Join Our WhatsApp Group

MIJIN UMMU NAH Complete Hausa Novel Document by MIJIN UMMU NAH


MIJIN UMMU NAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 66421



MIJIN UMMU NAH

Reading Time: 5 Hours

Added On: 26, Oct 2023

Author: Maryam S Indabawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08062882472

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 356.92 kb

File Type: txt

Views: 694+

Download: 379+

Last download: 1 day ago

Description/Story: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY


1


Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Bismillahir Rahmanir Rahim
Da sunan Allah mai girma da Rahma.


Na fara da sunan Allah mai Rahma mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Muhammad (SAW).


Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadil al fatihi lima uglika wal khayimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki wal hadi ila siradikal mustakim wa'ala alihi hakka qadrihi wal mikdarihil azim.













Wannan littafin naki ne yar uwa, rabin rai, NUSAIBA SULEIMAN INDAVAWA, Allah kara mana kaunar junan mu, Allah daurar da zumuncin mu AMEEN,

Allah baki miji nagari, Allah inganta rayuwar ke da little MEEN, HAUWA'U USMAN (YASMEEN) Ina kaunar ku ina alfahari da ku kannena,

Allah ya faranta muku a duk inda kuke Allah baku zuri'a ta gari AMEEN! Da dukkanin musulman duniya baki daya.










zaune suke shi da abokan sa a babban tsakar gidan, akan carpet suna cin abinci, mikewa yayai ya shiga cikin dakin sa, adai dai lokacin wata kyakyawar budurwa wace bazata wuce shekara 15 ta shigo gidan da sallamar ta gannin da Mutane a tsakar gidan yasa ta cire takalman ta, ta ajiye a soro dan girmamawa.

Karaso war ta ciki kenan shi kuma ya fito daga daki, da gannin ta ya rufe ta da fada.

"Ke baza ki girma ba har yanzu ji yawo ba takalmi,"

Ya fada yana nuna kafar ta, durkusawa tayi tace.

"Yana soro fa takalmin ganin da Mutane yasa na ajiye a can,"

"Karya kike ni wuce ki bani waje."


Daki ta shige inda Yayar ta take, tana matsar kwalla dan tana jin zafin yadda yake mu'amala dasu, amman in 'yar sa ce 'yar shekara 4 yai ta mata dariya amman su sam basa gannin fara'ar sa ko meyasa ohoo?


Antyn ta dake zaune kan kujera tana ta danne dannen wayar ta dan aikin ta kenan kullun.

Tana zaune tana fama da wannan abun, Mahaifiyar su wacce suke kira da UMMU ta kwada mata kira,

"KHADIJA!"

"Na'am,"

Ta amsa da sauri ta fice, ta durkusa tace

"Gani UMMU"

"Ungo maza je ki siyo Ruwa."

Karba tayi ta mike tayi waje dan daman da hijab din ta ajikin ta,

Aiken ta kai wa UMMU, sannan ta fada mata za taje gidan UMMA dan za suyi gwajin rawar gada, da za ayi bikin yar kannin mahiafin su,

Suna cikin yin Gwajin taji yo ana kwada mata Kira.

"KHADIJA! KHADIJA!"

"Na'am"


Ta amsa da karfi, dan katanga daya ce ana iya jiyo wa in an kirata,
Gida tayo tana addu'ar Allah yasa ba kuma wani abu tayi ba.

Ta shigo gidan da Sallama, tin a soro ta fara jiyo mitar sa,

"Ke dama ke kike kara daure mata gindi, ta fita taje tana ta rawa ai da Mahaifin su na da rai da bazai bar ta ba,"

"Haba dan Allah ai bikin yar Kannin. ABBUN su akeyi,"

"Kina ina ke zonan ki shige ciki."


Daki ta wuce inda ta samu Antyn ta na aikin da ta saba, wato danne dannen wayar ta. kallan ta KHADIJA tayi taga duk ranta a bace yake, dan Anty in Akwai abin da ta tsana bai wuce fada ba ki hayaniya.

Mikewa tayi ta shige dakin baccin su tayo Alwala tace,

"KHADIJA sallah"

Da sauri ta mike itama tayo alwalar, tare sukai Sallah Magariba.

Bayam sun idar da Sallah ne, sai ga Yaya Maimuna ta shigo yar gidan Umma ce.

"Ina UMMU"


Ta tambaya, KHADIJA ce ta mike taje ta kira ta.
"UMMU ina yini,"

"Lpy Maimuna,"

"UMMU daman KHADIJA ce zamu raka Maman Hidaya gida,"


"To shkn kar kudade,"

Suka fice KHADIJA na matsar qwalla dan har yanzu tana takaicin abinda ya faru.

HAFSAT wato Anty tana daki kwance kan gadon ta, tana ta danne dannen ta,

tin da suka fita basu dawo ba sai 10 dare, Yaya Maimuna ita ta rako ta har gida, KHADIJA ce tasaka sakata tayo ciki.

UMMU tace "sai yanxu kika dawo ko, bakya jin magana ko?"

Murya sa suka jiyo yana fadin

"ai gashi nan, yarinya bata jin magana....,"

KHADIJA dai daki tayo ta barshi yana ta mitar sa.

A daki ta iske Antyn ta HAFSA tana rike da wayar ta a hannu, fuskar nan ba walwala, ba tai dai magana ba amman ta tsani wannan mitar da yake wa Mahaifiyar su.

Abin ci suka ci sannan suka zauna kallo, daga baya kuma suka mike suka kwanta....





MUJE ZUWA



MS INDABAWA

08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

2




Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Wannan shafin naki Sis Rashidat Abdullahi Kardam (Rash Kardam).

Anty Rash ina alfahari dake, Allah ya kara miki daukaka, Allah yasa ki gama lpy, Allah ya shige akan duk al'amuran ki. Allah yasaki a gidan Aljannah.
AMEEN







Tin asuba HAFSAT ta tashi, sannan ta tashi kanwar ta KHADIJA, alwala suka yo sannan, sukai sallah.


UMMU ce ta shigo dan gannin sun tashi duk da dai tasan sun tashin, gaishe ta sukai ta fice.

HAFSAT falo tayi ta kunna karatun Al-qurani, ta mike ta shige dakin baccin su sannan ta gyara gadon ta ta share dakin,
Ban daki ta shiga ta wanke shi tas, sannan falon su ta share tayi mopping, duk da suna da ma aikata amman ita bata son ana gyara.mata dakin su.

Kitchen ta wuce taje ta daura ruwan tea sannan ta daura farfeson naman kai, dan tasan UMMUN su na son sa, firar dankali ta fara, ta gama ta soya ta gyare kitchen din, can bangaren ma aikatan gidan tayi, dan ganin me suke yi.

Baba Lami ta tarar tana soya musu doya da kwai, durkusawa tayi ta gaidata, Baba lami ta amsa cikin fara'a dan tana son HAFSAT duk da bata sakin fuska amman tana da girmama na gaba da ita.

Juya wa tayi ta shige cikin gida, ban daki ta shiga tayo wanka, ta fito mai ta shafa kawai sai powder sai man leba amman tayi kyau sosai, sabida ita din kyakyawa ce, doguwar riga ta dauko ta saka ta fito falon su bakin shayi kadai ta sha,

Sannan ta dau wayar ta ta kira UMMU, UMMU ce ta dauka, tace.

"UMMU zanje Makaranta,"

"To da kudi a hannun ki,"

"Eh,"

Kawai tace

"To a dawo lpy"

Wayar ta kashe, sannan ta fice, State Liberty ta nufa, ID Card ta nuna sannan ta shige, tin 11 taje wajen bata fito ba sai karfe 2 shima dan zatayi Sallah ne.

Sai da ta fito ta dauko wayar ta missed call ta gani guda 22, guda 2 na kanwar ta KHADIJA ne, guda 10 na HAUWA ne sai sauran 10 na FAIZA ne, tsaki tayi dan tasan yau sun zuba ido su ganta amman bata je ba, ita abinda yasa ta fito gaba daya ma dan MIJIN UMMUN tane, dan in yana gida ya fiya hayaniya, ita kuma ba abinda ta tsana kamar hayaniya.

Yau bata yi niyyar zuwa ko ina ba amman sbd da shi ta fito yin karatu kawai.

Sallah tayi sannan ta kira KHADIJA,

"Sis kina ina ne, su Hauwa sun kira wai baki je makaranta ba,"

"Eh naje karatu ne,"

"Ok adawo lpy, a tahon da ice cream nima,"

"Toh"

Kadai tace ta kashe wayar. HAUWA ta kira, HAUWA tace "Sisi ina kika shiga ne yau, duk ba dadi baki shigo makaranta ba, kin tafi ma buyar ta ki ne,"

"Eh," kadai tace, Hauwa tace,

"Dan Allah fada mana ma buyar nan,"

"Naki!, in anyi Sallah la'asar zan shiga shoprite mu hadu acan."

"Ok tace sai mun hadun,"

"Ina FAIZA,"

"Ta shiga Sallah ne,"

"Ok."
Ta katse kiran, Sai baya minti 10 ta daga waya ta kira FAIXA. FAIZA tace "Sisi yau buyar manan ce ta zo kenan, wa ya bata wa miki rai ya shafa mana har mu aka gudar mana."

"FAIZA kin fiya sa ido, ki tambayi HAUWA nace anjima mu hadu,"

Ta kashe wayar. A ranta tana cewa lallai su FAIZA sun karance ta dan kuwa ran nata ne a bace,

dayake in dai an bata wa HAFSAT rai to ranar bata son haduwa da kowa dan kar ta huce akan sa, to gudun hakan yake sata buyar wa kowa, yanzu haka mitar ABBI ce wato MIJIN UMMUN SU, shi ya bata mata rai sosai, dan a duniya tafi tsanar sa akan kowa.

Dakin karatun ta koma ba ita ta fito ba sai la'asar, Sallah tayi sannan ta zauna cikin garden din, sai 5 ta mike tayo waje.

In dai ABBI MIJIN UMMUN SU na nan bata son zaman gidan dan bata son ranta ya baci, kuma bata son ta batawa UMMUN su rai dan in ranta ya baci zata iya batawa kowa rai.

Napep ta tsara tace shoprite, ta shige sai da ta kusa sannan ta kira HAUWA tace,

"kina ina ne,"

"Gamu nan pls ki tsaya a bakin gate mu dauke ki,"

"Ok,"

Lokacin da taje har sun je ma, mai Napepe ta mikawa 1k tayi gaba, yace canjin fa Hjy, hannu ta daga masa kawai tai gaba, shi kam sai godiya yake mata.

HAUWA ce ta fito da sauri ta rumgume ta tace,
"Munyi kewar ki sisi,"

"Nima haka,"

Jan ta tayi suka shige cikin motar a wajen parking space suka tsaya su fito, tace,
"ya makarantar ne yau,"

FAIZA ce tace
"Ba dadi yau sisi bata nan,"

"Ke dai fadi gaskiya,"

"Allah sisi fada mata"
ta fada tana me son HAUWA ta kara mata bayani,

HAUWA tace "gaskiya ne,"

"Na ji, ni muje yunwa nake ji,"

FAIZA ce ta karbo musu abinci,

HAFSAT tace
"ni bazan ci bafa,"

A tare suka hada baki suka ce
"Saboda me sisi"

"Lemo kawai zan sha,"

"Haba dan Allah, kar fa Ulcer ta kama ki, ke bakya son cin Abinci, bayan kuma yunwa kike ji" Cewar FAIZA


HAUWA ce ta kamo hannun ta tace
"dan Allah sisi kici, keda kike jin yunwa,"

Kai kadai ta gyada musu ta dan tsakura ta barshi, sai lemo da take sha, tana zaune jiran su.

Sai da suka gama suka fice, suka je dan siyawa musu Ice cream, ta siyawa su HAUWA da FAIZA sai nasu da ta siyo musu da chocolates ta KHAIRAT.

FAIZA suka sauke a nan Zoo Road bayan gidan Buhari, sannan muka wuce nida HAUWA a bakin gate suka dire ni sannan suka wuce tana dagan hannu.....




MUJE ZUWA


MS INDABAWA
08062882472


08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
3



Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Wannan shafin naki ne yar uwata, Kawata HAUWA KAMILU ZIMIT, Allah ya biya miki dukkan bukatun ki na Alheri Ameen
Ina kaunar ki, ina alfahari dake a matsayin ki na kawata.







Da sallama ta shiga gidan, Baba Lami tasama a harabar gidan, tana gannin ta ta washe baki, tace
" 'Yar nan kin dawo,"

"Eh," tace sannan ta dan kursa ta gaidata tana tambayar ta ya gidan, "lpy, ya Makarantar" ta tambaye ta, "Alhamdulillah," ta amsa ta shige gidan.

A tsakar gida ta sami, UMMUN su karasawa tayi da sauri gun ta, ta duga tace "UMMU barka da gida,"
"Yauwah HAFSAT, ya Karatun dan nasan yau karatu kika je, dan su HAUWA sun kira wai baki daga ba."

"Eh wallahi," tace tana mike wa, muryar ta da KHAIRAT ta ji yasa ta fito a guje tana "Yoyo Taty,"

"Oyoyo baby nah, ya gidan,"

Dariya KHAIRAT keyi tace "lpy,"

Dire ta tayi, sannan ta mika mata leda, karba tayi tana lekawa, robar ice cream ta ganni sai chocolates dayawa, tsalle tayi tace "Nagode Taty,"

Murmushi na sakar mata na shige dakin mu, ita kuma da gudu tayi wajen UMMU tana nuna mata, Murmushi UMMU tayi tace "Iyye yar gidan Antyn ta,"

Daki tayi da gudu dan nunawa ABBIN ta.

HAFSAT na shiga daki, firiji ta nufa ta saka kayan dake hannun ta sannan ta shige dakin baccin su, toilet ta fada ta sakarwa kanta ruwa, ta cuda jikin ta sosai, Alwala ta dauro, sannan ta fito ta saka duguwar riga mara nauyi mai shimi, turare Aseel ta fesa sannan tayo falo rike da hijab, zaman ta kenan HAUWA ta kira ta, daga wa tayi da sallama, Hauwa tace "kin shiga gida lpy, yasu UMMU da KHADY da KHAIRAT,"

"Duk lpy, yasu Ummi,"

"Suna lpy, sai anjima toh,"

"Aha,"

Tana kashewa sai ga kiran FAIZA, Murmushi tayi ta daga, da karadi ta yi sallama, HAFSAT ta amsa cikin nutsuwa,
FAIZA tace "Sisi ya kuka je gida,"

"Lpy, kefa,"

"Nima lpy, yasu UMMU,"

"Kowa lpy,"

"To shkn sai anjima ki gaida min KHADY da KHAIRAT,"

"To ki gaida min Momy."

Ta kashe wayar tayi, sannan ta lalubo number kanwar tata KHADIJA,

KHADIJA ta dauka da sallama sannan tace "Sis munje gidan Anty Umma ne, kin dawo ne,"

"Eh, kuma kada ku kai dare kisa ai tai mana hayaniya a gida,"

"Kar ki damu yanzu zan dawo,"

kishingida tayi tana me kara jin soyayyar kawayen nata. Wanda suke kula da ita sai kace yar uwar su ta jini, ko yar cikin su.

Tana kwance ta jiyo kiran Sallah Magariba, zaune ta tashi, sannan ta mike tasa hijab din ta dan yin Sallah, sai da ta iddar sannan ta nufi kitchen din su, Madara ta diba a cikin kofi mai yawa, sannan ta fito, a daki ta zauna ta zuba ruwa kadan sannan ta diga zuma a ciki, ta zauna tana sha tana kallo, sai da akayi isha'i sannan ta mike tayo alwala tazo tayi sallah, UMMU ce ta shigo tace, "HAFSAT kinci Abinci ne," "A'ah UMMU na koshi,"

UMMU ta dube ta tace "HAFSAT ban son rashin cin abincin nan naki fa, kinsan kina da Ulcer amman bakya kiyayewa ko?"

"UMMU naci abinci, ki tambayi su HAUWA ma,"
"Shikenan tinda kince kin ci,"

Ta mike ta fice tana cewa "kina dai kula,"

Sai karfe 9 KHADIJA ta dawo a hankali ta shigo dan kar ABBI yaji shigowar ta, rike da system ta sameni ina yin game, gefe na ta zauna tace "washh, na gaji,"
kallon ta HAFSAT tayi ta gefen ido, kawai. KHADIJA tace "Anty ya karatun,"
"Lpy, sarkin yawo."
"Lah Anty gidan Anty Umman,"
"Eh nan din fa,"
"To yi hkri Sis, ina abun nawa,"
"Duba firiji,"
Firij ta nufa ta bude, robar ice cream ta dauka ta nufi Antyn ta ta, tana godiya.

UMMU ce can ta shigo tace "Sai yanzu ko!"
KHADIJA tace "UMMU na jima fa,"
"Allah shirya min ke KHADIJA,"

Daki HAFSAT ta mike ta shige tayi kwanciyar ta,


Muryar ABBI ta jiyo yana "ai in baki wasa ba, sai yaran nan sun saki hawan jini, yara basa ji sai kace me,"

Tsaki nayi na mike na wuce toilet na rufe kofar, sai da na tabbatar ya gama fadan sannan na fito nai kwanciyya tah.


Muje Zuwa...


MS INDABAWA

08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

4



Writting by MARYAM S INDABAWA

MANS






Wannan shafin naki ne, Zahra'u Muhammad Mahmud (Surbajo).
Allah kara basira, Allah kare ki daga sharrin mahasaada, Allah ya biya miki bukatun ki, Allah yasa kifi haka Ameen.





Yau ma tin asuba ban koma bacci ba, sai da na gama yi mana abinci sannan na shige nayi wanka, Mai na shafa sai powder da man leba da nasa ka, humra na dauka na murje jiki na da ita, sannan na fesa body spray na emergency, doguwar riga nasa mai A shape ta atamfa kalar yallow da ja, na daura dankwalin,

bangaren su Baba Lami naje, na tarar tana musu koko da kosai, har kasa na durkusa na gaida ta amsa cikin fara'a.

Gefe na koma na zauna, kosan ta mikon tana cewa "gafa mutumin naki,"
Murmushi nayi nace "na gani fa."
Mikon tayi a cikin filet, na amsa ina godiya, nace "kin tafasa ruwan zafi ne,"
"Eh, gashi can a fulas,"
Ta mike da nufin dauko min nace ta barshi, sai da naje na hado na zambada uban sugari sannan na...


Read / Download MIJIN UMMU NAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album