Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

ASP ZARAH book 2 Complete Hausa Novel Document by ASP ZARAH book 2


ASP ZARAH book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29688



ASP ZARAH book 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 29, Oct 2023

Author: Jasmine ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 154.84 kb

File Type: txt

Views: 888+

Download: 718+

Last download: 43 minutes ago

Description/Story: *ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 1*

_Federal Lowcost Gombe State._
_Monday 6:15am._

......Kwance yake a kan tamfatsetsen gadon shi hannunshi biyu dafe da cikin shi, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yana fama da matsananciyar rashin lafiya, banda gumk babu abinda yake haɗawa. Tsaki yaja a karo na ba adadi ganin ya kasa mirginawa ya isa ga wayarsa dake kan bedside drawer domin ya kira Abdallah yazo ya taimaka mishi.
Hamdala yayi bayan ya isa ga wayar lokacin da ciwon ya lafa, cikin sauri ya danna kiran wayar Abdallah ringing biyu kuwa ya ɗauka ya fara magana cikin zolaya kamar yadda ya saba.

"Ango na Zara'u ya da kiran sassafe haka."

Shiru yayi cikin son yayiwa Abdallah masifa amma tunawa da yayi cewa taimako yake nema ya sashi sassauta murya yace.
"Guy ka taimaka kazo ka kaini asibiti bani da lafiya ne."
Salati Abdallah yayi cikin tashin hankali yace.
"Meya same ka haka?."

"Wallahi yau da ciwon mara na kwana har yanzu yaƙi sakeni dakyar nayi sallar asuba."

Mamaki ne ya kamashi jin yaja tsaki tamkar wanda yaji mugun abu, shiru ya kuma jin Abdallah ya fara magana cikin fushi.
"Wai kai M J wane irin mutum ne haka da sam baka tsoron Allah, kanada iyali a gida amma kullum kana hanyar asibiti ciwon sha'awa na damunka, watan ku biyu da aure amma ka kasa sauke haƙƙin daya rataya a wuyanka, me zaka cewa Allah idan ka mutu da haƙƙin yarinyar nan, sanin kanka ne cewa zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya amma bazaka daina zargin yarinyar nan da aikata mugun abu ba."

Cigaba yayi da mishi faɗa tamkar ɗa da uba, shikuwa M.J bai ce komai ba har saida yaji Abdallah yayi shiru kafin yace
"Ka gama.??"

"Zan gama dai."

"Taimako na nema tunda bazaka taimakamin ba toh zan kashe waya."

"Wallahi Jawwad kaji na rantse koh, idan naji labarin ka kira wani likita saina gayawa su Daddy abinda kake aikatawa ga yarinyar nan."

''So kake na zauna da ciwo a jikina.??"

"Kana da magani a gida ai, wallahi na baka minti talatin naji sakamako mai kyau idan ba haka ba yanzu zaka amsa kiran Daddy."
Daga haka ya kashe wayar ya barshi sororo riƙe da waya a hannu cike da takaici, yana da tabbacin duk abinda Abdallah ya faɗa zai aikata kuma shi bayason iyayensa su san abinda ke faruwa tsakaninshi da yarinyar da yake tunanin mahaifansa zasu iya bada ransu a kanta, wannan dalilin ne yasa ya yanke yin amfani da shawarar Abdallah amma ta ina zai fara? Jim! Yayi kafin daga bisani ya saki wani shu'umin murmushi duk da ciwon dake nuƙurƙusarshi. Tabbas dole ya ƙara aure, hakan ne kaɗai masalaha a gareshi domin shi bai kasance mazinaci kamar ita ba, duk da yasan idan ya tado maganar ƙara aure yanzu za'a iya samun matsala amma dole hakan ne kaɗai mafita a gareshi domin bazai iya dinga haɗa jiki da rijiyar gari ba.
Agogon hannunshi ya kalla yaga 6:45am, yana da tabbacin yanzu bata fita aiki ba, a hankali ya miƙe hannu dafe da ciki ya saka bedroom slipper ɗinshi ya nufi sashin nata cike da zullumi.
Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yake tafiya har ya iso side ɗin nata, falon a kimtse yake ko ina ƙal tamkar ba'a rayuwa a jikinshi ga wani ƙamshi mai sanyaya rai dake tashi a falon.
"Tana da tsabta." ya faɗa a ƙasan maƙoshi domin yadda yaga falon abin ya burgeshi, daidai nan kuma ya iso gaban ƙofar bedroom ɗinta, shiru yayi na wani lokaci yana nazari kafin ya yanke shawarar buɗe ƙofar ya shiga da sallama a can ciki domin ba lallai wanda akayiwa sallamar taji ba.

A tsaye ya hangota gaban madubi tana ƙoƙarin rolling veil akanta jikinta sanye da kayan aiki, cikin sakanni ya ƙarewa ɗakin kallo ganin komai neat tamkar mutum bai kwana a ciki ba, maida kallonshi yayi gareta yana daɗa ƙare mata kallon cikin shigartata, sai yau ya iya yi mata kallon da zai iya zaƙolota a ko'ina ya ganta, tayi mishi kyau sosai zubinta ya mishi kama da wata jarumar Bollywood Deepika Padukone musamman yanzu da take sanye da riga da wando na aiki zubinsu yayi mishi kamanni a wani tallen fim ɗin jarumar daya gani( Fighter ft Hritik Roshan and Deepika Padukone. World wide release on september 2023).
Tun shigowarsa ɗakin ta hangeshi saidai tayi mamaki ƙwarai data ganshi a ɗakinta, watansu biyu kenan da aure amma zata iya ƙirga sau nawa ta ganshi a cikin wata2 domin tun ranar da aka kawota gidan yayi mata sharaɗim kada ta kuskura taje inda yake baya buƙatar komai daga gareta saidai duk sanda zasu haɗu sai yayi mata rashin mutuncin da take daɗewa tana mata ciwo. Tasan hakanan bazai shigo mata ɗaki ba dole akwai abinda ya kawoshi, batason abinda zai ɓata ranta a wannan safiyar domin tana da aiki sosai a office kwananta huɗu bata fita aiki ba saboda menstrual pain dake damunta baya ga haka kuma yau tana da ganawa da sabon commissioner da aka ce mata an naɗa bayan mutuwar wanda tazo ta tarar a garin, bata bibiyi labarin ba domin a zatonta mataimakinshi aka rantsar a madadinshi.

"Nazo karɓar haƙƙina ne."

Tunaninta ya katse lokacin dataji abinda ya faɗa, mamaki ne ya kamata wanda har yasata juyowa ta kalleshi lokacin da yake zama a gefen gadonta domin ta tabbatarwa idonta shi ɗin ne ke magana, batace dashi uffan ba ta nufi gaban wardrobe ɗinta ta zaro abayar da zata ɗaura akan kayan tana ƙoƙarin warwarewa da nufin sakawa.
"Nasan kinji abinda nace dan haka bani da bukatar maimaitawa." ya kuma faɗa cikin tsare gira.

"Zaka iya dawowa wani lokacin amma yanzu ba samu zakayi ba." ta faɗa bayan ta ɗauki handbag ɗinta zata bar ɗakin.
Cikin bazata taji yasa hannu ya fincikota ta faɗa cikin, matseta yayi sosai kafin ya fara warware veil ɗin nata, mutsu-mutsun kwacewa takeyi amma sam yaƙi bata damar hakan.

"Ki bar ganin kina ƴar sanda ba iya kwacewa zakiyi ba, gara ma ki nutsu ki barnj nayi abinda zanyi nagama. Kika baiwa wasu na waje ma bare nida nake mijinki."
Daidai nan ya ƙarasa warware veil din wanda hakan ya bama dogon gashinta mai kyau da sheƙi zubewa a gadon bayanta, da fari yayi tunanin wig ne ta saka amma sai ya gane gashinta ne yayi mamaki duk da yasan cewa suna da gashi irin na fulani amma na Zarah ya zarce irin nasu a tsayi da santsi. A hankali ya fara shafawa yana tusa kanshi a ciki _Mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki_ , nan da nan ya fice a hayyacinsa.
Taso yimai turjiya amma tunawa da tayi bata sallah yasa ta daina ƙoƙarin kwacewa ta barshi ya cigaba da abinda yakeyi.
Takaici ne ya turniƙeshi lokacin da ya gane dalilin dayasa ta nutso ta daina ƙoƙarin kwacewa, cike da takaici ya sauka a gadon ya fice daga ɗakin batare da ya tattara kayansa dayayi watsi dasu ba.

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi banɗaki, bata daɗe ba ta fito cikin hanzari ta ɗauko ɗayan uniform ɗin ta saka ganin har ƙarfe takwas ta kusa kuma ganawarsu da kwamishina 7:30ne. A hanzarce ta gama komai ta fice daga gidan ta wuce office ɗin.
Tun daga harabar gurin take ganin kamar tasan wasu daga cikin jami'an dake shawagi a farfajiyar wajen bata kula ba ganin tayi latti ya sa kai tsaye ta nufi office ɗin commissioner kai tsaye ko kula da sunan dake manne a jikin ƙofar batayi ba ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama. Tashin hankali _ba'a saka masa rana_, zuciyarta ce ta cunkushe _damuwa tayi adabo a fuskarta_. Jikin tsantsar baƙin ciki ta riƙe handle ɗin ta nufi ficewa a office ɗin......✍️

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

_Fans Mi😜😜😜 Meerah, Zee Bassa, Nab baby, Hussy, Mrs. Mukhtar, Miss Japanese and others da kuka hana kanku bacci jiya toh gashi nan kusha karatu😅😅 A daina hana kai bacci hilis dan nima bana hana kaina 🤦‍♀️._
_Su Ummu Huzaifah a sakar mini mara nayi fitsari, kada masoyiyata ta fara nata itama JJLuV😘😘_

Luv y'all.

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 2*

...Dariya yayi mai cike da ma'anoni kafin yace.
"Barka da zuwa Zarah, ya zaki koma tun baki yimin maraba da samun sauyin gurin aiki ba?."
A hankali ta juyo ta kalleshi cikin tsana tace.
"Abinda ya kawoni kenan na taya wanda aka naɗa murna saidai wanda na tarar bai cancanci hakan ba, hmm so kake na tayaka murna kabar garin Bauchi a matsayin commissioner ka dawo Gombe a matsayi iri ɗaya? Wani cigaba kenan?. Zuwa na ya ƙaramin aiki domin kuwa ganinka da nayi anan ya tabbatarmin da cewa akwai hannunka a kisan tsohon commissioner saboda kanaso ka dawo inda nake...


Read / Download ASP ZARAH book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

10 months ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album