Join Our WhatsApp Group

BABBAR HUJJA Complete Hausa Novel Document by BABBAR HUJJA


BABBAR HUJJA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12138



BABBAR HUJJA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 09, Mar 2024

Author: Fatima Dahiru Funtua Bintu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09162526909

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 79.57 kb

File Type: txt

Views: 472+

Download: 173+

Last download: 2 days ago

Description/Story: BABBAR HUJJA 1

NA

FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA 📖📚


Wannan littafin na suyarwane,gamai bukata .
Akan kudi naira dari uku N 300

Account Number zada ka/ki sa kudin.
1527970269
Access Bank
FATIMA DAHIRU

Ko kuma kasa katin MTN na naira Dari uku akan wannan Number
09162526909
Gamai bukatar cigaban labarin sayyayi magana ta wannan number
09162526909

Don Allah kada kadauki Number ta kayi Mani magana idan baka tashi siyen littafin ba.





Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai daya sake hadamu cikin wani sabon littafin.
Mai suna BABBAR HUJJA! Tsira da Amincin Allah sukara tabbata ga shugabammu Annabi Muhammad (S A W) da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya.
Narubuta wannan Dan littafine domin farkar da mutananmu ,musamman. 'Yan mata da samari akan kalubalan da yake acikin soyayya,kawai mutum yayi imani da Allah,akan dukkan abinda baisamekaba,to daga Allah ne,kuma komin son da kakeyima Abu idan ba rabonka bane sayya tseremaka,yafi kyau dukkanninmu mukoma ga mika All amarimmu ga Allah kawai,musamman akan soyayya,domin akan ta zan rubuta wannan Dan littafin.
Sodayawa zakiga mutum kina sonshi,kokuma shi yana sonki,amma karshenta abin ba Alkairi bane a tsakaninku,to mafi yawan 'yammata da samari idan hakan tafaru a garesu ,sai kaga suntada hankulansu,har ananeman rasa lafiya.
Don haka samari da 'yammata asa hakuri acikin zuciya,komai daga Allane.
Wadda kake hangen ko Wanda kike hangen,karshenta ba shine mujin ba.
Amma bazance komai ba akan haka ,kubiyoni acikin wannan littafin na BABBAR HUJJA kuji yadda soyayyar wasu masoya zata kasance.
Fatanadai a dauki abinda yakeda kyau acikin wannan littafin .
Sannan littafin BABBAR HUJJA kagaggen labarine,bawai yaru akan wani ko wata bane,AA kirkirarsa nayi,don haka koda kaga wani Abu kowani hali yayi kama da irinnaka,to bakaidin bane,don WATA kilamani bansankaba ko bansankiba,kirkirar labarinne kawai yazo da haka,don haka idan abin gyarawane ,saika gyara .

DAGA
FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA

GARGADI
Banyadda ajuyamin wannan littafin ta WATA sigaba har saida izinin marubiciyar.
Gaisuwa ga dukkannin masoyayana,aduk inda suke,ina sonku kamar yadda kuma kuke sona .
Ayi karatu lafiya

Dasallama tashigo falon fuskarta dauke da tsararriyar kwalliya ,wadda yayi mata kyau sosai,tasanya Dan madaidaicin hijabinta ,Wanda yakara fitomata da kyawun fuskarta.
Sannu da zuwa yaya Ahmad,tafada dai dai lokacin da take Neman wurin zama nesa dashi kadan.
Yadago kai yakalleta,sannan yace:bayan kingama shanyaniko?har nayi niyyar intashi intafi,donnayi zaton ko bakida lokacin da zaki futo inganki.
Tace tuba nake yaya Ahmed, Nina isa kazo ince bazan fitoba,kayi hakuri don Allah bansan sauri kakeba,amma kuma yaya Ahmad konakai dare ban fitoba,aibaka iya tafiya bakaganniba,kumafa tsayawa nayi inshirya kawai,amma shine harka gaji da zaman jirana.
Yace: yo shirimme kikayi?abinda kwalliyarma ba kyau tayi makiba.
Tayi dariya tare da fadin yabawa kayi kenan,lallai yau na tabbatar kwalliya ta taburge yaya na.
Yace:haka dai kikace.
Tace :kaima haka kagani,tare dasa gefen hijabinta tadan rufe fuskarta.
Yace:Hafsat dama nazone insanar dake cewa rana itayau zantafi kano,kuma idannaje akalla zanyi sati acan,shiyasa nace bari insanar dake tun yanzun,don kifara shirin yin kewata.
Cikin shagwaba tace yaya Ahmad yanzun nan harsai nayi sati ban gankaba?Ashe kana shirin ka azabtar da zukata biyu kenan,yaya Ahmad bazan iya tsawon sati gida bangankaba,don Allah kasaukaka tafiyar,yaya Ahmad karage kwanakin.
Humff!!yayi ajiyar numfashi ,sannan yace:nikaina saida na jinjina tafiyarnan,domin nasan haka saita faru,Hafsat nikaina inatunanin yadda zanje wani wuri inyi sati guda ba tare danazo nayi tozali da wannan kyakykyawar fuskar takiba,no kaina nakan tambayi kaina shin sai wane irin sone muke yima junanmu?Wanda dai dai da kwana daya bama iya hakurin bamuga junaba.
Hafsat inasonki,wani lokacin har nakema kaina azarbabin cewa na kagara inga na mallakeki a matsayin matata,awannan rana zan tasaki inta kallonki,karkicefa har saina gaji,a'a bazan taba gajiya da kallonkiba,bazaki taba gundirataba.
Yadaga hannayensa sama tare da fadin.
Ya Allah ka nuna Mani ranar da Hafsat zata zama matata.
Acikin zuciyarta ta amsa da Ameen,sannan afili tace:mezakaje yowa kano?
Yace:Abbane ya shaidamin cewa diyar kaninsa.
MARIGAYI ALHAJI KABIR take dawowa daga Englar karatu ,to shine waini zanje in tarbeta,daga Air port.
Cikin muryar kuka tace amma shine harsai kayi sati.
Yace:banda wannan akwai wani aiki dazan yimasa akamfaninsa,to zai daukeni tsawon kwana biyar.
Tace:nigaskiya saidai katafi Dani "
Yace:kiyi hakuri Hafsat akwai sauran lokacine,idan lokacin yayi ko abayana kikace inzagaye garin Kaduna to inhar zan iya zanyi,to amma yanzun mudan kara hakuri kadan,kokinaso insanar da Abba cewa kince adaura mana Aure dake kafin intafi,sai intafi dake?
Tace:Ahh!!kajika saboda nice sarkin marasa kunya?
Nina yanzumma zanyi Aureba ,sai nayi digri.
Yayi dariya tare da fadin kinjiki ahakadin,sukasa dariya baki daya.
Haka sukaita firarsu cike da kaunar juna,hadi da soyayyarsu maiban sha'awa.
ALHAJI SALISU mahaifin Hafsat tare da matarsa HAJIYA FATIMA,suna zaune afalonsu.
Hajiya Fatima tace:Al-amarin yarannan Alhaji,abin gwanin babsha'awa,sunason junansu sosai,karkaga yadda Ahmad yake diki akan Hafsat ,itama da ance gashi yazo karkaga yadda jikinta ke rawa,kaih!mudai wannan Al amari Allah ya tabbatar mama dashi,kagansu da wasa da dariya,komai sunayinsa gwanin bansha'awa.
Alhaji salisu yace:shi Allah haka yake hada siyayyar 'yan Adam,gashi dai mutane dadama suna gudun Auren Zuminci ,amma mudai yarammu Allah ya had a kawunansu,kafin mahaifitar Ahmad din tadawo daga kasar saudiyya ai yaran sungama dai saita Kansu ,wannan Al amari aiba Wanda zaifini jindadinsa.
ALHAJI SANI DA ALHAJI SALISU DA MAHIFIYAR AHMAD HAJIYA AISHA,mahaifisu daya ,indashi Alhaji Sani da Alhaji SALISU mahaifiyar su daya,ita kuma HAJIYA Aisha ita kadai mahaifiyar ta ta Haifa,kunga. 'Yan uba Duke kenan.
HAJIYA Aisha tare da mujin ta ALHAJI SULAIMAN da daya kawai suka mallaka wato Ahmad ,sunaji dashi sosai,dama kuma ga arzikin.
Shi kuwa yayanta Alhaji SALISU yanada 'ya'ya dadama,cikinsu harda Hafsat ,Wanda a yanzun yakeda shekara goma sha Takwas da haihuwa,lokacin da take zama budurwa,sai Allah yahada soyayyarta da Dan uwanta Ahmad,Wanda yazamana Abokin wasantane (kamar yadda mu hausawa mukecewa)
Domin kuwa da Babantaba da innarsa mahaifinsu daya,saidai uwace kowa data shi.
Alhaji SALISU da kaninsa Alhaji Sani sunyi farinciki da wannan Al amari sosai,domin koba komai zai kara donkon zuminci atsakaninsu,wannan kenan.
Ranar Alhamis kuwa dasafe tadauki motarsa,yatafi kano,acikin zuciyarsa cike yake da kewar abin kaunarsa Hafsat.
Yasauka gidan,su biyu ya Tatar kamar yadda ya tsammata ,daga kubura sai khadija,sai masu acikin gidan da suketa kaida komowa,sunayimasu hidima,
Cikin farin ciki suka tarbi yayan nasu,suka kaishi masauki,tare da kaimai da dadan abinci kala-kala,saida yagamaci sannan suka shigo,India yake domin susake gaisawa.
Yace :aah!kanbaina!yakaratu?
Sukace lafiya lau yaya Ahmad,yaya wajen acikin ka?
Yace :lafiya lau,Abba yace in gaisheku,kuma yace:idan yayarku suhailat tadawo,inkoma daku,don yace yanson ganinku.
Kubura tata hannayenta tare fadin Allah sarki!Abbanmu!!inaso Nina inganshi.
Khadija tace amma dai ba dadewa zamuyibako?Donni bànso inje wani gari indade.
Ahmad yace aidukkece matsalar dama,bakison mutane.
Tace yaya Ahmad bahaka bane karatuna.
Yace to Al huda huda!karatun guduwa zayyi?komai menenedai tunda Abba yacekije saikin je,inba haka ba kuma injaki da karfina inkaiki.
Sukasa dariya baki daya.
Tace saikace WATA 'yar yarinya,aibaka iya jana,.
Yace Atashi tafiyar kice baki zuwa kigani,da karfi zansanyaki cikin mota,alokacin zaki gane ke yarinyace,suka shekararki nawa?
Yayi saurin cewa goma sha shidda!
Yace kaji barauniyar shekaru!yaushe kikakai haka?
Tace Allah yaya Ahmad bakai,ya kake maidani bayane?
Yace:don kinga kinyi jikin girma.
Kubura dai dariya takeyumasu,harsai tagaji tace:yaya Ahmad idan kabiyema autannantamu,nanzaka shiririce,ko hutawa,bazaka samu kayi ba,
Gashi kuma gobe Aunty suhailat ke dawowa, yakamata kadan huta kasha hanya,sannan ta kamo hannun khadija suka fita,shikuma yasamu Dakar kwantawa bisa luntsumemen gadon dayake cikin dakin.
ALHAJI SULAIMAN mahaifin Ahmad,shima su biyune iyayensu suka Haifa,daga shi sai ALHAJI KABIR.
Shi Alhaji Kabir 'ya'yansa mata uku,da matarsa HAJIYA RAKIYA,wadanda Allah yayi masu rasuwa asanadin hadarin jirgin sama,Wanda sukabar 'ya'yansu,BABBAR itace SUHAILAT wadda a yanzun ta kammala karatun ta,kuma take shirin dawowa Nigeria daga kasar Engiler.
Maibimata itace kubura,wadda itama yayi karatun sosai,amma yanzun harkar kasuwancin mahaifinsu,yadawo hannunta,sannan sai 'har autarsu khadija,wadda a yanzun take shirin kammala makarantar secondary.
Su biyu Duke rayuwa acikin gidansu,sai ma aikatansu da suke tare dasu,maganar dukiya kam!!akwaita,dama iyayensu sun mutu sun barmasu ita,kuma kubura nakara tafiyar da harkar dukiyar cikin kwarewa da kuma ilimi.
Shekara suhailat biyar a kasar Engiler ,run bayabayan asuwar iyayensu,bata kara dawowa Nageriyaba,saida yanzun data kammala karatun ta,takeso tadawo gida dun!din!!dunn!!!
Yayan Babansu Alhaji SULAIMAN,mahaifin Ahmad,yasyaso yaran sudawo wurinsa,amma suka nuna sudai subfiso suzauna inda suka saba,dama ga kubura na harkar kasuwanci,khadija kuma tana karatunta.
Was he gari kuwa tunda safe aketa aikaxe-aikace,na hidimar tarbar Aunty suhailat,gidan yadau kanshin gurke-girke da soye soye,kowa magani cikin murna yau sunada babbar bakuwa!!!
Kubura da khadija sukayi wanka sukasa kaga masu kyau da tsada,
Haka shima Ahmad kana nan kayane yasanya. Sunyi masa kyau sosai,sannan suka Shiga mota,Ahmad yaja suka nufi aanyar cikin jirgin malam Aminu kano.
Basu jima sosai ba jirgin ya sauna gaba daya duk sun kosa suganta.
Cikin shigar Mayan turawane ajikinta,gawata hular gashi data Sanya akanta,kayan jikinta sun kamata sosai.
Ahmad baiji dadiba dayaga 'har uwarsa acikin irin wannan yana yin,tamkar ba 'har musulmibarigarnan tata hatta cibiyarta a wane,ga wani da mammen Wanda dayake ajikinta.
Cikin murna tabi. 'Yan uwanta tana rungumarsu,tanayimasu kiss,suma murna Duke sosai da ganinta cikin kishin lafiya.

Ahmad bai ankaraba sai jinta yayi tafado cikin jikinsa,ta kankamesa tana fadin ,oyoyo!ya Ahmad,ta kaimai sun bata akumatunsa,shikau yana ta kokarin tureta,amma bata fahimcima hakanba,murnar ganin. 'Yan uwanta kawai take.
Tace:YA Ahmad ki irin. 'Har ziyararnan?baka taba zuwa inda nakeba.
Cikin 'har dariyarsa dabatakai cikiba,domin ranshi baisoba,ganin kanwarsa da irin wannan shigar,yace:
Tuba name Aunty suhailat kiyi hakuri,yakara rungumarsa cike dajin dadin ganin Dan uwanta.
Shikuma yace kushuga mota muwuce gida.
Sannan suka shigo mortar Ahmad Yakuma tukawa suka tafo gida...................🖊️
Fatima Dahiru Funtuwa Binta,don Allah idan baka shirya siye ba kada kadauki Number ta kabari saika shirya
Suna isa gida Ahmad yawuce dakinsa cikin sauri,don yagaji da ganin suhailat airin wannan yana yin.
Aranar gidan ya kasance cikin annshuwa da farin ciki,bayan anci ansha,sannan suhailat tashiga yo wanka,tayi kwalliya,sai dai haryanzun wasu kayan turawanne takarayin kwalliya dasu.
Suna cikin falon gidan sunata fira irin tayaushe gamo,an hadu da 'yan'uwa.
Suhailat tace wai ina YA Ahmad banganshiba?duk gamu munfito falo anata fira,inayashige?
Khadija tace yanadaki nakaimai abincine,kila baigama Ciba.
Suhailat tamike tsaye tanufi inda dakin Ahmad din yake.
Zaune tatarar dashi yanata shafa wayarsa,ga Abincin da akakawomai nan ko tabashi bayyiba.
Tana isa kusa dashi tasa hannu takarbi wayar,tace bakaci abincinba.
Yabata ransa yace aizanci.
Takallai sosai tace YA Ahmad meke faruwa?
Yayi banza daita
Takumacewa naga bakaci abincinba lafiya daiko?
Yace lafiya lau,ya amsa mata adakile.
Tace fushi kakeyi ya Ahmad?
Yadaure dai yace kekika batamin rai.
Saita zauna daf dashi,tace menayi kuma daga dawowa ta?
Yadago ido yakalleta sosai gata zaune daf dashi,yace duka shekararki nawa akasar turawan?dahar zaki juyar da dabi'arki irintasu,karki manta kefa musulmace 'yar bahaushe,amma kidubi irin shigar datake jikinki,sannan kuma aikinsa niba muharraminki bane ,domme zaki rika kai hannunki ajikina?tashi kibani wuri.
Tabishi dawani irin kallo,sannan tace to ya Ahmad kacemani ba 'yar uwarkabace,shikenan daga dawowa ta saika fara fushi dani,inwani abunnayimaka aibatahaka zaka bullominba,saidai ingaba daya nidince bakason gani,kokuma katsaneni.
Yace batsanarki nayiba,amma natsani irin wannan mummunar dabu'ar dakikaxo da ita,kidubi kanki kigani mana,haka kikazo kika tarar DA sauran 'yanuwanki?meyasa kika manta datsarin Addininkine?nida kike gani ba muharraminki bane,ballantana inkin hada jikinki danawa kikeganin kamar ba laifi.
Tace ya Ahmad daga dawowa ta zakatirkeni dairin wadannan maganganu?basaikanunamin cewar banida wata daraja awurinkaba,nasani,shiyasa kafara fushi dani don injanye jikina daga gareka,bakomai,tamike cikin hanzari zata fita.
Yakira sunan ta dakarfi SUHAILAT!
Tajiyo takalleshi.
Yace banaso kidauki magana ta dawata manufa,kawai dai gyarawa nakeso kiyi,kisani kinbaro waccen kasar,kindawo cikin 'yan uwanki hausawa,toyakamata ace shigarkima tacanza.
Tafita tana fadin nidai takuramin kawai zakayi ya Ahmad.
Sannan takoma falon da 'yan uwanta suke sukaci gaba da firarsu.
Anan kubura keshaidama Aunty suhailat cewa tare zasu tafi da yaya Ahmad Kaduna,saboda Abba yace...


Read / Download BABBAR HUJJA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
2 Comments On BABBAR HUJJA
avatar
abasu-kala

2 months ago

Reply

Yes

avatar
ummu-swabir

2 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album