Join Our WhatsApp Group

LAULAM Complete Hausa Novel Document by LAULAM


LAULAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38623



LAULAM

Reading Time: 3 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Sadee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *????ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION????*

Author Phone : 09129216255

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 228.46 kb

File Type: txt

Views: 683+

Download: 284+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: *LAULAM* ( _Kishiyata_ )


Na



*{SADEEY}*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊAN TARWA GAMIDA WA'AZANTARWA HUNMM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITE'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITTE'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*






*GODIYA*
~Dukkan yabo da godiya su kara tabbata ga Allah ubangijin halittu, mai kowa mai komai, daya vani ikon rubuta wannan littafin, salatin da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu Annabin rahama SAW.~





*TSOKACI*
_Wannan labarin k'ageggen labarine, banyishi don wani ko wata ba, idan har kika ga yazo daidai da labarin rayuwarki, to kuskure ne._



*GARGAD'I*
_Ban yarda wani ko wata ya juya min littafina ba tare da izini ba, ko ya d'auki wani bangare daga ciki ba, don hak a kiyaye._



*SADAUKARWA*
```Na sadaukar dawannan littafin, ga mahaifiyata abun alfaharina, ```HAJIYA AYSHATU UMAR MADAKI``` Allah ya jinkanki ya gafarta miki, yasa kin huta, ubangiji yasa mutuwa hutuce a gareki.mukuma ubangiji ya k'ara mana hakurin rashinki.```




Page....1&2



––––– Nafara nisa cikin gyangyad’in dana fara, wanda haryakai ga mafarkan bazata sunfara ziyartar k’wak’alwata, batare da zato ko tsammani ba naji sauk'ar ruwa mai sanyin gaske yana ratsa sassan jikinta.
Sanyinne ya ratsa ilahirin jikinta wanda yai sanadiyar farkawata cike da fargaba, tsoro, da razani duka lokaci guda suka dirar mini, ba komai ya haddasamin hakan ba sedan sanin cewa INNA ce mai min wannan aika-aikar.

Kuka nafashe dashi wanda yai sanadiyar k’aruwar ɓacin ran Inna haryakai ga tad’aka mini duka tare da cemata...

”Munafukar Yarinya!  yanzu tadakin da nayi donki tafi d’ibamin ruwa ashe baccin naki na asara kika cigaba anan?, lallai kin isa kuma jikinki seya gayamiki, inhar baki tashi a gurinnan ba,”

Inna ta fad’i haka tare dasa k’afa tabuge ni sannan tawuce tana bambami.


Ina kuka tare da rawar d’ari haka nanufi inda tulun d’iban ruwana yake na d’auka sannan na nufi rafi, don dib'o mata, to wallahi muddin bai diboba, to wallahi na kahira sai ya fini jin dadi.....

Ahanya ban had’u da kowa ba saboda lokacin yawancin al’ummah suna gida suna bacci wasuma suna kaiwa ubangijin halittu kukansu kasancewar gari baigama wayeba.


Ina tafiya ina shan wahala haka harna isa rafin, kasancewar muna da tazara sosai da rafin amma hakan baisa Inna ta jin tausayina ba, watannin baya da suka wuce wani mai kud’i yashigo garinnamu tare dasawa akajawo musu ruwa kusa damu, amma saboda son zuciya irinna Inna tace batason ruwan dake fitowa daga k’arfe
na rafi takeso.


Haka  na isah  rafi  na debo ruwa.
 
Wanda ya ɗaukeni lokaci mai tsawon gaske. A  daidan wannan lokacinne
Kuma innah ta fito tana gyara ɗaurin  Zaninta tare da yin dogon hammah.

kallon ILHAAM tayi tare da jan dogon  tsaki "tace   me kike kallona da shegun idanu kaman na mayu  nikam karki cinyeni Mayyah  kawai, mai siffan aljanu,

"Shuru nayi tare da sadda  kaina ƙasa domin ina mugun tsoron innah.

Inna buta ta ɗauka  tayi hanyar band'aki.

tana fitowa daga band'aki tayi hanyar Badauru (madafi) domin yin dumame...



Kallona tayi kana tace " kije daki ki tayar min da yar lele, sauran ki mata mugunta, wallahi sai na sab'autaki,


Da to na samsa kana na kama haryar shiga ɗakinmu, inda muke kwana tare, ita a gado ni ka akan taburma,


Kallon yarinyar dake bacci nakeyi wacce a girme na girmeta, kafin nasa hannu a gefen kumtunta na fara tada da daga bacci,


Ido ta buɗe tana ganin nice tasa kuka ta ƙarfin gaske, wanda yasa INNA faɗowa ɗakin kaman an jehota,


Cikin kidima tace " `Yar Lele mene? Gaya min meke faruwa?


Cikin maganan ta na taɓararrun yara ta fara cewa "ba ILHAAM bace ta dinka kwad'amin mari, ta k'arasa maganar tana saka kukan karya,


Tass! INNA ta d'auke `yar k'aramar fusktata da mari, wanda yayi sanadiyya ganin duhu na wani lokaci,


Kana ta fara cewa " wato dai ni ban isa na saki kiyi abu, kuma kiyishi ba ko? tayar da itan da nace kiyi shiya baki daman marinta, to wallahi irin haka ya kuma sake faruwa kiga yadda zamu kwashe adashen tsiya dake, shegiya munafuka mai fuskar salihan bayi, wallahi ILHAAM idan kikayi wasa ni zanyi ajalinki! wuce ki ban waje, kuma yau baki da abincin safe a gidannan,




Kuka nakeyi tamkar raina zai fita, tunda naji sauƙin mari akan kumatuna, dama nasan hakanne zai kasance dani, kullum haka Zainabu take min, bandaketa ba tace na daketa, INNA kuma sai ta yarda kuma ta rama mata.


Hannun Zainabu taja suka fita waje, kafin tace min "aikin san ayyukanki ko? to dan Allah karki zo kiyi kici gaba da tsayuwa kina min kukan munafurci,



Fita sukayi hakan yasa nabi bayansu, ruwa tasa a buta ta miƙawa Zainabu a yayin da ni kuma na d'auki tsintsiya don yin shara,


*******
Bayan  innah ta gamane
Ta kalli gefen da nake, tare da jan dogon tsaki mtswww kana "tace wato ke bakisan ya kamata ba ko? sai na gaya miki kullum?

Shuru nayi  tare da tashi saga inda nake zaune na iso gurin da innan take,

Sunkuyawa tayi da niyyar ta daukan akushin da aka saka tuwon Bappah,. ba zato ba tsammani naji saukan  dundu a bayana wanda najishi har cikin ranta, kuka tasa tare da tsugunawa kasa,

Kafah innah ta sa sake  shuretah, wanda yayi sanadiyyar  buguwan kanta ajikin gini, ihu tasa  wanda ya k'ara hasalar da Innah, cikin haushi da kuma rashin controlling anger ta wawuri itacen murhu wanda yake da wuta ta jefini dashi.....





Idan naga ruwan comments sai naci gaba.




Ayi sharing fisabillah👏👏




09129216255
Sadeey ce

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/H0U1Ksenq6qD6oJn9H2Iyc


*LAULAM*
( _Kishiyata_)




*Alk'alamin SADEEY ce.✍️*






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_



Page....3&4


–––––––Jifana tayi da itace wanda cikin tsautsayi ya sauka akan ƙafata, cikin azaba na kurma ihuu, wanda ya k'ara hatsala inna cikin tsawa tace
"dallah rufemin bakin tun kafin na ƙona wannan jememmiyar fuskar mai kama da na tsohuwar jimage, wuce ki tafi dallah munafuka kawai yarinya k'arama sai shegen iyayi da gulma, munafuka annamimiya, wuce ko na sa'bautaki, ai wallahi idan kikayi wasa sai nayi ajalinki".



tashi nayi kawai ta nufi inda naga an ajiye akushin tuwon Bappah, da nufin na d'auka don kai masa, hakan ma Inna bata barni ba sai ta bata kyakyawan rangwashi, wanda sanadiyyar zubowar hawayena akan kyakkyawar fuskata.

d'auka tayi ta nufi hanyar waje,

tafiya nake cikin sand'a da kuma nutsuwa irinna nutsatstsun Yara.


Tafiya mai nisa ce ta kaini bakin wani Babban garke, mai cike da arzik'in dabbobi, duk dama garken jinsin dabbobi biyu kad'ai ya hada shanu da kuma tumaki, sai hakan bai hanashi cika ba.



Mutane biyu ne a cikin garken, wani farin dattijo mai cikar kamala, Wanda yake tsananin kama dani, yana tsugeni ƙarƙashin wata farar tsohuwar Saniya, yana tatsa cikin k'warewa, sai kuma wani d'an saurayi, dake d'an nesa damu kad'an.


Cikin sanyin muryan da Allah ya azurni dani, na gaishesa, duk da nasan ba amsawa zayyi ba. Don tunda nayi wayo ban tai taɓa yi min magana ba, baya shiga harkana, baya kulani,


Gefe na samu na rakuɓe, tamkar wata MARAINIYA ko kuma wata Mara galihu,



Bai d'au lokaci mai tsayi ba, ya kammala tatsan, sannan ya tura k'waryan gefe, kafin ya fara kunce dabbobin don tafiya kiwo,ganin haka yasani yin wajen k'waryan domin nasan koda zan kwana a wajen bazai taɓa tanka min ba.

cikin sanyin murya nace Bappah "Useeni rondam (dan Allah kad'aura min) shuru yayi tamkar baiji me tace ba, ko kuma wanda baya gurin.



sai daya gama abinda zaiyi kafin yazo ya d'aura mata, ba tare da ya kalli ko fuskarta ba, "Miyetti " (nagode) itace kalman data fito daga bakina.

Daga haka ta juyo don tafiya gida, ta samu ta isar da Nonon cikin gari, don wallahi idan nayi letti mai rabani da Inna sai na sama,


hanyar gida na kama ina tafiya cikin sanyi kasancewar k'waryan babbace sannan tana rawa-rawa, yasani tafiya a hankali,

Ina cikin tafiyanne naji ana kirana.
Sanin cewa bazan iya juyawa ba ya sani tsayawa a gurin tamkar an shukani, domin nasan ko wa cece mai kirana,

ba kowa bace fa ce k'awata, kuma Mak'ociyarmu wato
Malle Yar gidan Malam Liman abokin bappana,

tsayawa nayi mukad'an tab'a hira, acikin hiranne Malle kece mini ko yau zamu fita wasa kofar mai gari?



Cikin sanyin daya zama d'aya daga cikin d'abi'una nace " a'a

Cikin b'ata rai Malle tace meyasa?

"Nikam gaskiya bazan jeba, ranan ma da naje Inna tamin duka, kuma ta hanani abinci na wuni banci komai ba, kin tuna ranar sai da na ɓuya naje gidanku? ta k'arasa maganar cikin sigar tambaya .



Kai Malle ta gya d'a alamun ta tuna,
sannu tace "toh sai mun had'u ko a rafi ne kinjiko?.


Sallama mukayi
kana muka rabu kowa yayi hanyarsa.


Ina cikin tafiya kawai naci mugun tuntuɓe, kaman an d'agani sama haka naji,
Timm na faɗo ƙasa, ƙwarya tayi gefe, gammo gefe sannan ni gefe.
Acikin mutane masu wucewane wasu suka taru a kaina har aka tada ni,

kuka nake mai tab'a Zuciya, kuka nake na fitan hankali, irin kukan mai tsoron abunda zaije ya dawo, nasan ko wace irin mugunta na Inna duk da a shekara banfi 10 ba, amma babu abunda bansaniba, na daga komai na gidanmu.

Ina cikin wannan tunanin karaf idanuna suka sauka akan ƙwaryan nono wanda sanadiyyar fad'uwan da nayi ya rabe gida kusan biyar...






Wannan kenan



******
Kwance yake akan tank'amemen gadonsa k'iran Italy, Idanunsa lumshe suke tamkar mai bacci sai dai kuma nazartaccen kallo na minti ɗaya mai kallensa zai gane tabbas ba bacci yake ba.



K'aran murla handle ɗin da yaji anyi ne yashi sauke ajiyan zuciya, duk da yasan babu mai shiga masa d'aki ba knocking, ko sallama, sai mutum d'aya,



wato Meemy little sis d'inshi,(ƙaramar ƙanwarsa)
sai dai hakan baisa ya bud'e idonshi ba,
da gudu ta shigo tare da fad'awa jikin shi, tana haki irinna wanda ya gudu,



cikin sauri tace " ya IMRAAN Mamy tace na kiraka, wai kazo, daga fad'ar haka ta tashi da niyyar fita a guje hannunta ya rik'e, ciki sanyin murya yace "Meemy wai nikam ban hanaki shiga min D'aki ba sallama ba knocking ba?

Zumɓuro baki tayi cikin surutu tace "sorry bross na manta ne but bazan sakeba, i promise, next time zanyi sallama,



Shuru yayi don dama yasan abunda zai fito daga bakinta kenan, don kullum idan ta shigo kuma ya mata gyaran haka, to abunda zata gaya masa kenan.



Ganin bai saketa bane yasata cewa cikin shagwaba tace "please let me go, zanyi failing game dina,
cikin ƙosawa da maganan yace mata " ina Mamyn take?
cikin sauri tace "tana side ɗin Abba,



daga haka ya sake mata hannu , ai kaman jira take ta falfala da gudu, a d'ari ta bar masa ɗakin.

Tashi yayi ya nufi wajen wardrobe ɗinshi, don saka kaya, kasan cewar singlet ne sai 3quater a jikinshi.



Ana na samu daman k'arewa ɗakin kallo ganin irin had'uwar da ɗakin yayi ba kad'an ba ne, furnitures d'in ɗakin brown an milk colour ne, haka ma cotton milk, sai k'aramin carpet d'in dake ɗakin shima Brown ne da d'an ratsin milk, sai a d'an gefe akwai study table,(teburin karatu). Ɗakin bayida tarkace, komai a kimtse yake, ba k'aramin had'uwa yayi ba.


Bud'ewa yayi ya d'auki jallabiya White colour kana ya saka, daga nan ya d'auki wayoyinsa dake kan Bed side drower, d'insa ya zura acikin Aljihun Jallabiyansa , kana yayi waje, don amsa kiran Mahaifinsa.

Corridor d'in da zai sa dashi da side ɗin Abba ya nufa, tafiya yakeyi a hankali, tamkar mace mai ciki,



A kallon tafiyarsa mai kallonsa zai dauka cewa shi d'in ya hada jini da sarauta, sai sai shi ba kowa bane jinin MODIBBO. sai daya yaje dab da bakin ƙofa kana ya tsaya,



cikakkiyar sallama yayi cikin muryansa mai d'adin sauraro.

Chan ciki yaji an amsa kana ya kutsa kansa cikin palourn.



Magana yake taji k'asa-k'asa, acikin palourn. Kallon inda wajen nayi nan na hango mata da miji a zaune akan kujeran 3str daga gani kasan hutu, da kuma kuɗi sun samu wajen zama.
Mijin zai kai kaman 57-59 years. Itakuma matar bazata wuce irin 45-47 da haihuwa ba Amma kuma yanayin hutu da kuma jindaɗi yasa baza kice takai waɗannan shekarun ba suna tsananin kama da IMRAAN sosai especially ita ma don har kaman ta baci.



Zama yayi a ƙarƙashin ƙafafunsu, kana yace



"Barka da rana Abba,


Fallonne ya d'auki shuru bakajin karan komai sai karan AC da kuma TV, kowa da abunda yake tunani acikin ranshi, musamman Mamy wacce tunanin rabuwa da d'anta, da Ubangiji ya mallaka mata guda biyu.



Chann Abba ya numfasa kana yace "Babana dama na sa a kira kane akan maganan nan tamu, meka yanke akai?

Shuru yayi kaman mai nazari,

Harga Allah baya son tafiyannan, ba kaunar rabuwa da gidansu, Yan
uwansa yake ba,

Ganin yayi shuru bai tanka ba ne yasa Mamy cewa " amma kanaji magana dai ko?

Cikin yanayinsa na rashin son magana yace " ba komai abba, komai ku kayi a kaina dai-dai ne,
Ku iyayena ne, nasan bazaku zab'a min abunda zai cutar dani ba".


Numfashi ya fara mayarwa da sauri, saboda seconds d'in ɗaya daya ɗauka yana magana.



Numfasawa abba yayi kana yace.....




**********
Ihuna ne ya k'aru, saboda tashin hankali, da fargaban dana shiga,


don wlh nasan yau mai kwatana a hannun Inna babu shi a duniya, domin wannan k'waryan dana fasa k'waryane da take mugun ji dashi, saboda na gadone,wanda mahaifiyarta ta bar mata.

Da k'yar na tashi ina kuka mai ban tausayi, da tab'a zuciya, hanyar gida na nufa, ina tafiya ina kuka, har ta isa gidan,



Inna dake zaune da tsinke a hannunta tana sakace haƙora,


kukana ne take ta jiyowa daga nesa, har na shigo cikin gidan,


Harara Innah ta gallamin kana tace


" to yau kuma me aka kwaso ƴar jaraba? jarababbiyar banza, ke kallum kuka,


toh Wallahi ahirr ɗinki nikam...


Read / Download LAULAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album