mata ba zai ganeta ba duk da dacan din ma ba dadi take jiba amman da dama2" shiga d'aki tayi tana kwaso yan kayayyakin ta nasawa wadanda suka rage mata masu daraja a cikin werdrop dinta kawai sai ta arba da wata takada rubuce da number waya an rubuta HAFSAT AL'AMEN da sauri ta k'ara juyata takardar domin kuwa ta manta da ita tsawan lkc wanna da sauri ta janyo hijaf dinta ta ratayashi a wuya ta fita sai makwafata ta fada tare da yin sallama" makwafciyarta ta amsa" ko gaisawa ZAINAB ta jira sunyi ba ta tambayi makfciyarta ta ko wayarta da kati?" Amsawa tayi da cewar eh da kawai hadi da miko mata wayar kai tsaye" ZAINAB tasa hannu ta karba" tana karba ta fara latsa lambubin da suke rubuce a takardar da take hannunta cikin hanzari kamar wani zai kwance wayar tana gama loda lambobin ta tura kira hadi da karawa a kunneta,ta nasawa taji ta shiga sai tana k'ara amman ba d'aga ba har tagaji da gunji kiran ya yanke ba tare da an d'aga ba,haka ZAINAB ta sake kokarin sake tura kiran a karo na biyu har sai da ta kusa katsewa sanann taji an daga da cewar hello" jin haka yasa ZAINAB itama tayi sallama aka sake amsawa da tambayar wayem?" Da sauri ZAINAB tace nice ZAINAB ABDUL dan Allah ko da HAFSAT AL'AMEN nake magana?" Wata dariya taji an sakar mata da cewar eh itace shegiya kawata sai yau zaki nemeni ai nayi fushi"da sauri ZAINAB tace ko kadan wallahi tun lkc da kika bani number na rasa inda na jefa ta shine dalili yanzu ma da kika kirana wallahi banfi mutu biyu da ganinta ba cikin kayana shine dalilin da yasa na nace bari na gwada naji ko zata shigo" amsawa tayi da cewar OK karki damu ai komai yin Allah ne, yanxu gashi ya nufeki da ganinta kuma kinyi sa'ar ta shigo kashe na kiraki"ZAINAB ta katse layin" HAFSAT ta sake bugowa hadi da tambayar ZAINAB da cewe wanna ne layin naki na ajje shi" girgiza kai ZAINAB tayi kamar tana ganinta da cewar a'a banida wata ai har yanzu"wani tsaki HAFSAT ta saki da cewar ban gane ba, bakida ra'ayine ko kuwa lalacewa tayi?" A'a ZAINAB tace babu d'aya daga ciki banida ita ne gabaki d'aya"mamakin ya kama HAFSAT daga can bangaren da cewar daman har yanzu akwai wadanda basuda wayar hannun a wannan lk duk saukinta? haba kawata karki bada mata mana" murmushi ZAINAB ta yi da cewar k'awata kenan ai nima ba haka naso ba" tamabayarta HAFSAT tayi da cewar toh lefin waye gayamin? Da kina da ita ai da gaisawa batayi wuya ba.sun dade suna hira anan ne ZAINAB ta sanarwa da HAFSAT rasuwar RUKAIYYA nan HAFSAT ta jajantawa ZAINAB bisa rashin da sukayi da cewar insha Allah gobe zatazo da yamma da zarar ta gama uzuririkanta" ba karamin dadai ZAINAB taji ba domin kuwa hakan ya nuna a sarari" amsawa tayi da cewar babu damuwa Allah ya kaimu goben"HAFSAT ta masa da amen"sannan sukayi sallama juna ta yanke wayar ta."itama ZAINAB ta mikawa makwafciyarta wayarta tayi godiya"ta amsa da babu damuwa"ZAINAB ta fito ta koma gida zuciyarta cike da farin cikin albishir din da taji daga bakin k'awarta wacce suka rabu tun tsawan lkc. Haka dai ZAINAB ta zauna tana ta jiran kashe garin ranar tazo kamar ta k'arawa lkc gudu,har dare haka takai tana jiran tsammanin gari ya waye." A wanna daren ne kuma ZAINAB ta k'ara fadawa tsaka mai wuya domin kuwa a cikin daren ne ANAS ya farka da wani irin mugun ciwan ciki haka yayi ta murkusu!!"ba ZAINAB ba hatta MARIYA da take yarinya sai da ta kokawa ANAS din" sakamakon yadda taga yaron yana wata irin zambarma hadi da koka mai ban tasauyi"ga gida babu namiji domin kuwa yanzu RABI'U sai ya ga dama yake zuwa gida ya dubasu babu abinda ya damesu da a wanne hali suke yana can yana sharholiyarshi ba tare da yasan halin da iyalanshi suke ciki ba." Haka dai ZAINAB da MARIYA sukayi kwanan zaune ba tare da d'ayansu ya ritsaba,a ranar ZAINAB taci kuka kamar idonta zai tsiyaye sabida tsakanin kuka da tunanika iri da kala, domin kuwa a daren RUKAIYYA ce ta bijiro mata domin kuwa tasan ita kayiwa mutuwa ba kowa ba,hakika da tana raye tasan tashin hankalinta kadane koda zatayi bazai kai kamar wanda take ciki ba" haka dai tai ta tuna al'kairin RUKAIYYA gareta lkc da take raye." A haka har gari ya dauko waye was sannan ANAS ya samu ciwon ya dan lafa masa yayi bacci" ganin ya rintsane yasa ZAINAB tashi ta gabatar da sallolinta sannan ta dawo tacewa MARIYA itama taje tayi tata sallah" toh tace sannan ta mike ta fita"bayan ta dawo tayi sallah itama ta koma ta kwanta ta koma bacci domin ta dan rintsa." Ita kuwa ZAINAB tashi tayi bayan ta gama lazimi ta shiga kitchen ta huwara wuta domin Samar musu abin kalaci a gurguje"bayan ta gama ta daura musu ruwan wanka,ta koma ta tashesu ta sannan ta fito da ANAS ta fara yi masa wanka"bayan ta gama masa ta umarci MARIYA da taje tayi nata wanka" toh tace" ta fita cikin k'aramin lkc ta dawo" ZAINAB ta hada masu abin kari sannan ta fita ta yi shara itama ta shiga nata wankan batafi muti sha biyar ba ta fito ta dan goga mai kadan sannan ta saka yan kod'add'un kayanta ta zauna tana nazarin yadda zatayi da ciwan ANAS duk da ya farka jikin nashi da sauki amman dai ta firgita matuk'a domin kuwa ko kudin chemis batashi bare na motar da zata hau taje ta kaushi suga likita" haka dai ta zauna tana ta sake2 a zuciyata babu amsa daga k'arshe dai ta mika wuya ga Allah tana kallon hanyar domin sauraron zuwan bakuwarta."
Karfe goma dai2 HAFSAT ta yiwa gidan ZAINAB tsinke domin kuwa kugin tsayawar motar HAFSAT ce tayiwa kunne ZAINAB tsine koda bata leka ta gani ba amman tasan babi wanda zaizo kofar gidan ta a wannan lkc da mota har kofar gida, domin kuwa mai zuwa da motar da can RUKAIYYA ce kuma Allah ya karbi kayarshi" da sauri ta mike tsaye daga inda take zaune tun tsawan lkc domin kuwa Jin sallamar HAFSAT tayi a tsakar gida" cikin farin ciki da murna ta fito ta tafi da gudu ta rumgume k'awarta ta,hadi da yi mata sannu da k'arsowa"amsawa HAFSAT tayi hadi da daukan kafadar ZAINAB da cewar yimin a hankali k'awata kar ki kayar dani" murmushi ZAINAB tayi da cewar wace ni? Na kayar da manya irinku" dariya HAFSAT tayi da cewar ke kuka bakya ganin takalman da na sako ne?" Sai a wannan lkc ZAINAB ta kula da uban tsinin takalmin da yake kafar HAFSAT domin kuwa tsininshi ya kai tsini matuk'a gashi da kyau da walwali kalashi daya da yar karamar jakar hannuta wanda ta cikashi da awarwaron gold da zubuna suna duk na gold kai tsayawa ma lissafa tsaddadun kayan jikin HAFSAT 6ata lkc ne." ZAINAB ca tacewaw ZAINAB oh yi hakuri ai sam ba kula ba kisan abinka da wanda idonshi ya rufe da ganin k'awarshi sam bazai kula da abida yake a gabanshi ba" murmushi HAFSAT ta k'ara yiwa ZAINAB da cewar ai na lura kin shiga da yawa k'awata farin cikin ki yaki 6uyuwa a fuskarki naga alamar hakan" amsa ZAINAB tayi da ko? Toh mushiga daga d'aki man,kya cigaba da yankata k'awata" amsawa HAFSAT tayi da cewar ba wani yanka muje dai" ZAINAB ta shiga gaba HAFSAT na biye da ita a baya tana k'ara yiwa gidan kallon tsanaki tana mamakin yadda ZAINAB take iya rayuwa a cikinshi kuntattace ga rashin iska ga wani irin kauri da take Jin yana taso mata kamar ana k'ona taya ga wasu tarin kayan wanki daga can gefe abu dai babu dadi kallo" ZAINAB ta lura da irin kallon da HAFSAT takewa gidan amman ta share har suka shiga d'aki ta shifida mata sallaya tace mata ta zauna"nan fa HAFSAT ta k'ara tsinkewa da lamarin da ZAINAB take ciki sai da taga d'akin da take ciki babu uwar komai sai tari shirgin tsumo karan da suka cikashi" zama HAFSAT tayi akan sallaya ta kalli ZAINAB da cewar k'awata ya kwana biyu toh?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar sai kairan ,hadi da cewar bari na debo miki ruwa duk da dai har yanzu da sauran safiya" amsawa HAFSAT tayi da cewar a'a basai kin debo ba wallahi na gode, zauna muyi hirar ta abota ta kalli ZAINAB" zauna ZAINAB tayi tana fuskantar HAFSAT da cewar k'awata wallahi nayi mamakin ganinki a wanna yanayin domin kuwa da wani ne ya gayamin cewa zanyi k'arya ne ke kuwa yaushe kikayi auren da har zaki mayar da kanki tsohuwar dole? haba k'awata karki bayar da mata mana, ina RABI'U yana kallonki haka kika lalace kuma baiyi yun kurin yi miki magana ba ke kuwa?" Murmushi ZAINAB tayi da cewar ai shine ma silar lalacewar komai nawa da kika gani" amsawa HAFSAT tayi da cewar kamar yaya? Yanzu fisabilillahi shine zai zauna yayi miki gyaran gida da na daki da sauran kulawarka da duk ta dace?" Hmmmm kawai ZAINAB tace sanna ta dora da cewar da dai banyi niyyar gaya miki hujjar hakan ba, amman yanxu tunda har kina gani baki yadda ba toh bari kiji dalilin da yasa nace hakan kwashe lbr komai da yake guna tsakaninta da RABI'U tayi tun daga lkc da ta fara samun matsala da shi har kawo wannan lkc da take ciki duk wata cutarwa da yake mata ita da yara babu abinda ta boyewa HAFSAT har zuwa yau da take bata lbr" koda ZAINAB tazo karshen lbr ta ta dago ido domin tambayar HAFSAT meye nata laifin sai tayi arba da ita tana ta faman zubar kallah da share majina" bude baki tayi da kyar ta cewa ZAINAB sannu a gaskiya ko kwatar hakurin da kikayi ni bazan iya ba amman ki barshi idan yasan wata, ai biasan wata ba ,ba dai shi karuwan namij ba? toh da hannushi zaiyi nadamar abinda ya aikata miki a rayuwar shi ta duniya" zaro ido ZAINAB tayi da cewar a'a k'awata nifa tsoro gareni domin wallahi RABI'U ya wuce inda kike tunani ni dai ki rufa min asiri" amsawa HAFSAT tayi da cewar ai rufin asirinki kenan ki tashi tsaye tun kina raye basai takaici ya kasheki ba,irisu zuma ne sai da wuta, idan kina ganin zai baki matsala kiyi k'arshi zuwa kotu mana"sake zaro ido ZAINAB tayi da cewar kin manta da sharad'in da nace miki MALAM tayi min tun kamin ya rasu?" Amsawa HAFSAT tayi da cewar haka naji kince a cikin lbr da kika bani,toh ya zame miki wajibi tunda girmanki, ki samarwa kanki mafita tun kamin dare yayi miki domin hausawa sunce mace kamar ruwa take idan aka tsare mata hanya sai yiwa kanta, dan haka ki shirya d'amarar yak'ar bakin ciki d'a namiji daga zuwaciyar ki" wani dogon numfashi ZAINAB tayi da cewar toh ta yaya k'awata" hmmmm HAFSAT ta fara cewa sanna ta budi bakin tace toh ki zama karuwar gida mana domin yanzu wanna harka ita ce Sana'a mafi sauki domin majority matan yanzu ita suke dalili kuwa a matan da suke gidajan aure25% ne suke zaune da mazajen su lfy sauran duk rubabine kinga kuwa idan nace miki 75% karuwar gida ne kar kiyi mamaki domin maza basuda tabbas sune silar jefa matansu zuwa ga neman kudi ko ta halin k'ak'a" dafe k'irji ZAINAB tayi da cewar haba kawata sam wannan kalmar bata kamaceki ba domin wannan shawarar taki sai nake ganin bayi ba" amsawa HAFASAT tayi da cewar OK sai ki zauna zafin sha'awa ya kasheki da taikaicin d'an namiji wallahi kawata sam baki san yadda rayuwa ta juya bane" wani sabon numfashi ZAINAB ta k'ara saki da taji maganar HAFSAT kamar al'mara ta rasa bakin magana" ganin haka yasa HAFSAT tace ai k'awata ko dan ki rama abinda RABI'U yayi miki kya aminta da magana ta kuma ai karuwanci gida shine domin kuwa ko cinki aiki babu wanda zai gane tunda da aurenki,ke nifa wallahi matsalar da na samu da nawa mazajan sam bata doshi irin taki ba amman na nuna bazanyi zaman auren ba akan me zan zauna takaici ya kashe ni?shine dalilin ma da kika ga yanxu banida aure karena nake ci babu babbaka banida wanda zai matsamin nayi" amsawa ZAINAB tayi da cewar gaskiya k'awata bazan iya ba" jin haka yasa HAFSAT fusata tace ai sai ki zauna takaici ya kasheki!! hadi da mikewa ta bude Jakarta ta zaro kudi yan dubu2 ta mikawa ZAINAB hadi da yi mata sallama tace ta tafi" karba ZAINAB tayi tai mata godiya ta kara da tambayarya sai yaushe?"tabe baki HAFSAT tayi da cewar sai na sake samun time zan kewayo ku" godiya ZAINAB ta k'ara yi mata sanna tayi mata rakiya har zaure.

Shikuwa RABI'U tunda ya 6usa yaga da jini ai can ya tare gurin JAMCY ko waiyayar ZAINAB bayayi daga ibedi sai garesu na gyaran mota haka rayuwarshi ta sauya ko tsoran Allah bayayi bare tausayi maraicin ZAINAB" suna zaune a garejin su masu aiki nayi masu hira nayi irin wacce aka saba ta yau da kullum,guda daga cikin su ya nisa da cewar kai bari na tashi na shiga kasuwa tun kamin na shagala da hirar na" farat kuwa RABI'U ya amsa da cewar me zakayo a kasuwa yanzu? kamar wani mace" amsawa tayi da cewar wallahi tunda zan fito iyalina ta sanar min da cewar kayan abinci mu sun taho k'arewa"shine yanxu na tuna da maganarta toh kaga ai na hanzarta naje na sayi komai tun kamin dare yayi ko?" Wata dariyar mugunta RABI'U ya saki ya kalli na gefenshi da cewar kaji mutumin ka fa wai har wani rawar jikin shiga kasuwa yake madam ta gaya masa kayan abinci ya kusa k'arewa amman dan shine kaluluwa sarkin d'oki bazai jira ya k'are din ba amman kaji zaije ya sake sayo wasu"wancan ya bushe da dariya mugunta yace ai kasan mijin tace ne" mik'o hannu RABI'U yayi suka tafa yace wannan bai san mata ba abin tausayi bane wallahi ai mace tsakani ka da ita shine ta biya ma buk'ata malam amman da zarar ka nuna kana tausayinta babu d'an iska rinka kasan Allah ni dai yanzu a gidana bazan iya sayan kayan abinci da za'ayi sati ana ci ba" mikewa wancan din yayi da cewar oga RABI'U duk naji dalilanka dan haka kayi rayuwarka da iyalainka yadda kaga dama, nima ka barni nayi yadda nake so ya juya ya barsu ya tafi" yana juya suka sake kallon juna suka bushe da dariyar RABI'U ne har da cewar a haka zaka k'ara d'an wahala.


Ita kuwa ZAINAB tunda HAFSAT tabar gidan ta take ta tunanin maganar ta hadi da jinjina al'amarinta na ko kadan bataji nauyi irin shawarwarin da take bata ba? Wanna ai gurguwar shawarce ta yaya ma za'ace ita din tayi hakan, domin a ganina tuni mahaifinta yake guje mata faadawa rayuwar da batada ammafani,a tunanishi rashin aurene yake haddasawa ashe ba anan gizon yake sak'ar ba.........

~AMENAT KABER KIRU~






*KARUWAR GIDA*

*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*


*SADAUKARWA GA:*
*_HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMED)_*


*_Kuna Raina Kamar kudin haya yasen🤾‍♀_*
*yadomma mohmd Bello,my zuk,Sadiya I. Baso matar kirki, zainab sarki Mustapha Kiru, zainab b. Sani kiru(ta rabe), 🤭yar yola karuwar gida fans,Fatima Abubakar abaza life,Hauwa'u Umar Mohammed karuwar gida fans, Abdul h2, my bro amaccid'o Abubakar, Yaya hayat, Bashir sardauna mashek'i & mawasgi😜Ina gaisuwa kamala Bala yaron kirki Ina yinku over Kuna k'albina😘🥰*


*12*

Kadai ZAINAB ta wani tana juya maganar HAFSAT a zuciyarta............ Domin kuwa yanzu abin ya wuce tunanin duk wani mai tunin"haka dai ta yini tana jinana maganar Kawarta ta. "Allah sarki rayuwa (Ina ya Allah babu ya Allah sarkin iko da buwaya k'asaitaccan sarki gagara misali) a cikin wannna daren ranar ne Allah ya sake sakkowa da ANAS cutar ciwan ciki ya sake damk'arshi haha dai ZAINAB ta sake kwanan zaune har gari ya waye basuyi bacci ba daga ita har yaron " Kamin gari ya waye ANAS ya suka kusan sau hudu zuwa biyar wannna ce tasa ZAINAB ta Kara rikicewa da shiga rud'u domin batayi tsammanin ciwan nashi har zai kaishi ga suka ba" k'agara tari gari ya waye domin ta kaishi asibiti"tun ZAINAB tana kuka a sarari har yakita da tana na zuci domin kuwa ji tayi ruwan idonta ya dauke baya iya zubowa ko kadan, haka dai tai ta zarya da yaron a hannuta daga d'aki zuwa tsakar gida"a haka har gari ya waye.....


Gari na wayewa ta shirya ta fita domin Kai ANAS asibiti" tana zuwa cikin gwaugawa likitoci suka kar6eshi ba tare da sun tsaya neman wani bayani daga bakin ZAINAB ba."domin kuwa tana shigowa dashi cikin asibiti ya sake someway, wanna ce tasa aka wuce dashi emergency domin duba lfy sh"wani irin kukan zuci ZAINAB takeyi domin kuwa ta rasa yadda zatayi sau kinda MA Allah yasa jiya HAFSAT ce ta Bata kudin da tazo asibitin dasu wannna ne ya takaita tashi hankalinta"shi kuwa ANAS tun bayan da aka tafi da shi dakin gwaugawa likitoci ne suka taro akanshi domin ceto lafiyar shi"bayan ya farfado daga suman da yayi ne babba Dr yace ta kaishi dakin bincike na musaman domin yana son ya k'arayin bincike akan matsalarshi duba da yadda cikinshi yayi wani irin girma Kamar ba cikin k'aramin yaro ba." gani an sake fito dashi daga 6angaren da aka kaishi yasa ZAINAB tayi saurin zaburowa daga inda take zaune tana tamabayar likita da cewar Dr ya jikin nashi? "kallonta yayi Shima cikin tausayawa yace ai yaji sauki zamuje dashi d'akin bincike na musamman ne domin sake dubashi dan gano asalin matsalar shi" amsawa ZAINAB tayi a hike a sanyaye da cewar toh Dr Allah yasa a gane din" amsawa yayi da cewar amen" Sanna yaruba yabi bayan k'ananun likitoh cin da yabasu umarnin sukai mass ANAS din d'akin bincike"bayan sun shigar da ANAS din suka daurashi a Kan gadon daya daga cikin gadajen da suke d'akin Kai tsaye sukai wa ANAS (x_ray)watau hoton cikin ya dauka"Kamin wani lkc Dr ya fitar da

Please Login or Register in order to submit comment