Join Our WhatsApp Group

DIYANA Complete Hausa Novel Document by DIYANA


DIYANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38379



DIYANA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 09, Aug 2023

Author: Zainab Habib Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 205.96 kb

File Type: txt

Views: 1158+

Download: 376+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*DIYANA*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



Whtsapp: 08141799224


*BIRNIN TARAIYYA ABUJA WUSE TWO.*

Anguwa ce mai cike da manyan masu kuɗi ga kuma tsararun gidaje kamar a ƙasar turai .

A cikin anguwar akwai wani ƙeraren gida mai kyan gaske gidane daya sami ƙwararun magina masu aiki da ilimi , tun daga wajen gidan zaka gane mai gidan hamshaƙi ne wato Alhaji Sani ana kiransa da Alherin Allah , babban ɗan kasuwa ne sananne a kowace ƙasa kuma kowane fanni yanada kamfanoni da dama dakuma motoci wanan kenan.
daga gefe ɗakin mai gadi ne can kuma gefen kudu da arewa shuke shuke ne na wasu kyawawan flowers gwanin sha'awa , ga wasu ɗawisu da suke kaiwa suna komowa guwanin birgewa .
Iyalan gidan ne zaune a palon da za'a iya kiransa da aljannar duniya iya tsaruwa ya tsaru nera tayi kuka musamman ma danƙara danƙaran kujerun da suka mamaye palon ,wata farar mata ce zaune a ɗaya daga cikin jerin kujeru sai wasu ƴan mata su biyu masu kama da ita amma sun fita haske matashiyar matar ce ta dubi ɗaya daga cikin ƴan matan tace "Diyana zakuyi dare fa kinga har yanzu dadynku bai fito ba ,
Wace aka kira da Diyana ce ta taɓe baki tare da lumshe fararen idanunta masu ɗauke da zara zaran gashin gira tace "mom ni dama bason zuwa ƙauyen nan nakeyi ba dady ne ya matsa mini wai nice banison zuwa duk cikinmu ,
Budurwar dake gefe ce ta dubi momy fuskarta da alamun ɓacin rai tace " mom village ɗinnan ya cika sauro gakuma rashin tsafta ,
Diyana ce tace " good Afreeda ashe kin gane ,jin maganar tasu zatayi yawa ne momy tace " shiii alamar suyi shiru dan tajiyo takun mai gidan nata ,
ƙarasowa yayi da shiga ta alfarma a jikinsa shadda ce gezna fara wace tasha aiki , momy ce take ƙare masa kallo da murmishi a fuskarta shima mayar mata yayi tare da kallon su Diyana da Afreeda da hankalinsu ke kan wayar dake hanunsu ,
Dady ne yace " to nagama so ke nake jira rau rau Diyana tayi da ido tana kallon mom ganin batace mata komai ba yasata miƙewa tana bubuga ƙafa Afreeda na dariya ƙasa ƙasa ,
Dan tasan ita zata iya jure wuyar ƙauyennan amma Diyana kam tana tausaya mata, dady waje yayi dan shima ba mai son yawan magana bane kamar mom ,
Hand bag ɗinta Afreeda ta ɗauko mata tare da wata jaka mai kyau da alamu itace jakar kayan nata ,
mom ce ta miƙe ta nufi step ɗin dake tsakiyar palon bata ɗau lokaci ba sai gata ta fito da wato leda fara ƴar baba ta miƙawa Diyana , buɗewa Diyana tayi taga su man shafawa ne masu tsada dakuma takalma harda atamfa itama mai tsada kana ga turaruka , taɓe baki Diyana tayi tace "mom wanan kayan wa za'a kaiwa granny ɗinku taɓɓ hmm Diyana tasa kai ba tare da takuma cewa komai ba ,
Jerowa sukayi tare da Afreeda idan kaga yanayin tafiyarsu kai kace ƴaƴan sarakuna ,
Fuskar Diyana babu fara'a kasancewar dady na cikin mota yana waya hakan ya basu damar yin magana , Afreeda ce tace "Anty Diyana saifa kin daure da mutanen village ɗinnan dan lokacin da mukaje wlh cemin sukeyi anyi jar fata tashigo ƙauye kokuma sudinga bina suna kallo na ,
Dafe kai Diyana tayi kana tace " nashiga uku nikam nima haka zasuyimin ? har Afreeda zata yimata magana dady ' ya katsesu zo mu tafi ,
dady na back side ita kuma ta shige gaba dan batason zama kusa dashi kasancewar ba tun yanzu ba ya hanasu chart eyepice tasa a kunnen ta kana ta jingina kanta da kujera ta lumshe ido driver na shiga suka ɗauki hanyar ƙauye .

*KANO. ƘAUYEN SHAFA*
Ƙauye ne mai gidaje jifa jifa dakuma mutane iri iri yawancin gidaje nasu duk rufin ɗakin anyishi ne da jinka basu damu dayin katangu ba wasu kuma sunayi kana babu ginin siminti sai a wani gida dake gefe shi kaɗai .

Bacci mai daɗi ne ya ɗauki Diyana dady kam hankalinshi na hanya dan sun shiga kano a halin yanzu ma hanyar ƙauyen suka dosa , wata irin gargada suka shiga wace tayi nasarar farkawar Diyana a tsorace ihu ne kawai bata kurma ba ga mumunan faɗuwar gaba ,
Ƙarewa ƙauyakun kallo tashiga yi tana salati badai nan ne kauyen ba taɓɓ gashi dady yace " 5 days zanyi ina bazan iya ba , duk cikin zuciyarta take wanan maganar jin anyi parking yasata ɗago kai tare da juyawa ta kalli dady dake tattara wayoyinsa a kan siddin motar dady har mun iso ne ?" yes daughter yau zakiga granny ɗinki , yana maganar da murmishi a fuskarsa,
driver ne ya fito ya buɗewa dady mota kana ya buɗewa Diyana , a tare suka fito daga motar hanunta riƙe da wayoyinta guda biyu tabi bayan dadyn ,
Daga bakin ƙofa dady yai sallama jin muryar wata tsohuwa yasa Diyana waro ido dan ganin wacce mata ce zata fito ?".
Wata tsohuwar mata ce fuskarta taɗan tamushe haƙoranta sunji jiki tsabar cin goro tasa riga da zani dakuma ɗankwalin yadi barka da zuwa Alhaji tanata faɗaɗa fara'arta ywwa Hajiya , Hajiya ce tace " to kuzo mushiga jikalle ansha hanya ta dubi Diyana ,
Yamutsa fuska Diyana tayi batare da tace " komai ba suka shige ciki .
Tsakar gidan da yaji siminti fess yake a share ko tsinke babu amma hakan bai sa Diyana dena yatsina fuska ba tana tattare kayanta wai karsu ja ƙasa , shiga cikin ɗakin sukayi da yake malale da leda babu kujera sai ƴar tuguno Hajiya ta miƙawa Diyana batare da tayi magana ba ta karɓa ,Hajiya ce tace " Alhaji a ina ka samo wanan ƴar gwallin ?"dan naga kamar ba wannan bace da ta taɓa zuwa shekarun baya ?.
Kawar da zancen dady yayi ta hanyar durƙusawa yace " Hajiya bamu gaisa ba ina wuni washe baki Hajiya tayi tace" lafiya lao Alhaji ya aiki ya hidima yakuma Faɗimatun buɗe baki Diyana tayi cikin zuciyarta tace " waye Faɗimatun komai sai an ɓatawa mutum suna mom ce Faɗimatu taɓɓ ,
Dady ne yace " tana gaisheki Diyana ce ta kalli driver tace " kaje motor ka ɗauko wata farar leda ka kawo min , to driver yace " cikin rawar jiki ya fice Hajiya ce ta miƙe ta fita sai gatanan da kwanon fura da nono a wani baban kwanon silba da suga a leda dakuma ludayi ,
Tunda Hajiya ta shigo da nonon Diyana take keɓe baki dan inba na kanti ba batashan wanan , driver ne ya dawo hanunshi riƙe da ledar ya durƙusa yace " ranki shi daɗe gashi karɓa tayi ta ajiyesu gaban Hajiya batayi magana ba , kallonta kawai Hajiya takeyi dan a bisa dukka halamu jininsu bai haɗu da Diyana ba , dady ma ya lura da rashin sakewarta dama yasan halin abarsa ko anyi abinci a gida bataci inba tayi ra'ayi ba drinks sune kayan shanta sai cake da shauransu .

Alhaji nayima magana a inaka samo wanan yarinyar mai kamada aljana kayimin kunen uwar shegu ko ? dady ne yace "Hajiya Diyana ce fa ko kin manta ta yayar Afreeda ,kaji ai kusawa yara sunan mutunci bazaku sa ba sai wani suna mai kamada na biririka ,dariya ce taso kuɓucewa Diyana amma ta make , miƙawa dady haɗin furar tayi kana ta miƙawa driver dake zaune can gefe a tabarma takuma ajiyewa Diyana a gabanta yatsina fuska Diyana tayi kana tace "I dont like this thing dady ta miƙe tana tari , la haula wala ƙuwata illabillah Hjiya take ta mai maitawa tana tafa hannu ta dubi Alhaji tace " mudai bamu ɗauko wanan mugun halin ba gaskiya ɗayar ƴar uwarta tafi daɗin sha'ani ,
Nikam yaushe zamu jitu da wanan mai kamada zabiyoyin chaɓɗijan ,
Diyana dai na zaune dan hankalinta na kan wayarta maganar da taji dady nayi ne yasa ta juyo a tsorace " zaku jitu ita da zata yimiki sati ,
Washe baki Hajiya tayi tace "aiko dana sami ƴa suka haɗa ido da Hajiya Diyana ta sakar mata harara ,
Dady ne ya kalli Diyana yace " wai kin mance gurin wacce nace miki zanzo ne ?" wanan fa da kike gani mahaifiyata ce walh zan saɓa miki , Diyana dai kanta na ƙasa ba ma'abociyar surutu bace , wata yarinya ce ta shigo da gudu tana cewa kaka yau bazakije itacen bane ? Hajiya dake shan rahowar furar da dady ya rage tace " nayi baƙi jeki cewa mamanki Alhaji yazo to yarinyar tace " kana ta fice da gudu .
Da isarta gidan nasu dake zagaye da dangar kara tafara ƙwalawa mahaifiyar tata kira tana cewa " Talatu ki fito wanan yayan naki na bini yazo wlh harda baturiya kiyi sauri ,
Talatu dake ɗaki tana fere rogo ta leƙo tare da cewa da gaske kike yi tinene eh ? yasin kizo zaki ganhi harda baturiya ,
Yafo gyale talatu tayi jiki na rawa ta saka takalmin ta ' ta fice ta kwashi sauri dan tasan yau ta warke .
Kasancewar basuda nisa sosai dan danan sai gata a ƙofar gidan ganin sabuwar mota ne yasata tabatarwa ,tinene ce ta biyota da gudu tana cewa " Talatu kinga zahiri ko ga motarhi nan , ƙarasawa sukayi tayi sallama Hajiya ce ta amsa gimbiya Diyana na sallah a sallayar da ta ɗauko a mota ,
Harkin iso Hajiya tace tana washe baki yayanki ne yazo kuma yau ze wuce shine nace "tinene ta kirawo ki , Talatu na fama da susar kai tace " ai ganinan Inna ina yaje ne ? Hajiya ce tace?yaje sallah ai ba jimawa zaiyi ba yanzu zai dawo,
Talatu ce ta cire mayafin kanta tare da cire ɗankwali tasa hanu biyu tana sosa kanta ,
Hajiya ce ta dubeta tace " wai talatu har yanzu baki sawa ƙwarƙwatar magani bane ?dagudu Diyana ta miƙe ta daka tsalle sai gata a waje , shigowar dady ne yasata sunkuyar da kai tace "sannu da dawowa dady ywwa daughter lafiya na ganki a nan ?" kafin tayi magana Hajiya tace " uwarta Talatu take gudu dady ne yace " to maiya faru ? Diyana idanunta cike da hawaye tace " Dady ka tafi dani wlh bazan iya zama a nan garin ba ,

Kinci gidanku dady ya cewa Diyana , ya shige ɗakin Hajiya washe haƙora Talatu tayi tace " yaya hannu da zuwa kunsha hanya , wlh kuwa ya yara ? lafiyansu lau Alhaji ya hidimomi mungode fa , babu komai Alhaji yace " yana kallon tinene wanan ƴar gurin waye ?, Hajiya ce tace " ɗiyar Talatu ce fa gatanan kamar ka kifeta da kwando ga guru gurun idanuwa kamar na waccan ta wajen ,

Kwashewa da dariya sukayi Alhaji ya miƙe yace "toni zan tafi Diyana kiramin driver kokuma kice ya kwaso kaya a mota oky tace " ta fice tare suka shigo da drivern hanunsa ɗauke da buhunnan shinkafa da katan ɗin taliya da jarkar man gyaɗa da maggi da gishiri , dubu arba'in dady ya miƙawa Hajiya ita kuma Talatu ya bata dubu ashirin ai kamar an jefata a aljanna tahau zuba godiya tana ƙarawa ,
Dady ne yace "hajiya nanda wata ɗaya zaki dawo ABUJA dan wlh kina kusa abin zai fi ,zaro ido Diyana tayi tana nazarin irin zaman da zasuyi da wanan tsohuwar mai bala'in sa ido amma babu komai da ƙafarta zata nemi ta dawo ƙauyensu , hajiya na kuka tana sanyawa dady albarka tare da duk abinda yasa gaba ,
Shigewa cikin palon Diyana tayi tare da ɗauko jakarta ta dubi dady zan bika bazan iya zama a nan garin ba cikin ɓacin rai dady yace " anan na girma komai nawa anan yake kaf cikin ƴaƴana kece mai tsananin ƙyamar jinina ,to dole ki zauna har sati ya zagayo saboda zumunci abu ne mai ƙarfi , kuka Diyana takeyi kamar ranta zai fita da ajinta da komai ta zauna a wanan banzan gidan wanda ko ɗakin zuba shararsu bai kai ba wajen kyau , niko nace wanan gida da kike rainawa shine ƙurewa gurin kyau a wanan ƙauyen ,
20k dady ya bata yace " to mu mun tafi Hajiya najin duk dramar da sukeyi taƙi kulasu Talatu ko tsabar murna har yanzu murmishin fuskarta bai ɗauke ba, dady 20k is to shot tana bubuga ƙafa 5k ya ciro ya daɗa mata yana bata haƙuri akan zai turo driver ya zo ya ɗauketa , Hajiya ce ta matso tana cewa maganar sai kace ta munafurci da wani yare kukeyi dan kar ajiku ko , wlh Alhaji ka sakalta ƴaƴanka da kashe kuɗi , dariya dady yasa dan inya biyewa Hajiya bazai tafi yanzu ba , shigewa mota yayi yana ɗaga musu hannu ,
Tinene dake gefe tana ƙarewa Diyana kallo gaskiya kaf cikin ƙauyenan bata taɓa ganin mai kyau irinta ba gaskiya ƴan binni sunji daɗi ko kaushi basuyi bare faso, Hajiya ce tace " baiwar Allah taso mu higa gida yamma tayi Talatu ce tace " Hajiya nikam nayi gida yau zamu hyarɓi jar miya yasin yaya Sani ya jiƙani da nera ai wlh ko Ado bazan nunawa ba dan yana ƙyala ido to zai rabani dasu ,
Hajiya ce tace " harkin gama abincin ne ? a'a wlh ina cikin gyaran rogo he ga tinens tazo kirana wai Alhaji yazo inafa zan gama tinene ce ta kwashe da dariya kana tace " wayaga kaka a binni yasin sai sun koroki ,

Hajiya da haushi ya ɗebeta tace " cin uwaki niɗin bzan iya zama a can ɗin bane to kikasa wasa ma dake zani , Diyana ce takuma cika a zuciye ta shige tabarsu anan sunata surkulllen maganarsu....!

Kubiyo ni dan jin cigaban labarin ya rayuwar Diyana zata ƙare a ƙauye biya 200 ki karance shi cikin kwanciyar hankali .
[

Mangariba ta sako kai Talatu ta wuce gida itama kamar ba mai son mutane ba dan kamar batasan Diyana yarinyar Alhaji bace kodan yangar da taga tanayi ne oho ,
Tinene da bata wuce gida ba ta dawo gidan Hajiya ta zauna a bakin kofa ,
Hajiya ce tace " tahi karki janyo mana fitina kina sane almuru tayi ,tinene ce ta harari Hajiya kana tace " wlh sa ido yayi yawa ƴar birninnan da wuya ta iya zama dake wataran sai tayi kamar zata gudu ga ki da gani babu ƙyalewa ,
Tafa hannu Hajiya tashiga yi tana salati tare da cewa" au ni zakiyiwa cin mutunci wlh Ado kika yiwa ba niba hyahya hya kawai wanan kalmar tabawa Diyana dariya dan duk ɓacin randa take ciki sai da ta dara ,
Tinene ce ta miƙe tare da karkaɗe...


Read / Download DIYANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album