Join Our WhatsApp Group

BIRNIN GAYU Complete Hausa Novel Document by BIRNIN GAYU


BIRNIN GAYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 112721



BIRNIN GAYU

Reading Time: 9 Hours

Added On: 16, Sep 2023

Author: Sa'adatu Waziri Gombe ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 605.76 kb

File Type: txt

Views: 3512+

Download: 2158+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: a zallah
Birnin gayu
Chapter1
BIRNIN GAYU. BOOK1
tunkwal Tunkwal Tunkwal "Sautin daka ne ke
tashi daga Cikin kewayayyen Gidan Karan wanda
aka yi masa danga da
itacen Dalbejiya. , , . Tafiya ta ke cike da nutsuwa
dauke da
Littattafan karatunta a hannu ta" nufo Gidan, ga
dukkan alamu yunwa da Gajiya na tattare da ita.
Da sauri ta shiga Gidan tare da yin sallama.
Cikin nutsuwa, "Assalamu alaikum".
Abin da ta gani ne ya sa ta yi sororo kamar
wacce aka zarewa rai.
Inna mai Fura ce ta fara kokawar kife wani '
qaton Turmi wanda ga dukkan alamu itama
gadon shi ta yi daga Kakanninta. A qiyasi na zan
iya cewa Turmin ya bata . shekaru'. ” Inna mai
Fura, kenan, yadda mutane suke kiranta ta juyo. '
"Au Deeda har an taso ku?" "Eh mun taso
walléhi".
Inna ta yatsina fuska ta dan kau da kai.
"Ni wallahi banga amfanin wannan zuwa
Makarantar 'ba. yanzu in a Gida ki ke da tuni
mun
‘ Surfe Gero yafi Kwano uku, kin ga, Gidan su
Talle .da suka aiko ma sai mayarwa nayi don aiki
ya yi min
yawa.Shiga ki cire kayanki ki zoki karasa min
sallanabku dai". Aka yi sallama daga waje. ' Inna
ce ta amsa sallamar. ' "Allah Ya yi mana. Wa na
keji haka kamar Tabawa?" . ' , . ' "Ni ce wallahi
cikin ranar nan "To shigo ga Tabarma nan ki
zauna”. Inji Inna. Kan wata- busasshiyar
Tabarmar Kaba suka zauna Bayan sun gama
gaisawa Tabawa ta dubeta kamar .matar da aka
ba ta labarin mijinta zai kara Aure, ta ce, "Wata
magana nazo miki da ita idan har zaki amince '
Kin san dai wannan jikar taki .duka 'yan matan
garin nan ba sa'arta,,yanzun ga shi shekararta
goma sha takwas har yau ba manemi, to me zai
hana ki bani ita in tafi DA ita birni don ko kinsan
dai lalurar data kashe Yan,uwanta har biyu Ina
tabbatar miki da harta manyanta ba zata taba
samun mijin aure a kauyennan ba in banda
wannan jarababbiyar bokon DA take zuwa Wanda
daga ke har ita baya tsinana muku komai
kalleki Ki gani yanxune lokacin Daya dace ace kin
huta Amman kinanan kullum surfe da saida fura
ya kamata Ki amincemin dan Ina tabbatar miki da
akwai alkhairi acikin wannan lamarin kika sanima
ta wannan dalilin ta samu mijin aure DA maganin
matsalarta
Inna tai shiru tana nazarin tayin tabawa Anya
kuwa bazan amince wannan Karon DA tayin
tabawaba kuwa to saidai kuma deeda miskilar
gaske ce banajin zata amince
Ta kalli Tabawa tace, "To ban ki ta taki ba, ‘
amma fa kin san Deeda halinta sai ita..." "Duk
halinta ai batafi karfinki ba, sai dai in
keki ka so... _ Ni fa taimako na ke son yi, don
kuwa BIRNIN GAYU zan kai ta Aiki".Inna ta zaro
ido jiki rawa ta ce, “Me..me...me kika ce BIRNIN
GAYU fa?" Tabawa ta gyada kai ta ce, "Kwarai
’BIRNIN GAYU zan kai ta Kin San k0 dan kammin
Yaro da ke cikin Kauyen nan ya san sunan Birnin
Kin san irin kudinsu ‘kuwa ba irin‘ masu kudin
yanzu'bane ba, don tun zamanin da...tun
xamanin da za a iya kirga masu kudi a kasar nan
suke . Tuni Inna ta susuce Ta mike jiki na rawa
ta ce "Ah, gaskiya na yarda kina sonmu da.
arziki. Wai Ai dole Deeda k0 tana so, k0 ba ta
so...ta wuce Birni.. Can kuma ta yi KaSa da
murya, cikin sanyin jiki tace "To amma Tabawa
ba kya ganin lalurar Deeda zai shiga tsakaninta
da wannan dama da ta samu?" ‘
' Tabawa ma ta mike ta ce "Karki damu, lalara ce
da a Keuye kawai aka santa, kuma ya shafi
Aure ne, amma ai lafiya take ba mai kallonta ya
cr ‘ tana da wani lalura..in kina son zuwanta Birni
to, dole lalurarta ya zama sirri tun da anan
Kauyen ne" kawai aka sani, don haka maganar
Kauye a barta a Kauye...Yanzu dai babbar
matsalar Deeda ta yarda".
"Ba zan yarda ba Suka ji muryar Deeda ta ratso
kunnuwansu. Tsaye take a Kofar daki ta ‘rike
kugu tana dubansu. ' ‘ 1 "Sanin kankine Tabawa
ba inda za ni k0 da ‘kuwa Inna za tai kuli-kulin
kubura da ni ba zani aiki Gidan waSu ba, k0 da
kuwa zan tafi tsirara ne don talauci balle Allah Ya
rufa min Asiri. In ban da son zuciya me na ke
nema da zanbar Mahaifata in tafi wata uwa
duniya don neman kudi...?." "To mara kunya‘
Inna mai hura ta fada cikin hasala. Deeda ta Bata
fuska .ta ce, "K0 me za ki ce sai dai ki fada
amma ba mai canja min ra'ayi.
Ke kuma Tabawa ja jiki ki bar mana Gida kar
ki kuma zuwa mana Gida in kin san ba abin arziki
yakawo ki ,ba.
Kuma duk na ci da maitarki ba za‘ki yi
' nasarar kaini Birni ba. Ba mai shiga tsakanina
da ’ tushena
Tana fadin hakan ne cikin tsiwa da, daga murya.
Tuni Tabawa ta harzuqa, haushi ya cikata. Ta
ce"Magani na Daga yin abin arziki yarinya karama
Za ta tsaya min da rashin kunya?" Nan ta fita
cikin fishi tana mita.
Inna ta_ bita tana ba ta hakuri amma ba ta
saurareta ba. Nan ta juya ta hau Deeda da fada
da zagi. -
Cikin zafin zuciya. ta ce, "Ai sai ki rayu ki mutu
da karatun. Me karatun zai tsinana miki‘?
Ban ga uwar da ki ke daukowa a Makarantar ba,
ki ci uban tafiyar Kafa ki je ki tsugunna Gindin
Bishiya ga Kishi ga Yunwa duk inda ki ka wucé a
garin nan Zaginki ake ana tsegumi, qatuwar
Budurwa dake ba Mijin Aure, maimakon ki zauna
a Gida ki rufawa kanki Asiri amman ina gara dai
ki fita ki Kara tona mana Asiri.
Ni ba ki ’min amfani ba, ke baki yiwa kanki wani
amfaniba. To ni na gaji da miki Wahala, duk ran
da bakincikinki ya kasheni sai ki Huta.
Bakincikin ki da shi nake kwanaina dashi nake
tashi duk kin zame min Larura, k0 Ubanki kasa
‘rike ki‘ya " yi sai ‘ni da ki ka zamar min dole,
don na uwar ki
Bakincikin' Yayunki ya kasheta, kema
kema kikeaon naki ya karasani. To baki isa ba
“Deeda ta 'kalléta' cikin_ zuciya da
tsantsar bakin ciki da Bacin rai, idonta yayi jawur.
Tayi murmushin takaici tace, "gara
. maganar jama'ar Kauyen nan ai ba komai bane
kan
wanda ki ke min'kullum. . '
Idan bar kin ga na zame miki larura kina da
damar' ki koreni a Gidanki...sai dai Gorinki hade
da Bakaken Maganganun da kike fadamin'bazai
sa na
karaya ba k0” yasa naje Birni Aikatau ba."
"‘ Tana gama fadin haka ta juya tama bar
gidan ta nufi can wani gindin Gadah ta ,zauna
kan
wani Dutse tana kukan bakinciki wanna kan
dutsen shine ya Zame matar tamkar cinyar
mahaifiyarta DA take hawa idan ta shiga wani hali
na baqin ciki tashin hankali KO kuncin rayuwa
@@@@@@@@@
Nana khadija yar asalin kyauyen hayin hago ne
dake qaramar hukumar tofa dake kanon dabo
mutanen kauyen sun shahara ne akan sana ar
Zuma matuqa ba boyayyu bane indai akan harkan
Sana,ar Zuma ce
sun shahara wajen noman tumatir DA albasa
garine Wanda ya hada Hausa fulani hakanan aure
na shiga tsakanin su khadija ta fitone daga
Hausa Fulani mahaifinta bahaushe inda
mahaifiyarta take bafulatana
dukda qaramin kauyene Amman suna rayuwansu
cikin jin dadi DA kwanciyar hankali sunada
tsangayu na karatun alqur,ani a yayinda
makarantar
Boko sai an yi tafiyar' kusan kilo mita uku kafin a
samu firamari daya jal sabo da karancin Dalibai
da su kansu Malaman. ‘ ' Haka itama Sakandare
(Secondary) a na daf'
Suna karatun Boko dai—dai 'gwargwa'do; sai‘ dai
da alama mutanen Kauyen bokon bai'damesu ba
musamman ma sabo da wadannan abubuwan
Na- farko, ga nisan tsiya kafin akai ga zuwa
Makarantar.
Wani lokacin ga rashin Malamai. da rashin
'fahimta, don haka da yawa suka watsar do
karatun. Mahaifin Khadija ba shi da sana‘ar da ta
wuce Zuma.
Mahaifiyarta kuwa tana sai da Nono ne, ya yin ”
da Kakartake sana'ar Fura‘ Sunan .Mahaifin -
Khadija Mallam‘ Audu: Mahaifiyarta kuwa
Halima', suna kiranta da" hali‘ , Su uku rak
Mallam Audu ya haifa, dukkan su’ Mata ne
Jamila ce babba sai Mariya sai kuma ' Khadija
wacce ake kiranta da suna DIJA‘. ' ' Sunan
DEEDA kuwa ya'sam'asali ne’daga wurin Kakarta
Inna mai Fura lokacin da aka yayeta’ ‘
ta koma hannunta ta yayeta, in tana kukan
‘shagwaBa irin na 'yan yayan nan sai ta yi ta
mata Wasa'da; cewa Deeda na yar gidan Inna
ma’iFura ". Da haka sunan ya bita duk kauyen
sunan DIJAN ya Bata sai 'DEEDA'. ' ’Kusan girma
da wayon Deeda ta yi shine a hannun 'Kakarta
wacce ‘ta haifi Mahaifiyarta kasancewar Inna mai
Fura ita kadai ce a gidanta Mijintaya jima da
RasUwa-'yan tsoffin da suke tare ko duk sun
rasu, ’yan uwa kuWa kowa ya kama gabansa,
don haka Deeda ke debe ma ta kewa. Kauna da
shakuwata shiga tsakanin-su sosai, duk da Kaka
ce Inna mai Fura ba ta yi ma ta goyon Kaka ba,
tana kokarin sanyata a hanya da ba ta tarbiyya
dai-dai gwargwadon tunaninta da saninta. ,. .
,Iyayen Deeda suna .rayuwa cikin kWanciyar
hankali Yayyun Deeda Jamila _da Mariya ba su
damu da_'karatun zamani ba, don haka iyaycnsu
‘ba su matsa musu ba suna dai Kokarin zuwa” na
Allo, shima a kwana a tashi suka watsar.
Matsalarsu ta- fara, ne a lokacin da aka yi Auren
Jamila yayar Deeda, an kaita gidan miji washe
gari ta tashi da wani irin ciwo marar kyan
gani. jikinta ya dawo tamkar waccé ta yi shekaru
tana jinya. Mijinta bai Bata. lokaci ba ya dawo da
ita
gida ta'dinga jinya.
‘ Duk .wani abu da suka mallaka sai da ya kare
a jinya, masu magani ko ba Kauyen da ba a shiga
ba
amma ba nasara 'kowa da irin abin da ya ke fadi
‘ wasu su ce Asiri, wasu Su ce Aljanu, amma" ba
wanda ya samo maganin, da haka har'kwanan
Jamila ya kare a duniya ta koma ga Mahaliccinta.
Haka abin da ya faru da Jamila ma dai irinsa ya
faru da Mariya ciwon iri: daya. ne
Daga nan fa aka camfa gidan su Deeda cewa'
Aljanu sun aure jinin gidan. '
Wasu kuma suce Aljani. ne ya auri uwarsu ba
'ya'yan mutum bane
' . Wasu kuwa‘ su ce‘ Asiri aka yiwa Babansu
wani Saurayi da aka kasa gurin ‘neman auren
Mahaifiyarsu. -_
‘ Abin ka da Kauye, Kauyen ma na sosai, ’ akwai
karancin-ilimi da wayewa,~haka duk maganin
nan da suke ba wanda ya gwada na Asibiti don
ba su yarda da shi ba. ‘
. Asalin garin ma wani ’busasshcn (Dispensary)
ne don sai a dau tsawon shekaru k0 nurse babu
balle Likita. ' Haka nan “sun fi 'bada gaskiya ga
maganin gidan akanna Asibiti.' Wannan champi
da aka yiwa gidan su' Deeda ya kuntata rayuwar
Mallam Audu da. zuri'arsa, ' Dukkan; jama,ar gari
sukayanke huld'a dashi,
wai aljani ya auri
' Matarsa k0 haka baibata lokaci ba ya saketa ya
kuma ta. ..
ce ta kwashe kayanta a lokacin tabar masa
gidansa ' Haka nan Deeda ya yafe mata k0 ganin
.fuskarta bayasonyi wai don karta. shafa ‘masa
cutar maita ta manta ma tana da Uba. shi kuma
zai dauka ‘kamar baitaba haihuwar wata'ya-
Khadija. a duniya ba
Haka Inna Hali ta koma gidan Inna mai Fura , ;
tana' kuka, ta labarta mata yadda aka yi.- Inna
mai Fura tai ta bata haquri 'gami da kalamai
masu ‘_kwantar. da hankali a matsayin .ta’na
Uwa, ta shiga qunci .da‘ 'bacin ran ganin 'yarta a
wannan hali ga Saki " ga ‘ wulaqanci, 'yar .tasa
ma baya so
Sai dai Inna Hali ta fita shiga tashin bankali sabo
da Mace mai runi yayin da Inna mai Fura ke karfi
hali.‘kawai
' Deeda. na shckara bakwai. rabonta-da ganin
Mahaifinta suna gari daya kuma guri guda amma
ko. ahan’ya bai son ganinta, daga karshe ma
aurensa ya yi ya ci gaba da' rayuwarsa da
sabuwar Matarsa
Wannan bakinciki yayiwa Inna Hali-Yawa, ta _
kwanta Ciwo, haka Deeda ta ga Mahaiflyartacikin
ciwo da wahala, tana- tausaya mata har
kwananta ya kare ta barta a'hannun Inna mai
Fara, lokaci guda Deeda ‘ta zama marainiya ba
Uwa ba Yayye duk da k0 tana da Uba Amman
dashi DA babu duk Daya suke' rayuwarta ta dawo
daga ita sai Kakarta. -
Deeda ta, tashi yarinya shiru-shiru da ba ta da
magana kwata—kwata, in har ta bude Baki to
dole ya zama-za ta. tambayi wani abu ne ko ,ta
fadi wani abu ~ mai muhimmanci
Wannan abu da ya yi' ta faruwa a gidansu ya
zame mAta~ ayar tambayoyi da yawa a
KwaKWalwarta .wanda ba 'ta da amsarsu da
alama idonta da zuciyarta tare da Kwakwalwarta‘
suna, fadawa duniyar yawon neman amsar ne
kowanne lokaci.
Wannan al'amari ya dasa ’babban' Ayar 1
"tambaYa a kwakwalWarta Haka Inna mai Fura
za‘tasata'tai ta yi mata Surutu, wani lokacin
Waka, wani lokacin - , Zolaya, wani lokacin
‘Ta'tsuniya,’ amma'Decda ba ta’" taba tanka ma
ta ba sai in ta gaji ta fashé da‘ kuka.‘ 'Hakan
yasa tsoro ya darsu a zuciyar Inna 'mai ' F ura ta
fara :tunanin cewa karfa wani ciwo ya kama
Deeda, tana tsoron rasata, don ita kadai ’ta
mallaka duk duniya. Sannan tana tunanin idan ta
mutu tabarta kuWa ya rayuwar-Deedan zata
kasance? bata da kowa bata da komai? - ‘ ' .
Inna‘mai Fura bata gaza ba, ba'ta karaya har ta
tashi rokon Allah iya iliminta da kuma da rubu da
addu'o'i a wurin Malaman Kauyen. ‘ . Duk 'yan
kwabbanta sun. kare-a. wurin, neman samun
canji a tare da Deeda
‘Wani yammaci' Deeda ta fita karkashin " gada
ka'mar yadda ta saba kullum sabo
" da ba komai take yi ba ba k0 ina take;
zuwa batada DA abokan yawon Amman wani
zubin takan taya Inna Mai hura surfe KO aikin
Gida
rai bace ta shigo gidan Inna Mai hura tai mata
tambayan duniyannan Amman taqi kulata harta
gaji ta koma kan harkokinta kaman daga sama
taji deed na cewa Inna menene wannan dake
fitowa a jikina DA Sauri ta janyota tana dubawa
cikin tashin hankali tace menene wannan deeda
kuma tun yaushe ya Fara fito miki cikin tashin
hankali ta jero mata tambayoyin har biyu
deeda tace na cikina yadan Dade yanxu kuma
harda cinyata yanabin kafafuwata Inna mai hura
ta Saki salati
deeda ta kalleta menene Inna!?tai dan murmushin
DA za,a Iya kiransa DA yaqe tace ba komai gobe
idan Allah ya kaimu Zan kaiki wajen me mAgani
a ranan Inna bata rintsaba don tunda take bata
taba ganini irin wannan ciwonba was he gari DA
sassafe suka nufi wajen Mai magani shimadai
abin sabo ya zame masa amman ya basu wani
magani yace a dinga shafa mata za,a dace a
hanyarsu ta dawowa deeda ta dubi Inna taga
yaddah hankalinta ke a tashe tace inna a kaini
asibity mana Inna ta dubeta tace asibiti sai birni
deeda kumama wannan ciwon naki bana asibity
bane tundaga nan bata sake cewa komai ba shafa
wanna maganin ake Amman Ina Abu sai qara
fesowa yake anyi maganin anyi maganin Amman
Ina hakan baisa an daceba tsoron kada mutane
su game halin DA deeda ke ciki yasa Inna ta Fara
Neman mafitar yaddah zatayi domin ta boye
wannan lalura na deeda
tai dabarar dinka ma ta riguna masu dogon
hannu da tsayi wadda idan ta sa har kusan rufe
mata kafa takeyi, haka kuma rigunan suna da
kwala wadda take rufe mata har wuya. . Abin
wasa-gaske, sai da ta kai wannan abin '
ya bi dukkan jikinta ya gewa'ye, ya zamo fuskarta
ce kawai ta tsira. ,
Wannan kalar kayan su suka zama kayan
Deeda. . ‘ ' Akwana a tashi bar Deeda da Kakarta
suka saba da lalurarta.
Deeda na da shekara tara ta matsawa Inna mai‘
Fura akan ta sakata a makarantar Boko, yara
tsiraru ' da take gani a garin suna zuwa boko ne
hakan ya ba ‘ ta sha,awa, _ta sawa ranta' Son
karatu; Inna k0 ta ce sam ba bokon da za ta
sakata in ba neman fallasa ba yanzu ma tana da
lalura ta ce za ta shiga Makaranta?
Nan fa Deeda ta dage, kukan rana daban, na dare
daban, haka ma na safe daban, har da rashin
lafiya. Dole Inna mai Fura ba don ta so ba 'ta
amince
akan za ta sakata a makarantar.
Ranar kasuwar dawakin Tofa ta fito ita da Deeda
da kafa, ta tattara 'yan kwabbanta ta saya ma ta
irin kayan gwanjon nan biri da wando na dai-dai
shekarunta ta sai ma ta guda hudu, biyu‘masu
nauyi biyu marasa nauyi. '
Duka kayan da Deeda za ta saka sai ta...


Read / Download BIRNIN GAYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

6 months ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

6 months ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

6 months ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

6 months ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

4 months ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

4 months ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album