Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina da magana da kai" amsawa yayi da uhmmm sai ki fada naji" shiru ta d'anyi sannan tace daman wasu tambayoyi ne zanyi ma idan bazaka damuwa ba" toh kawai RABI'U yace ina jinki bana son takura da hana bacci" nisawa tayi da cewar daman naga ka k'ara sauyawa ne bisa yadda na sanka dan Allah idan akwai laifin da nayi ma ka sanar dani, nayi al'k'awarin gyarawa, bana jin dadin zaman mu a haka ba ni kadeba harta yar da muka haifa baka kulata wanne laifin nayi da har ya shafeta haka?" Wani guntun murmushi ya saki wanda bai kai zuci ba, sannan yace tunda har kina neman sani yanzu saki san dalilin sauyawata, a gaskiya bana zaman k'arya da ko waye ZAINAB ya kamata ki san da hakan, why not zanyi miki bayanin abinda nake so tun kamin muyi aure amman ki kasa?" Na sanar miki ni ba mutum ne mai son tara iyalai ba amman kin kasa daukan mataki,ko kinason kullum sai na gaya miki kamar karatu?" A gaskiya ZAINAB bazan boye miki ba matuk'ar kinason zama dani toh ki dauki mataki akan duk abinda nakeso ayimin shi,baya yuwa matan waje mu kafa musu doka subi amman matarka ta gida ka gaya mata tak'i bin umaranin ka,idan kin shirya daukan matakin sai ku sanar dani gobe muje a cire cikin da yake jikinki nan" wani gumine ya dinga zubowa daga fuskar ZAINAB tunda RABI'UN ya fara bayanin bata tsinke da al'amarinshi ba sai akan kalma biyu watau matan waje da cire cikin jikinta" nisawa tayi da cewar gaskiya bazan iya cire, cikin da yake a jikina ba dalili kuwa duba da yadda cikina ya gota wata tak'was ya shiga na tara a gaskiya koda daga waje nayo bazan iya haka ba bare d'ansinnah" kuma kana maganar daukan mataki ai babu wani bawa da ya isa ya k'etare k'adararsa, banga dalilin daukan mataki ba,a maganar shigar ciki tunda kudurar Allah ce!!" Murga mata wata uwar harara yayi da cewar sai kije kiji da kudurar Allah ke k'ade basai na kara kusantar kiba ma bare hakan ta faru!!" Aikin banza kawai ga matacan masu jajayen cinyoyi a waje, kwanciya sai irin yadda yakaso akeyi ma ita, ni ina zan zauna ina batawa kaina lkc akan matar da bata ilimi zamantakewar rayuwa?" Ya juya ya kwanta yana ta faman zazagawa ZAINAB bak'ak'en maganganu" taji bakin cikin maganganunshi matuk'a" Wani kukan bakin ciki ZAINAB ta rushe da shi mai fauna zuciya da tausayawa, mik'ewa tayi ta koma gurin kwanciyarta tacigaba da yin kuka a haka ta yi mai isarta ta gama har kusan asuba bata rintsa ba,haka bata sami shawarar yadda zatayi da RABI'U ba,dalili idan ta daka ta tashi akeje cire ciki ta mutu fa? mai zata gayawa ubangijinta"domin kuwa tasan ba'ayiwa abokin hallita biyayya a sa6awa mahallici, ta dai barwa zuciyarta ta rabu dashi har zuwa lkc da zata haife cikin kinga ayi duk maj yuwa" koda gari ya waye tan tangarau RABI'U yana ta kwasar bacci abinshi, yi ZAINAB tayi kamar bazata tashe shi ba, yadda MARIYA take ta kukan neman abinci kari,ta duba kuma basuda sauran kayan tea wanna hujjar CE tasa ZAINAB kasa jurar kukun MARIYA,dole ta nufi har inda yake RABI'U yake kwance ta ta6ashi a hankali tace ya tashi gari ya waye har karo uku, amman yana jinta, sai daga ta koma na karo na hudu ya sanar mata wani irin wawan tsaki" ko kadan bata ji bata jira ya kara cewa wani abu ba ta ce masa dan Allah ka tashi MARIYA ce take ta kukan zata sha tea shine dalilin sake dawowata" tashi yayi ya zauna ya bude idonshi tas sannan ya kalli ZAINAB da cewar anki a sayo kayan tea din, ke dakata kiji daga yau an daina shan tea a wannan gidan indai da kudina ne ban hanaki idan kinaso ki saya ba sai ki bata" mamakine ya kama ZAINAB bisa furucin RABI'U gareta, yi tayi kamar bazata tanka ba,daga kashe tace kana ganin hukunci da kaynake yayi dai2 kenan?" Amsawa yayi da cewar wannan kuma ruwanki nidai nagama duk abinda yake hannu ki bata taci ni ba shashabane da zan dinga asabar kudina akan wanna 'yar tsigigiyar yarinyar" shiru ZAINAB tayi ta fice ta bashi guri ta tafi ta nemawa MARIYA abinci da zata iya ci a keching mai sauki," ganin ta fita shima ya tashi yaje yayo alwala yayi sallah ya fice bai ko yi mata sallamar tafiya ba. Haka ta nemi dan abinda taga MARIYA zata iya ci ta dafa mata cikin irin kayan ganar da aka kawu musu,tun ZAINAB tana daukan halayen RABI'U da wasa,kamar zai sauya amman ina sam,ko abinci ta dafa ta kawo sai ya lankwasa chukalin domin ya lalace da wuri" inda RABI'U yaso arziki ya bata cefenan da zai ishesu Ita da 'yarta shi, idan yaso tsiya ya hana wanda zai isa, ZAINAB tasha kwanciya da yunwa ga tsohun ciki,amman RABI'U ko a jikinshi haka ZAINAB tayi ta fama da halinshi na yau da ban na gobe da ban'' har cikinta ya isa haihuwa. Tun yamma ZAINAB take jin ciwo mara yana karta mata amman haka ta daure tayi abinci dare tanayi tana hutawa, har ciwo yaci karfinta ta koma d'aki, daga ita sai k'aramar 'yarta haka ZAINAB ta haihu wajan sallah magariba ta sami santalelen d'anta namiji kyakykyawa dashi, babu kowa a kusa da ita haka taci murkusunta ta gama, ga ba waya a hannuta bare ta buga waya gidansu ta sanar da mahaifiyarta ta haihu, yunkurawa tayi da kyar ta sani bero da takkada tayi rubutu a ciki ta bawa MARIYA 'yarta duba da yake yarinya CE mai wayo tace tayi maza ta kaiwa makwafciyar ta" karba tayi tana murna ta fita da sauri duk da tafiyar yaro babu sauri amman kai da ganin yanayin tafiyar kasan itadin sauri takeyi" bata fi muti biyu da fita ba sai gashi sun shigo tare da makwafciyar tasu, ita kanta tayi mamakin juriyar da ZAINAB tayi har ta bari ta haihu ita kade ba tare da ta sakarwa kowa ba,sannu yayiwa ZAINAB hadi da jinjina mata bisa namiji kokarin da tayi na haihuwa ita kade!" Murmushi kawai ZAINAB tabita da shi domin batada ta cewa" k'ara lek'a jaririn tayi da cewa sannu ZAINAB kinsha aiki" amsawa ZAINAB tayi da yawwa ta sunkuyar da kanta k'asa" nan da nan makwafciyar ZAINAB ta cire hijab din ta kama aiki dora gawarwar wanka, bayan ta gama ta shigo ta fitar da duk kayan da ZAINAB ta bata da jini taje ta wanke sannan ta dawo ta goge d'akin tas ta samu gwaurashin wuta ta saka turen k'anshi, sanna ta yiwa baby boy din wanka, data gama ta cewa ZAINAB ta bayar da kaya asaka masa" nan fa ido ya raina fata domin tunda ta sami cikin ko wando RABI'U bai saya ba, bai kuma bata kudin da zata saya ba domin tanaji" mikiewa tayi ta dauko tun irin na MARIYA da ta rage ta bata haka tace asawa baby kamin yadawo ya sayo musu" kar6ar kayan kawai makwafciyar tata tayi ba tare da tace komai ba tasawa yaron ajiki ta kwantar dashi sanna ta mik'e ta koma keching ta juyewa ZAINAB nata ruwan wanka ta dawo ta sanar mata ta juye ruwan wankan" toh amsawa ZAINAB tayi da toh ta gode" mikewa tsaye tayi da k'yar sanna tayi shirin shiga wanka" inda tabar makwafciyar tata a d'akin tana k'arasa gyara inda ta tashi" bata jima a bayi ba tayo wankanta ta fito" ta gyara jikinta kamar ba ita ba,ganin haka yasan makwafciyar ta koma gida ta dauko kayan baby boy masu kyau sat biyu ta bawa ZAINAB" godiya ZAINAB ta k'ara yi dayatayi a sanna ta roketa aron wayarta idan akwai kudi a ciki zata kira gidansu ta sanar ta haihu"amsawa tayi da cewar akwai sanann ta mikowa ZAINAB wayar tata" ZAINAB ta sa hannu ta kar6a ta latsa lambar mahifiyar ta, bugu d'aya tayi aka daga kiran nata daga can bagaren Sallama ZAINAB tayi"mahaifiyarta ta amsa da cewar lfy dai ko?" Amsawa ZAINAB ta k'arayi da lfy qlu suka sannan ta sanarwa mahaifiyarta ta tasauka lfy" murnace ta kamata acan 6agaren hadi da mik'awa Allah godiyar ta a sarari' sannan ta tambayi lfy ZAINAB din da jariri"ZAINAB ta amsa da cewar lfy su lau" yanke wayar ZAINAB tayi ta k'ara latsa lambar mahaifiyar mijinta, itama ta dauka suka gaisa bayan gaisawa ZAINAB ta sanar mata ta haihu, murnace ta karad'e duk ka gidanje guda biyu kamin wani lkc gida ya ciki da yan uwa, basu bar gidan ba har bayan insha,magaifiyar RABI'U kuwa zama tayi da cewar sai zuwa safiya zata tafi ba zata iya barin ZAINAB ita kad'e a gidan ba,jin RABI'U shiru bai dawo ba har tsawan dare yasa mahaifiyarshi tambayar ZAINAB ina yaje ko yayi tafiya ne bai je ya sanar musu ba?" Murmushi ZAINAB tayi kamin ta bawa surukarta amsa,sanna tace ko kadan inaga aikine ya rik'eshi tunda kika ga haka" mata da miji sai Allah sam ZAINAB bata nunawa mahaifiyar RABI'U haka yakeyi ba gudun kar tajawa kanta wani sabon bala'in da yafi wanda take ciki a halin yanzu" sun dade suna hira kamin bacci ya kashe ZAINAB duba da yadda ta k'ago tayi baccin daman duk tagaji tunda akayi haihuwar bata kwanta ba. Barin surukarta ta tayi zaune inda ta kama bacci abinta,ita kuwa zama tayi domin ganin lkc da d'an nata zai dawo" ta kwashe tsawan mutuna a zaune bayan baccin ZAINAB har ta fara gyangyad'i ita kanta sannan taji motsin shigowar RABI'U ko sallama babu zubur tayi ta farka da cewar waye?" Jin muryar mahaifiyarshi ne yasa yaji wata irin fargaba kad'an sallama yayi a kofar d'akin da suke ciki, amsawa mahaifiyarta shi tayi" ya shiga ya durkusa har k'asa ya gaisheta,ta amsa fuskarta cike da annuri tace masa daga ina haka?" Sosa k'eya yayi kadan da cewar ina gareji tun d'azu wallahi wata mota aka kawo min gyara gaf da zamu rashi daga aiki toh kuma mai ita zainyi sanmako da ita zuwa MAIDUGIRI shine na tsaya na sallameshi duba yadda motar ta wahalar damu,banda abokin harka ne ai da bazan tsaya nayi dare haka ba" murmushi mahaifiyarta shi tayi da cewar tunda ka sallameshi ai shikenan haba nayi mamakin ace tunda akayi haihuwar nan babu dadewa nazo gidan amman banga gelminka ko sau daya ba?" Nayi magana ZAINAB tace aikine ya rik'e ka kunyi waya ita kamin na k'araso" sosa k'eya RABI'U yayi da yaji mahaifiyarshi tana gaya masa yadda sukayi da ZAINAB ya amsa dacewar eh wallahi"karbar maganar tashi tayi da k'ara nuna damuwar ta akan rashin shigowa tashi tayi da cewar" dalilin da yasa na kasa bacci na zauna jiran shigowar ka kenan" tashi RABI'U yayi da rawar jiki kamar da gaske ya dauko jaririn da yake kwance a kusa da ZAINAB da take ta faman ware baccin gajiya" kallon yaron ya dinga yi yana shafa sumarshi" har wani lkc suka kai shida mahaifiyarshi suna shawarar yadda komai zai gudana bai mata musu ba ya amsa da cewar Allah ya kaimu zuwa safiyya duk za'ayi abinda kika lissafa" ta amsa da Amen itama" yayi mata sallama ya mike ya tafi shiga k'aramin da yake kusa da na ZAINAB ya kwanta. Ka shegari tun asabar fari ya baro k'aramin dakin da kwana ya dawo wanda ZAINAB take tare da mahifiyarshi suka gaisa da mahaifiyar shi cikin kulawa da girmamawa, fuskarshi cike da fara'a kamar bashi ba,ya k'arasa ihar bakin gadon da ZAINAB take zaune"ganin haka yasa mahaifiyar tashi fita daga d'akin tace zataje ta keching ta duba abincin karin da ta daura musu" amsawa ZAINAB tayi toh mama"shi kuwa zaunawa yayi a gefen gadon da ZAINAB take zaune shima hadi da mik'a mata hannu ya k'arbi jaririn da yake hannun ta" mik'a tayi ba tare da ta kalleshi ba,ya kar6a yayi masa huduba sanna ya cigaba da rikonshi a hannun tsawan mutuna bai bawa ZAINAB yaron ba,sam batayi mamakin hakan daga RABI'U domin tafi kowa sanin waye shi din da zarar yaga idon mutane, makirine na k'arshe idan ana maganar karuwa a cikin maza toh RABI'U yana daga cikin kuruwai maza tabas baya ta6a barin wani bakon fuska ya fashinci irin zaman da yakeyi da ZAINAB," jin tayi masa shirune yasa shi tamabayarta da cewar ko taba buk'atar wani abu?"shiru ZAINAB tayi hadi da tamske masa fuska"yasan me ZAINAB take nufi dashi,tana son nunawa mahaifiyar shi akwai damuwa kenan" nunawa yayikamar baisan tanayi ba, ya fuske ya k'ara tamabayarta a karo na biyu" kamar bazata amsa ba, jin motsin dawawar mahifaryashi yasa ta saki fuska da cewar duk abinda ya samu,bata k'ara ce masa komai ba tayi shiru dashi" ya mike ya yayi wa mahaifiayashi bayanin sunan da ya yiwa yaron huduba dashi watau ANSA murmushi tayi da cewar haka Allah ya ciyar dashi kenan?" Amsawa RABI'U yayi da cewar eh ai tun jiya ban kwanta bacci ba sai da na kira wayar ABBA na shawarce shi, shine yace ya banmin za6in sunan da za'a saka.........


~MAENAT KABER KIRU~





*KARUWAR GIDA*



*STORY WRITEEN BY✍*


*AMENAT KABER KIRU*

*SADAUKARWA GA:*

*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*



*TSOKACI*

*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*


_not editing📵_

*🅾6⃣*


Wa yaro" d'adine ya k'ara kama mahaifiyarta shi dacewar toh Allah yaraya manashi bisa sunnah" amsawa RABI'U yayi da amen, kamar gaske yana sunkuyar da kanshi k'asa kamar wani muminin gaske" duk abinda suke tattaunawa tsakanin mahaifiyar mijin nata da shi kanshi RABI'U ZAINAB taba jiyosu daga d'akin rana sauraron wani takaici ne yake ta cinta a inda take zaune ji take kamar ta fito ta zaiyanawa mahaifiyarta duk halin da suke ciki,can wani shashi na zuciyata ya kwa6eta da cewar karki zama silar rushewar farin cikin da mahaifiyarshi take ciki a halin yanxu,kuma kina ganin duk abinda kika sanar mata zatayi amanah da hakan?"ki rabu da harkar d'a da mahifi kawai."Wata ajiyar zuciya ZAINAB ta sake wanda har sai da yakai kunneh mahifiyar mijina nata da shi kanshi RABI'U" atare suka shiga d'akin ZAINAB din da saurin su,hadi da tamabayrta ko lfy?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar lfy lau" wani kallon tuhuma RABI'U ya biya shi" hakan ce tasa ZAINAB tsuke bakinta ba tare da ta kara cewa komai ba, rarrashinta surukarta ta ta shiga yi da cewar haba ZAINAB ki zuba wannan uban tagumi haka ga gajiyar zuciyar da kikayi wallahi sai da tasa hanyar cikina kad'awa,akan me zaki dami zuciyarki?" bayan Allah yasa kin haihu lfy,ai sai ji gode masa bisa ni'imar da yayi miki ,ko kinajin wani ciwo ne?" Sai a lkc ZAINAB ta girgiza kai alama babu wata damuwa,shi kuwa RABI'U tsayawa yayi ya kafeta da idanu hadi da yi mata muzurai duk a nashi tunanin yana yi mata barazana"shiruce ta ratsa tsakanin su tsawan mituna ganin haka yasa RABI'U sake budar baki shima yayiwa ZAINAB tambayar cewa idan kawai abinda yake damunki ki fad'a a kira likita ko muje asibiti" amsawa ZAINAB tayi da cewar babu abinda yake damuna" jin haka yasa RABI'U yiwa mafiyarshi magana ko da k'arin abinda suke so banda wanda ta lissafa masa a daren jiya domin fita zaiyi" amsawa tayi da cewar inaga shawarar da mukayi ai tayi" sai dai ko ka tambayi ZAINAB ko tana da wani abinda zaka sayo mata" juyawa yayi ya sake kallon ZAINAB da cewar kina buk'atar wani abune ne? Inason zanje nayo muku sayayya" zanwa ZAINAB tayi da cewar babu wani abu duk abinda ka sayo babu damuwa" toh kawai yace da cewar sai nadawo" ZAINAB ta amsa da Allah ya tsare"yace amen" mahaifiyarta shi ce ta k'ara jefa masa tamabaya da cewar tun yanxu zakafita bazaka jira ka karya ba?" Ya amsa da cewar eh inason zanje banki ne na ciri kudin bana son bin dogon layine ,sabida inason shiga kasuwa da wuri,"toh kawai tace masa hadi da yi masa fatan dawowa lfy" amsawa yayi da cewar sai Allah yasa ya fita." Yana fita kai tsaye banki ya fara wucewa kamar yadda ya sanarwa da mahifiyarshi" bai wani dade akan layi ba duba da safiya mutane basu fara ciki bankin ba ya cire kudinshi masu yawa sanann ya tari dan adaidata sahu ya ka k'arasa dashi kasuwa" yayi siyayya kamar ba gobe har da abinda ba'a lissafi masa ba ma sai da ya sayo tun daga kan kayan baby har zuwa na MARIYA ita kwanta kala goma ya sai mata kama daga dogayen riguna zuwa masu dogon wando, ko wanne sat da takalmi, sanna ya juya kan na ZAINAB mai jego itama haka ya sai mata kaya har kala goma kama daga atamfofi zuwa les da shadda da material',har da takalma itama da jakarsu da mayafai" ita kanta mahaifiyar tashi bai barta haka ba sai da taci arzikin haihuwar da aka yiwa RABI'U kai abin ba'a magana domin drop din mota ya dauka ta kaishi har kofar gidanshi da wanna kayan haka ya rika daukar su d'aya bayan d'aya yana shiga dasu,sai da ya gama shigar dasu ya dawo ya sallama driver ya koma ciki" tunda mahaifiyashi ta ganshi niki2 da kaya ta dinga washe baki yak'i rufuwa kallon mamakin sayayyar da RABI'U yayi har da ita domin ko haihuwar ko haihuwar fari da akayi masa baiyi siyayyar da ta zarce hakan ba, nan fa ta shiga samasa albarka" yana amsawa kamar da gaske" ita kuwa ZAINAB tunda ya fara shiga da kayan batayi mamaki ba domin tasan halin RABI'U dan yaga idon duniya zaiyi sama da hakan bare yaga idon mahaifiyarshi,murmushi ZAINAB ta ringa saki mai kamar yak'e, domin kuwa idan zata shekara fad'an aibun mijinata ga mahaifiyarshi ba yadda zatayi ba." Yana fita kai tsaye banki ya fara wucewa kamar yadda ya sanarwa da mahifiyarshi" bai wani dade akan layi ba duba da safiya mutane basu fara ciki bankin ba ya cire kudinshi masu yawa sanann ya tari dan adaidata sahu ya ka k'arasa dashi kasuwa" yayi siyayya kamar ba gobe har da abinda ba'a lissafi masa ba ma sai da ya sayo tun daga kan kayan baby har zuwa na MARIYA ita kwanta kala goma ya sai mata kama daga dogayen riguna zuwa masu dogon wando, ko wanne sat da takalmi, sanna ya juya kan na ZAINAB mai jego itama haka ya sai mata kaya har kala goma kama daga atamfofi zuwa les da shadda da material',har da takalma itama da jakarsu da mayafai" ita kanta mahaifiyar tashi bai barta haka ba sai da taci arzikin haihuwar da aka yiwa RABI'U kai abin ba'a magana domin drop din mota ya dauka ta kaishi har kofar gidanshi da wanna kayan haka ya rika daukar su d'aya bayan d'aya yana shiga dasu,sai da ya gama shigar dasu ya dawo ya sallama driver ya koma ciki" tunda mahaifiyashi ta ganshi niki2 da kaya ta dinga washe baki yak'i rufuwa kallon mamakin sayayyar da RABI'U yayi har da ita domin ko haihuwar ko haihuwar fari da akayi masa baiyi siyayyar da ta zarce hakan ba, nan fa ta shiga samasa albarka" yana amsawa kamar da gaske" ita kuwa ZAINAB tunda ya fara shiga da kayan batayi mamaki ba domin tasan halin RABI'U dan yaga idon duniya zaiyi sama da hakan bare yaga idon mahaifiyarshi,murmushi ZAINAB ta ringa saki mai kamar yak'e, domin kuwa idan zata shekara fad'an aibun mijinata ga mahaifiyarshi ba yadda zatayi ba" Bare kuma wani wanda baiga san RABI'U da wata muguwar halaiyya ba' wannan ce take k'aryawa ZAINAB zuciya akan duk lkc da tayi yunkurin tunkarar iyayen mijin nata halin da take ciki da d'ansu."

Abu kamar wasa haka RABI'U ya dinga jifgowa ZAINAB kayan bukatun gida tun kamai ranar suna ta zagayo babu wani abu da bai ajjiye ba a gidan duk wani abinda yasan za'a nema sai da ya tanaza.Tun daga lkc da akeyiwa suna mahaifiyarshi bata bar gidan ba har sai da ZAINAB ta gama wankan jego a cewar ta gara ta bari kwarin jikin ZAINAB din ya dawo" ko kadan RABI'U da ZAINAB basu sake samun sa6ani ba haka ya dinga bawa ZAINAB kulawa ita da yaranta guda biyu watau MARIYA da ANSA dan jariri" sai dai tun bayan suna aka fashinci ANAS bashida koshin lfy" ko kadan RABI'U bai ta6a gajiyawa da sayan magunguba ,ko kai shi ganin likita."Duk wani hali da mahifiyarshi zata gani na banza ya dainasu kamar bashi ba,hatta kaiwa daren da yakeyi duk dainawa yayi" mahaifiyarshi tana tafiya ya ciki gaba da gasawa ZAINAB gajiya a hannu" sauki da ZAINAB ta samu d'aya ne babu wani abu da zata nema dag RAB'U sai yarjewarshi zuwa kai ANAS asibiti" duk ranar da yaga dama ya barta ko kuma ya hanata" hatta yawo daren da yakeyi ya dawo da yin abinshi." Haka ZAINAB ta cigaba da hakuri da yanayin da RABI'U ya koma duk dan abinda yake hannuta haka ya tasama k'arewa dole ce ZAINAB sake shiga cikin wata damuwar" shi kuwa ko kadan baya kallon ZAINAB a matsayi mace tunda ta haihu gashi har ta tasama wata na uku da haihuwa, yanke shawara ZAINAB tasakeyi na tun karara mijinta ko dan ssauke nauyin da yake kanta nashi" tasa ZAINAB zaman jiranshi a wannan dare,koda ya dawo tayi masa sannu da dawowa"ya amsa a ciki kamar baisanta ba,ko kadan ZAINAB bata kiyeyeshi ba,sai da ta shigar da buk'atarta ta bashi hakkinshi" wata harara ya wurga mata da cewar Ashe ganin buzu a masallaci bazai sa tunkiya taji tsoran Allah ba?" Ke wai waje mara fashinta ce? Nace miki ina buk'atarki ne? Ko nace miki ina sha'awar kwantawa da ke ne?" Ni banza ne kenan da zan k'ara kusantarki"ai tun daga lkc da nace miki muje a cire cikin wannan yaron kika k'i naci alwashin daina kwanciya da ke" wasu zafafan hawaye ne suka ziyarci kumatun ZAINAB hadi da zafin rai dana zuciya"yi tayi kamar taci kwalar RABI'U tace ya saketa kawai ta huta,sai ta tunda da maganar mahaifinta na cewar ko da wasa taja sanadin da mijinta ya saketa ko bayan ya mutu bai yafe mata ba" wannan hujar ce tasa ZAINAB mik'ewa tsaye tsam ta har kusa da RABI'U ta kuma yiwa kanta al'k'awarin ko zafin sha'awa zai zama shine ajalinta bazata k'ara zuwa gareshi ba itama" Ganin haka yasa RABI'U shima ya fita a rayuwar ta" duk abinda ya zama wajinbinshi ya daina bata sai yaga dama kama daga sabulun wanka da na wanki da dai duk wani kayan tsafta wanda ZAINAB zatayi amfani dashi ya daina bayarwa tunda yana ganinta dasu,kuma bai ta6a tambayarta waye wake kawo mata ba." Ko kadan ZAINAB bata gaban RABI'U abin har ya dain 6ata mata rai da zuciya' fatan ta Allah ya dawo dashi kan hanya a kullum addu'ar ta kenan.

ZAINAB na cikin wanna gallazawar ta mijinta Allah ya saukar mata da maraicin rashin iyaye duk biyu dare daya,hakan ya farune sakakon annobar amai da guduwa da ta sami iyayen nata cikin daren da bazata ta6a mantawa dashi ba!!! ZAINAB tasha kuka ita da k'anneta da suka ragemata kamar basu daina ba". Haka dai sukayi ta kuka har suka hakura" bayan an k'are saman makokine dangin mahaifin ZAINAB da na mahiafiyar ta suka raba k'anneta a tsakaninsu,ranar ne ZAINAB ta k'ara tsikewa da labarin duniya!! Tun kamin kowa ya watse aka yanke shawarar zuba yan haya a gidan mahaifin ZAINAB din" kowa ya aminci tsakanin dangin duba da MALAM bashida d'a namiji babba duk mutuwa suka ringa yi,sai daga kan ZAINAB 'ya'yan nashi suka fara zama"gashi har sun koma ga Allah basu sake samun haihuwar namijin ba.
Haka dai aka yanke shawara,kowa ya amice ZAINAB tasha kuka mai isa gani za'a tafi da k'anne nata danginsu"ba iya ita ba hatta dayan sunyi kukan suma duk da ba wani wayo suka cikaba" haka dai suka

Please Login or Register in order to submit comment