Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel Document by Inda Rai Book 1


Inda Rai Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 81011



Inda Rai Book 1

Reading Time: 6 Hours

Added On: 07, Jul 2024

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09097853276, +22790899076

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 451.42 kb

File Type: txt

Views: 919+

Download: 1654+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: ********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
[1/1, 12:35 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
23/10/2023 Monday. 2:18 PM.

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 1*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, tare da salati ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.* Alhamdulillah yau Yau 23 ga watan 10 shekara ta 2023, Allah ya nufeni da kafa alƙa'amina na fara rubuta sabon littafina mai suna INDA RAI, Ya Allah ina tawassali da kyawawan sunayenka, Allah ka bani ikon rubuta alkhairi a cikin wannan littafin nawa, kayi riƙo da hannayena da rubuta sharri duk ƙanƙantarsa, ka bani hikima da basirar rubuta abinda zai amfanin al'ummar musulmi baki ɗaya, Alhamdulillah Yah Allah ngd maka dama ka nuna min forkon littafin nan Lfy. Ya hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, ka nuna min ƙarshe littafin nan Lfy dani da masu karatun baki ɗaya,Yah Allah ka nuna mana forkon littafin da tsakiyarsa da ƙarshensa dama duk wani sashi da layi da ɗigo na cikin littafin nan Lfy. Yah Allah kayi riƙo da hannayena da tunani da yatsuna da rubuta abinda zai zame min masifa ko wahala ko tozarta na nan gidan duniya da ƙiyama. Yah Allah gamu gareka kaine mai rawaya, mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, Yah Allah ka rayamu bisa imani kan tafarkin Muslunci da bin dokokin shariya, Rabbi ka azurtamu da lfya, da imani, da wadata, da kwanciyar hankali, da zaman lafiya, kasa muyi kekkyawar rayuwa, ka bamu kekyawan karshe, kasa mucika da imani, da kalmar shahada, ka sadamu da mala'ikun rahama yayin fita ranmu, ka sauƙaƙa mana amsa tambayoyin Qabari, ka yalwanta mana makwancinmu ka faɗaɗamana, ka haskaka mana, ka ni'imta mana, ka ƙamsashamana, ka sayan ƙaburburanmu su kasance dausayin Jannatul Firdausi, damu da iyayenmu da ƴaƴanmu da yayunmu da kannemu, da kullum musulmi. Ya rabbil izzati ka samu ƙarƙashin inawur al'arshinka a ranar da babu wata inuwa sa ita, badan mu ba, badan ayyukan muba, Yah Allah sai dan rahamarka da ƙaunarka garemu, Allah ka sauƙaƙa mana tsallake siraɗi,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Yah Allah kasamu cikin al'ummar Annabi amintacciya. Yah Allah mu bayinkane masu yawan zunubai, sai dai hasken gafararka da rahamar ka ya rinjayi duhun zunubanmu, Yah kayi mana gafara da rahama ka shafe zunubanmu. Ka shiryemu bisa tafarkin gaski ka ɗaurar mana da imaninmu a zukatan mu, Yah Allah kada ka jarabcemu da ƙaddarar Jarrabawar da zata raunata mana imaninmu bare ya rabaku dashi.
Ya Allah ka azurtamu da halal, ka nesanta haram daga garemu. Yah Rabbi mu ma buƙatane a gareka kai kuma mai badawane da baya yankewa. Yah Allah masu lafiya, ka ƙara mana Lfy da imani, marasa lafiya ka basu lfya da imani, masu ciki Allah ka sauƙesu lafiya, masu son haihuwa ya Allah ka azurtasu da nagartattun yara. Yan Allah mu masu Yara Allah badan halinmuba Allah ka shirya manasu ka tsaresu da sharrin akiruzzaman, Yah Allah masu neman mazan Aure Allah ka azurtasu da maza na gari, maza masu neman aure ka azurtasu da mata na gari. Yah Allah masu son zuwa aikin hajji da niya, Allah ka kawo mana sauƙin rayuwa da rogomin farashin komai na rayuwa ka bamu ikon zuwa Hajji kasa muyi Hajji Mabrooq, Yah Allah yan uwanmu musulmai dake Palastine Yah wahidulqaharu, ka shigar musu faɗanan ka tozarta waɗanan baƙaƙen kafuran Yahudawa da basa son ci gaban addininmu. Yah Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu. Yah Allah ka kawo mana sauƙi da ƙarshen yan ta'adda dake addabar ƙasarmu Nigeria, Yah Allah ka karemu damu da maƙotanmu, musamman Niger, dama duk Afirka baki daya da duk inda musulmai suke a faɗin duniyar nan. Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati.


*Littafin INDA RAI, na kuɗine, kuma nawa ne ni AYSHA ALIYU GARKUWA, hakkin makalarsa nawa ne, ban yardaba ban amince ba, ban lamunceba, a juya min labarin littafina ta ko wacce sigar, har sai an nemi sahalewata da yardana... idan na amince na bada dama sai ayi. Zama Lafiya yafi Zama ɗan sarki barin haƙƙin wani shine zaman lfyar tauye haƙƙin wani kuwa ko ka zauna Lfy a duniya tofa kasan/kinsa/kunsan gida biyu Allah yayi mana.....!*


*Yah Allah ka jiƙan mahaifinta, Faɗimatuzzahara, Rabbi kayiwa (Dedde na) Rahama da gafara alfarmar Annabi da Alqur'ani, Yah Allah kasa mutuwa hutuce a gare ta. Da ita da Yah Abubakar na da Kakata Ayshae, Innayi na, da kakana M Muhammad Babayo Maiturare da kuma Muhammadu Daniya. Da ma dukkan yan uwana Amin Ya Allah*

_Wannan littafin sadaukarwane, ga ɗaukacin ƴan uwanmu musulman ƙasar Palastine da aka kashe Yah Allah ka jiƙansu kayi musu rahama ya hayyu ya ƙayyum ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai ka ƙasƙantar da Kafirci da Kafirai._

*Littafin INDA RAI na kiɗine 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 mutan Niger ku kuma 1000fc ne wato kaka ɗaya kacal ta wurin Mommy zaku biya +22790899076. Please mommy babbar macece dan Allah mu girmama shekarunta.*


Adamawa Yola. Yau garin an tashi da tsananin sanyi mai ratsa jiki da ɓargon ɗan adam, sanyine kuma irin na damuna, wanda aka kwana zuga ruwan saman kamar da bakin ƙwarya, kana aka wayi gari dashi, domin har yanzu karfe 5:00 pm. Ana sassayan yayyafin da ya tsananta sanyi a garin wanda ya tilastawa mafi akasarin, mazauna garin sanya rigunan da zasuyi musu Garkuwa Da sanyin...

Yola international airport.
Cike yaƙe maƙil, da tarin dan-danzo Mahajatan jirgin ƙarshe da zai tashi daga Nigeria zuwa Saudi Arabia.

Gaba ɗaya taron matafiyan, duk wanda ka gani, fuskarsa cike da tarin Alihini, ɗimuwa,gami da matsanancin bugawar zuciya mai cike da Fargana kana da taraddadin mai tsananin gaske, irin fargabar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ya binne miliyoyin kuɗaɗe a campaign, yake riskar kansa a lokacin da ake faɗin sakamakon zaben, to irin wannan fargabar maniyatan suke ciki baki ɗayansu.
Saboda hukumar amsar jiragen baƙin mahajjata na duniya baki ɗaya, ta fitar da sanarwar cewa, da ƙarfe sha biyun daren yau ɗin ne, za'a rufe KING FAHD international Airport, Saudi Arabia, wanda dama shine ƙarshen rufewa, duk sauran Airports ɗin a rufe su, saboda dafifi da ƙurewar lokacin.

Cikin tsananin shiga ruɗu, wani farin Dottijo da bazai gaza shekaru 52 da biyu ba, ya shiga cikin asalin taron Maniyatan, gyaran murya yayi tare da fuskantar su, da kyau a matsayinsa na Amirul Hajj, na Adamawa wanda kuma a shekarar ne aka ɗorashi, yayin da tuni tsagin adawar sa suke farin cikin, ganin a shekararsa ta farko Maniyata sama da ɗari bakwai da hamsin ne bazasu samu damar zuwa Hajji ba.
Fuskantar taron ɗaruruwan Mutanen maza da mata, yayi cikin Muryarsa dake cike da rauni, tashin hankali da Karaye yace.
“Da forko ina mai baku haƙuri, bisa jinkirin da aka samu na isowar jirgin ƙarshe da zai kwashi mahajjatanmu, zuwa ƙasa mai tsarki.
Kuyi haƙuri ku kwantar da hankalinku, kun sani na sani alƙawarin Allah tabbaceccene, in dai Allah ya ƙaddara bana zamuje Saudi Arabia kuma muyi aikin hajji to in sha Allah, sai munje, in kuma Allah yayi bamu da rabon zuwa bana, tofa duk nacinmu da ƙoƙarina wurin ganin hakan ya tabbata bazai yuwuba, so mu maida lamarinmu ga Allah domin shine kaɗai mai iya mana...”
Sai kuma yayi shiru tare da zurawa P.A ɗin tsohon Amirul Hajj ido, wanda aka sauƙe, kafin a ɗorashi.
Cikin haƙilo,hargowa gami da ɗaga sautin murya mai tattare da kishi ya kalli taron jama'ar tare da cewa.
“Na nawa kuma, ai kunga banbancin aikinsa da wanda ya gabata ina tunawa last year, tun saura kwana biyar a rufe Jidda Airport, aka gama kwashe mahajjatanmu, bana kuma gashi duk, Nigeria mune kuran baya, kai Bama Nigeria kaɗaiba duk duniya mune kuran baya, yanzu fa ku duba karfe 5:00 pm. Jirgin namu ma bai isoba bare aje ga batun scaring...


Read / Download Inda Rai Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album