Join Our WhatsApp Group

GABA DA GABANTA Complete Hausa Novel Document by GABA DA GABANTA


GABA DA GABANTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 143337



GABA DA GABANTA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 24, Sep 2023

Author: Aeysher Cool ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08081012143

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 727.61 kb

File Type: txt

Views: 1645+

Download: 1150+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: GABA DA GABANTA 💫

Page1

Cool ce!

Free book ne, Comment kawai nake buƙata please, if not zanyi abunda bakwa so 🌝
Typing ba kullum ba, sai an ganni kawai.

Ƙirƙirarraren labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba.

Wannan rubutun mallakina ne, ban yadda a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina, kuma ban yarda a sɗora mini shi a kowane website ba sai da izinina.




BISMILLAHIRAHMANNIRAHIM







Dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin, zaune akan benci hannunsa riƙe da 'yar ƙaramar radio, yana saurara.

Wata Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Annoconda, aka kwararo dogon layin da Ita, wanda gudun da motar take ta haddasa tashin wata 'yar ƙaramar guguwa.

A ƙofar wani makeken gate motar tayi birki, aka fara wani irin horn, sai kace yaƙi.

A gigice ya yasar da radiyon da ke hannunsa, ya miƙe a zabure ya nufi gate ɗin, yana gaganiyar buɗe shi.

Yana buɗe gate ɗin, aka turo hancin motar, zuwa wani sashi na gidan.

Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Motar, gata nan dai kamar bata cin abinci, ban da yanayin jikin ta da kuma kayan da suke sanye jikinta, ba ka ce mace bace, saboda tsabar rama, sai dai fatar jikinta za ka kalla ka gane 'yar hutu ce, da ga ita sai doguwar rigar material, da hula a kanta tana sanye da wani uban takalmi me shegen tsini.

Ta nufo gurin da dattijon nan yake kokawar maida gate ɗin ya rufe tsigil- tsigil, tana zuwa ta ƙare masa kallo sannan tace "wai kai dan Allah wani irin mutum ne? Kai ta abu kamar mara jini a jiki ko wanda baya cin Abinci? Duk Abincin da kake ci kamar gara amma ba ka da wani Amfani iye?, wallahi daga yau na kuma dawowa, ka barni a waje ina horn sai na tatala maka rashin mutunci, aikin banza ni ban ga amfanin ajiye ka a gate ɗin gidan nan ba, Daddy ya nace lallai sai kai za kai gadi"

Shiru dattijon ya yi, ya sunkuyar da kai, yana jin yadda Yarinyar ke surfa masa fitsara, 'yar da ba ta fi 'yar cikin sa ba.

Ta buɗe jakarta ta ɗakko dubu uku ta zubar da ita a ƙasa, ta ce "gashi nan ka ɗauka ka siyo mini Irish, za'a dafa mini, na store ya ƙare"

Cikin girmamawa ya duƙa ya ɗau kuɗin yace "ranki ya daɗe sai dai ban gane me ki ka ce in siyo ba"

Ta kalleshi a wulaƙance sannan ta ce "Kai abun naka ma ya yi maka yawa, to dankali nake nufi, kai Allah ya rabamu da rayuwar ƙauye rayuwar jahilci"

Bace mata uffan ba, ya juya ya fara tafiya, ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan.

Wani ɗaki ta shiga cikin muryarta ta iyayi take faɗin "Mummy, Mummy"

"Na'am har kin dawo?"

"Eh na dawo, ina wannan yaran suke?"

"Suwa kenan?"

"Maids ɗin nan mana"

"Suna sashin su"

"To na bawa wannan tsohon kuɗi ya siyo mini Irish, dan na gidan nan ya ƙare, ni kuma shi nake son ayi min fatensa da dafaffen ƙwai in yi lunch da shi"

Mummy ta ce "shikenan, Allah sa kar ya yi miki shirme"

"Wallahi kuwa, ni wallahi da za'a bi ta tawa kawai a sallami mutumin nan, shekara da shekaru ya ci abun da ya ci ai, Amma Daddy ya dage lallai sai shi ze din ga gadin nan, dan Allah Mummy ki ba shi shawara a canza tsohon nan"

Zare ido Mummy tai tace "ke Fadila rufa mini Asiri ina zaman zamana, ba ruwana"

Ɗan tura baki ta yi, sannan ta ce "Any way, bari in je in kwanta dan na gaji sosai, idan ya kawo sa karɓa, ayi mini fatensa a saka yaji sosai, sai a dafa mini ƙwai guda uku a ɗora a kai ".

Mummy ta ce "Ina fatan kin gaya musu da kan ki?".

Fadila tace "Ai ni ƙarasawa kitchen ɗin ma wahala zai bani, ni dai kya gaya musu". Ta ƙarasa Maganar tare da juyawa, ta bar ɗakin.

Tana zuwa nata ɗakin, ta jefar da takalmanta a tsakar ɗakin, ga gurin ajiye jakunkuna, amma ta yi jifa da ita wani gurin, ta cire hular kanta ta yar a ƙasa, ta haye kan ɗan matsakaicin gadonta tana hamma, tare da yin miƙa".

*******
Zaune take a gaban murhu, tana tura busassun kararen tafasa, sai uban hayaƙi ne yake tashi, sai fifita wutar take da wani ɗan ƙaramin murfin bokiti, tana jan majina, ga idanunta sun yi jawur saboda yajin hayaƙi.
Can da ƙyar wutar ta kama, a hankali ta furta "Alhamdilillah" ta sake gyara zaman tukunyar da ke kan murhun.

Sai da ta tabbatar wutar ta kama sosai, sannan ta miƙe ta tattare duk tarkacen da ta tara a gurin, ta gyara gurin, ta bar iya murhu da kararen da ke cikinsa.

Ta koma ta ɗakko garin masara a cikin buhu, da ƙwarya da rariya, ta samu guri ta zauna akan tabarmar kabar da ke shimfiɗe a ɗan ƙaramin tsakar gidan, ta fara tankaɗe.

Wata farar mata ce ta fito daga wani ɗaki, hannunta riƙe da carbi, take faɗin "Masha Allah, yarinyar kirki wutar ta kama kenan?".

Shiru tayi ba ta amsa ba.

"Ke Amina magana fa nake miki".

Firgigit ta dawo daga tunanin da take, ta fara kokawar kwance buhun garin masarar nan.

Matar tace "Amina, wai tunanin me kike yi haka ne?".

Wadda aka kira da Amina, ta yi ajiyar zuciya tace "Inno, Wallahi tunanin jarrabawar placement ɗin mu nake yi".

Inno ta taɓe baki tace "Ai sai ki yi tayi, wannan bokon ko ita ce karatun shiga aljanna yaci ace kin haƙura haka".

"Inno, dan Allah ki fahimce ni, ina matuƙar son karatun nan ne, dan Allah ko rance ne, ki aro kuɗin nan, in biya jarabawar nan, kafin Baba ya turo kuɗi".

Inno ta ce "ba abunda zan aro Wallahi, shegiyar boko da bata da wani amfani, kin yi abun da ki ka yi, sai ki haƙura haka, ki dawo ki yi Aure, amma ana ta ƙananun maganganu akan ki a garin nan, saboda baban ki ya ɗaure miki gindin wani wai sai kin yi boko, har yanzu banda tarkacen takardu, ba uban da ki ka ajiye a bokon, shekara da shekaru kina galmashura a titi yawon boko, kullum sa dai ki kawo takaddun banza ki ajiye. Ni na kusa ɗakko buhun takardun ma, in yi makamashi da shegu kowa ma ya huta".

Ba tare da gazawa ba, Amina ta kuma cewa "to dan Allah Inno, ni ki bari in rubuta wasiƙa a kaiwa Baba, ya taimaka mini, ya aikon da kuɗin in biya jarrabawar, tun da ba zaki biya mini ba".

Inno tace "Ke Yanzu ya turo da kuɗi ai muna da tarin buƙatun da suka fi na wannan bokon banzar ta ki amfani, ba wani kuɗi da zan bari ki kai wata makarantar boko".

Amina ta ɗan tura baki tace "Inno dan Allah ki dena cewa bokon banza, Wallahi ilimi yana da matuƙar mahimmanci ga rayuwar 'ya mace".

"Dalla rufe mini baki, mahimmancin me? Mu da ba muyi bokon ba mutuwa mu kayi? Ko kuwa wani abu ya same mu? Ni yi sauri ki yi ki gama mini aikina, kije wancan tijararren ƙanin uban naki, yace kije ki kaiwa matarsa Niƙa".

Take Amina ta tsuke fuska tace "ba in da zani, 'ya'ya nawa ne a gidansa, amma ni aka mayar kamar jaka, in yi aikin gidanmu, na gidansa sai naje na yi musu, Wallahi ba zani ba, idan na gama girki ruwa zan ɗebo mana".

Inno ta ce "Ni dai ba ruwana, kin san halinsa, kar ya zo yana mana ihu a cikin gida".

"Yayi da wata ba dai da ni ba" Amina tai maganar tana hura hanci.

***********

"Ke! Meye sunan naki ma? Ina Abincina da nace ku girka mini?".

Wadda aka yiwa kiran wulaƙancin, ta ɗan risuna tace "Anty ai ba'a kawo dankalin ba"

"What? Kamar yaya?"

"Eh, Hajiya tace Baba Hassan zai kawo dankali, mu karɓa mu girka miki, amma be kawo ba".

"Yanzu duk wannan yunwar da nake ji, ba'a kawo dankalin bama, balle in saka ran a dafa a bani, wato yunwa ta kasheni ba shi da asara ko? Lallai wannan an yi tsohon kawai".

"Kaiii, Fadila ya ne? Tun daga ɗakina ina jiyo muryarki kina faɗa, ke da waye ne haka?" Tai maganar tana ƙarasowa cikin falon.

Fadila kamar za ta yi kuka tace "Mummy, kinga tsohon nan ko? Tun da na dawo fa na aike shi, saboda yunwar da nake ji, amma wai haryanzu be dawo ba" tai maganar ƙwalla na taruwa a idonta, saboda ɓacin rai.

"Sorry sweetheart,yi haƙuri a kawo miki ko custard ne ki sha, kar ki zauna da yunwa, ni kaina lamarin tsohon nan na ƙular da ni, amma kiyi haƙuri". Haka ta dinga rarrashin Fadila, kamar wata jaririya.

Kaɗan ta sha Custard ɗin, ta nemi guri ta kwanta a kan kujera tana chatting, Matar gidan kuma ta maida hankalinta kan kallo.

Sallama ya din ga kwaɗawa a ƙofar falon, amma daga Fadila har mahaifiyarta, babu wanda ya iya amsawa.

Hakan ya sa shi shigowa, da uban buhu a kansa, a zatonsa ba kowa a falon.

Yana shiga yai kiciɓis da Fadila, da babarta a falon, wanda hakan ya haddasa masa faɗuwar gaba.
Ya dake tare da faɗin "Hajiya sannunku da gida, nace dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri, Wallahi na sha wahala sosai kan in samo saƙon naki, dankali yayi wuya, kiyi haƙuri dan Allah". Takaici ya hana Fadila Magana, sai wani uban tsaki da ta ja, ta gyara kwanciyarta.

Ganin ba ta da niyyar Magana, ya sa ya miƙe ya kuma sunkutar buhun, zai yi ciki da shi, har ya kai ƙofar da zata sada shi da kitchen, A sukwane Fadila tace "Kai zo nan, zo da sauri".

Ba shiri ya juyo cikin hanzari, ya dawo falon.

"Wane irin dankali ka siyo ne?" Tai maganar tana kallonsa cike da masifa.

Yace "ranki ya daɗe dankali ne dai da kika ce".

"Oya kwance buhun nan, in ga wane iri ne?".

Ba musu ya sunkuya, ya kwance buhun, ya zura hannu ya ɗakko wane irin murgujejen dankalin Hausa, jikinsa duk ƙasa, kamar a jefi mutum da shi yana nunawa Fadila.

"Innalillahi, meye wannan? Nice zanci Wannan abun? Mummy kalli abunda ya siyo, ni na taɓa cin wannan abun ne?".

A dirirce yace "hajiya ai shine dankalin".

"Shut up please, ba Irish nace ka siyo mini ba? Banda jahilci i even repeat myself, irish potatoes, kawai sai ka kawo mini wannan abun? Is not late for you, yakamata ko yaƙi da jahilci ka je kayi, ko ka dinga gane abubuwa, kar ka yadda tsufa ya ƙarasa riskarka cikin jahilci. And Carry that rubbish and leave my view, before I open my eyes, ka ɗauka kaje ka ci, wannan abincin yunwa ba zan iya ci ba, ka tashi ka bani guri"

Kalmar Jahilci, ta fi komai ɓatawa Baba Hassan rai, tare da tsaye masa a wuyansa, wani irin zafi da raɗaɗi ya dinga ji a zuciyarsa, duk da kasancewar sa mutum mai haƙuri, amma yau ya ƙulu, tabbas ba dan yana duba wasu abubuwa ba, da tuni ya bar aikin nan, amma maigidan mutum ne mai alkhairi da karamci a gareshi, kuma idan ya bar wannan aikin be san wanne ze yi ba.
Haka nan ya tashi, ya ɗau buhun dankalin nan, ya baro falon zuciyarsa a cunkushe, yana jin kamar yayi kuka, amma ya danne, saboda be san me hawayen na sa ka iya haifarwa Fadila a rayuwarta ba.

Fadila kuwa saboda tsabar ɓacin rai, sai da tayi kukan baƙin ciki, saboda yadda tsohon ya ɓata mata lokaci, ga kuma yunwa tana ji, amma ba yadda ta iya.

*******
Tana zaune a ajinsu, wanda galibi 'yan ajin nasu, 'yan wasu ƙauyukan ne, amma daga ƙauyensu su biyu ne suke zuwa Makarantar haryanzu, sauram duk an musu Aure, wasu tun a primary ma.
Abun duniya ya ishi Amina, ta rasa yadda za ta yi ta samu wannan kuɗaɗen, ta biya kuɗin jarrabawar nan.
Ga lokaci yana ta ƙurewa, idan aka riga aka yi jarrabawar nan babu ita, shikenan karatunta ya koma baya.
Duk yadda za tayi ta samu kuɗin nan ta yi, amma ba ta samu ba, gaba ɗaya dabararta ta gama ƙarewa.

"Amina Hassan, ki zo inje Malam Lawan" cewar wata ɗaliba da ta zo ta tsaya a kan Amina.

Amina tace "to ina zuwa".

Sannu a hankali ta tashi, ta bar ajin, jikinta duk a sanyaye, damuwa ta hanata sukuni gaba ɗaya.

Sallama ta yi a Staff room, ta tarar da Malam Lawan a zaune shika ɗai.

Ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa Sannan yace "Amina, yaya haryanzu shiru ba ki kawo kuɗin jarrabawar ki ba, ga lokaci yana ta ƙurewa, yaya ne?".

Jiki a sanyaye tace "Malam zan kawo insha Allah".

"To ai lokaci ne yake ƙurewa, bana son a rufe baki biya ba".

Amina tace "Insha Allah, zan kawo malam".

"To shikenan, Allah ya dafa".

Ta amsa da Ameen, ta fita ta koma aji, tana cigaba da tunani.

Duk da tsananin zafin ranar da akeyi, ba ta ji, sannu a hankali take tafiya, ita zafin ranaf sam ba ya damunta Kamar yadda biyan kuɗin jarrabawar ta ya dameta.

"Aminatuu" aka kira sunanta.

Tsayawa ta yi ta waiwaya, wani dogon matashi ne baƙi a gefen wata bishiya.

Murmushi tayi tace "Laa Saminu, ina wuni".

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya Makaranta?"

"Lafiya ƙalau, ashe ka shigo garin namu?"

Saminu yace "eh na shigo jiya, babanki har ya bani saƙo na kaiwa Inno ɗazu da safe".

Amina tace "kashh, ina ta neman yadda zan magana da shi, kafin yayo mana aike, har an biya albashi ne?".

Saminu yace "A'a, ai wata ko rabawa be yi ba, naje gaisheshi ne nace ko yana da saƙo, shine ya bani dankalin Hausa kaya guda yace a kawo muku, da dubu ɗaya".

A ranta tace 'dana san za'a kawo dankalin nan, da siyar da shi a kayi, aka bani kuɗin in biya jarrabawa, dan yanzu ko me zanyi, Inno ba za ta bari a saida dankalin nan ba'.

Ta kalli Saminu tace "dan Allah Saminu, ka aramini Salularka, in kira Babanmu, ina son yin magana da shi".

Saminu yace "ba damuwa" ya ɗakko wayarsa, ya kira lambar baban Amina ya bata wayar.

Baba Hassan kuwa yana zaune, yau tsawon kwanaki huɗu kenan, da cin zarafinsa da Fadila ta yi, amma ya kasa mantawa, ya dinga tuna lokacin da ake binsu za'a kama su a kaisu Makaranta amma iyayensu suka hana, Yanzu ga ranar ilimi.

Wayarsa da ya ji tana ruri, ya ɗauka ya kara a kunnensa, tare da yin sallama.

Cikin farinciki Amina tace "Babana".

"Na'am Aminatu na, ya kike?".

"Lafiya ƙalau Baba, munga saƙo mungode Allah ya saka da alkhairi".

"Ameen Aminatu na, kuyi haƙuri ba ayi albashi bane, ya Innar ta ki?".

"Lafiya ƙalau Baba, sai dai....

"Sai dai me?".

"Baba ance mu kai kuɗin jarrabawa, kuma bani da kuɗi, Inno kuma tace ba zata biya mini ba" Amina ta ƙarasa Maganar Kamar za ta yi kuka.

Jiki a sanyaye Baba yace "nawa ne kuɗin?".

"Baba dubu huɗu ne"

Baba Hassan yai shiru yace "Uwata kinga ba'a daɗe da yin wancan albashin ba, ki kai rashin lafiya na turo muku da duk kuɗin, kuma yanzu wata ko rabawa be yi ba, amma in Allah ya yadda, zan laluba, sai in bayar a kawo miki".

Amina tace "to Babana,...


Read / Download GABA DA GABANTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

4 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album