Join Our WhatsApp Group

SAMIMI MACIJIYA CE Complete Hausa Novel Document by SAMIMI MACIJIYA CE


SAMIMI MACIJIYA CE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28359SAMIMI MACIJIYA CE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 25, Jan 2024

Author: Momy Ahlan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 147.04 kb

File Type: txt

Views: 1004+

Download: 474+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: [02/09 à 08:44] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)

Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)

Gajeran labari.


BABI NA FARKO. ✍🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*_ALHAMDULILLAH,DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI, SALATI, DAUKAKA, TSIRA,AMINCI SU KARA TABBATA GA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU S,A,W, YA ALLAH YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA_* 🤲🏻


_Ƙirƙirerren labari ne, kuma free ne ba na kuɗi bane, ban yarda a juya min shi ta ko wani siga ba, banyi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yayi dai-dai da labarin ka/ki kuyi hakuri akasi ne_


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!! Innalillahi ilayhirrajun!! Yanzu Baba Malam *SAMIMAN* ce _Macijiya!!!_?"
Nisawa Malam ya yi ya kalli Mahaifiyar Samima wacce zufa duk ya wanke mata fuska sabida tsananin tashin hankalin da take ciki, ya ce.
"Tabbas, shakka babu *SAMIMA MACIJIYA CE* kuma sihiri aka yi mata ta zamo haka, ba ƙaramin sihiri bane, kuma dole wacce ta yi mata ita ce zata ruguza wannan sihirin, in ba haka ba zata ci gaba da kisa ga duk wanda ya tabota, kuma a zahirin gaskiya ba ita ke kisan ba, miyagun da take tare dasu su ne suke kisan, sabida itama basu barta ba, lokaci zuwa lokaci su na gana mata azaba, ba ƙaramin babban yaƙi bane rabata dasu, kuma na gaya maki dole wanda ta yi mata wannan sihirin itace zata warware shi, kuma ta cikin gida ce ta yi mata wannan sihirin" share hawaye Umma ta yi ta ce.
"Malam, kana ta faɗin ta cikin gida ce, to wacece kenan?" shuru Malam ya dan yi yana nazari kafin ya nisa ya ce "a gaskiya baya cikin tsarin aiki na gaya maki, amma sabida Samima tana bukatar taimako cikin gaggawa yasa zan faɗa maki, ba kowa bace ta yi mata wannan sihirin illa *ASABE*" a zabure Umma ta miƙe ta ce.
"Baba Malam!!!? Asabe!!! Asabe!! Asabe fa ka ce!!? Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!! to me na yi wa Asabe? Ko kuma nace me Samima ta yiwa Asabe? Abun da Bamu haɗa Miji ba, balle nace ko kishi ne yake nukurkusanta da zai sa ta yiwa ƴata asiri , ina da ƴa mace tana da mace, to miye haɗina da ita da har zata mai da Samima rabi mutum rabi Macijiya?" murmushi Baba Malam ya yi ya ce.
"Kadan daga cikin halin Ɗan Adam, *ZULAIHA* shekara na 30 kenan a garin nan tun kuna ƙanana a lokacin da muke tare da iyayenku kafin Allah ya ɗauki ran mahaifinki, nine Malamin da da yawan yan unguwan nan ake kawo min su laluri, kumq alhamdulillah Allah ya horemin baiwa iri da kala, bazan iya gaya maki dalilin da yasa Asabe ta mai da Samima Macijiya ba, kije da kanki ki binciko wannan lamarin dan taimakon yarinyarki ɗaya tilo, tashi kije Zulaihatu, nima nan zan din ga tayaki da addua, dan kuwa aiki ne ja a gabanmu" share majina da gefen mayafi Umma ta yi ta miƙe ta yiwa Malam godiya sannan ta fice, Malam ya nisa cike da damuwa dan kuwa Samima tana cikin babbar matsala.


A hanya Umma tana tafiya tana zancan zuci.
"Asabe!? Asabe!? Asabe fa? Lallai kam na yarda da karin maganar da ake cewa ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa, yanzu me nayi wa Asabe? Da har zata cutar dani ta wannan hanyar? Dole ne naje na ji dalilin da yasa ta yi min wannan mugun aikin dan bazan iya gani a hallaka min ƴata ba" ta sake share hawayen da ya gaza tsayuwa a idanuwanta, ta nufi gidan Asabe.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Kwance take a dakinta a kan ɗan karamin gadonta, sai juyi take yi tana ihun azaba, dan wani irin raɗaɗi ne take ji a kowani sassa na gangar jikinta, tamƙar ana wanke mata fatar jikinta da narkekken ruwan dalma, har kwakwalwarta take jin wannan azaban zafin, a hankalin bakinta ya fara zufar da hayaƙi wanda kafin giftawar ido da bismillah daƙin ya gauraye da hayaƙi, gurnani ta fara tana murkususu, idanuwanta tamƙar jini haka suka rine, kafin nan da ɗan wani lokaci ta galabaita, a hankalin jikinta ya fara b'anb'ara yana fitar da sab'an maciji, ihu ta ci gaba da yi tana huci ,ta kumbure ta koma ta sab'e, wani razananniyar kara ta saki lokacin da ta ji kamar an soka mata mashi a tsakiyar kirjinta, fatar jikinta ya hau sabulewa, kafafunta ya hau babbanƙarewa, daga kafarta ne ta fara rikiɗewa, nan ta ci gaba da juyi tana murƙususu tana gurnani, nan jelar maciji ya fara bayyana daga kafafunta, nan ta koma rabi mutum rabi macijiya, wani juyi ta yi ta sake sakin ƙara fuskarta ta yi jajur kamar wacce ta ƙone, a ihun ne gabaki ɗaya ta rikiɗe ta koma macijiya, wanda girman wannan macijiya ya cika ɗan ɗakinta, nan ta kananneɗe ta haɗe rai sannan ta sauƙo kasa ta sulale ta fice tabar gidan.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
😂😂😂😂😂😂


*_ARADU BAZAN DOGON TYPING.. BA SAI NA GA RUWAN SHARHI, MA'ANA DAI KO KUN KARBI BOOK DIN, SAI MU ƊORA, KARKU MANTA NA GAYA MUKU GAJERAN LABARI NE_*
_GA MASU BUKATAR CI GABAN LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH RETURNS, MAI TAKEN SUNA *GAWURTACCEN SOJA* ZAKU SAME SHI AKAN FARASHIN #300 VIP #500, GA KUMA *AHLAN* WANDA ZAKU SAMESU AKAN FARASHI MAI SAUKI WA INDA AMINAI BIYU NE ZASU GWANGWAJEKU, IDAN DAYA KIKESO #200 NE, IDAN BIYU NE #300 VIP #500, VIP NA MUTUM ƊAYA #400, DUK A LITATTAFAN MU MASU TAKEN SUNA *AHLAN, NA ZAHRA ABDUL (MOMYN AHLAN) DA KUMA, WACECE KARUWAR? NA RASHEEDAT USMAN(UMMU NASMAH)* KARKU BARI A BAKU LABARI_.MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻
[02/09 à 08:44] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)

Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)

Gajeran labari.


SHAFI NA BIYU. ✍🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*_MA SHA ALLAH! GASKIYA NAJI DADIN YADDA KU KA KARBI WANNAN LITTAFI, NA GA SAKONNIN DA DAMA ALLAH YA BAR KAUNA, WANNAN PAGE DIN NAKU NE, WA IN NAN GRPS DIN_* 👇🏻

*SLIMZY FANS GRP*
*MSS FLOWER*
*MASAUTAR A GARKUWA*
*FADAR MOM FAREESA*
*XAHRA FAROOQ*
_DAMA SAURAN GRPS DIN DA BAN AMBATA BA, DUK WANI MASOYIN BUK DIN NAN, SONSO DOMIN ALLAH_💓💓
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

"Assalamu alaykum!!! Asabee!!! Asabeee!!!?" Umma ta shiga gidansu Asabe tana sallama har tuntube take yi" Asabe dake uwar daki taji sallamar Maman Samima, wani shu'umin murmushi ta saki sannan ta miƙe daga gefen gadon da take zaune, wani kullin magani ne a hannunta ta yi saurin je fa shi ƙasan gado, sannan ta miƙe ta fito a yangace, tana fitowa ta sauke idanunta akan Maman Samima wacce kallo ɗaya zaka mata ka gane halin da take ciki na tashin hankali, wata uwar harara Asabe ta wurgawa Maman Samima, sannan ta turo ɗankwalinta gaban goshi, cike da rashin mutunci ta riƙe ƙugu ta ɗora dayar hannun nata a bakin kofa, har jijjiga jiki take yi, ta ce.
"To fa!! Su Zulaiha wannan uwar kiran da kike kwala min ta menene iyeee!!? Ko dai nima anzo a kasheni ne ,ni da ƴata? Kin ga Malama dan Allah ki wuce ki fice min daga gida ehe, karki goga min tsiya!!" da mugun mamaki Umma ke bin Asabe da kallo, da ace wani ne yake faɗa mata Asabe ce ke wannan maganganun zata karyata, amma sai ga shi ma ita ake gaya ma wa, uwa uba kuma Malam ya ce ita ta yiwa Samima asiri ta koma macijiya, amma yanzu kalli abun da take yi, tamkar bata san abun da ta aikata ba, Umma bata gama tunanin zucinta ba, ta ji Asabe na cewa "Dan Allah ni kam ki wuce ki fita min a gida" cikin ƙunar zuciya Umma ta ce "Allah ka rabamu da masu fuska biyu, wanda zasu gwada mana su na son'mu a fuska amma a zuciyarsu ba haka abun yake ba, Asabe!? Me na aikata maki a rayuwa!? Me nayi maki da har kika zauna kika kulleceni da wannan abun!? Asabe!? Na daukike tamƙar yar uwan da muka fito ciki ɗaya da ke, ni a tunani na duk abun da zan miki ko Samima ta yi miki bai kamata ki saka mana ta wannan hanyar ba, Asabe ina haɗaki da Allah ba dan ni ba,idan har ni ko Samima mun yi miki wani abu marar kyau a rayuwa dan Allah Asabe kiyi hakuri ki yafe mana, dan adam ajizi ne bai fi ba ko a wajan Allah mai laifi ne, balle kuma mu bayi masu kura-kurai da zunubai, dan Allah na roƙeki Asabe ki mai da min da Ƴata ta koma mutum, kinsa yanzu an fara gudun Samima, duk in da ta gitta a cikin unguwa sai da a din ga ce mata *SAMIMA MACIJIYA CE* idan kuma aka yi rashin sa'a ranta ya b'aci sai ta yi kisa, shekaran jiya tare-tare aka din ga yi da matasan unguwa su na so su kasheta, kuma Baba Malam yace ba ita ke kisan ba, na roƙeki ki mai da min da ƴata yadda take a da can baya, ko me muka miki kiyi hakuri a rashin sani ne, ko kuma ki fada me kikeso a wajan'mu, dan Allah Asabe ki karya asirin da kika yiwa Samima" Umma ta haɗa hannunta alamun roƙo ta zube guiwowinta a ƙasa a gaban Asabe ta saki marayan kuka tana ci gaba da roƙon Asabe, wani dariyar shekiyanci Asabe ta sake gami da cewa 'Ayyyyyriiriiii nanayeee!! Inyee!! Zulaiha? Sharrin naki ta kai har haka? Ki zo har cikin gidana ki min sharri? To ni ina ruwana dama sun kasheta!! Yarinyar da ta addabi kowa a garin nan, waye bai san da cewa *SAMIMA MACIJIYA BA CE??* kuma dan munafurci da sharri ki ce ni na mai data macijiya? To akan me? Ke da yarki masu kama da mayu sabida shegen kyau? Wallahi!! wallahi!! Wallahi!! Zulaiha kinji na rantse miki ko? Idan ba ki tashi kin fice min daga gida ba zan saka maki ihu, idan jama'a sun shigo abun da zan faɗi har ki mutu idan kikaji an kira sunan Asabe sai kin girgiza, dan za ki san wacece ake kira da Asabe ikon Allah wanda naci dubu sai dai ceto wallahi, ba a mai da ta mutum din fice min!!" Asabe ta fara yiwa Umma korar kare, ingizata ta dinga yi har ta fito da ita kofar gida ta cillata ta faɗi kasa, sannan ta yi mata kallon wulakanci ta mai da ƙyauren gidanta ta rufe, a hankali Umma ta miƙe jiki ba kwari ta kama hanyar gida tana tafiya tana kuka gami da tunanin jarabtar da Allah ya jarrabe ɗiyarta, yanzu wacce hanya zata bi wajan ganin ta taimaki ƴarta ta dawo asalin mutum? ba rabi mutum rabi macijiya ba? tana kan tunaninta kenan tana shawo kwanar gate din gidanta taji wani uban guguwar hayaniya na tashi, da gudu ta diba dan ganin meke faruwa, tana zuwa ta ga ciccirindon mutane matasa yan unguwa ko wanne dauke da mugun makami a hannunsa, daga gani a tunzure suke matuƙa har da masu fetur da cerozin ga ashana, zaro ido Umma ta yi ta karaso tana tambayarsu lafiya kuwa? Wani matashi ne ya zo gaban Umma ya ce "Maman Samima ki shiga ki fito mana da Samima,yau babu shegen da ya isa ya hanamu yin gunduwa-gunduwa da Samima" ɗaura hannu akai Umma ta yi tana salati ta ce " Habu? haba Habu? Me Samiman ta yi?"
"Taya za ki ce ba ki san abun da ƴarki take aikatawa ba a garin nan yanzu? To kalli abun da ta yi" ya faɗa yana nuna mata gawar wani ɗan matashin saurayi wanda ga tabon saran maciji a goshinsa da wuyansa, baya-baya Umma ta yi tana furta "Innalillahi wa inna ilayhirrajiuna!!!!! Na shiga uku ni Zulaiha' injiwa ya ce Samima ce ta kashesa!?"
"Dalla ki rufa mana baki!! Da wa yasan cewa ƴarki ba mutum bace? Shekara nawa kenan tana kashe mutane, ban da kwanan nan da muka san gaskiya, wallahi ko ki fito mana da Samima ko mu ƙona gidan nan kuma sai kun bar garin nan ehe" cewar wani mutum,wani ma ya ce "to wai ma me muke jira ne? da ba zamu fara ta kan Uwarta ba!!" suka yi kan Umma yuuuu, da sauri Umma ta yi wuff ta shige gida, ta danne karamin kofar dake jikin gate ta wuce ciki da gudu ta ɗaga waya ta kira mahaifin Samima ta faɗa masa halin da ake ciki, sannan ya tambayeta ina Samiman ta ce masa bata ganta ba ,bata gida kuma kafin ta fita sai da ta kulle ta dan Baba Malam ya ce a daina bari tana fita, Baban Samima ya ce "to a garin ya ma ta fita tun da kin kulleta? Kin ga kwantar da hankalinki gani nan zuwa" yana faɗi ya ajiye wayar ya tashi da sauri ya fara tattara kayansa, ya fito kenan zai shiga ƴar motarsa ta rufin asiri mai su na toyota sai ga yaron ogansa wanda shine Manager a Companyn, yana ganinsa ya ce "ah Baba, ina kuma zaka je na gan ka a haka? cikin tashin hankali da damuwa mahaifin Samima ya sunkuyar da kansa ya kasa ba wa yaron ogan nasa amsa dan yana jin kunyarsa ba kadan ba, dan yaron akwai natsuwa da hankali da sanin ya kamata ga shi da girmama mutane, tun da ya dawo daga ƙasar waje shekara shidda kenan yanzu bai taba yi masa rashin kunya ba, duk inda ya gansa zai duƙa ya gaishesa Baba sama Baba kasa, ranar da ya ga Samima kuwa ya ce yana sonta da Ƙanwa dan shi ma shi ɗaya ne a wajan iyayensa, shaƙuwa mai karfi ne a tsakanin *NUREN* da Samima, dan haka taya zai fara gayawa Nuren cewa Samima Macijiya ce? Jikin Mahaifin Samima ne ya fara kakkarwa tamkar mai jin sanyi sai ga hawaye na zuba a idonsa, abun da Nuren bai taba gani ba kenan, ganin haka ya sake ɗaga masa hankali ya shiga jerowa Baban Samima tambaya, amma ganin ya kasa ba shi amsa yasaka shi cewa "to Baba ina zaka je sai muje tare?" da kyar mahaifin Samima ya furta cewa "Gida" sannan Nuren ya karbi key din motarsa ya bude masa ya shiga sannan ya shiga shima ya dauki hanyar unguwarsu Samima, da dan sauri yake driving din, su na zuwa suka ga ana wanke gidan su Samima da fetur ana shirin cinnawa gidan wuta, da karfi Nuren ya ce "heyyyyyyyyy!!!!!! Stoppppp!!!" juyowa kuwa suka yi gami da tsayawa cak su na kallon Nuren, dan gidan ALHAJI IBRAHIM MAI AGOGO wanda babu wanda bai san shi ba a cikin garin ADAMAWA, da sauri ya karaso yana tambayar meke faruwa, nan wani yake faɗa masa ai ga...


Read / Download SAMIMI MACIJIYA CE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album