Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KISHIN MATA Complete Hausa Novel Document by KISHIN MATA


KISHIN MATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 47230



KISHIN MATA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 24, Oct 2023

Author: Hafnancy Lurf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Intelligent Writers Association

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 264.93 kb

File Type: txt

Views: 735+

Download: 488+

Last download: 2 days ago

Description/Story:  *🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*
*#Love#fiction*
_•Copy cats are advised not to transform or reproduced this publication by all means including recording or any other electronic methods without the prior written permission of the writer°_

_#In this article, we will investigate what is going on in the minds of men who seek to marry more than one wife. What are their views on the matter? We also want to know what their wives think about their husbands’ looking to marry again_

    _*FREE PAGE…!*_

      _*💫BABI NA DAYA…☝*_

       _*★CENTRAL AREA GARKI,FCT ABUJA*_

______________★Awani tangamemen gida ne wanda ya amsa sunansa da gida,ginin zamani ne wanda aka ginashi on a low key,ma'ana anyishi ne very simple and attractive bbu wani tarkacen decorations da akewa irin mighty house dinnan,no wannan is juz too simple and beautiful,kana sada kanka cikin wannan gidan,from ur first view zaka tabbatarwa kanka da cewa wannan family house ne,sannan kuma acike yake fam da mata,yan'uwa ne da kuma abokan arziki duk anzo taya *'DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO'* murnar karin auren da yakeyi ayau wanda ya kasance ashirin da biyu ga watan nuwanba ah shekarar dubu biyu da goma sha bakwai,

Ko ina kabi zaka ga duk mata ne dake yau ne ake yinin bikin,ansha anko kai kace ko bikin farko ne,da yawan matan sunyi gungun,anyi group group ana tsegumin zancen auren,kowacce da gutsiri tsomar da takeyi akan *Jameelah* wacce ta kasance uwargida sarauniyar mata agdn DPC Suleiman Gidado,

Ramlah k'anwa ga DCP Suleiman wacce tafi kowa tsanar Jameelah tace da cousins dinta wa'enda suke kewaye da ita''Aini wlhy karku so kuga yadda nake cikin farin ciki da wannan auran da Hamma Gidad'o ya kara don atleast zai saka annamimiyar matar nan tasa nutsuwa da kuma yin ladab...''

Da sauri wata meh suna Baddo tace''Ramlah wai nifa ban san dalilin dayasa kika tsani anty Jameelah ba bayan matan tana da kirki sosae,ki duba fa wlhy idan kaje gidansu na rantse da Allah sai ta rasa inda zata sakaka dan murnar taga yan'uwan miji,kyautatawar da zata maka kuwa abun har baa magana,idan zaka tashi tafiya haka zata sallameka da sha tara ta arziki,sannan kuma ku rabu amutunce cikin raha da kuma fara'a,nidai gsky matar tamun don haka bana tsammanin Hafsah zatazo ta fita samun matsayi awajen dangin miji idan akayi duba da yadda Jameelar ta riga ta siye zuciyoyin dangin mijinta.....''

Ramlah data kai lomar abinci baki tayi saurin hadiyewa tare da kwasar Boddo da uban harara tace''Tadai siye zuciyoyinku amma banda nawa,sannan kuma ki bari ita Hafsan ta shigo mana kiga irin tata kalar kissar da kisisinar,ni na tabbata ma dole ta saukar da zamanin Jameelah aji kawai an bar yayinta,Allah i trust Hafsah bazata ta6a bani kunya ba.....'

Wata Hanifa tace''Don tana yayar babbar kawarki ko?'' ta furta tana harararta,ta6e baki Ramlah tayi kan tace''Abar batun wai tana yayar kawata yasa na fadi hakan,maganar gsky Hafsah karshe ce,she's juz a wife material 100yards,ga iya girki da kwalliya,iya karairaya murya,infact kar kuso kuga yadda take bamu labarin irin yadda zata tarairayi mijinta da danginsa idan tayi aure tou dalilin daya sanya na hadata da yayah kenan don shi yafi dacewa ya mallaketa,sannan kuma nasan zata share masa hawayen daya dad'e yana zubarwa ta rashin ya'ya wanda waccen juyar ta kasa share masa.....''

Dariya duk suka sanya su wajen biyar,Boddo ta cikon shiddan ce kawai bata yi ba illah takaicin Ramlar da take ji,tace''Ramlah wlhy kibi asannu don kema gidan wani zaki kuma idan dangin miji suka sanyaki agaba Allah bazaki ji dadin rayuwar aurenki ba,sannan kuma ita haihuwar ai naga ahannun Allah take,idan yaso ya azurtaka dashi,haka kuma in yaso yaki baka,don haka ki dena ganin laifin anty Jameelah don ita kanta bawai ason ranta take zaune ba haihuwa ba,and again ke baki tunanin ko matsalar daga wajen dan'uwanki take sai ita?ki duba fa duk sauran yan'uwanki ma bbu wanda ya haihu,kamawa daga Gidadon,mustapha har Surayya tou meyasa baki tunanin ko matsalolin daga wajensu yake?

Afusace tace''Wallahi ko rantsuwa nayi tou bazai ta6a kamani ba donni nasan duka yan'uwana lafiyarsu qalau don haka karki kuskura ki kakaba musu lalura if not zamu kwashi yar kallo anan wajen,mahassada kawai.....''

Dafe kirji Boddo tayi tace''lallai Ramlah ni kike fad'awa wannan bak'ar maganar?hassadar meh zan muku?okay na fahimceki,mungode da kasancewarmu talakawa acikin zuri'a,tunda dai har muna cikin qoshin lfy sannan kuma bamu rasa abunda zamu saka acikin bakin salati ba,alhamdulillah da wannan rufa asirin ta ubangiji,amma ki sani ke baki taka matsayin da har zan miki hassada ba tunda ba aljanna ce kika samu ba,sannan kuma idan matsalar ba daga wajensa take ba ai zamu gani idan Hafsan ta shigo......''

Fatima tace''Don Allah ku bari kar abun nan ya zamo muku fad'a kunga har hankalin jama'a ya soma dawowa garemu....

Da sauri Ramlah ta mike tana cin damara da gyalenta tace''Ai walhy karamar magana ta riga ta zama babba don bbu wanda zai hanani cin uban Baddo yau agidan nan,sai ta gayamun ko ni din sa'artace ko kuma ita Jameelar kanwar uwarta ce da take goyan bayanta....''

Hayaniya ta barke awajen,jama'a suka soma taruwa don tuni Ramlah takaiwa Boddo mari,ta rike kunci amma ta kasa mayarwa,cikin huci Ramlan tace''Don sarkin garinku sake maimaita abinda kikace idan kinsan baki tsorona kuma kin haifu dakyau,,shegiya sai iyayin bala'i wai ita kyakkyawa wacce tafi sauran matan zuri'ar nan kyau shiyasa tsoho ya sanya maki suna *'BADDO'* ,ai wlhy dama ina da cikinki akan wannan abun,shin wa kika fi kyau?in kin fisu tou ni Ramlah baki fini ba ehe....'' ta karashe maganarta cike da kishi,

Kuka Baddo ta fashe dashi tallafe da kuncinta dake azabar yi mata zogi,wasu suka rirrike Ramlah ayayin da wasu suka kama Baddo suna bata haquri,Anty Jameelah wacce zance har yakai kunneta itace ta fito ah rud'e,ta kutsa cikin jama'a tana zubda ruwan hawaye,sai kallo ya koma gareta ganin tana shirin magana,Ramlah ta rik'e kugu tana girgije girgije da kuma hararan anty Jameelah tamk'ar idanuwanta zasu fad'o waje,sosae Anty Jameelar ta lura da irin kallon da Ramlan ke watsa mata kuma tun ba yau ba tasan da cewa kanwar mijin nata ba kaunarta take ba,runtse ido tayi ayayin da sabbin hawaye suka tsiraro mata na takaicin abu biyu,wato auran da mijinta ya karo da kuma yadda wasu acikin danginsa suka bi suka tsaneta akan rashin haihuwa,haka ma sun tsangwami matar k'anin mijinta Azeema ammh sai dai ita basu saka mata ido ba kamar yadda ita aka saka mata,

Hada hannaye tayi tace''Don girman Allah na rokeku ku dena fad'a akaina,ni ban taka matsayin da zaku zauna kuna cece kuce akaina ba,da masu cewa bani da amfani sai faccala da dukiyar mijina,ni na rako mata ne zuwa duniya am fruitless,na rokeku pls stop bani na daurawa kaina rashin haihuwar ba,ayau da'ace mutum ne ke azurta kanshi da ya'ya tou wlhy da tuni na haifawa mijina ya'ya kan ya'ya don kawo karshen fitina da habaice habaicen dangin miji da nake fuskanta daga wajen wasunku da yawa......

Dakatawa tayi tana shesshek'a tare da sanya er yatsa ta dauke wasu hawayen da suka ziraro mata sannan ta cigaba''Ayau matar so zata shigo and i believe insha Allahu zata baku abinda kukeso wanda ni Jameelah na gagara baku shi for good 10years,ko kadan bana bakin ciki da wannan auran don ba'a kaina zata zauna ba amma pls you people should stop making me to feel dat am useless,sannan kuma Albishirunku nida kaina zanje dakko amaryata anjima don haka bni buqatar kowacce shegiya tamun habaici da jifana da kalamai na tuhuma don na rantse da Allah asannan ne zatasan ainihin kalar *JAMEELAH AHMAD SADDAM*

Tana gama furta hakan ta juya tabar wajen cike da dacin rai,kalilan mutane ne kawai ta birge ayayin da yawancinsu sun dauki hakan ne amatsayin nata salon *'KISHIN'*

   ________________★★★★

        _*BABBAN FALON GIDA*_

Babban falo ne wanda yake da girman gaske,anan ne ahalin _*TSOHO'*_  ke yada zango asha fira,ko ahadu aci abinci ko kuma aduk sanda family meeting ya taso,

  *'TSOHO'* kamar yadda ya'ya,surukai da kuma jikoki ke k'iransa,,haifaffen rugar Lugbe ne dake garin Abuja,fulanin usuli kuma wayayyen dan boko,kuma tsohon dan sanda wanda ya dad'e dayin ritaya,matan auransa biyu kuma kowanne ta zuba ya'ya ba laifi, *MAMA BARAKAH* itace uwargidansa kuma ya'yanta takwas, Alassana da Alseny (yan biyu),Haruna,maimuna,ladidi,karime,Munniru,sai Aissatou,

*MAMA DALANDA* Itace amarya mai ya'ya biyar,ita kuma duk ya'ya mata ne sai namiji daya kwal,Fatoumata,binta,Boddiya,Ma'u sannan autan gida Shagari,

Akwai zaman lfy sosai atsakanin wannan ahalin,tsoho be samu wani matsala da matayen nasa ba,,har suka koma ga Allah dukah yana mai alfahari dasu,bayan yayi ritaya shine ya'yansa maza suka daukeshi zuwa sabon gidan da suka tare da iyalinsu gabaki...


Read / Download KISHIN MATA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album