Join Our WhatsApp Group

MATAR HAIDAR Complete Hausa Novel Document by MATAR HAIDAR


MATAR HAIDAR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 247945



MATAR HAIDAR

Reading Time: 20 Hours

Added On: 29, Oct 2023

Author: Maryam S Indabawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 1.25 mb

File Type: txt

Views: 1355+

Download: 4101+

Last download: 4 days ago

Description/Story: 
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 1

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



******* ****** ******
Zaune suke a falon su wanda yake a gyare sai tashin kamshi yake ga sanyin AC da ya karawa dakin ni'ima. TV na ta aiki, komai na dakin red kaa ne daga manya manyan kujerun har labulayen dakin da center carpet din dake tsakiyar dakin mai uban taushi, wata dattijuwar mata da ba zata wuce shekara arba'in da biyar zuwa da takwas ce zaune gaban ta system, sanye take da less mai kyau da tsada daga yadda take kallon system din zaka san aiki take a cikin ta. Sai gefenta wani dan yaro kyakyawa wanda a ido bai zai wuce shekara biyu ba, sanye yake da wasu riga da wando bakake wanda suka kara fito da hasken fatar sa, gashin kansa a kwance baki sidik sai sheki yake, wasa yake da mota, sai wata kyakyawar budurwa da bata wuce shekara sha tara ba sanye da maroon kalar hijab wanda yake har kasa, waya ce a hannun ta tana daddanawa gaba daya hankalin ta na kan wayar. Sallama akai dabwata muryar mai dadin da zaki, daga bakin kofa amsawa sukai a tare. Wanda yai sallama ne ya shigo cikin takun sa na kasaita sanye yake da suit ash kala wacce ta amshi shi sai bakin takalmi sau ciki baki, hannun sa rike da brief case din sa. Fari ne tas dogo ga saje, idanun sa manya wanda suke ko da yaushe a lunshe sai dogon hancin sa, da madaidaicin baki sa ai agaye da pink lips masha Allah kyakyawa ne sosai.

Yaron dake wasa da mota ne ya d'ago yana ganin sa ya mike yayo wajen sa a guje yana fadin
"Abbi Oyoyo!"

Brief case din ya ajiye akan kujera ya daga yaron sama ya rumgume shi, yana murmushi wanda kumatun sa suka lotsa kan yaron ya shafa yace
"My Son ya gidan?"
"Abbi i miss you (nayi kewar ka)"
Ya fada da harshen da zaka san magana bata gama zama a bakin sa ba.

Matar dake aiki a system ce ta d'an d'ago tana kallon sa, ya karaso cikin falon ya zauna a kan carpet din dake tsakiyar dakin tare da d'aura kan sa a gefen kafar matar yace
"Ummi nah sannu da gida ya aiki?"
"Alhamdulillah Dr ya aikin?"
Ta tambaya cike da kulawa.

"Alhamdulillah!"
Ya fada yana shafa sumar kansa da take kamar ta indiyawa sai sheki da kamshi take. Budurwar dake zaune ce ta dago fuska ba yabo ba fallasa tace
"Sannu da zuwa Yaya."

"Yauwah!"
Kadai yace ya mike rike da yaron yai hanyar dining inda wata kofa take suka shige. Da kallo ta bisu ta d'an tabe baki mikewa tayi tace
"Ummi bari naje wajen Inna."

"To ki gaishe ta."
Ta fita tana tafiya a hankali kamar ba zata taka kasa ba, saboda wayar da take dannawa kamar daga sama taji an zare wayar hannun ta da sauri ta d'ago fuska ta marairaice tana kallon wanda ya amshe wayar, wani kyakyawan saurayi ne wanda ba zai wuce shekara talatin ba, dogo ne fari tas dashi wanda yake da faffadan kirji, yana da idanu da hanci da bakin sa dan madaidaici, murmushi yake wanda ya kara masa kyau, fuska ta kara shagwabewa kamar zatai kuka tace
"Yaa Faroukkk"

Wanda aka kira da Yaa Farouk ne ya zuba mata ido wannan yasa tai saurin yin kasa da kan ta tana son wucewa ta gefen sa. Ya d'an kamo gefen hijab din ta, ta juyo yace
"Kina tafiya kina danne danne sai kin fadi kinji ciwo ki barewa mutane baki kina kuka ko?"

Ido ta zaro ta, tace
"Kai Yaa Faroukkk ni din?"
Ta fada tana nuna kan ta.
"Eh ke din fa ke wa ya kai ki ragwanta, ko Haidar ya fiki jarumta."

Baki ta dan turo tace
"Uhmm ai kuwa na fishi wancan dan mitsitsin yaron."
Yai murmushi yace
"Shi fa. Yanzu ina zuwa?"

Bangaren Inna ta nuno masa tana fadin
"Wajen Inna."
"Nima can zani. Wai me kike dadannawa a wayar ne ko chat kike da siriki nane?"

"Kai a'ah ni ba ruwa na Yaa Farouk."
"A'ah fah ki fadan gaskiya in dashi ne a bani mu gaisa."

"A'ah Yaa Farouk ni bani da wani saurayi fa, da Jawahir muke chatting fa."
"Wannan Jawahir din dai har na gaji da labarin ta ita bata kawo wa mutane ziyara ne?"

Ido ta zaro tace
"kai Yaa Farouk ranan fa nace maka tazo itama tana ta tambayar ka, kasan ma me? Kun fiya sabani shiyasa."
"Duk tsiya dai watarana zan ganta in ma bakya so na ganta ne."

"A'ah ni ba ruwa na."
Suka karasa kofar sasheb Inna wanda yake babban compund ne da aka zagaye ahi da shuke shuke wanda ya karawa wajen kyau, kofar dakin Inna suka karasa sukai sallama ta amsa suka shiga.

Daki ne madaidaici wanda yaci set din kujeru Ash kala da kayan kallo bakake, labulayen da center carpet din duk ash and black ne, dan a gyare yake sai kamshi da yake, tiles din kuka kamar kaga kanka a ciki haka kayan kallon sai kyalli suke kamar wanda aka shafe da mai. Maryam ce ta fara shiga tace
"Inna tah."

"Na'am Maryama yau ina kika shiga tin safe baki leko ba."
Wata tsohuwar mata da zata kai shekara tamanin da wani abu, saye cikin atamfa super tai kwaliyyar tai maganar tana kallon Maryam din cike da so da kauna. Maryam ta zauna a kusa da ita tace
"Ina can ina aiki na danyi sanitation ne a bangaren mu."

Inna tace
"Sannu ina Haidar din?"
"Yana wajen Abbin sa."

Baki Inna ta tabe ta kalli Farouk tace
"Ai sai ka zauna ko ka tsaya sai kace wanda ya hadiyi tabarya."
"To wa ya sani."
Farouk ya fada yana danna wayar Maryam.

Inna ta gimtse baki tace
"Ai da ba lafiya."
Maryam tai dariya tace
"Ai kuwa dai Inna."

Ya zauna yana kallon Maryam yace
"Kina biyewa Inna Allah batawa zamuyi."
"Yo ku bata din mana, sai me kuma me kake mata ci ko sha ko sutura."
Inna ta tambaya tana hararar sa.

"Dukka."
Ya bawa Inna amsa yana zaro wayar a aljihu.
"Ba mu gani ba."

"Ai daman Inna ke ba komai kike gani ba."
"Tinda ga makauniya ko?"

"Nifa bance ba Hajiya Inna."
"Kai ka sani dai."

Inna ta kalli Maryam tace
"Dazu nayi dambun nama ni dan ke nayi ma wallahi to sam baki shigo ba."
"Zamu ci dadi."
Farouk ya fada yana mikewa daga kishiginden da yake.

Inna tace
"Duk jikokin na babu kwadayeyye kamar ka Umaru kuma in naga dama dandanawa ba zakai ba."
Dariya yayi yace
"Mai gidan naki guda."

"Kai tafi can ai na fiyi da wancan mai fuskar shanun."
Baki ya bude yana dariya yace
"Lalalah Yaa Haidar din Inna ai kuwa sai na fada masa."

"Ba abinda yayi sai hada mutane fada to yanzu shi yaji ne amman kin ji shi wai zai fada masa salon dan abinda yake bani ya daina bani."
Murnushi Maryam tayi tace
"So yake ki sammishi kuma Yaa Aliyu ba yadda zai ba."

"Ai dai mai hada husuma bashi ba Allah."
Dariya Farouk yayi yace
"Hajiya Inna ai kin fada dai."

"Kai ka sani."
Wayar sa ce tai kara da sauri ya dago yana kallon Maryam dake wa Inna magana sam bata san ma yana yi ba da sauri ya mike ya fita yana kara wayar a kunnen sa.

"Hello Baby."
"Kana ina Baby kace zaka zo kuma naji shiru."

"Kinga magarib ta kusa ki jira ni bayan magrib zan karaso."
"Ok ina jira."
Ajiyar zuciya ya sauke ya koma dakin.

Inna ta kalli Maryam tace
"Yau na ganki duk wani iri me yake damun ki?"
"Ba komai Inna yanayi ne kawai."

"A'ah in akwai abinda ke damun ki ki fada min ko ita Aishan ce tai miki wani abu?"
"A'ah Inna me Ummi zatai min?"

"Ah na sani."
"Ni ba abinda tai min."

"Wannan mai fuska a dauren fa?"
Baki Maryam ta tabe tace
"Shi da dawowar sa kenan."

"To shikenan."
"Hajiya Inna kudi zaki bata kawai."
Farouk ya fada.

"To ina ruwan ka. In kudin take so ai zata fada min ko Maryama."
Kai Maryam ta gyada tana jingina da kujera. Wayar tace tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dauka tayi ta kai kunne tace
"Hello Jawa."

"Na'am wai ya zancen addimision din kine?"
"Nifa har yanzu su Ummi basu ce komai ba."

"Kuma ke ba zaki iya musu magama ba?"
Mikewa tai ta fita tana fadin
"Ai suna sane na sani."

"Shikenan ni dai gashi nan an amso min gobe Dady yace naje nayi registiration da so nayi muje tare."
Kofar dakin Inna ta juya tana kalla tace
"No Jawa kije kawai ba matsala in zan yi kya raka ni kar kije ki samu matsala."

"Shikenan amman ki fadawa Yaa Aliyu mana."
"Zan masa magana bai jima da dawowa ba ai."
Juyowar da zatayi taga Aliyu tsaye a wajen Haidar kuwa har ya shige falon Inna.

Kai tayi kasa dashi da sauri ya wuce dakin Inna ita kuma ta juya tayi sashen su. Ummi ta sama a inda ta bari sama kawai ta haye, Ummi ta d'ago tana kallon ta sai kuma ta d'auke kan ta. Tana shiga ta fada bandaki tai alwala ta fito ta tada sallah bayan ta idar tai addu'a Alkur'ani ta d'auko ta fara karantawa tana zaune har akai isha'i ta mike tai sallah tai addu'a tare da shafa'i da wuturi. Mikewa tai ta cire hijab tare da cire kayan ta, wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan bacci ta feshe jikin ta da turaren ta mai kamshi. Kan gado ta hau duk da ba bacci take ji ba amman so take ta dan huta.

Tana kwanciyya aka turo kofar d'akin Ummi ce ta shigo da sallama mikewa zaune tayi. Ummi tace
"Kin ci abinci ne naga kamar kin kwanta?"

Cikinta ta d'an shafa tace
"Ummi na koshi ne."
"Me kika ci?"

Kai tayi kasa dashi. Ummi tace
"Tin abincin rana ko? To maza sauka kije kici abinci."
Kafarta ta diro kasa ta mike ta d'auko hijab ta saka sannan ta fita a d'akin Ummi tabi bayan ta, ba kowa a d'akin dan haka ta karasa dining. Abinci ta fara ci kamar ba zata ci ba, sallamar sa ta jiyo sai ta ji Haidar ma na sallama a ciki ciki ta amsa ya shigo bai kalle ta ba yayi d'akin sa. Haidar ne ya karaso yace
"Addah kalli abinda Abbi ya siyon."

Ya fada yana mika mata ledar hannun sa, amsa tayi ta leka tace
"Yaron Abbin sa kace angode?"
Kai ya gyada tace
"Good to jeka."

Ya ruga a guje ya shiga dakin Abbin. Abincin ta karasa turawa da kyar ta mike tana kwashe kayan Haidar ya dawo yace
"Addah Abbi yace kizo."

"Ni!"
Ta fada cike da mamaki. Kai ya gyada mata, tace
"To jeka gani nan."

Ta dibi kayan ta kai kitchen sannan ta dawo ta nufi dakin Aliyun. Sallama tayi ya amsa, ta shiga kanta a kasa, Masha Allah wani kamshi da sanyi ya doke ta, ta lumshe ido, ta bude yana daka kan kujera yana danna system. Komai na dakin fari ne tas sai kace ba a rayuwa a cikin sa, daga gefen kujerar ta durkusa tace
"Gani Yaa Haidar."

Da sauri ya dago kan sa ya kalle ta da lumsassun idanun sa, lumshe du yayi sai kuma ya dauke kan sa, envelope ya mika mata. Amsa tayi ta tsaya jin ko zai magana amman bai ba mikewa tayi tace
"Nagode."

Ta fita sama ta hau ta shiga dakin ta, ta ajiye envelope din akan side doruwa ta zare hijab ta hau kan gadon addu'a tayi ta kwanta ta gefen dama envelope din ta gani ta mike da sauri ta dauka budewa tayi ta zaro takardun dake ciki ta zube su akan gadon daya ta dauka ta fara karantawa da sauri ta zaro ido murmushi ya bayyana akan fuskar ta.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah nagode maka ashe nima zan yi karatun nan."
Sai hawaye ya hau zubo mata a saman fuskar ta. Shin wa zata fara fadawa wannan abun farin cikin Ummi, da sauri ta mike ta fita a guje a dakin hannun ta rike da takardar addmision din, kofar dakin Ummi taje tai knocking Ummi ta bata izinin shiga da sauri ta bude ta shiga tana shiga ta karasa wajen Ummi ta rumgume ta tana fadin
"Ummi kalli ki gani."

Ummi ta amshi takardar tana dubawa itama murmushi ne ya sauka akan fuskar ta tace
"Masha Allah. Allah yasa a fara a sa'a."

"Amin Ummi nah ki tayani yiwa Yaa Haidar godiya."
"To Maryama Allah bada sa'a da nasara."

"Amin Ummi."
Ta mike ta fita a dakin. Dakin ta ta koma ta duba dayar takaradar form ne na banki sai wasu kudi masu yawa kirgawa tayi taga dubu dari biyar ne. Ido ta zaro tace
"Na menene kenan?"

Tsaki ta dan saki tace
"Yaa Haidar shi ba zai yai min bayani ba ni nasan menene da zai ban abu kawai ba bayani to da ban bude ba fa."
Ta fada tana lallubar wayar ta.

Jawahir ta kira tana dauka tace
"Albishirin ki?"
"Goro."

"No ban son goro ni ba tsohuwa bace."
"To chocolate."

"Hmmm yanzu Yaa Haidar ya bani takaradar addmision fa."
"Da gaske Angel?"

"Wallahi yanzun nan fa."
"Alhamdulullah kinga gobe sai muje registeration tare ko?"

"Eh nawa ne registeration din?"
"Sai mun shiga ckul amman dai naji Yaa Khalid yace kamar 150k ne."

"Ok Allah kaimu goben."
"Amin sai da safe."
Sukai sallama.



**
Washe gari da safe da wuri ta shirya tana kitchen tana aiki taji Haidar na kwala mata kira yana fadin
"Addah Addah!"

Da sauri ta leko, ta ganshi sanye cikin wandon jean da jar riga, sai agogo daure a hannun sa, ta kamo hannun sa tace
"Ya akai Boy."
Hannun ta ya hau ja zuwa dakin Aliyu tace
"Haidar bari na sako Hijab d'ina."

"Aah Abbi na so kizo yace."
Yai maganar da gwaranci. Zatai magana Aliyu ya fito da sauri tai kasa da kai shima kallon ta ya danyi tana sanye da doguwar riga wacce ta kamata, daga sama, kan sa ya dauke yace
"Kin cike form din da na baki jiya?"

Kai ta girgiza, saboda ba ganin ta yake ba, ya dan d'ago ya kalle ta da shanyayyun idanun sa yace
"Magana fa nake."
'Dagowa tayi sanye yake da wasu Blue kalar suit wacce tai masa kyau, gashin kansa ya kara baki sai sheki yake, leben sa ya kara yin pink sai kyalli yake kamar wanda ya shafa masa janbaki ko man lebe, suna hada ido sukai saurin kawar da idanun su, jiki a sanyaye tace
"A'ah."

"Ke zan tsaya jira to kije ki cike ki kawon kar ki batan lokaci."
Tai saurin fita tai sama, da gefen ido ya rakata ya zauna akan kujera yana mai lumshe idanun sa. Tana zuwa ta cike form din. Hijab ta saka ta fito ta same shi a kasa. Tana mika masa ya mike har ya kai kofa yace
"Nayiwa driver magana zai kai ki banki wajen aboki na shi zai bude miki account daga nan sai kiyi registeration dan a satin nan za a rufe."

"To nagode Allah saka da alheri."
Ya juya ya fita tace
"A dawo lafiya."

Hannu kawai ya daga ta koma ta karasa abinda zatai. Tana fitowa sai ga Ummi ta sauko cikin shirin ta na tafiya aiki. Ummi tace
"Ya zancen registeration din naki?"

"Yaa Aliyu ya bani kudin yace anjima driver zai kaini nayi."
"To madallah ina Haidar din?"

"Sun fita tare."
"To shikenan sai kin dawo ki kula dai."

"Insha Allahu!"
Ta koma sama. Waya sukai da Jawahir suka dai...


Read / Download MATAR HAIDAR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album