Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'arayi ba domin ba nisa yayi ba tasan da zarar yazo ya sameta tare da ZAINAB din zaice tana kitsa mata wani abune na rashin arziki tunda tun farko sai da ta nuna bata son ZAINAB ta auri RABI'U amman ZAINAB ta k'ek'ashe idonta da cewar shine za6in zuciyar ta." ZAINAB bata fi minti talatin da kwanciyar ba mahaifinta ya shigo inda mahaifiyarta ta sanar masa cewar ZAINAB tazo"da kanshi ya k'arasa har kofar d'akin da take kwance yayi sallama yasa d'aya daga cikin k'anneta su taso ta,a firgice ZAINAB ta tashi domin tasan mahifinta mutune mai a k'idar gaske baya daukar raini, fitowa tayi da sauri wanda yayi dai2 da tashin zuciyarta nan fa ta dinga amai babu k'auk'autawa ganin haka shine ya hana mahaifinta yin fad'an daya saba. Ya koma dakinshi kai tsaye da cewar idan ta natsa yana jiranta ta sameshi can" kai kawai ZAINAB ta daga alamar toh ta cigaba da yin aman a inda ya barta. Mahaifiyarta yi tayi kamar bazata kawowa ZAINAB dauki ba, sai da taga abin ya ta'azarra sanna ta baro inda take zaune take aiki ta zo kanta domin tallafa mata" a hankali ta janyeta daga inda take ta samo ruwa da tsumma ta gyara wajan sanna ta sake komawa ta hada ruwan wanka takai mata band'aki, a sanyayye ZAINAB, ta mik'e tayi wanka,ita kuwa mahaifiyar tata dakin yaran ta koma ta kara gyrawa sannan ta koma kan aikin da takeyi, ta fahinci halin da ZAINAB take ciki watau na samun cikin nata ko daga yanayin sauyawar walwalarta da kuma daukewar da jikinta yayi ga uwa uba amai da takeyi," wannan ne ya tabbatar mata cewar yar tata ciki gareta., Ba wani 6ata lkc ZAINAB tayi ba wajan wanka ta fito ta koma dakin k'annen nata ta takure, kunun tsamiya mahaifiyar ta damo mata ta shigo ta bata tace tasha"ba qaramin dadi kunun yayiwa ZAINAB duba da yadda ta kasance cikin rashin jin dadin bakinta, a hankali ta ringa shan kunun sai gashi ta shanye shi kamar wasa ga mamakinta kuma batayi amai ba, ganin ta sami natsuwa ne yasa mahaifiyar ta, shigowa ta sanar mata da cewar taje mahaifinta na jiranta" amsawa ZAINAB tayi da toh ta tashi ta nemi hijab dinta ta saka ta bi bayan mahaifiyar tata dakin mahaifinta ,tayi sallama suka amsa mata" zaune ta sameshi mahaifin nata yana duba littafin addini, ya taso akan son yawan karatu k'ananun littafai na addini, sai da yakai k'arshen karutunshi ya dago ya kalli ZAINAB da cewar na tamabayi mahaifiyarki ko lfy kika zo gida? Tace min bata san dalili ba shine nace kizo naji daga gareki" amsawa ZAINAB tayi cikin rawar baki da cewar daman banida lfy ne shine na taho" kallonta ya k'arayi cikin ido da cewar uhumm?" Tai shiru a karo na biyu" Ko RABI'U ne yace kizo gidan? Ta girgaza kai", ya k'ara da cewar toh mekike nufi? Tayi shiru nan fa ya ringa yi mata fad'a kamar zai doketa hadi da cewar shi gidanshi ba'a isa a ce anyo yaji har an zauna ba" dan haka ta tashi ta shirya ta koma dakinta, ganin yadda mahaifin ZAINAB yake ta fada babu sauki ko daga k'afa hakan ne yasa mahaifiyarta bata saka baki a maganar ZAINAB ba." Hakan ce tasa ZAINAB dole ta sake kamo hanyar dawowa gidan RABI'U gwaiwa babu kwari ta dawo,ko data dawo haka rayuwa ta cigaba da tafiya a tsakaninta da mijinta yau da dadi gobe babu, gashi tana tsoran taje gida ta Sanar a haka dai har cikin ZAINAB ya isa haihuwa bata tsinke da al'amarin RABI'U ba sai a wannan daren da zata haihu da ta rok'eshi da magiyar yaje ya sanar da mahaifanta halin da take ciki" ya amsa, fita yayi ya nemi mai mashin ya daukeshi yaje gidan su ZAINAB yayi sallama a lokacin yayi sa'ar mahaifinta ya dawo daga masllaci ya sanar masa da cewar ZAINAB tana gida tana nak'uda aje kanta, da sauri malam AUDU watau mahaifin ZAINAB ya koma ya sanarwa da mahaifiyarta halin da ZAINAB take ciki hadi da yi mata umarnin ta shirya taje gareta," toh kawai tace a hanxarce ta koma dakinta, ta dauki hijab, " bai tsaya jin ta bakin matarshi ba yasake dawowa kofar gida domin neman shawarar sirikin nashi kan yadda za'ayi da ZAINAB ga mamaki yana fitowa baiga dan mashin da yakawo RABI'U gidansu ba bare RABI'UN mamaki ne ya rufeshi amman sai ya kawo ko firgicine hakan tasa ya koma cikin gidan domin kara SA mahaifiyar ZAINAB tayo hanzari su tafi tare, A soron gidan yayi kaci6us da mahaifiyar ZAINAB din yace mata yawwa kin taho?" Ta amsa da cewar eh" yace hanzarta muje na rakaki mamakine ya kama mahaifiyar ZAINAB ganin yadda MALAM AUDU ya keta rawar jiki, batayi tsammanin hakan daga gareshi ba tunda tasan mutum ne mai tsatsauran ra'ayi" tafiya suka cigaba da yi har suka k' arasa titi motar ta ratsa ta tsakiyar unguwar tasu, suka yi sa'ar samu mai texi din da zai kaisu unguwar da ZAINAB take, a hanya ne MALAM AUDU ya roki mai motar ya taimaka ya kaisu har kofar gida yar tasu da sanar mishi halin da suke cikin ya tausaya musu matuk'a driver, sanna ya karfafa musu gwaiwar zai taimakesu zuwa gidan yar tasu." ita kuwa mahaifiyar ZAINAB jinsu kawai takeyi amman bata fashintar maganar da malam yakeyi da driver sabida hankalinta baya tare da ita, har suka k'araso kofar gidan yar tasu," koda sukazo a bude suka sami kofar gidan ZAINAB kamar yadda sukayi tsammani, kaitsaye mahaifiyar ta kutsakai cikin gidan bata tsaya jiran umarnin mai gidan na taba, sallama tayi tun daga tsayar gidan amman shiru har ta kusa k'arasawa d'akin Sai taji ZAINAB ta amsa da k'yar hakan ne yasa ta k'arasawa cikin dakin da saurin inda ta sami ZAINAB kwance cikin jini kware_kaware a gigice ta dagota tana yi mata sannu,kai kawai ZAINAB ta d'agawa mahaifiyarta, da sauri ta jinginar da ita jikin gado takoma waje wajan MALAM AUDU domin ta sanar mishi halin da ZAINAB take ciki" tana fita ta sanar mishi, tambayarta ya farayi da ina sirikinshi?"amsawa mahaifiyar ZAINAB tayi da cewar ai babu kowa a gidan sai ita kad'e mamaki ne ya kama MALAM AUDU amman sai kuma yayi tunanin RABI'U ko yaje kiran likitane" duk abinda akeyi driver taxi din nan yana tsaye bai tafi ba, yana jiransu ya ji idan asibitin zai kai su toh ya jirasu" nuni MALAM AUDU yayiwa matarshi da cewar ta koma ciki gashi nan zuwa"komawa mahafiyar ZAINAB tayi ba tare da tacewa mijin nata komai ba' tana shiga sai ga mai gidan nata ya shigo shima ya shigo har tsakiyar d'akin ZAINAB din bai jira wata_wata ba ya kalli matar tashi da cewar HALIMA mai zamu jira garinyi?" Ai kawai kamomin ita muje asibiti tunda naga alamar tana jin jiki"toh kawai mahaifiyar ZAINAB tace domin ta dade bataji mai gidan nata ya ambaci sunana ta, sabida tsabar kawaici" daukanta sukayi chas har mota suka sakata,sanna mahaifiyar tata ta dawo ta gidan nata ta dauki zannuwa ZAINAB ta janyo d'akin nata ta fito ta fad'a mota,shigar su mota ke da wuya sai ga RABI'U ya dawo da sauri MALAM AUDU ya fito ya tareshi da cewar munzo gidan ne tunda nazo bamu ganka ba,gashi ZAINAB tana buqatar taimakon gaggawa shine zamu kaita asibiti" yak'e RABI'U yayiwa MALAM AUDU hadi da juya yar bak'ar ledar hannushi da cewar babu damuwa, kuje kawai zan biyo bayanku, bari na shiga na ajje ledar hannuna daman magani naje sayo mata"toh kawai MALAM AUDU yace ya koma mota a tunaninshi abinda RABI'U ya fada gaskiya ne,suka ja mota suka tafi amman ko lek'awa baiyi yace wa ZAINAB y jiki ba" haka suka nufi asibiti suka kai yar tasu babu RABI'U babu dalilinshi bare bare wani nashi duk da dare ne" a haka har Allah yasa ZAINAB ta haihu lfy ta sami santaleliyar budurwa duk da tsammaninsu ko RABI'U bai sami abin hawan da zai hayo ba tunda dare ya shura, MALAM AUDU ya buga wayar RABI'U arufe daga baya ya yanke shawarar bari ya jira gari ya k'arasa wayewa ya kira ta mahifin RABI'U ya sanar mishi, haka Kuwa akayi domin MALAM AUDU yana fitowa daga masallacin asibitin ya latsa lambar mahaifin Yayi sa'ar mahaifin na RABI'U wayarshi na bude yayi sallama a ka amsa daga can 6angaren ,bayan sun gama gaisawa ne cikin girmamawa sannan ya sanarwa da mahifin sirikin nashi cewar ZAINAB ta haihu tun daren jiya ta sami mace amman suna asibiti tare da ita,yayi murnar matuk'a shima mahaifin RABI'U sanna ya k'ara da cewar basuda labarin rashin lfy tata, domin kuwa d'an nasu bai sanar musu ba,koda mahaifin RABI'U yazo kan wannan maganar sai MALAM AUDU ya nuna mishi babu komai hadi da sanar mishi da sunan asibitin da suke watau SAUDAT clinic wanda yake bayan katangar B.U.K a nan unguwar kabuga Jan bulo daman nan ZAINAB ta sanar musu tana zuwa awon ciki, anan k'awarta RuKAIYYA SHITU ta sami aiki shine har ta bude mata file anan," basu wani bata lkc ba suma iyayen RABI'U suka hallaci asibitin da kayan baby kaca_kaca nan fa dangin suka shiga yiwa juna murnar haihuwar da ZAINAB tayi, amman har a wannan lkc gogan naku baizo asbitin ba bare yazo yaji halin da ake ciki, duk gwaje_gwajen da za'ayiwa ZAINAB da baby anyi sanna aka sallamesu daga asibitin kai tsaye ZAINAB gidatan aka mayar da ita ta bakin mahaifin nata, wai bayason wata bid'ar tafiya gida wanka hakan baiwa mahaifiyar ZAINAB dadi ba,amman su iyayen RABI'U sai sukaji dadi kalmar MALAM AUDU domin kuwa suna ganin baya kyau tuwa ayi sunan surukar tasu a gidan iyayaenta, tunda daga asibiti MALAM AUDU yayi ma su mahifin RABI'U sallama yace zai koma gida ya shirya yaje kauye domin sanar da danginshi ya dauko wacce zata kula da ZAINAB wajan yi mata wankan jego godiya, suka k'ara yi masa da yabawa bisa hallacin da yayi musu sannan ya tafi,. Ita kuwa mahaifiyar ZAINAB kafarta kafar yarta har gidan ta,inda suka rankawa tare da iyayen mijin ZAINAB din ,suka tarar da RABI'U yana gidan yanata sharbar bacci abinshi har wannan lkc,mahaifiyar ZAINAB batayi mamakin abinda yayi musu ba tun daga daren jiya har kawo safiyar yau din" shi kanshi RABI'U tashi yayi a kunya ce bisa ga abinda yayiwa iyayen matar tashi, koda ya fuskanci basu sanarwa mahaifanshi ba sai ya marzaye idon shi kamar bashi yayi wannan rashin mutuncin ba. Da mahaifiyar ZAINAB da tashi, haka da sauran dangin haka suka hadu suka gyara ZAINAB da babynta kana suka gyara komai wanda ya lalace tun farkon fara nak'udar ZAINAB ta fara a gida" daga k'arshe mahaifiyar ZAINAB tayi musu sallama itama ta koma gida domin ta sanarwa nata dangin da mak'ofta cewar ZAINAB ta sauka lfy, "Tana isa gida ta fara aikawa makwaftanta cewar ZAINAB ta sauka lfy" nan fa gida ya cika da jama'a duk da ba ta sami natsuwar da zata aikawa da sauran danginta da suke nesa ba,amman anyi mata kara iya mutuk'a" shi kuwa MALAM tun bayan dawowarshi daga asibitin shima gida ya dawo ya shirya ya tafi kauye su watau GULU domin sanar da yan uwanshi cewar ZAINAB ta haihu lfy, ko da ya isa ya sanar musu da hakan sunyi matuk'ar farin ciki da jin yar tasu ta sauka lfy,haka dai sukai ta aikawa 'yan uwansu na kusa ana sanar dasu cewar ZAINAB ta haihu" MALAM AUDU bai baro kauyesu ba sai da yayi duk wata shawara da yan uwanshi kan cewar INNA TALATU ce zata zaunawa ZAINAB tai mata zaman da6aro" sakamakon ita kade ce mace a gurin mahaifan su MALAM AUDU" tana zaman gida ne sakamakon rasuwar mijinta wannan hujjar ce tasa koda suka sanar mata da kudirin yayan nata,batayi musu ba, batada miji bare ta buk'aci jiran umarni" a yammacin ranar suka taho da yayan nata hadi da kayan sha tara ta arziki wanda yan uwa da dangin suka hado aka fara yo gaba dasu kamin su biyo bayan su kashe gari Domin ganin lfy maijego"
bayan saukar MALAM AUDU gida da shi da y'ar uwanshi, gaisawa kawai tayi da matar yayan nata, tayi musu sallama da cewar ta tafi kula da tafiyar yarta watau ZAINAB" zo kaga rawar kai gurin angon karni watau RABI'U domin shima kayayayaki ya sayowa jaririyar da ZAINAB masu kyau da tsada, sai shiga yake yana fita shima kamar bashine yake nuna halin ko in kula da ZAINAB din ba"Ita kanta tayi mamakin yadda taga cikin k'ank'anin lkc mijin nata ya sauya kamar bashi ba".
"Dangin mahaifinta dana mahaifiyarta duk sunzo ganin lafiyarta kashe garin da ta haihu kamin yan suna su zo suna".
Haka dai RABI'U yayi ta hidima shida iyayenshi da sauran dangin da abokanan arziki" Suma a nasu 6angaren dangin mijin na ZAINAB sunyi duk abinda ya dace sannan domin kuwa tunda suka dawo daga asibiti lbr ya ishe sauran danginsu haka sukaita zuwa ganin jaririya da kayayayyakin su na barka"Abufa yakai Abu domin kowa yasan mahaifan RABI'U mutane ne masu kara da zuminci shi yasa duk wanda yaji matar d'ansu ta haihu baya k'asa a gwuiwa sai yazo yaga lfy ZAINAB da 'yart haka dai 'yan uwa da abokanan arziki sukai ta zuwa da abin arzik'insu".
Acan ma gidan su ZAINAB haka iyayenta da danginta suka kawo nasu kayan sha tara ta arzik'in suka kawowa ZAINAB,"
"har akai suna yarinyar taci suna MARIYATU sunan kakar RABI'U ce ta wajan uwa gidan baya yankewa da jama'a wannan ce tasa RAB'IU ya mayar da hankalinshi sosai kan ZAINAB da 'yarsu gudun kar aga wani bak'on yanayi daga gareshi lbr ya sami iyayenshi wannan ce tasa ya mantar da ZAINAB duk wata cusgunawar da yayi mata a baya"..............





~AMENAT KABER KIRU~









*KARUWAR GIDA*



*STORY WRITEEN BY✍*


*AMENAT KABER KIRU*

*SADAUKARWA GA:*

*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*



*TSOKACI*

*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan mu,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan auren mu a wannan zamanin*

*🅾3⃣*

"Ko dan idon k'anwar mahaifin ZAINAB tasa RABI'U ya sauya taku?" haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya ZAINAB da RABI'U cikin basu kulawar gaske, kamar wasa kwanci tashi har yarsu ta cika shera biyu chif babu wani abu na cutarwa da RABI'U ya cigaba da nunawa ZAINAB" bayan an d'auke MARIYA ne zuwa gidan su ZAINAB yaye" RABI'U ya shiga rayuwar ZAINAB da wani salo na nuna kulawa da kyautata mata,baya son yaga wani abun da zai 6ata mata zuciya ko ranta, kullum a gida yake kusan yini ko gurin sana'arshi bai ciki fita ba yana manne da ita"fahintar da ZAINAB tayi na cewar RABI'U d'anson biyan buk'atane da jin dadi daga mace, wannan ce ta bata damar daura dammarar yi masa duk abinda yake so shima," ko kadan bata nuna gajiyawarta akanshi wajan jure masa akan duk wata buk'atuwa tata zuwa gareshi"ko kadan shima RABI'U baya gajiyawa da jikin na ZAINAB domin kuwa hakan yafi so tunda yanxu babu wani abu da zaiyi masa birki 'ya ce an dauke ta,tana hannun kakanninta, abu kamar wasa dai ZAINAB batayi wata biyu da yaye MARIYA ba wani cikin ya sake shigarta haka ta fara amaye_amaye kamar dai lkcn da tasami cikin MARIYA" nan fa RABI'U ya fara jin haushinta had'i da cin zarafinta" kullum fada da masifa babu kama hannun yaro" Haka RABI'U ya dinga gara ZAINAB,daga kashe ya bijiro mata da cewar lallai sai ta zubar da cikin jikinta" ZAINAB kin yadda tayi da kudirin RABI'U" shi kuwa ya fita harkarta" ganin hakan tasa ZAINAB ta shirya ta je gidan iyayenshi domin sanar musu da halin da suke ciki ita da mijinta, koda ZAINAB taje kasa gaya musu tayi duba da yadda dan nasu yake kyauta ta musu tasan idan tagaya musu ba lallai su yadda ba kuma kamar ta ragewa kanta k'imane a idon surakan nata,duk da mu'amalar da yake nuna mata daban wacce yake nunawa iyayenshi daban" wannan ce tasa ZAINAB ta rasa kwarin gwiwar gaya musu komai"sai da yamma likis ta koma gida yammar da bazata manta da ita ba a rayuwar ta ,tana komawa gida ta tsinci kanta a wani irin yanayin mai ban tausayi domin kuwa wani irin jiri ta ringa gani hadi da ciwan kai mai tsanani har wani Kore_Kore take ganin garin yana juya mata, da k'yar ta k'arasa shiga d'akinta ta sami guri ta kwanta,tana faman kiran sunan ALLAH, batafi mutuna goma da shiga wannan halin ba sai ga RABI'U ya dawo gida" yana shigowa ya sameta a wannan halin yi yayi kamar bazai bata agaji ba domin gani yake kamar karya take ganin ciwan nata yana qara ta'azara ne yasa ya budi baki ya tamabayeta ko lfy?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar batada lfy hadi da sanar mishi irin yanayin da take ji" sannu kawai yace mata ya sake kada kanshi waje ya fita" koda ya fita chemist ya wuce yaje ya sayo mgunguna ya kawowa ZAINAB yace ta tashi tasha" a gwaugwauce tasha maganin ido rufe domin ji take kamar ranar zata bar duniya" ALLAH sarki ZAINAB shan maganin nata ke da wuya baifi mitin biyu zuwa uku ba ciwo ya k'ara tsananta tun tana iya fahintar inda kanta yake har ta daina ganewa" tana cikin wannan halin ne jini ya yanke mata ya fara zuba ganin zubar jinice ta kara rikitar da jikin ZAINAB kamin kace wani Abu tuni ta sume a inda take ko motsi ta daina!" ganin halin da ta shigane yasa RABI'U fita daga gidan a gurguje yayi waje ya samu motar da zata kaita asibiti cak ya dauke ta ya fitar da ita zuwa kofar gida ya jefata jikin motar da ya samo ba tare da ya sanarwa kowa ba"da zuwansu aka kar6esu cikin gaggawa duba da irin halin da su kaga ZAINAB na ciki" nan da nan likitoci suka zo kanta aka fara kokarin ceto rayuwarta, cikin k'aramin lkc" koda ZAINAB ta farfado batayi mamakin ganinta a asibiti ba domin tasan komai zai iya faruwa da ita, koda kuwa mutuwa ce a yadda ta tsinci kanta,"ba wani ciwo da yake damun ZAINAB illa rashin kwarin jiki da takeji ko da ta farfado" Da sauri RABI'U ya k'araso kusa da gadon da ZAINAB take kwance yayi mata sannu!" Amsawa tayi ba tare da ta kalli fuskarshi ba tace yawwa! Ta mayar da kallonta xuwa ga silin din dake saman d'akin, suna cikin wannan halin ne wata nurse ta shigo dauke da faranti wanda yake cike da allurori ta k'araso inda ZAINAB take kwance tayi mata sannu hadi da yi mata nunin ta gyara zata yi mata allura" amsawa ZAINAB tayi tare da gyara wa lkc guda,"Nurse din tayi mata allurorin har guda biyu,bayan ta gamane ta kalli ZAINAB da RABI'U a tare ta fara yi musu tambayar menene dalilin da yasa zasu zibar da ciki wanda a sakamakon haka da kyar suka sami ceto rayuwar ZAINAB din?" Kallon2 suka fara a tsakanin su wanda yasa ZAINAB kasa jure hakan domin batasan amsar Da zata bayar ba" shi kuwa RABI'U da yasan komai shima kasa bud'e bakinshi yayi, ya yiwa Nurse bayanin shine ya bawa ZAINAB k'wayoyin da yasa ta cikin ya zube,wani gumine ya fara karyo masa tare da bayyana fargabarshi na furta shine ya bawa ZAINAB maganin a sarari" jin basuda niyya bata amsa yasa ta fara yi musu masifa tare da yiwa ZAINAB gargadi hadi da Jan kunne da nuna mata idan bata son ta dauki ciki kar ma ta bari ta dauka bare har taje tana shan maganin da zai k'arar da rayuwatar"tun kamin takai k'arshen maganarta ZAINAB ta saki salati hadi da wata irin k'ara tana fadin RABI'U ka cutar dani idan baka sona ka sakeni na huta ba sai ka kasheni ba ,ka kashe abinda yake cikina ba!!!" Jin wadan nan kalaman da suke fita daga bakin ZAINAB yasa Nurse din ta tabbatar bada sanin ta cikin ya zube ba, rarrashin ZAINAB ta shiga yi da nuna mata muhimmancin yadda da kaddara" kukane yaci k'arfin ZAINAB da take kwance a kan gado mai ban tasauyi da rikita zuciya" wannan dalilin ne ya hana RABI'U ko motsi a inda yake yana dai kallon su yana kuma sauraron duk abinda yake wakana" banda kugin kukan ZAINAB babu abinda yake tashi a d'akin" jin hakan ne yasa Nurse din tayiwa RABI'U nuni da tafiya waje" amsawa yayi kawai da toh ya fita." bayan fitar shine ta k'ara gyara murya ta kira sunan ZAINAB a hankali" ZAINAB ta dan saurara da kukan da tayi ta amsa da mata" jin dadin hakan Nurse tayi da taga ZAINAB din har ta kawo hankalinta gareta sai ta k'ara yi mata nasiha hadi da rarrashinta da bata shawarwari akan yadda zata kauracewa duk wani abu da zai daga mata hankali dangane da irin hakan idan ya taso, ta nuna mata abu mafi mahinmmanci shine idan kinsan zaki sami ciki da mai gidanki yazo yana baki k'wayoyin da zasu jefa rayuwarki cikin hadari to karki fara daukan cikin ma sai ki dauki matakin daukan baki daya,duba yadda rayuwar nan ta sauya mafi akasarin maza basa buk'atar haihuwa gaskiya abinda nake so na sanar miki kenan ina fatan zaki karbi shawarata?" kai kawai ZAINAB ta daga mata domin kuwa jinta kawai takeyi tunda ta fara maganganunta ita ba fashimta take ba sabida tsananin bugar zuciyar da take ji" fuskantar hakan da tayi daga ZAINAB yasa ta ci gaba da bata bakin tayi hakuri akan duk abinda ya faru da ita"toh kawai ZAINAB ta cewa Nurse din ta kara kwantar da kanta gefe tana cigaba da zubar da hawaye" jin zainab tayi shiru ne yasa nurse ta k'ara tambayar ZAINAB ko tana jin wani ciwo?" A'a zaina tace kawai " hakan ce tasa nurse din fita daga d'akin inda tayi kacibus da RABI'U ya k'osa ya shigo domin kuwa ya kosa a wajan da ya fita shima" Domin kuwa gani yake kamar Nurse din zata matsa ma ZAINAB da tambayoyi shine dalilin kosawarshi"murmushi Nurse din tayi masa hadi da cewar ka gaji ta jirana ko?" Amsawa yayi da cewar ko kadan likita" sake murmushin tayi a karo na biyu da cewar bari na dawo ai yanzu zamu sallameku duba da yadda abin yazo da sauki kuma tace min babu wani ciwo da take ji a halin yanzu wannan dalilin yasa zamu sallameku yanxu amman jirani k'adan dan Allah ina zuwa" toh RABI'U yace cike da gwarin giwar jin kalaman Nurse din" yasa kai ya shiga d'akin fuska a sake kamar bai aikata komai ba" ganin haka yasa ZAINAB tamke tata fuskar a gareshi" yi yayi kamar bai san tanayi ba ya k'ara matsawa kusa da gadon da take kwance hadi da kamo hannunta" fizgewa ZAINAB tayi had'i da dakatar dashi da dayan hannun da cewar dakata MALAM bakada wata magana da zaka gayamin maha'inci kawai" hakan shine yayi dai2 sallama Dr tare da nurse da sukaji yasa tayi shuru amsawa RABI'U yayi fuska a sake" k'arasawa Dr yayi jikin gadon ZAINAB ya duddubata sosai sanna ya karbi katin ta a hannun Nurse din take biye dashi yayi rubuce2 da zaiyi sanna ya mik'awa RABI'U" karba yayi jiki na rawa hadi da yiwa Dr karin godiya" Dr ya amsa hadi da mika masa hannu sanna ya kara jaddada masa cewar lallai yasa yi magungunan da ya rubuta musu sanna ya ringa saya mata kayan fruit wadanda zasu kara mata jini"amsawa RABI'U yayi da insha Allah" sanna Dr ya koma kan ZAINAB da bayaninshi da cewar ta ringa yawan shan abu mai dumi banda mai Sanyi koda wankane kar tayi da mai Sanyi har sai bayan sati biyu ta kuma daure ta ringa shan magani

Please Login or Register in order to submit comment