Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MIJIN MAMY Complete Hausa Novel Document by MIJIN MAMY


MIJIN MAMY

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 47465



MIJIN MAMY

Reading Time: 3 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Rahma Ladingo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : GARKUWA WRT ASS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 270.66 kb

File Type: txt

Views: 486+

Download: 685+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: *🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*


_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ1️⃣&2️⃣*



Matashi ne d'an kimanin shekaru 24, fari ne kyakkyawa, mai matsagaitan idanuwa, masu wani irin sirrin baiwar kyawu acikin su, wanda ba kowa yake iya had'a idanu da shi ba. Yanada dogon hanci da k'aramin baki kalar pink, ingarman namiji ne mai cikar halitta. Duk yadda zan suffanta shi ya wuce nan. Yanada faffad'an k'irar jikinsa irin murd'add'an jikin nan ne, wato k'arfaffan namiji. Dogone Masha Allah, idan ka gansa zakayi zaton ya kai shekaru 30 aduniya, shi kuma yanzu ya Shiga 24, aduniya. gefe-gefen fuskarshi, dab da kunnensa yanada tsagarsu uku² 'yan k'ananu, ta cikakken yaren (Zarma). Amman tsabar kyansu da farinsu zaka zaci zuri'arsu buzayene, wanan k'ananun uku² ta garden kunnansu, kawai ita take saka agane family's d'insu (zabarmawa) ne. Gudu yake shararawa saman sabin mashin d'insa, kamar zai tashi sama. Ya na tsakanin k'uyan (Frandey) da dosso. Tun bayan salar asuba ya tafi sai yanzu ya juyo. Fuskar nan ta shi tam ad'aure,ba annuri kana gani kasan an tab'o 'yan mazan, sai tsaki yake ja, ya na fesar da zazzafar iska mai d'umin gaske daga bakinsa. Ko da ganin yadda yake murza kan mashin d'in kasan ba k'aramin k'warewa yay ba wajan tuk'in mashin. *Dosso* Unguwar (Cité mangué) Unguwace tsarariya wacce take cike da ginin zamani, kala². Wani babban gida na hango gidane ginin talaka, amman yasha siminti, kana ganin gidan kasan an had'a family's acikinsa. Babban zaurene kafin ashiga asalin tsakiyar gidan. Gidane mai b'angarori daban-daban. Ya na d'auke da b'angare guda biyar kowane b'angare, da kewayansa, da k'ofarsa ta shiga, da iyalinsa, kowane gida d'aki uku akayi da kitchen atsakar gida da band'aki atsakar gida, haka kowane kewaye ashafe yake da siminti gwanin kyau. Gida na biyu, gidan Sa'id mai unguwa. Mata ce y'ar kimanin shekaru 50, fara kyakkyawa, tana zaune tana tsince shinkafa. Sai wata dattijuwa gefenta zata kai shekaru 67. Goggo Nandou tana gurzar goro ta saka Ummuh gaba da masifa. Da harshan zarma ta ke fad'in, “Wallahi Maryama mun gaji da ganin tsohuwar yarinyar nan mai sunana agidan nan, sabida Allah sai na mutu banga d'anta ba, batada niyar kuma aure. Wlh yanzu da ta aurar da 'ya 'yar shekaru 17 inda ta sake aure ta samu rabo. Idan kuma bak'in aljani ya aureta inaso na sani. Wlh Bari mai unguwa ya shigo,ko sadakane abadata shine ma yake biye mata d'an ashatta kawai...” Idanuwa Goggo Nandou ta gwalo waje ta saki magurjin goron ak'as ta tafa hannuwa tare da salati, sakammakon wata zankad'ed'iyar matashiyar mata, fara siririya kyakkyawa ma'abuciyar fara'a mai cikar halita, da ta fito daga band'aki d'aure da towel ta ajiye bokintin agindin fanfo ta kunna fanfon ta d'auraya pant d'inta tana murmushi dimples d'inta suka lob'a ta nufi d'akinta, cikin siriryar muryata, da yaren zarma ta ce“Uhmm su Goggo Nandou ina kwana? Anzo ayi kicihin safe ko? Toh Allah temaka, ni zan fita abun yi.” ta k'arashe maganar tana d'aga mata gira had'i da kashe mata ido d'aya, ta fad'a d'aki wuff, tana dariya. Daman Sai da ta tabbatar gidan ba kowa yara sun tafi school,ta fito ahakan dan tsokanar Goggo Nandou. Doguwace mai manyan idanu farare masu lumshewa, tanada fad'in labb'a jajaye masu kauri Wanda suka mata kyau, fuskarta nada d'an fad'i kad'an, akwai gashin idanu gazar-gazar, da na gira kirjinta tamtsam-tamtsam duk da sirintakarta akwai hips masu matuk'ar d'aukan hankali, k'irar coca cola, idan tana tafiya zaka zaji karairaya take da gangan duk da batada jiki amman k'aramin jikinta sai ya mata mugun kyau. Batada gashin kai sosai ko kitso aka mata iya k'asan wuyanta yake tsayawa, amman yanada samtsi bak'ik'irin da shi, yana shan gyara sosai. Amman ita sam bata son k'iba komin k'ank'antarta. Akwaita albarkatun k'irjinta masu k'ayatarwa. Shekarunta 34 ahaife amman bazaka tab'a cewa takai 25 ba, sabida d'an k'aramin jikinta mai kyau haka fuskarta bata nuna shekarunta, ita d'in tamkar matashiyar budurwa ta ke. Goggo Nandou tace“ Maryama kinga halin 'yarki ko? Wlh nasan maganinta, Bari mai unguwa ya dawo daga kasuwa, Bilkisu irin abinda kika min shi kikewa maza awajan aiki? Ai dole suyita haukanki.” Ta k'arashe maganar tana mik'ewa tsaye tana dogara sanda. Ummuh tace“Dan Allah Goggo kiyi hak'uri naji jiya tana fad'awa baban yara yau ALHJ AUTA zai turo magabatansa, daman ita tak'i yanzu kuma tinda na mata wannan nasiyar taji zata auresa acewarta....”Goggo Nandou tace“Ai gwara da kikace acewarta maza nawa tama haka? Toh wlh Bari yazo inaso kafin nan kafin sati ad'aura auran, bazawara jiran me ake? Haba ina dalili akanta aka fara mutuwar miji shekara goma sha bakwai kana zawarci. Ai maganinta kenan gashinan D'an da takusa Haifa yana mata shegantaka wai shine mijinta abadan.”Goggo Nandou ta k'arashe maganar tana dariya ta kamar hanyar fita. Ummuh murmushi tai tana tsintar shinkafarta batace komai ba. Amman ita kanta lamarin 'yarta tasan akwai jinnu aciki, da zaran ta an saka auranta bata sake moruwa, ciwo jajir sai ankwantar an tayar, har masu auran su gaji su fasa. Goggo ta hango Zaharadin, ya faka mashin d'insa jikin part 1 yana waya. “Baban Zuhura yauwa zo d'an albarka.” Cikin daddad'ar muryashi yace “Ok anjima zamuyi mgna aunty Zuhura yanzu na shigo gida zanyi wanka.” Ya k'arashe maganar cikin amon muryashi mai dad'in gaske ya tsinke kiran ya jafa wayarsa k'irar Tecno camon 11, cikin aljihun gaban rigarsa, ya nufo kakar tasa yana sakin tattausan murmushi Wanda ya k'awata kyakkyawar fuskarshi. Sam bazaka zaji d'azu shine ya had'e fuska ba. Ya na isowa ya rungumeta yace“Daga wajan ummuh kike? Ina my Mamy uwar 'ya'yana?.... “Kai Zaharadini wallahi ka kiyayeni uwar me zakaci da matar da lokacinda aka mata aure ma baka saka wondon kirki? Kanaji yau za'azo tambayar auranta, shine sabida banida daraja mai unguwa da Yaro basu fad'amin ba Ko?” Wata irin zabura yayi ya Saki Goggo Nandou. Take k'irjinsa ya dinga sama da k'asa ransa ya kuma b'aci yace“Ok kenan da gaske ne ba wasa take ba? Ina kan hanya naga message d'inta OK Allah ya sanya alkahiri. Goggo Bari nayi wanka.” Ya k'arashe maganar yana Kama hannun Goggo. Zatayi magana ya rufe mata baki“Dan Allah Goggo kiyi shiru.” ya rakata k'ofa ta farko wacce sukama lak'abi da Babban gidan Wanda Ana d'akinta yake, kuma nan ne part d'in iyayan Zaharadin. Lace ta saka uban-ubansu, bak'i mai adon flowers fari da pink kad'an. Dinki Riga da zani tayi kyau matuk'a sai baza k'amshi take, ta saka takalmi bak'i mai d'igon fari, haka jaka bak'a, wadataccan mayafi ta lullub'e jikinta tsaf. Idan ka kalleta bazaka tab'a cewa badaga gidan akwai ta fito ba! Sabida tana kashema jikinta kud'i duk salary d'inta Rabi ajikinta yake mutuwa Rabi iyayanta da k'aninta, ga zawara masu arzik'i da suke mata b'arin kud'i amman tana k'in amsa, na ALHJ AUTA kawai take amsa. Kyawawan idanuwanta ta zubawa agogon dake d'aure atsintsiyar hannunta, ta ga goma saura. Narkakkun idanunta ta waro cikin siririyar muryata tace“Ya Rabbi! Irin wannan makara haka? Bari nai sauri...” Turus taja ta tsaya ganin Ummuh tsaye k'ofar d'akinta ta had'e face. Kai langwab'ar cikin sigar shagwab'arta da bata girma, tace “Ummuh kiyi hkr na makara da yamma idan na dawo zamuyi magana. Inaji kina cewa waccan kinibabbar tsohowar Abba kadai na fad'ama zuwan iyayan Autana ko? Uhmm na tafi ummuh.” ta k'arashe maganar tana k'if² da ido. Ummuh tace “D'azu dan ki saka Goggo taje babban gida ta mana tereran bankad'a kika fito kusan tsirara ko?... “Ni kimin addu'a na fice.” “Allah ya tsare ya bada sa'a kici gaba da rik'e mutuncinki da darajarki, da Kimar gida nan, kiji tsoron Allah aduk inda kike, idan mu bama ganinki Allah yana ganinki...”Ngd ummuh insha Allah zan kasance kamar baya.” ta mata kiss ta fice da sauri tana mitar samun adedeta sahu ma kadai zai b'ata mata lokaci, itako ta hana AUTA ya na kaita amota sabida kare mutuncin gidanau da Nata, sun iyama talaucinsu. Acikin nutsuwarta take tafiya, yayin da dukkan jikinta ke motsawa. Duk da batada jiki ko kad'an amman hakan bai hana kyakkyawar surata rausaya ba, tare da manyan albarkatun k'irjinta, halittace daga Allah ta iya tafiya mai tsayawa arai. sai da tazo tsakiyar gidan lokacin hankalinta ya Kai kan mashind'in Babandi. Manyan idanunta ta zaro waje, cike da fargaba, yayin da ta fara sauri tana addu'ar Allah yasa kar su had'u da yaron nan, ya b'ata mata lokaci abanza, ko ya sakata b'acin rai, k'ilan ma da kuka. Tana shigowa k'aton zauran gidan taji k'amshin mayen turaransa, Wanda yake sakata jin kasala da wani irin yanayi, ya bugi hancinta. Ahankali da yaren zarma tace“Shegen yaro duk kud'insa idan ya samu A turare mai dad'i yake k'arewa, ji baya wajan amman k'amshinsa ya manne asoron k'ofa, zan saka my...


Read / Download MIJIN MAMY

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album