Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

number tana shiga amman bai daga ba, inaga baya kusa hadi da mikowa ZAINAB wayarta da cewar ya gode sosai " amsawa ZAINAB tayi da babu damuwa ta karba" hakan shine yayi dai2 da dawowar Dr ya shigo da sallama suka amsa masa ya kalli su ZAINAB da cewar kuyi hakuri na bata muku lkc ko? " Amsawa ZAINAB tayi da cewar a'a Dr ai kana kan aikinka ne ta k'arasa maganarta da murmushi" kuwa wannan mutumin bai tanka musu ba domin hanakalinshi yana kan wayar hannushi" amsawa Dr yayi da cewar OK nagode, ya fara yi mata bayanin yadda( x-ray) din ANAS ya nuna da cewar Alhmadulillahi jiki ya bayar da yadda akeso domin kuwa ko a ido kika kalleshi ya sami sauki ko nace ya warke akan matsalarshi ta taruwar ruwa a cikinshi yanxu abinda ya ragya mana shine zamu cigaba da bashi jinya ta hanyar shan maganin koda yaushe duba da yadda shi kanshi asalin ciwon hantar tashi yayi k'asa sai dai muce an sami nasara sosai kema ya zama wajibi a jinjina miki bisa bin dokokin da kakayi na bashi kulawar da tadace ya Kara maganar shi da faden haka yana kallon ZAINAB" wani farin cikin ne ya baiyana a fuskarta k'arasa da cewar masha Allah Dr nagode sosai bisa taimakon da kayimin kaima tun da fari Ina alfahari da hakan na yaba da tausawarka garemu ni dashi" amsawa Dr yayi da cewar babu komai ai mu nan gidan abin kikazo dalili kuwa duk Wanda yake da cuta gurin mu yake zuwa ya kawota aikinka ne mu bashi kulawa shawarar da tadace dan haka karki damu yanzu zan sake rubuta miki maganin da zaki sake saya masa fatana dai Allah yasa kin zo da shirin haka?" amsawa ZAINAB tayi da cewar eh Dr babu damuwa ka rubuta nazo dasu zan kuma saya nagode dai kawai" murmushi yayi hadi da janyo katin ANAS gabanshi ya rubuta mata magunguna ya mika mata" hannu ZAINAB tasa ta Karbi kati ta cewa Dr tagode" ya amsa da cewar OK" sannan ya juya suka cigaba da magana da bakonshi" ita kuwa ZAINAB mikawa tayi ta kalli ANAS da wacer zauna anan naje na sayo magani a pharmacy na dawo" sai a lkc wannna mutumin ya sake magana da cewar zo ka zauna tare dani ta dawo ko?" tashi yayi ya tafi ba tare da yayi musu ba" ganin ya je gurin nashi ne yasa ya daukeshi ya daura akan ciyar shi da cewar yawwa malam ANAS mama taje ta dawo ko? "d'aga masa kai ANAS yayi da alamar cewa eh" ganin haka ne yasa ZAINAB ta juya ta fita ta barsu a office din ta nufi pharmacy. Tana fita ya kalli da cewar malam ANAS a gida ka baro Abban ka kenan ?" sai a lkc ANAS yayi magana jin harshin tamabar abbanshi da a kayi yasa yace a'a ban sanshiba!!" duk hankalinsu bai Kai ga ANAS haushi yayi ba sun dauka da da gaske ne maganar yaron " wanne tasa da Dr ya gyara muyar ya fara magana cikin harshen turanci da cewar buri yayi kama da mutum ranka ya dade domin tun lkc da aka kawo yaron nan na fuskanci Kamar marayane kaga kuwa dan yace bansan bansanshi ba ai ba zamuyi mamaki ba ya kare yana murmushi" shima murmushi yayi Sanna ya mayar wa da Dr amsa cewar ashe har ka fashinci yaron inda ya dosa ita kanta mahifiyar tashi gani nayi bata yimin Kala da matan aure ba gaskiya" dariya Dr yayi da cewar ko ranka ya dade?"amsawa yayi da cewar kasan mu wadanda mukayi aure_aure muna Iya gane bazawa koda wajan tafiyar ta muka kallah" dariya Dr ya sukeyi da cewar kardai kayi shigar sauri ranka ya dade a dai Kara bin cikawa ya fada yana yi masa murmushi" amsawa yayi da cewar Dr bazaka gane irin halin da na shiga bane, idai wallahi ba shigar sauri bayar shigar wuta_wuta ma zan iya akan wacce matar ne domin tunda na gane inda karatu yake tuni na dau mamaki ta hanyar hima da wayo na Karbi aron wayarta na kira layina Wanda yake a cikin mota a jjiye da duk layikan wayarta" dariya Dr yayi da cewar kace na fara yima Allah ya sanya alkairi tun daga yau!!!!" dariya yayi da cewar haba kai ko tun yanzu ai ka bari ciniki ya fada?" dariya suka fashe da ita a tare wanda shine yayi dai2 da dawowar ZAINAB shiru sukayi da maganar da sukayi ita kuma ta shigo tare da yi sallama suka amsa
mata sallamar atare" ita kuma ta nemi gurin da tabari ta zauna da cewar Dr na dawo ga makaganin ta mika masa" yasa hannu ya Karba ya cirosu daga leda daya bayan daya Sanna ya rubuta mata yadda zatayi amfani da su Sanna yace zata dawo bayan sati biyu a sake dubashi, hadi da sake bata shawara akan yadda zata cigaba da bawa ANAS kulawa" Karba tayi hadi da yi masa godiya sosai " sannan ta mike ta kalli ANAS da yake kan ciyar mutumin nan a zaune ya kwanat da kanshi a kirjinshi tace toh sarkin son jiki taso mu tafi" kallon ta yayi ya make kafada da cewar a'a ni ki barni a gurin babana" kallon mamaki ZAINAB tayi ANAS jin ya fadi hakan can kuma a kasan zuciyarta tace tabbas ba iyakar kulawarta ANAS yake bukarta ba yana bukarta kulawar mahaifi"murumshi tayi da cewar haba ANAS karka rana ta ruske mu anan mana kaga jikinka baya son rana ka taso mu tafi "sake nokewa yayi da cewar ta tafi ya taho" duk su duka ukun sai da suka yawa maganar ANAS din dariya" bama wannne ya basu mamaki ba illa yadda yake ta Kara dagewar bazai tafi ba sai da wanna mutumin " hannu ZAINAB ta sake kaiwa a karo na uku amman ANAS yak'i yadda ya taso hadi da k'ank'ame mutumin" ganin haka ne yasa idon ZAINAB ya ciko da kallah saurin mayar da ita dan gudun har su gano yanayin da take ciki " ta sake kai hannu zata finkoshi" mutumin ya dakatar da ita da cewar bashi mana ai yarone ku ba'a takura musu ki rabu dashi kawai tunda yaga abbanshi yau Kam dan haka karki damu" hmmm kawai ZAINAB tace ta rasa abinda zata ce musu su duka ukun har Dr da yake kara tsokanar ANAS da cewar dan baba sakko ku tafi, ANAS na Kara nokewa a jikin mutimin" Shi kuwa yamike da ANAS din Wanda ya cukuikuiye shi hadi da makaleshi ya kalli Dr da cewar Dr bari muje Idan kun k'arasa shigar da abubauwan da kuke bukata kayimin waya kawai" OK ranka yadade Dr yace, tare da cewar sai ka jini din muna godiya bisa bayar da tallafinka akan wannna asibiti" amsawa yayi da cewar karka damu " sannan ya kalli ZAINAB wacce take tsaye tun tsawan lkc tana jiran ANAS akan ya hakura ya sakko daga gurin mutumin su tafi" yace mata muje ko?" toh kawai ZAINAB tace hadi da Kara mamaki mutumin da shi kan shi ANAS din domin bai taba yi mata irin hakan ba tunda take dashi sai yau"ta juya ta kalli Dr Wanda shima mamakin yake, tace toh Dr sai nan da satin biyan nagode " ya amsawa mata da cewar babu komai Allah ya kaimu. sannna ta juya ta be bayansu itama ta fita daga office din.

A get ta sami su ANAS a tsayi a jin wata rantsat iyar mota suna jiranta wacce tasa sai da kirjinta ya buga tai makar zata kwarma Ihu sai kuma ta dake hadi da tunawa da maganar shi ta karshe da Dr akan bayar da taimako da alama bazai cutar dasu ba, ta k'arasa ya bude mata gidan baya Sanna ya Mika mata ANAS Sannan ya koma ya zagaya ya shiga gurin Zaman shi yaja motar"
Suna zuwa Kan tagwayen titi nan da ya ratsa ta kusa da asibitin ya juyo k'adan ya kalli ZAINAB da wacce take rungume da ANAS ta gefenta afirgice"shima ya fashinci hakan daga gareta dalilin da yasa yayi mata tambaya da cewar ina zamuyi hagu ko dama?domin ni ina son zuwa unguwar rijiyar zaki ne" ya ya fadi hakane dan yasa hankalin ZAINAB ya Kara kwanciya" amsawa tayi da cewar ai mu Dorayi muka nufa"ok yace da hadi da ce mata babu damuwa bari na Kaiku sai nabi bafas na wuce ta can" jin ya fadi haka ne yasata ta Kara samun kwanciyar hankalin ta kalli ANAS Wanda yake ta faman zuba surutu a cikin motar da cewar Kai baka gajiya da magana ne?" daga Kai yayi da cewar eh ai lbr nake baki" dariya tayi da cewar toh ka bari muje gida mana" toh kawai ANAS yace mata sannan yayi shiru" tsoma musu baki mutumin yayi da yaji ZAINAB ta hana ANAS din magana yace ai ni malam ANAS kana burgeni da hirar nan taka sai dai dan an hana kane babu yadda zanyi" dariya yayi yana daga gefe ZAINAB da cewar indan munje gida zan baka wani lbr ai" dariya mutumin yayi da cewar nagode" haka dai yayi ta jan ANAS da hira sai suka zo inda danja ta tsayar dasu ganin yawan motoci da mutane ne yasa ANAS yayi shiru ya mayar da hankalin zuwa ga kallonsu"basufi muti bakwai a tsaye ba aba basu hannu su wuce wanda yayi dai2 tsayar da hannu da yake d'anta 6angaren, ciki kuwa har da mashin din da RABI'U yake ciki" suna tsaye ne ya hango wata Kamar ZAINAB ce a motar da ta wuce, karyata idonshi yayi hadi da zancen zuciya da cewar ta ina ZAINAB zatayi haduwar wacce matar? Kuma bugu da kari ta ina zata ga irin wacce zafafaffiyar motar yasan dai duk danginta babu mai arzikin da zai iya mallakarta bare ace har ta hau irinta da haka ya kawar da zargi da Idonshi yake masa hakan ne yayi dai2 basu hannu da fila tayi ya wuce garejinsu zuciya babu dadi sakamakon gallazawar da JAMCY take masa da cewar ya zauna ya tayata rainon cikin da yayi mata" da bakin cikin rigimar ya fito."

Ita kuwa ZAINAB ba ita hankalinta ya Kara kwanciya ba sai da taka an shigo unguwar su, suna zuwa dai2 din titin da zai shigar dasu layinsu ta kalli mutumin da cewar anan zamu sauka""OK yace hadi da yin parking Sanna ya sakko ya budewa ZAINAB motar hadi da mika hannu ya karbar ANAS wanda yayi bacci tun Kamin su k'arasa" mika masa ANAS din tayi zuciyarta cike da tambayoyi hadi da sakowa ta dauko jakar hannuta bayan ta gama sakowa ne ta kalli mutumin da cewar mungode fa Allah yasaka da alkairi" amsawa yayi da cewar babu damuwa sai hadi da ce mata dan tsaya dan Allah" tsayawa tayi tana jiran taga abinda zai faru duk da taji sauki a zuciyarta gani ya kawo su har unguwar su ba tare da ya cutar dasu ba haka bai nuna yana bukarta wani abu daga gareta ba"ciro cak yayi na banki ya mika mata da cewar gashi dan Allah Idan yaron ya tashi ki bashi a ace in jini ya sayi sweet" da mamaki ZAINAB tasa hannu ta kar6i cak din hadi da yi masa godiya" amsawa yayi cikin kulawa da cewar toh madallah nima nagode hadi da komawa cikin motarshi yaja ya tafi ya bar ZAINAB a tsaye." kallon ZAINAB tabi bayan motar dashi hadi da cewar toh wannna waye shi? At zuciyarta " da wanna tunanin ZAINAB ta sake tare mai mashin a daidaita sahu ta hau dan ya k'arasa da ita layin su" basufi muti bayar da hakan wan mashin din ba ya kawo su har kofar gida ta cire kudin shi ta baya shi ta shiga gida da tunanin mutumin da ya daukosu daga asibiti..........


~AMENAT KABER KIRU~



*KARUWAR GIDA*

*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*


*SADAUKARWA GA:*
*_HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMED)_*

*_Jinjinar bangirma a gareku gaggan masoyan ZAINAB hakaki kanu bawa zuciyata Kala launi mai kyau bisa commet naku Aisha magaji kd, ummu Abdulssalam kt kuyi yadda kakeso da wanna page🤸‍♀🤸‍♀_*

*23*
Haka dai ZAINAB ta cigaba da mamakin mutumin musamman da ta buda cak din da ya bata kudine da suka ta samma duba dari mamaki ne ya dada kamata daga karshe dai ta barwa kanta cewar wani bangarene na taimako ubangiji domin tunda ta shigo motar mutumin bai nuna mata wata alama da zata zarge shi ba", babu abinda ya dad'a bata tausayi sai da ANAS ya tashi daga bacci domin yana tashi da maganar mutumin ya tashi da cewar UMMA Ina ABBA mai mota yake? " murmsuhin takaici ZAINAB tayi da cewar ya tafi gidansu tun dazu" bata rai ANAS yayi da cewar shine baki tasheni na bishi ba!!? "mamakin yaron ne ya Kara kama ZAINAB da cewar toh ai sauri yakeyi sai kayi hakuri wata rana sai ka bishi Idan mun sake ganinshi" hakika a wanna ranar ZAINAB ta Kara jin haushi RABI'U sosai fiye da yadda take ji a da can domin abinda ANAS yayi mata a yau ya nuna mata ba ita Kade yake son yayi rayuwa da ita ba, yana bukatar rayuwa da mahaifi" sai dai shi baya mahaifin nasu baya bukatar yayi rayuwar da su, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da (cewar babu gari mai cutarwa ga mutum face a kirashi da mara uba watau shege) domin duk Wanda ya mallaki uba ya wuce waccen gorin" abinda ya dada dugunzu zuciyarta a ranar domin kuwa ita kanta ba iya kudi take bukata ba a rayuwar ta tana bukatar wanda zai tausaya mata da gaya mata kallama mai dadi da kwanta da hankali da biyan bukatar ta a koda yaushe amman abin ya gagara inda tana butar wanna jin dadi sai ta fitar da kanta daga layin mata masu Kamin Kai ashe kuwa bata ci ribar auren RABI'U ba ta kare tunanin da zubar da hawaye ganin yaran duk suna kusa da ita shine abinda yasa tayi saurin gogewa" daga karshe ta kawar da tunanin shi ta kama aikace2 da ya rage mata na gida.

Shikuwa RABI'U baifi mutuna goma da shiga gateji ba sai jin wayarshi tana Kara da sauri ya dauka hadi da fita daga cikin mutane da suke gurin yayi can gefe da cewar hello Ina jinki" bani ne ya kirashi ba face JAMCY wacce ta zama masa tamabyar karka " ta amsa da cewar na kasa cin abincin da ka dafamin ne shine na kiraka naysanar maka abinda nake jin zan Iya ci ba wani babu bane face fizza da naman kaji sai dan abinda zansha na nau'in lemo ba kuma ko wanne nake so ba face kalar ja domin na fi son na haifi farin yaro ta kare maganarta da fadin haka" wani huce mai zafi RABI'U ya firzar da cewar wai meyasa kike min irin wannan abin ne!!?kamata yayi ki sanar min da abinda kike so tun Kamin na fito, duk Zaman da nayi na bata lkc a gida fa dan ke nayi amman shine Zaki ce min na saki aikin da nakeyi na dawo!!!" amsawa JAMCY tayi cikin masifa da cewar au ni kakewa irin wannna tamabyar?amman dai kasan dalilin da yasa na kiraka ko? Ko kuwa kanason yunawa ta kama min yaro tun yana ciki?"" kusik'i yayi yana janta tana zafga masa musifa Kamar wata uwarshi ya cigaba da sauraron kalaman ta ba tare da ya tanka ba " jin yayi shiru ne JAMCY ta kar da cewar toh bari kaji wallahi Idan baka saki duk abinda kake kazo ka kawomin duk abinda na lissafa ma ba wallahi sai na biyoka har garenji munyi duk bura ubar da zamuyi, kuma maza haka kuke da zarar kunga mace ta dau ciki sai rainin wayo da iskancin ta kare maganarta da sakar masa kusan karya hadi da tsorata shi da cewar gata nana zuwa" jin tace hakane yasa RABI'U cewar kiyi hakuri dan Allah karki taho yanzu zanzo kinji? Nifa bana nufiki da abinda kika fada na cewar zan jazawa cikinki matsala amman dan Allah ki jiran yanzu zan zo Idan akwai wani abu da kike bukata bayan Wanda kika fada sai ki gayamin na sayo miki yanzu " amsawa JAMCY tayi cikin shagwaba da shashshakar kukan karya da cewar iya su nake buta amman Idan kakawo wandan nan din Idan naga da bukatar wani abu na gayama ta yanke wayarta da cewar sai kazo din" toh kawai RABI'U yace mata" bayan sun gama wayar ji yayi Kamar ya fasa wayar tashi dan takaicin da JAMCY ta bashi, domin ban takaici ta ba Iya na kirashi bayan ya fito bane har da na bashi aikin gida da takeyi wajan sashi girki da wani,, shara da wanke2 uwa uba wankin kayanta domin hatta wandonta da rigar nononta shi yake wankewa hadi da gyaran dadi duk abinda yake mata baya hanata ta zazzgeshi yana ji ba tare da ya tanka ba bare ya dau mataki" ji yake Kamar yabar garin Sabida masifar JAMCY sai dai ya ssn rashin mutincita dai dai da yini daya tayi baganshi ba zata Iya zuwa gidansu ta sanarwa da iyayrnshi halin da suke ciki" Da wannna tunanin ya koma cikin garejin fuska babu walwala ya nemi izinin oganshi da cewar anyo masa waya daga gida yaroshi babu lfy ciwon shi ya tashi bayan ya fito" amsa masa yayi da cewar Allah yabashi lfy kaje babu damuwa " toh kawai RABI'U yace ya fito. Daman kusan kullum da wannna karya da yakeyi ne yake samun damar komawa gurin JAMCY" wannna hujjar ce tasa komai na RABI'U ya tasamma karewa domin baya wani zama yayi aikin da zai samu kudi masu yawa ga kananun fituntunun JAMCY da suke Kara yi masa yawa kullum, ga abokan harkarshi masu kawo masa gyara duk sanda sukazo baya nan basa Iya jiranshi sai su bawa sauran abokin aikishi suyi" wannan abun ne yasa RABI'U duk ya fita haiyacin shi domin kuwa duk yayi baki hadi da rama uwa uba ga rashin kwanciyar hankali da yake damunshi" yana baro garejin haka ya je ya saiwa JAMCY duk abinda tace masa tana so da yan kudin da suke jiranshi ya Kai mata wani abun haushin ma da tayi masa shine sai da taci ta koshi ta kwanta tana birgima da malele kuwar cikinta na ciwo haka ta faman wahar dashi da amai karya da ta k'akaro duk the malaye d'akin dashi ba tare da ta tausaya masa ba " haka yayi ta faman dauki ba dad'i da amai da tayi ha tare da ya huta ba bayan ya gama gyara d'akin da wanke abin da ta bata sannan ta umarce da cewar ya zauna yayi mata tausar jiki" "haka ya zauna ya dinga yi mata tasaur Kamar yadda ta bukata ba tare da ta barshi ya koma gurin aikin shi ba, har yamma tayi. " ganin yamma ne gashi ya rasa aikin shi na wannne ranar yasa shi tamabayarta da cewar babu wani abu da zai yi mata? Domin yana son zuwa gida ya duba iyalanshi" wani kallon bazan JAMCY ta watsa masa da cewar yau kuma kaji Munafinci yaushe rabonka da zuwa gidan naka sai yanzu zaka kawo tsirfar tafiya gurin iyalai ko Kunya bakayi sau nawa da can nake ce maka ka yafi amman sai kak'i hmmmm Sannu sukari sarki iyalai ta kare maganarta dayi masa tsaki" kasa d'ago ido RABI'U yayi domin yasan duk abinda JAMCY ta fada gaskiya ne""jin yayi shiru ne yasa JAMCY ta kar cewar bazan hanaka ka ganosu ba amman Idan kaje karka manta da wasu iylan naka anan suna jira domin kasan bana iya komai yanzu idan naji shiru kuma zanje inda za'a kula maka dani da abin da yake cikina" toh kawai RABI'U yace ya fito daga gidan. Ana kiran sallar magariba yana shiga gidan shi lkc yayi dai2 da fitowar ZAINAB daga wanka" ganinta RABI'U yayi ta sauya masa sosai Kamar ba ita ba domin gani yayi tayi wani jajawur Kamar balarabiya ga gashi kanta ya zuba har gadon bayanta uwa uba kuwa kibar da tayi ta bude Kamar ba ita ba" waigawa yayi gefe ya kalli su MARIYA suna sai yaga yaran duk sun sauya Kamar basu ba kallon kanshi yayi da jin Kunya lkc da yayi ANAS magana da cewar ANAS ya jikin naka kuwa?"Shiru yaron yayi masa Kamar bai ji ba har sai da MARIYA da take alwala a gefenshi tace ba dakai ake magana ba ka najin" tsaki ANAS din yayi da cewar toh ke ki amsa masa masa mana ya kara mikawa hadi da shigewa Dakin su " jin haka ne yasa MARIYA ta wuce tabi bayan ANAS din ba tare da ta sake cewa komai ba" Shi kuwa RABI'U tsayawa yayi yana mamakin yadda yaron ya wulak'anta shi, kulawa yayi da niyyar ya saukewa ZAINAB masifar akanta sai kuma yaga tayi masa kwarjini dole tasa yayi shiru bai tank ba " ganin haka yasa wuceshi tana faman buga uban kanshi turarukan wankan da tayi ta shiga d'akin ba tare da ce masa cinkan ba bare ta kwabi ANAS" biyo abayanta yayi a gigice da yaga ko ina yana motsawa domin jinshi yake tamkar ya rugumeta lkc da tazo giftawa ta gefenshi " yana shiga d'akin wayar shi ta kama kara" cirowa yayi daga aljihunshi da nufin daga sai yaga JAMCY ce da wannna kiran da sauri ya mayar da wayar cikin aljihu ya fito daga d'akin ba tare da daga ba ya fita daga gidan cikin hazari" abinda ya bawa ZAINAB mamakin da yasa ta tambaya kanta cewar wannna lfy kuwa? Domin taga abinda ya bata mamakin har guda biyu na tambayar ANAS jikinshi da kuma Kasa d'aga kiran waya a ganinta."
RABI'U na fita daga cikin gidan shi ya sannan ya daga wayar JAMCY" yana dayawa ta fara zazzaga masa ruwan bala'i hadi da ci masa alwashin matuk'ar Bai dawo inda take ba Kamin miti tallinta sai tayi masa rashin mutuncin da bai zata ba, haka dai tai tayi masa rashin albarka a waya babu kaukautawa ko daga kafa" sanin halinta yasa bai koma cikin gidan shi ya dada ganewa kanshi abinda baiyi tsammani ba watau sauyawar ZAINAB wacce tunda ya tafi yake tunaninta duk sayan " gashi ya rasa ta Ina zai fara da ita domin yana ganin yaje gareta a wanan yanayin Kamar ya zubarwa da kanshi kima ne, uwa uba kuma ga sharadin da ya gindayawa kanshi na cewar bazai ne mata ba har sai ya ciki shekara goma toh fa gaba kura baya shayaki kenan domin wata irin sha'awar ZAINAB yaji tana firgarshi sannan gefe ga yar masifa JAMCY wacce take zama barazaba ga fashewar zuciyarki domin kuwa bata wani burin da ya wuce taga 6acin rashin Sabida taga ta daureshi da jijiyar jikinshi ji yake dama baisanta ba tun fil'azal a rayuwar shi domin kuwa a wanna ranar ne ya Kara jin nadamar haduwarshi da ita " yana komawa ta daura masa wani nauyi da cewar tana marmarin siyayyar kaza" haka RABI'U ya fita yaje ya sayo mata rabi tunda bashida isasasun kudi a hannushi dan kar ta hanashi bacci ne ma yasa ya Iya so rabin Kamar " kawo mata yayi da rawar jiki da cewar ta tashi taci gashi ya sayo mata hadi da bude ledar ya tura mata gabanta" tana tashi daga kwanciyar da tayi ta Kai kanta kenan Idan ledar take ta buude bakinta ta zurara amai a ciki da cewar bata son kanshin naman haka dai tayiwa RABI'U asarar rabin kazar da ya sayo"da sauri ya mike ya fitar da ita waje wai duk dan kar ta bashi aiki, sanna ya dawo ya tattare ledar da naman yake ciki ya fitar dashi waje shima hadi da dauko tsumma ya goge d'akin " duk da wannna aikin da yayi bai hana JAMCY ta ta Kara gabatar Misha da wani aikin ba domin kuwada cewa tayi ya fita ya nemo mata goro zata ci a wannan daren" haka RABI'U ya sake fita yawan nemar mata goro da kyar ya samo mata ya kawo mata taci Sanna ta barshi

Please Login or Register in order to submit comment