Join Our WhatsApp Group

RUBUTACCEN ALAMARI Complete Hausa Novel Document by RUBUTACCEN ALAMARI


RUBUTACCEN ALAMARI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 110136RUBUTACCEN ALAMARI

Reading Time: 9 Hours

Added On: 04, Nov 2023

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 675.91 kb

File Type: txt

Views: 966+

Download: 910+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 馃摑馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌

*亘爻賲 丕 賱賱賴 丕賱乇 丨賲賳 丕賱乇 丨賷賲貙*

06/09/2017.10:24 PM

*A TRUE LIFE STORY*

馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Page 1鈨�

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌馃崌*Gargad'i! Gargad'i! Gargad'i! dan Allah kar a juya mi wannan labarin tako wacce siga har sai an nemi izinina dan Allah ko harafin (A) kar a canza min bana so*
*Ina mik'a sak'on Barka da sallah na ga d'aukacin al'ummar musulmai baki d'aya Allahu rabbi ya amshi ibad'un da muka aikata Allah ya maimaita mana shekaru masu yawa da al'bakar wad'anda ke k'asa mai tsarki Allah ya dawo daku cikin lafiya**Alhamdulillah lillahi ala kulli halin na godewa Allah da ya bani rai da lafiya da nitsuba da konciyar hankali har na samu damar fara rubuta wannan littafi cikin k'oshin lafiya ya Allah ka bani iko da damar gama shi lafiya kamar yadda na fara lafiya Ameeen ya rabbil izzati*
Suna iso kan layin uguwar tasu Usman ya dafa kafad'un abokin shi Nura dake jan motar tasu cikin dan fidda ido yace.
"Kai Nuru tsaya a nan ba sai ka shiga cikin gidaba zan sauk'a a nan!."
Kai Nuru ya juyo tare da k'are mishi kallon sai kuma yayi murmushi ganin yadda Usman sarkin surutu ya wani zaro ido cikin murmushin yace.
"Kai Usman ni wallahi Hamma Umar mamaki yake bani ji yadda yake wani tsareka a gida kamar mace! ji yadda kake wani zaro ido dan kasan yanzu yana harabar gidan yana duba marasa lafiyan dake zuwa gunshi."

Shi dai Usman balle marfin motar yayi ya fita yana hararan Nuru tare da cewa.
"Ban za kawai lailamajanun duk ka zama majanuni akan mace sai dare yayi kazo kace in raka ka kakuwa sani sarai Hamma Farouq zai nemeni dan zai bani magani na."

Shi dai Nuru dariya yayi tare da jan motarsa ya tafi.

Shi kuwa Usman cikin sand'a da d'an d'aga k'afa da lek'e-lek'e ya shiga cikin gidan,
gaba d'aya hankalin shi na can gefen wasu yan bukkoki da akayi da ginin zamani sai samansu kuwa da akayiwa rufi da ciyawa suka fita kamar bukkokin rigar Fulani sai fulawowi masu kyau da suka zagaye harabar gidan da haske tako ina cikin bukkokin da sukafi kama dana shak'atawa wani farin matashi ne mai cikar haiba da tsurawa wanda yafi kama da laraba Dr Umar Faruoq kenan shine yake zaune kan kujerun dake zagaye a bukkokin sai mutane kusan 8 dake zaune daga dukkan alamu sunzo ya duba lafiyar sune gaba d'aya hankalin shi na kansu.

Shiko Usman ganin haka yasa cikin sauri da d'an d'aga k'afa ya zille yayi cikin gidan,
kai tsaye Parlour Nenne ya nufa cikin yana yinsa na fara'a yayi sallama,
tare da shiga cikin Parlour yana ta haki da d'an zare ido.
Nenne ce ta fito daga cikin bedroom cikin sakin fuska tace.

"Usman daga ina haka kaketa zare ido?."

Dariya ya d'an yi tare da zamewa ya zauna gefen Ummul dake ta binshi da ido sai ya Adam da ya Sadik dake zaune a gafe duk sun zubawa Usman ido cikin murmushi Ummul tace.
"Mugun ne ya koroka ko ya Usman?."

Kai ya d'an juya cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.

"Tab Nenne Hamma Umar yazo ya nemeni ko.?"
Cikin sauri da salon tsokana ya Adam yace.
"Ehh yazo k'afa 3 yana neman ka."

Ido ya kuma d'an zarowa yace.
"Toh ni fa ba wani wuri naje ba!
kawai na d'an raka abokina Nuru zance gun budurwar sane,
kuma yanzu nasan Hamma Umar zaice yawo natafi ban sha maganina ba."

Dariya Nenne tayi cikin kula tace.
"A a baizo bafa Usman."

Shima dariya yayi cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.
"Ummul me kika dafa mana me? Dan wallahi yunwa nikeji."

Ya Sadik ne yace.
"A a saidai ta tashi ta dafa maka ko indomi ne dan miyar ganye tayi kai kuma kasan an hanaka ci."

Fuska ya d'an tsuke cikin badda zancen yace.
"Ummul kawomin zanci na yau kawai bazai min komai ba."

Nenne ce ta kalleshi cikin kula tace.
"A a fa Usman ka kiyaye dokokin Doctors ko dan samun lafiyar ka."

Baki ya kuma turawa yace.
"Wallani ni nagaji da wannan dokokin ace duk wani abu green bazan ciba,
dan Allah Nenne yau kawai kinji ko?."

Ita kam Nenne gaba d'aya take jin tausan Usman a ranta sabida ciwon dake tare dashi gashi yaro matashi .

Shi kuwa Usman cikin dariya ya kalli Ya Adam yace.
"Ya Adam kasan me Nuru yakeyi in munje gun babynshi?."

Murmushi ya Adam yayi tare da cewa.
"Inako zan sani sai ka fad'a min dai."

Ummul ce tayi carab tace.
"Ya Usman me yake yi?."

Hannu yasa ya kamo na Ummul d'in cikin yanayin shi na abin dariya yace.
"Jeki kawo min abinci zan baku labari."

"Toh" tace tare da haura saman d'an steps d'in da zai sadata da kitchen d'in sauri-sauri tasa mishi abincin a pilet sannan ta dawo parlour stol tajawo gaban shi ta ajiye mishi abincin cikin son jin zancen tace.
"Toh ga abin cin bamu labarin."

Murmushi yayi cikin raha ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Nenne kina jiko kullum Nuru zaizo yace na rakashi zance amman sam in munje ba abinda yake sai shirme."

Ido ya Adam ya tsura mai cikin gimtse dariyar shi yace.
"Kamar yayafa?."

Dariya ya kuma tare da cewa.
"kuna jiko Nenne kullum in munje muna zuwa k'ofar gidan su budurwar tashi sai Nuru ya kalle ni cikin in inarsan nan yace min k.. k.. kai Bosho k.. katsaya a cikin motar nan karka fito,
ni kuma sai nayi dariya nace toh ,
in an aika ta fito sai yace ta zauna kan motar ,
ita kuma sai ta wani d'ale saman motar ta zauna tana kallon shi."
Ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Hmmmm Nenne kin san me Ruk'ayyan take ce masa?."

Su ya Adam kam da ya Sadik tuni sun fara dariya itama Ummul sai dariya take .
Ita ma Nenne murmushi take yi tare da girgiza kai alamar a,a.

Shi kuwa Usman cikin nuna musu abin a zahiri ya jawo hannun Ummul ya ajiyeta kan hannun kujera shi kuma ya matso gaban ta gab da ita ya d'an sa k'afarsa d'aya a gaba d'aya kuma ya maidata baya sannan ya rink'a d'an sunkuyawa yana d'an d'agowa kamar maiyin wazifa sai kuma ya kalli ya Sadik yace.
"Ya Sadik Kunga haka ko?,
wallahi haka Nuru yake tsayuwa a gaban ta kamar mai jin bacci yayi ta layi ita kuma sai tayi ta wani mishi murmushi kamar sokuwa."
Sai ya kuma kalli Nenne yace.
"Nenne kin san me take ce mata kuwa.?"

Cikin dariya tace.
"Me yake ce mata?."

Dariya yayi tare da koikoyar muryar Ruk'ayya budurwar Nurun yace.
"sai tace ,Nuru ina sonka."

Sai kuma yayi dariya yace.
"Nenne ba tace masa Nuru ina sonka ba?."

Cikin dariya Ummul tace.
"Ehh".

Shima dariya ya kumayi tare da cewa.
" shi kuma soko sai ya kalleta murya can k'asa yace.
"Allah ya d'aiyiba."

Sai kuma suka rink'a dariya cikin dariya Usman yace.
"Kijifa Nenne wai Allah d'aiyiba sai kace wad'anda akayiwa haihuwa Allah ko Nuru yana bani dariya shi yasa nake son rakashi zance,
kumafa kullum haka suke hirar tasu ,tace
Nuru ina sonka shiko gogan yace,
Allah d'aiyiba."

Gaba d'aya dariya suke shiko Usman yaja pilet d'in abincin ya fara ci kamar bashi ya basu dariyar ba.

Autan gidan ne Aliyu ya kalleshi cikin sanyi yace.
"Ya Usman ba doctor ya hanaka cin duk wani abu green ba kuma kake cin miyar ganye kasan fa Hamma Umar zaiyi fad'a."

Harara ya cillawa Aliyu tare da cewa.
"Toh sai dai in kaine zaka gaya mishi naci miyar dan nasan ka ka iya gulma."

Haka yaci gaba da cin abincin suna ta dariya da hira da raha.

Yana cikin cin abincin ya d'ago kanshi da sauri jin k'amshin turaren Hamma Umar na ratso hancin sa,
da sauri ya ture pilet d'in kasan kujara sai kuma yayi zuru-zuru da ido yana sauraron ta ina Dr Umar d'in zai shigo.

Shi kuwa Doctor Umar dama sarai yasan Usman baya cikin gidan kuma ya ganshi lokacin da ya shigo cikin gidan haka yasa yana gama sallaman marasa lafiyan kai tsaye part d'in su ya nufa wonka yake sonyi amman bazai iya zama har yayi wonka baije ya bawa Usman maganin shi ba hakan yasa ya d'auko magungunan tare da goran FARO a hannushi ya nufi cikin gidan.

Sallama yayi tare da tsayuwa a bak'in k'ofar yana jin suna ta hira da dariya bai shiga ba har sai da ya kuma sallama Nenne ta amsa mishi tare da bashi izinin shiga.


Shi kuwa Usman tuni ya tonk'oshi kai yayi kalan tausayi .
Ummul kuwa mik'ewa tayi ta koma gefen Nenne dan jin muryar Hamma Umar d'in dan ta sanshi sarai yanzu zai samo laifin da zai turama .

Ya Adam da Ya Sadik kuwa Usman suka tsurawa ido.

Shi kuwa Dr Umar kan shi a sunkuye ya shiga cikin parlon cikin girmamawa ya gaida Nenne amsawa tayi fuska a sake tare da cewa.
"Umar bak'in naka duk sun tafi kenan?."

Murya can k'asa yace.
"Ehh"
dan shi baida rakad'i irin na Usman kuma baya da yawan surutu bashi kuma da shiga sabgar wani baya kuma wasa da yara kasan cewarshi shine babba a family nasu baki d'aya gashi da iya horon marasa jin magana.

Usman ya kafe da ido cikin tsuke fuska da yanayin tuhuma.

Shi kuwa Usman a hankali ya tashi ya matso gaban yayan nashi cikin ladabi da tsantsar k'aunar juna yace.
"Afwan Hamma Umar bazan sake ba."

Ido Hamma Umar ya kawar sannan yasa hannushi ya rok'k'oshi kan Usman tare da kamo kunnen shi ya d'an matse cikin yanayin hukun tawa.

Hannu Usman ya rink'a d'an yarfawa yana d'an k'ara tare da cewa.
"Hamma na natuba kayi hakuri bazan kuma zuwa yawo ba."

Sake mishi kunnen yayi sannan ya ajiyeshi kan kujera yana kallon fuskar sa,
Magungunan ya b'abb'allo sannan ya mik'a mishi,
hannu Usman yasa ya karb'a tare da afasu a bak'in sa yana mai yamutsa fuska,
shi kuwa Dr Umar goran ruwan FARON ya b'alle cikin kula yasawa Usman bak'in goran a bak'in shi,
shiko Usman ido ya rumtse sannan ya had'iye magungunan nashi.

Murya can k'asa Umar yace.
"Kaci abinci?."
cikin sauri Usman yace.
"Eh Hamma naci."

Kai ya gyad'a sannan ya tattara magungunan tare da rufe goran ruwan ya juya ya kalli Nenne da ta zuba musu ido cikin tausayin su da mamakin irin kauna da kulawan da Umar yake bawa k'aninshi Usman.

A hankali Doctor Umar yace.
"Nenne sai da safe."
cikin kula Nenne tace
"Allah ya bamu al'heri Faruoq,
Allah ya biya ka hidiman da kakeyi da d'an uwanka,
Allah ya bashi lafiya."

"Amin ya rabbil izzati."

Yace tare da ficewa .

Kai tsaye Bedroom d'in su ya wuce wonka yayi tsab sai k'amshi yake zubawa yana fitowa yasa wonddon shi 3 qtr sai rigarshi Mara hannu turare ya d'an fesa sannan ya jawo woyarshi da laptop d'in shi,
Usman ya kira,
Shi kuwa Usman tuni ya biyo bayan Hamman nashi ganin ya shi ga wonka ne ya dawo parlour ya zauna yana kallo,
ganin kiran Hamma Umar d'in nashi yasa ya mik'e da sauri ya nufi cikin bedroom d'in,
yana shiga gefen shi ya zauna cikin son juna suka kalli juna,
a hankali Dr Umar Faruoq yace.
"Na had'ama ruwan zafi kaje kayi wonka."

"Toh" yace tare da mik'ewa ya dawo gaban Hamma Umar d'in ya tsuguna yana mai kallon shi da yana yin shi yake jira.

Shi kuwa Dr Umar laptop d'in nashi ya d'an ture gefe sannan yasa hannu ya b'abb'ale boturan jikin rigar Usman d'in,
yana gama bud'e mishi boturan Usman d'in ya mik'e ya cire rigarsa,
sai kuma ya matso gaban Hamma Umar d'in ya tsaya ,
kai Hamma Umar ya girgiza tare da b'allewa Usman d'in beld'in dake k'ugunshi sannan ya d'an sunkuyo ya fara kuncewa Usman d'in igiyoyin takalman shi.

Shi kuwa Usman sai kallon hannun d'an uwan nashi yake yi.

Yana gama kunce mishi ya kalleshi a hankali fuska a d'an tsuke yace.
"Wai kai Usman yaushe zaka koyi kula da kanka ne? ,
ace kana namiji baka iya d'aure igiyan takalmin ka da kuncewa ba bel d'in jikin kama baka iya. mannashi ba hatta botur bazaka iya sawa da cirewa ba komai sai nayi maka randa bana kusa da kai kuma toh ya za kayi?."

Dariya yayi tare da shigewa toilet yana cewa.
"Hamma Umar ai ko Aure kayi tare zamu tare a gidan bazan bari kayi nesa da niba."

Shi dai Hamma Umar kai kawai ya jinjina tare da bin d'an uwanshi da kallo.

Bayan ya fito wonkan ne,
Umar ya had'a mishi tea sannan ya bashi ya sha,
yana gamawa ya konta gefen Hamma Umar d'in nashi dake ta lallatsa laptop d'in shi.

A haka har zuwa d'an wani lokacin sanna Hamma Umar ya rufe laptop d'in tare da jawo blanket ya rufe Usman d'in cikin kula yace.
"B'iyaye na Usman kayi Addu'a kayi bacci kasan gobe ma akwai zuwa office ko?."

Fuska ya d'an tab'e tare da d'ago hannushi zai fara Addu'ar yace.
"aikin bankin ko aikin jaraba ni wallahi na gaji da aikin ma fa Hamma."

Ido ya d'an tsura mishi tare da tsuke fuska yace.
"Bacci fa nace muyi ba surutu ba ,
dan na lura kai kafi son zaman banza."

Addu'a sukayi sannan suka konta baccin su.

2:00 Am Doctor Umar ya tashi yayi ta nafilfili tare da karatu k'ura'ani yana mai nemawa d'an uwanshi lafiya a gun mai bada lafiyar.

Haka yayi ta karatu sai da aka kira assalatu sannan ya tashi Usman suka tafi masallaci..

Bayan sun dawo masalla cin ne Doctor Umar ya d'an koma bacci bayan ya fitarwa Usman kayan aikin shi tare da had'a mishi ruwan wonka,
yana konciya
lokacin d'aya bacci ya saceshi ,
shi kuwa Usman bai tasheshi ba dan sanin yau sai azahar zai tafi hospital d'in su.
wonka yaje yayi sannan yazo ya kimtsa ya saka kayan shi,
shiru yayi tare da kallon Hamma nashi sai kuma ya matso gaban Dr Umar Faruoq d'in cikin kallon fuskarsa yasa yatsunsa biyu ya matse hanc.........
By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBATACCEN AL'AMARI*

Page 2⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Ya d'an matse saman hancin shi kad'an tare da tsura mashi ido,
cikin bacci Hamma Umar Faruoq ya d'an bud'e ido jin an rik'e mishi hanci yasan ba maiyi mishi haka sai B'iyayen shi,
idon ya tsurawa Usman yana kallon fuskarsa da hannushi dake rik'e da net d'inshi,
a hankali ya mirgino bakin gadon yayi rufda ciki tare da zuro hannayen shi k'asa,
shi kuwa Usman k'afarshi ya turo kusa da hannayen Hamma Umar d'in.

A hankali Dr Umar Faruoq yasa hannu ya d'aurewa Usman igiyoyin takal man nashi sannan ya d'an d'ago hannushi ya manna mishi bel d'in shi,
shi kuwa Usman duk abinda Hamman nashi ke mishi binshi da ido yake yana jin k'aunar B'iyayen nashi har cikin ranshi,
yana gama manna mai bel d'in ya mik'e tsaye tare da kamo net d'in wuyan Usman d'in ya gyara mai zaman shi sannan ya kalleshi cikin muryar bacci yace.
"zo kasha tea."
Kai...


Read / Download RUBUTACCEN ALAMARI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

7 months ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

7 months ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

6 months ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album